x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 10 - KIBIYAR AJALI

  • 27001 words
  • 30000 words
  • Out of 49194 words

Category: Love Stories

Views 519

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

48
mahaifiyarmu, ina kuma son na sanar da kai cewa
mahaifiyarmu ba kanta xaya ba, tun lokacin da ta xauki
ranta ta qwallafa akan sarqannan ta gadonmu, haka
nan sai duk al'amuranta suka canza, son zuciya da
sharrin shaixan suka ruxeta ta fara tunanin mallakar
sarqar ko ta halin qaqa. Fadil da farko na xauka wasa
take min, daga baya sai naga abin ya fi qarfin wasa, ka
yafe ni Fadil ba don ni ba, wallahi duk abin da na yi ma
a da takura min aka yi, saboda mahaifiyarmu ta ce idan
ban yaudare ka ba sai ta harbe ni, ni kuma da na ji haka
sai tsoro ya kama ni saboda ina gudun ta harban
matuqar ban yi abin da ta ce ba to tana iya halaka ni,
domin kuwa ba kanta xaya ba. Tun farko da na fahimci
cewa qwaqwalwarta ta tavu naso naga na sanar da
hukuma, to amma sai na tuna da cewa muddin na sanar
dasu cewa mahaifiyata tana barazanar kashe ni, to
gidan mahaukata za su sa ta, kasan kuma yadda gidan
mahaukata yake ba a ba su kyakkyawan kulawar da ya
kamata saboda an ga yawancinsu duk talakawa ne da
mara sa gata kuma koda ana ba su kyakkyawar kulawar
ma ba zan so ace mahaifiyata tana cikin gidan
mahaukata ba, bayan haka kuma Fadil za ka so ka ji
inda muka sami bindiga har muke wasa da ita akan
rayuwarka, bindigogin dai su uku ne, kuma na baban
mu ne tun yana da rai mahaifiyarmu ta sace su, an
neme su har an gaji. Bani na sake ganin su ba sai bayan
da mahaifiyarmu ta fara shirin tsunduma ka a cikin
bala'in nan, sannan ta fito da su, ta xauki xaya ta
baiwa. Salman xaya ni kuma ta bani xaya, amma ni ban
tava amfani da tawa ba, kada na cikaka da surutu ni dai
ina son kasan cewa ni masoyiyarka ce, kuma duk abin
da kaga na yi ma har dukan da Salman ya yi ma a cikin
dajin nan na Kaduna, na bar shi ya dake ka ne don
babu yadda zan yi da shi ne domin ina nuna alamar
raina ya sosu. Salman zai faxawa mahaifiyarmu domin
shi ta xauko shi haya ne domin yana kula da duk abin
da nake aiwatarwa a kanka, saboda ta lura da cewa tun
lokacin da ta nuna min kai a matsayin saurayin da zata
tsunduma cikin bala'i don ganin ta cimma burinta, ta
gane cewa na kamu da ciwon sonka.
Kamar yadda na ce a baya ina son na sanar da kai
wasu abubuwa masu haxari guda uku dake tattare da
gidan Kanal A. Mukhtar, na farko dai ina son kayi
hankali idan ka shiga saboda akwai Karnuka masu cin
naman mutane, na biyu kuma gidan yana xauke da
qofofin shiga har guda goma sha biyu, kowacce qofa
akwai qosassun Karnuka guda uku, da kuma Sojoji
masu jajayen idanuwa guda huxu, idan ka yi jimla, zaka
sami Karnuka talatin da shida kenan, Sojoji kuma
arba'in da takwas, ban da kuma na qofar farko wacce
ke xauke da Sojoji goma sha biyu, kowannensu kuma
bai xauki ran mutum a kan komai ba.
Sai kuma abu na uku wanda shima yana da
muhimmancin gaske sarqar da mahaifiyarmu take son
ka xauko mata tana cikin wani gilas ne mai xauke da
wata irin fitilar lantarki mai tsananin haske, babu kuma
wanda ya isa ya je kusa da gilas xin sai inuwarsa ta faxa
kan gilas xin, inuwarka kuma tana faxawa, wata na'ura
wacce ita da inuwa take aiki zata xau qara. Don haka
nake shawartarka a matsayina na mai qaunar ka, kar ka
sake ka kusanci gilas xin da sarqar take har sai ka
kashe duk fitilun xakin. Xakin kuma zaka same shi a
qarshen qofar gidan ta goma sha biyu, daga hannunka
na hagun idan kuma zaka shiga gidan kar ka sake ka
shiga ta qofa, ko da ya ke ba sai na faxa ma ba, nasan

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

49
kana da qwaqwalwar da zata iya fitar da kai, Allah ya
taimake ka masoyina.
Daga Masoyiyarka Badura,
mai neman gafara a gare ka.

A can wani vanmgare na cikin gidan qararrawar
agogo ta fara kuka, wannan shi ne yake nuna alamar
qarfe goma sha biyu ta yi. Na linke takardar na mayar
aljihuna na nufi gado na kwanta, amma na kasa barci,
na sake zaro takardar na ci gaba da karantawa, kafin
gari ya waye na karanta takardar ya kai sau sittin.










9
a duba agogona sai na ga qarfe goma sha biyu
saura minti xaya, nan da nan na tashi tsaye na
saqala jakar da Yayana ya ce kar na rabu da ita,
sannan na fito daga xakin na rufe gidan na jefa xan
mukullin a aljihuna, sannan na kama hanya, ina
rarravewa a cikin duhu kamar varawo.
Tafiya ta tafi kenan ko na dawo ko kuwa Sojoji su
harbe ni, babu mamaki kuma na zama abincin
Karnuka, abin ya zame min gaba siyaki baya damisa
idan na dawo ban yi nasara ba. Hajiya Binta ta yi min
alqawarin aikawa dani barzahu, idan ma nayi nasara
a biyu nake, ko na bar qasar ko kuma 'yan sanda su
kama ni qarshe kuma a xora min laifin kisan Zainab a
rataye ni, idan kuma duk wannan ma bata faru ba,
idan na yi kuskure wajen shiga gidan Kanal Muktar
to nan ma dai na lalace, wannan shi ne zavin shaixan
ko ina halaka.
Bayan tafiyar minti goma sha biyar ina bin bango
kamar qadangare, na qaraso (Sultan Road), qirjina
yana dakan uku-uku, titin (Sultan) a haskake take
kamar rana, akwai qwayayen wutar lantarki sama da
tamanin a nan, tun daga nesa na toge ina tunanin ta
idan zan lallava na qarasa gidan Kanal, ba tare da ana
ganina ba. Amma hakan ya ci tura, saboda babu
damar nayi taku biyar cikin titin Sultan, sai Sojojin
sun hango ni. Na duba vangaren kudu na titin, ga
mamakina sai na hango wani kangon gida wanda a
tsammanina babu kowa a cikinsa, kuma tsakaninsa da
gidan Kanal Muktar gida xaya ne, wanda shi naga
alamar akwai mutane, na sake duban gidan dake
tsakanin kangon nan da gidan Kanal, sai naga biyu
daga cikin tagogin xakin dake fuskantar iya gajeriya
katana gidan a buxe suke, daga inda nake tsaye ina iya
sauraron lallausan sautin turawan dake tashi a gidan,
hakan shi ya sani tunanin in har zan iya shiga gidan ta
baya to da wahala masu gadin su ji shigata, saboda
kixan dake tashi bai iya barinsu su ji komai, bayan
haka ma kuma ai dare yayi babu mamaki ma mutum
xaya ne kawai ya rage bai yi bacci ba a gidan kuma
N

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

50
koma wane ne ina tsammanin saurayi ne, dan haka ba
tare da na bar zuciyata ta sake min tunani ba, sai na
nufi katangar kangon nan na xare kamar varawo
kafin na dira ciki sai da na hanga qofar gidan Kanal
Muktar, wacce ke cike da 'yan mazan jiya.
Abin mamaki qofar gidan Kanal Muktar kamar
rana, sojoji sun rarrabu har kashi uku, kashin farko
mutum huxu ne suna tsaye suna muzurai kowannensu
riqe da zungureriyar bindiga a hannu suna jiran koda
quda ne su harbe. Kashi na biyu kuma mutum uku ne
suna hira, biyu daga cikinsu suna riqe da karan taba a
bakinsu, xayan kuam yana wasa da hancin bindigarsa,
kashi na uku kuma mutum huxu ne suna wasa da
karta. Daga can gefe su kuma wani qaton soja ne mai
naxaxxen gashin baki, yana zuqar sigari, qaton
takalminsa na qafar dama yana barazanar fashewa,
ga dukkan alamu dashi sojan yaje yaqin duniya na
xaya. Sojan ya kai kimanin shekaru saba'in ina kuma
tsammanin shi ne mai faxa aji a gurin, na tabbatar da
hakan a daidai lokacin da wani dogon soja ya faxo
wajen kamar daga sama. Sojan na sanye da hular
malafa mai kamar gare-gare, sojan ya qame a gaban
qaton sojan nan.
"Morning Sir." (Barka da asuba) ya ce da shi cikin
harshen turanci, qaton sojan ya xaga kansa sannan ya
ci gaba da zuqar sigarinsa. Shi kuma xaya sojan sai ya
zauna wajen masu wasa da katin, a daidai lokacin ne
na dirga cikin kangon gidan nan.
Akan wani abu lallausa na dira takalmina ya bada
wani qara cus. Na yi tsalle gefe guda cikin razana,
sannan na ji wani irin wari ya daki hancina, na yi
sauri na zaro 'yar qaramar fitila (touch light) cucila
na haska kan abin da na taka cikin kaxuwa sai naga
mushen wani qaton kare mai xauke da farin qyalle a
wuyansa, abin da zuciyata ta raya min shi ne, wannan
xaya daga cikin karnukan Kanal Mukhtar ne ya mutu
aka jefo shi nan. Na godewa Allah da yasa ba akan
mai rai na dira ba. Na yiwa karen kallo xaya sannan
na yi gaba da sauri ina haska cucilar, kangon an fara
gina shi amma ginin bai yi nisa ba, hakan ne ma ya sa
ciyawa ta fara yiwa fargajiyar tsohon kangon
qawanya.
Gidan ya yi shiru kamar maqabarta baka jin
komai, sai sautin bugun zuciyata, na ci gaba da tafiya
ina sanxa, na nufi katangar gidan nan da yake
maqwabtaka da kangon, ina tafiya a hankali, tare
kuma da zagaye duk inda wata duhuwar ciyawa take,
a duk lokacin da na xan taka sahuna da qarfi a kan
ciyawar, sai veraye da javaye su fita da gudu, su nufi
ramukansu, wasun su kuma cikin qarqashin wani
tarin katako suke shigewa. Katakon ta ri guda ne
kuma a zube yake a gindin katangar gidan wacce ita
nake qoqarin kaiwa domin na samu da shiga xaya
gidan na kusa da shi.
Koda na matsa kusa da katakon da niyyar na taka
shi na kama katangar sai na ji motsin wani abu a
saman katangar tsohon ginin nan. Motsin ya so ya
razana ni, amma da na tuna da cewa gidan fa a cike
yake da veraye sai na dake, da farko har na ja da baya
na maqale a jikin katangar, amma da tunanin veraye
ya faxo min sai zuciyata ta ce da ni babu komai kai dai
ka yi hankali kar shegen tsoronka ya sa har ka dirga
xaya gidan da qarfi su jika. Don haka sai kawai na
nufi katakon da sauri.
Takun farko na yi shi ne da qafata ta dama, kafin
kuma na xago qafata ta hagun sai na ji wani abu ya

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

51
faxo akan qafata ta damar, abin lallausa ne kuma ina
tsammanin yana da tsayin gaske, na gane hakan ne ta
hanyar nannaxe qafata da abin ya fara yi, cikin xan
lokaci qanqani sai na ji kaina ya yi min nauyi xim,
tsoro da fargaba suka hana ni motsi, abu na farko da
ya xarsu cikin zuciyata shi ne, maciji ne ya nannaxe ni.
Na yi qarfin hali na zaro fitilar cocilata daga aljihu na
haska kan qafata domin naga abin da ke faruwa.
Abin da hasken fitilar ya xauko min ya sa
numfashina xaukewa, ya kuma sa gumi ya fara zuba
daga fuskatam zuwa wuyana kamar ruwa, a lokaci
guda kuma ya sani tunanin mutuwa. "Innalillahi
wa'inna ilaihi raji'un." Na ce cikin zuciyata. Wani
dogon maciji ne wanda nake tsammanin ya yi ya ni a
tsaye. Idan har bai fi ni tsawo ba to ni kuwa ba zan fi
shi ba, baqi ne kakkaura. Wani abu mai kama da xan
kunne dake maqale a kunnensa na hagu, shi ya qara
fito da siffar sa ta masifa da kuma razanarwa. Na
lumshe idanuna ina jira ya sare ni na huta, daga inda
nake tsaye ina jin sautin kixan bandirin dake tashi a
xaya gidan dake maqwabtaka da ni da kuma maciji.

**
Ban san iya tsawon lokacin da na yi a sume ba, ni
dai na farka na ji wani abu yana gugar qafata, na
haska cocilata cikin tsoro da fargaba, ni da a tunanina
rayuwa ta zo min qarshe, amma yanzu sai na ji kamar
macijin ya bar qafata. Na tabbatar da hakan a lokacin
da hasken fitilar ya xauko min qaton macijin nan a
kwance gefe guda, haqiqa idan akwai abin da ya fi
mutuwa, to shi wannan macijin ya yi, domin kallo
xaya na yi masa na tabbata ba shi da rai, an kuma
fara yi masa rami a ciki. Na juya hasken fitilar wajen
qafata don ganin abin dake lasar qafata, anan ne to na
gane abin da ya cinye macijin nan, hasken fitilar ya
xauko min idon wata qatuwar java mai dogon baki
kamar asuwaki, tana lasar qafata, ga tsammaninta
nima ko maciji ne. Na yi zunbur na miqe tsaye sannan
cikin zafin nama na nufi katanga da gudu, ina zuwa
na yi tsalle na kama katangar ta hanyar taka tarin
katakon nan dake yashe a gindin katangar. Veraye,
javaye da kuma sauran ire-iren qwarin da suka saba
zama cikin tsohon ginin, wasun su kuma suka nufi
cikin ciyayin da suka yiwa gidan qawanya. Koda na
lura sai na ga java ta fi yawa fiye da vera a gidan.

*
Na yi kimanin mintuna biyar ina zagaya cikin
gidan, kamar varawo, ina tafiya da sanxa kamar
gajimare. Kamar yadda na yi tsammani sautin kixan
dake tashi shi ya bani damar tsirga gidan ba tare da
wani ya jini ba. Ginin gidan ginin gidajen gwamnati
ne, kamar dai yadda sauran gidajen suke a wannan
titin. An gina shi ne a tsakiyar farfajiyar gidan,
wannan shi ya bani damar zagawa ko'ina cikin gidan.
Xaya daga cikin abin da na lura shi ne, katangar
gidan da ta rava gidan Kanal Muktar da gidan, tana
da tsayin gaske, akan katangar kuma qusoshi ne da
miyagun kwalabe masu barazana ga hannun duk
wanda ya yi qoqarin kamawa. Abu na biyu kuma da
na lura, na kuma gargaxi kaina shi ne gidan da nake
ciki akwai maigadi, na gane hakan ne saboda ganin
wata 'yar rumfa a qofar gidan, a cikin rumfar na lura
da wani kasko na qasa cike da garwashin wuta
jajawur. Wannan alama ce da ke nuna cewa maigadin

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

52
tsoho ne, don haka cikin gadara sai na ci gaba da
zagayawa ba tare da fargabar komai ba.
Har yanzu sauti na tashi a cikin xakin, sai dai
kuma wannan lokacin an canja kaset xin, daga na
bandiri zuwa na Turawa. Zan so ace na kowane ne
cikin xakin nan. Tuni zuciyata ta fara zargin wanda ke
xakin shin me ya hana shi barci? Wannan tambayar
ita ta sani na nufi tagar dake vangaren gabas da
gidan, wacce kuma ita ce take fuskantar katangar
gidan Kanal Muktar. Na yi sa a na sami tagar a buxe
take, ban jira wani abu ba sai na fara buxe ta a
hankali, har dai na sami 'yar qofar da zan leqa, to
sannan ne na sake ganin, tana zaune akan kujera ta yi
tagumi a kusa da ita kuma xan tsohon nan ne mai
fuska kamar matsattsen lemon tsami, yana gyangyaxi,
ban gama mamakin abin da na gani ba sai na ji wani
na tava bayana, na juya cikin razana, sannan muka yi
ido huxu da 'Salman' yana murmushi.
"Daman na san tanan zaka biyo." Ya ce da ni.







10
ada ka yi mamaki da ganinmu a nan Fadil."
Salman ya ce da ni. "Wannan alama ce da
take qara tabbatar da maganar uwargidata, kuma
shugabata Hajiya Binta, inda take cewa, duk inda
kake ina biye da kai, kuma wannan gidan ma da ka
ganmu a ciki, ni na bada shawara a kama shi haya,
wata xaya kenan yanzu tun lokacin da Hajiya Binta ta
xauko hayata."
Na yi shiru cike da mamaki, lokaci guda kuma ina
kallon tagar xakin da su Hajiya Binta suke.
"Kar wannan ta dame ka." Salman ya ce dani,
"sun riga sun san kana cikin gidan, domin tunda ka
shigo titin nan nake biye da kai, duk kuma zagaye-
zagayen da kake yi ina kan soron xakin nan ina
kallonka, don haka nake qara gargaxinka da cewa ka
yi qoqari ka ci nasara idan kuma har ka kuskura ka
faxi, to ka lissafa kanka cikin matattu.
Bi ta can ka tsallaka. Da fatan zaka ci nasara."
Kafin na buxa bakina, Salman ya zagaya ya shige
xakin. Koda na lura da inda Salman ya nuna sai naga
wani dogon tsani jingine.

**
"K

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

53
Abu
End Ads