x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 12 - KIBIYAR AJALI

  • 33001 words
  • 36000 words
  • Out of 49194 words

Category: Love Stories

Views 524

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ta hanyar haxa
soyayyata da ta 'yar'uwata Badura. Na ji na yarda
tunda in dan ma na yi miki bayani ba za ki gani ba. Na
ce da ita. "Sai dai kuma kina ganin duk wannan ya kai
ace kin kore ni zuwa ga halakata?" Na tambaye ta.
Maganar ta yi tasiri a kanta, saboda ganin irin yadda
ta yi kasaqe tana kallona, kuma tana wasi-wasi kafin
ta sake magana, sai muka ji ana qwanqwasa qofa. Ta
kalle ni, na kalle ta sannan Amina ta sake kallona

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

58
cikin takaici, gumi ya rufe ni saboda na san Amina a
shirye take ta damqa ni a hannun Sojojin.
Hawaye ya fara kwaranyo wa kan kyakkyawar
fuskar Amina, a lokacin da su kuma 'yan daxi
bindigar dake waje suka ci gaba da buga qofar a
hankali, duk da yake kuwa Sojoji ne. Wannan ba abin
mamaki ba ne idan aka yi la'akari da kasancewar
Amina 'yar gidan Kanal Muktar dole ne ita ma a bata
girma iya nata. Allah ya isa soyayya, wallahi soyayya
kin gama da ni, kin kuma cuce ni tunda kika fi qarfin
zuciyata har kika sa zan ceci ran maqiyin mahaifiyata.
Amina ta ci gaba da kuka, bayan wasu 'yan lokuta sai
ta tura ni cikin xaya daga cikin xakunan da ke
fuskantar xakin, ban jira wani qarin bayani ba sai
kawai na faxa xakin na rufe na jingina kunne na a
jikin qofar xakin ina sauraron abin ke faruwa a xakin.
"Ranki ya daxe." Wani kurtun Soja wanda
cikakkiyar hausa bata ishe shi ba ya ce da Amina.
"Sannunka dai." Ta amsa sama-sama, har yanzu
ina iya sauraren haushin Karnukan da ke maraba da
ni gasasshe a waje.
"Kin ga motsin wani abu ko kamar gudun mutum
anan wajen." Sojojin suka tambaye ta.
"A'a wallahi ban ji komai ba." Amina ta amsa. Na
yi mamakin irin yadda muryarta ke bada amsa ba
tare da ta yi rawa ba.s
"To shi ke nan. To daman mun xauka ko kin ji
wani abu ne, sai da safe." Sojojin suka ce da ita.
"Lafiya dai.?" Ta tambaya.
"A'a babu komai." Suka ce da ita. Sannan na ji an
turo qofar an rufe.
Bayan 'yan daqiqu sai na buxe qofar na fito.
Amina na zaune a kan xaya daga cikin kujerun da ke
xakin, sai yanzu ne na lura da cewa ashe ma wai akwai
kujeru a cikin falon, bata yi min magana ba nima
kuma ban yi mata ba, saboda raina nima ya yi
matuqar vaci ganin irin yadda Amina ta kasa fahimta
ta, na matsa kusa da tagar da ke xakin Amina, sai
naga wani tsani a tsaye a jikin katangar gidan dake
fuskantar xakin. Ga dukkan alamu sabon fenti aka yi
wa bangon, su kuma ma'aikatan suka bar tsanin
jingine, na gane haka ne ta hanyar ganin gwangwanin
fenti a maqale a jikin tsanin.
NA sami hanyar tsira na ce cikin zuciyata, ba tare
da na sake duban Amina, sai kawai na buxe xakin, ina
jin lokacin da Amina ta yi firgigit ta tashi tsaye, amma
vacin rai bai sa na juyo ba sai kawai na nufi tsanin da
gudu ina jin lokacin da wani qaton kare ya kawo wa
qafata sura, amma nasan na yi masa fintinkau, daqiqu
biyu sai gani a katangar gidan daga varin gabas,
sannan ne kuma na ji wani raxaxi ya bugi hannuna
kamar an soke ni da kibiya.
Qarar bindigar da ya biyo baya shi ya tabbatar
min da cewa harbina aka yi, qarfin harsashin bindigar
shi ya yi jifa da ni qasan katangar na faxa a cikin wani
qaton kwalabati. Da qyar nake numfashi, juwa na
xaukata, a haka na lallava na ja ciki na shige cikin
bututun kwatar dake fuskantar qaton lambatun
kwatar. Raxaxin da hannuna ke yi bai hana ni jin
kukan Amina ba lokacin da aka harbe ni.
"Fadil!!" Ta kira sunana cikin qaraji.

**
"FADIL!" Na ji wata siririyar murya ta yi kirana
duk da yake raxaxin harbin da aka yi min a hannuna
na damuna, sai da muryar tasa gabana ya faxi,

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

59
muryar da ba zan tava mantawa da ita ba ce, muryar
yarinyar da har yanzu zuciyata ta kasa tantancewa
shin masoyiyata ce ko kuwa a bar qina ce.?
"Fadil ni ce Badura. Kada ka ji tsoro, na zo ne na
ceci ranka, saboda qaunar da nake yi ma." Badura ta
ce da ni a daidai lokacin da ta sunkuyo ta kama
hannuna tana niyyar fitar da ni daga cikin qaton
lambatun kwatar da nake ciki.
"Badura." Na kira sunanta. "Idan kina
tsammanin zan sake yarda dake to kin zolayi kanki."
"Idan kana tsammanin ni ba masoyiyarka ba ce
Fadil, to haqiqa ka yi kuskure, son ka ma yanzu na
fara." Badura ta amsa min.
Na sami kaina a kafaxar Badura tana jana, ina
tangaxi saboda jinin da ya zuba a jikina yana da
matuqar yawa. Idona a rufe Badura ke jana.
"Zan saka a cikin but xin motata." Badura ta ce
dani, "saboda duk 'yan sandan garin nan an basu
kamanninka a shirye kuma suke su kama ka, a cikinsu
har da qwararrun 'yan sandan ciki daga Durba Otal
Kaduna." Ban samu damar ce mata komai ba, saboda
duk jikina ciwo yake, a haka na lallava da taimakon
Badura na faxa cikin but xin motarta ta mayar ta rufe
da ni, ba ni da wani zavi sai abin da Badura ta yi da ni
a halin yanzu duk da yake kuwa har yanzu zuciyata
bata amince da duk abin da ta ce ba. A haka na
kwanta cikin but xin motar kamar matacce. Amsa
kuwwar muryar Amina shi yake ta kai-komo cikin
qwaqwalwata.
"Fadil! Fadil!! Fadil!!!"
Ban san iya lokacin da na yi kwance ba, qafata ta
qage saboda rashin isasshen sukuni a cikin but xin
motar, ba ni kuma da tabbacin shin bacci nayi ko
kuwa suma na yi, ni dai kawai na farka na ji Badura
tana ta tafka musu da waxansu waxanda daga qarshe
na gane 'yan sanda ne.
"Muna son muga bayan motarki." Xaya daga
cikin 'yan sandan ya ce da ita.
"Na ce ma babu komai, amma ka qi ka yarda."
Badura ta ce.
"Ina son naga babu komai xin, domin an bamu
damar binciken duk wanda ya biyo ta nan, don haka
dole ki buxe bayan motar."
Ciwon dake damuna shi ya hana ni fargaba ko
kaxan. Ban damu ba ko su buxe ko ma su bari, saboda
idan ma sun barni babu mamaki mutuwa zan yi.
Saboda jinin da ya zuba a jikina.
"Ba za ku buxe ba to." Badura ta ce da su cikin
tsiwa.
"Kai kirawo 'yallavai, wannan yarinyar bata da
gaskiya." Xaya xan sandan ya ce, bayan wani xan
lokaci na ji takun sawun wani xan sandan a gingin but
xin motar.
"Ke yarinya muna son ki buxe mana but xin motar
nan, idan kuma ba haka ba zamu valla da qarfi."
"Ba ka isa ba." Badura ta ce.
Tas!! Na ji qarar mari ya daki dodon kunnena.
Badura ta qwalla qara mai tsanani.
"Ku kama ta, ku sa ta a mota." Xan sandan ya ce,
"To 'yallavai." Saura suka amsa.
"Kai kuma xauko mana guduma." Xan sandan ya
sake bada umarni.
Na lumshe idanuna ina sauraron a buxe bayan but
xin da nake. Xan lokaci sai na ji an fara dukan but xin
motar, dukan but xin motar da ake daidai yake da
bugun zuciyata.

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

60





























KASHI
NA UKU

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

61
12
ka ci gaba da dukan but xin motar kamar za'a
ragargazata. Ba dukan motar ne ya dame ni ba,
abin da ya fi damuna shine jijjiga jikin motar da suke
yi. Duk lokacin da jikin motar ya yi rawa sai na ji
hannuna kamar ba a jikina yake ba. Har yanzu jini na
zuba a gurin da aka harbe ni, na gane hakan ne ta
hanyar jin danshi-danshi, ko ina a hannun rigata.
"Ku buga da kyau mana." Babban 'Yan sandan ya
bada umarni, nan da nan suka buxe wuta suna dukan
but xin motar tun qarfinsu. Sannan ne kuma naji
shiru an daina dukan bayan motar, irin shirun da
zaka ji ne a duk lokacin da aka xauke ruwan sama
kamar da bakin qwarya, sannan kuma aka xauke
lokaci guda. Babu mamaki shirun da naji tafi haka.
Qaqaraf! na ji qarar bugun takalma a qasa, ga
dukkan alamu wani 'yan sandan suke sarawa. Sannan
ne to na ji abin da ya sake sani fitar da rai daga
rayuwa. Duk da yake hankalina ba a jikina yake ba
hakan bai hana ni gane muryar Sojan nan da ya yiwa
Amina tambayoyi ba.
"Ba ku ga wata yarinya ba ta wuce tanan gurin?"
Sojan ya tambaya.
"Gata can 'Yallavai a cikin motarmu, daman ita
muke bincike mun xauka bata da gaskiya, don haka
ne ma kaga muna valle bayan motar."
"Bayan motar wa?" Sojan ya bugawa xan sandan
tsawa, sannan ya ci gaba da cewa, "Shin kasan ko
motar wacece kuke lalatawa?"
"Ranka ya daxe wallahi ban sani ba, na tuba."
Xan sandan ya ce jikinsa na rawa.
"Ai kana da sauran tuba." Sojan ya ce, "Sai ma ka
ji ko 'yar gidan wacece."
"Na tuba 'Yallavai." Xan sandan ya sake tuba.
"Mu tafi gurin Kanal Muktar ka tuba a gabansa."
Sojan ya ce dashi, sannan ya buga masa tsawa, "ku
fito da ita."
"To 'Yallavai." Xan sandan ya ce.
Na yi shiru ina sauraro, numfashina sama-sama
saboda jini mai yawan gaske ya zuba daga jikina, da
qyar nake buxe idanuna. Na kuma godewa Allah,
lokacin da aka harbe ni ta fito nemana.
"Gata 'Yallavai." Xan sandan ya ce, aka xan yi
shiru sannan Sojan ya ce a fusace.
"Ai ba wannan muke nema ba, ban da ita ba ku ga
wata ba?"
"Yallavai wallahi ba muga kowa ba sai wannan."
Alamar jin daxin ya fita daga bala'i a baiyane take a
cikin kalamin da ya yi.
"Ban ga amfanin zamanku a nan ba, tunda har ku
ka bari 'yar gidan (Oga) ta vace, kuma ta nan ta
biyo."
"Yallavai wallahi bata nan ta...."
"Ku saki wannan yarinyar." Sojan ya buga musu
tsawa."Ina son ku shiga motarku, ku zagaya ko zaku
gano mana ita, mu kuma zamu bi ta bayan titinnan ko
zamu ganta, kun gane ko?"
"Yes Sir!" 'Yansandan suka amsa baki xaya. Ga
yadda na fahimta, Sojan yana da xan muqami, saboda
irin yadda naji 'yan sandan na bin umarninsa sau-da-
qafa basu gardama.
A

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

62
Qarar cin tayar motocin 'yansadan, dana sojoji ne
ya tabbatar min da sun tafi. Ba a daxe ba sai naji
Badura na qoqarin buxe but xin motar, da qyar ta
samu ta buxe, saboda 'yansandan sun mammogaxa
bayan motar. Na kuma yi mamakin 'yan sandan,
saboda gani basu karvi xan mukullin but xin ba daga
hannun Badura, da sun karvi xan mukullin motar, da
tuni ina hannunsu, na yi mamaki mutuqa da dabarar
hakan bata faxo musu ba, idansu ya rufe,wannan wani
abu ne daga Ubangiji, na ce cikin zuciyata.
"Fadil!" Badura tayi kirana.
"Na'am." Na amsa da qyar. Ta yi ajiyar zuciya,
sannan ta kamo hannuna marar ciwon da niyyar fitar
dani daga cikin bayan motar, matsanancin ciwo ya
soke ni, na yi 'yar qara, Badura ta riqe numfashinta.
"Sannu Fadil!" Ta ce dani. Na yunqura da kyar
jikina babu laka ko kaxan, da qyar Badura ta fito dani
daga bayan motar, tana fito dani na yanke jiki na faxi
numfashina sama-sama, da qyar nake shaqar iska,
Badura ta sake xago ni sama ta hanyar sake kama
xaya hannun, da haka ta jani ranga-ranga har jikin
motar, muna zuwa sai ta buxe ta turani ciki a hankali,
sannan ta rufe, ta zagayo gaban motar ta shiga, ta
tashi motar sannan ta tuqa ta tafi dani inda ban san
ko ina ne ba, koda yake dai a lokacin bani da zavi,
amma kuma har yanzu ban saki jiki da Badura ba, ba
don harbin da aka yi min ba, to da yanzu mun rabu.
Ciwon ya sake sukata, na ji kaina ya yi dum, ba a
jima ba baqaqen taurari suka bayyana a idona, daga
baya ne na fahimci ashe suma nayi.

**
Sassanyan ruwan sanyin da aka yayyafa min a
fuska, shi ya taimaka wajen farkowa ta daga suman
da na yi. Badura na zaune a kusa dani kofin ruwan
sanyi a hannunta na hagun, hawaye na kwarara akan
kumatunta, abin yakan bani mamaki idan na tuna da
cewa wai yau ga Badura tana kuka da hawayenta
saboda wani mummunan hali da na shiga. Na dube ta
nayi murmushin qarfin hali, sai bayan da ta dawo min
da murmushina ne, na lura da inda aka harbe ni, a
xaure yake da wani farin qyalle.
"Mene ne kuma abin kuka Badura.?" Na tambaye
ta. "Ba abin da kuke so kenan ba, ku ganni cikin
bala'i, bada haqqina ba? Ai abin da ya kamata kiyi shi
ne farin ciki da dariya, ba kuka ba. Kina jin zan sake
yarda da ke ko kuwa..." Jiwa ta xauke ni, na ji kamar
zan sake suma numfashina sama-sama nayi luuu! zan
faxi Badura ta tare ni tana kuka, bayan xan tsawon
lokaci, sai hankalina ya xan dawo jikina, na buxe ido,
Badura na kallona.
"Daman nasan ba za ka sake yarda dani ba Fadil."
Badura ta ce dani, muryarta na rawa. "Mahaifiyata ta
riga ta lalata rayuwata, tunda tayi sanadiyyar da ka
tsane ni ka kuma tsani 'yar uwata Amira. Na faxa ma
ba laifina ba ne Fadil amma ka qi yarda." Ta ce dani
cikin qaraji da shesshekar kuka.
Tausayinta ya kamani duk da yake kuwa ban
yarda da ita ba, saura kaxan na amince da ita kuma
sauran kalamanta.
"Kar ka yarda da ita." Wata zuciyar ta ce dani.
"Shashasha ka manta abin da ta ce da kai a Durba
Hotel Kaduna? Daga baya kuma ta butulce maka?
"Kai ne mutum na farko da na fara jin sonsa a cikin
zuciyata." Lallai kam na tuna, ba zan amince da ita

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

63
ba, tunda kalamin da ta faxa a baya bai hana mata
cutata ba, da kuma sanadiyyar jefa ni a wani
mawuyacin hali "kana jin zaka kashe Zainab a banza
ne?" "Bani na kashe ta ba." Maganganun Badura da
suka faru a kwanakin baya ne suke dawowa zuciyata,
zaman kuma da nake yanzu a gaban Badura, wacce
hawaye ke kwarara daga fararen idanunta, ina iya jin
siririyar muryarta garai-garai kamar a faifan rediyo,
inda take cewa "Xaure shi da kya, don ka san qaqqarfa
ne..."
''Badura." na kira sunanta bata amsa ba.
"Bana jin akwai wani sauran kalami daga bakin ki
da zai iya sa wa na amince dake, tuni kin faxa min ire-
iren kalamaimasu sanyaya zuciya, masu kuma karyar
da zuciya, su kuma yaudari duk wanda ya amince da
mai muryar, don haka duk wani daxin baki da zaki yi
yanzu, kamar maimaici ne ga abin da kika faxa min
kwanakin baya, kuma ki ka yaudare ni. Bari na
tambaye ki Badura." Na ce da ita, kanta a sunkuye
tana zubar da hawaye, har yanzu kofin ruwan sanyin
na hannunta, tayi far da fararen idanunta, waxanda
ada sukan sa gabana faxuwa, saboda so da qauna,
amma yanzu ba zan iya fayyace tsakaninmu da ita ina
ganin sanin abin dake tsakaninmu da Badura sai ko
Ubangijin da ya halicci qaddara, damu kuma baki
xaya.
"Me kake son tambaya?" Ta ce dani cikin
shesshekar kuka. Na dubeta, sannan naci gaba da
cewa, "ke a ganin ki Badura, da kece a matsayina ni
kuma a matsayinki na Badura kina ganin za ki sake
amincewa dani?" Tayi shiru bata amsa ba, sannan na
ci gaba da cewa, "To ashe kuwa in dai haka ne bai
kamata ma ki fara ganin laifina ba, don naqi
amincewa dake, ke bari ma ta wannan shin halin da
nake ciki a yanzu kina ganin zan samu damar tsira?
Ki tuna fa duk wani xan sanda dake garin nan
nemana ruwa a jallo yake, ina amfanin baxi babu rai
Badura? Ina ganin zancen na amince da ke bai ma
taso ba, domin kuwa damar tsirata kaxan ce, nasan ko
ba daxe ko ba jima zasu kama ni, ba zai kuma yiwu
ace kullum ina ta guje-guje ba, cikin tashin hankali.
Na
End Ads