ya sharara min mari, wani abu ya bi ta
qwaqwalwata, sannan ya gangaro ta babban xan
yatsan qafata. Da farko na xauka kunne na ya fita
bana jin kome, sai irin qarar da za ka ji a yayin da ka
kara kunnenka a kan titin motoci. Haqiqa ba a tava yi
min mari irin wannan ba. Bayan na yi qoqari na dawo
da numfashina sai na sake xago kai na da niyyar na
sake tofa masa yawu, amma wannan karon sai na
kasa, jajayen idanunsa ne suka tsorata ni, suka kuma
yi min kashedin cewa yanzu fa in na sake ya qara mari
na, to kurumcewa zan yi. Sai kawai na koma kan
gadon na kwanta. Har yanzu akwai murmushin
mugunta a fuskarsa, wuqa ta faxo hannunsa, daga ba
ko ina ba, don ko ni kaina ban san daga inda ya zaro
ta ba, na yi tsammanin fexe ni zai yi, amma daga
qarshe sai na ga ya kama igiyar da ke jikina ya fara
yankewa.
"In ka sake qoqarin tofa min yawu." Ya gargaxe
ni "Sai na yi maka marin da uwarka ba za ta gane ka
ba."
"Gara ma ni ina da uwar." Na ce da shi. "Kai taka
uwar ma ba a san ta ba." Idanunsa suka sake kaxuwa,
amman wannan karon bai kawo min mari ba, sai
kawai ya ci gaba da tsinke igiyar. Bayan jiran da ya yi
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
18
kamar shekara a wurina, daga qarshe na sami kaina
ya warware igiyar sannan ya kama wuyan rigata ya
tashe ni tsaye na ji kamar qafata ba za ta iya xaukana
ba. Kwana biyu a xaure ba ci ba sha ba wasa ba ne,
saura kaxan na faxi amma sai kore da fari ya taro ni,
ya kama hannaye na yana ja na kamar mai koyon
tafiya.
Muka fita daga xakin, muka shiga wani da bai fi
wanda muka fito yanzu kyau ba, daga gefen hannun
dama akwai qofofi guda biyu, sai mutumin nan kore
da fari, ya ce da ni.
"Shiga ka yi wanka, ina nan ina jiranka ka kuma
shiga taitayinka." Ya gargaxe ni. Na lallava na shiga
banxakin ta hanyar dafa bango, na ja qofar na rufe,
banxakin ya fi xakin da aka xaure ni girma da kaxan.
Yana xauke da kwamin wanka irin na Turawa guda
biyu kowannen su yana xauke da kan famfo xaya da
kuma shaya xaya. Akwai qaton madubi a manne a
jikin bangon banxakin daga kudu. Na dubi fuskata a
jikin madubin sai na ga duk ta faxa, lallai na ji jiki
ciwon dake kaina yanzu ya daina zafi sosai. Na lallava
na tuve kayan dake jikina, sannan na kunna shaya na
shiga qarqashinta ruwan yana kwarara a kaina ni
kuma ina wanke busasshen jinin dake kaina. Lokaci
ya yi da ya kamata na nuna wa baqi mai kore da fari
cewa nima fa ba matsoraci ba ne, ni ma fa ba qaramin
shaixani ba ne. In dai har mutum ya biyo da ni da
hanyar shaixancin to zan nuna masa na fishi. Bayan
na wanke jikina tsaf na kuma shafa mai sai na sa
kayana sannan na daki qofar banxakin da qafa ta
buxe, na fito ina muzurai wai dan ya gane cewa to
yanzu babu wasa. Mutumin ya xago ya kalle ni a
yatsine a hannunsa na dama jakata ce wacce na xauko
daga otel xin mu shekaranjiya, lokacin da muke shirin
gudu.
"Yi sauri ka sa kayanka suna can falon suna
jiranka." Ya ce da ni.
Sannan mutumin ya jefo jakar saitin fuskata, da
farko na yi niyyar na kauce dan kada jakar ta same ni
a fuska, amma da na tuna da halin da nake ciki yanzu
bana tsoro ba ne sai kawai na tsaya waje xaya ina
jiran jakar ta qaraso. Na sa hannun hagu na cafe ta na
girgiza ta a gabansa sannan na ce da shi.
"Ka je ka cewa uwarka Badura ta jira ni minti
biyu."
Fuskarsa ta canja kala daga baqi zuwa toka-toka,
na kalle shi na fashe da dariya. "Matsoracin mata."
Na ce da shi "kar ka xauka ni ma tsoranta nake ji
kamar ka." Hannayensa suka dunqu le ya fara
matsowa inda nake tsaye, in yana tsammanin zan
tsaya ya dake ni to lallai yana buqatar sake sabon
tunani. Na ja da baya ina duban ko'ina cikin xakin ko
zan ga makami.
Can sai na hango wani manjagara a jingine a qofar
banxakin daga hannun hagu, na yi sauri cikin daqiqa
biyu sai ga manjagaran ya faxo hannuna, xakin ya yi
shiru ba ka jin komai sai qarar xisar ruwa a banxakin
dake gefenmu.
"Kada kayi faxa da shi Salman." Muryar Badura
ta ratsa shirun dake xakin, mutumin yaja da baya jiki
na rawa, sannan ya daka min harara, ya juya ya fice
daga xakin yana ta faman haxiyar zuciya.
A karo na farko tun ranar da a ka xana min
tarkon sai na gane sunan mutumin nan mai koren
wando da farar riga 'Salman' ban tava jin suna irin
wannan ba, muka yi ido huxu da Badura, tana tsaye a
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
19
qofar xakin wacce nake tsammani za ta kai ni babban
falon, sannan sai na ji gabana ya faxi qofar xakin ta
buxe wata kuma Badurar ta fito. Al'amarin zai ba ka
mamaki, idan na ce maka na kasa banbancewa
tsakanin 'yanmatan biyu da suke kallona kamar a
majigi. Suna sanye da baqaqen riguna, dogaye, an yi
musu adon fari a wuya muryarsu iri xaya ce kamar su
xaya, babu banbanci ko kaxan, tsawon su xaya kalar
jikinsu kuma xaya ce, idan aka haxa su su biyun zan
iya kiransu Badura. Waccan Badura da na sani amma
haqiqa a yanzu ba zan iya cewa wannan ce Badurar
da na sani ba.
"Muna son magana da kai idan ka gama
shiryawa." Sannan xaya Badurar ta ce. "Badura da
Amira shi ne sunayenmu, idan ka shirya muna jiranka
a falo." Sannan suka yi min murmushi iri xaya suka
juya suka nufi xakin. Na yi qoqarin gane
bambancinsu, amma na kasa. Tafiyarsu iri xaya
sannan na tambayi kaina tambayar da za ta fitar da ni
daga tarkon da na faxa, shin wacece Badurar, wace ce
kuma Amira? Na tabbata xaya daga cikin su ita ce ta
harbe Zainab, 'Amira kenan?' Na tambayi kaina,
wacece to Amirar daga cikinsu, duk abin da ya faru
tun daga farko har zuwa yanzu sai ya zama kamar
mummunan mafarki a gare ni, kiran da Salman ya
kwaxa min shi ya tabbatar min ba mafarki nake yi ba.
**
A haka na shiga xakin a ruxe na tsaya a bakin
qofar falon, qato ne mai xauke da kujeru goma sha
shida, kowanne bango na xakin yana xauke da kujeru
huxu. Kyakkyawan kilishi mai taushin gaske ya
mamaye xakin, a kusurwar xakin dake vangaren
gabas akwai qatuwar kanta mai xauke da litattafai
sama da xari bakwai kamar xakin Alhuda-huda, ba na
tsammanin gidansu ne, sai dai in na wani ne suka ara.
Koma na wane ne zan iya cewa xakin ya tsaru daidai
misali.
"Shigo ka zauna mana." Badura ta ce.
Na shiga cikin xakin a hankali, tattausan kilishin
da ya mamaye xakin yana barazanar shanye qafata
iya idon sawu. Na zavi kujera daga vangaren arewa na
zauna, ina fuskantar su. Badura da Amira suna zaune
a kujera guda, idan har kasan sunansu shi ne Badura
da Amira to za ka iya kiransu cikakkun 'yan biyu.
Idan kuwa ba ka san sunayen su ba za ka iya kiran
Badura inuwar Amira, ko kuma Amira inuwar
Badura. Da gangan suke komai iri xaya domin kawai
su rikita min qwaqwalwa. Salman na zaune a can jikin
bango a kusan kantar nan mai xauke da t arin
littattafai. Muka haxa ido da shi a karo na farko tun
da muka haxu da shi, sai ya yi min murmushin da ya
kai har idonsa.
"Fadil." Xaya daga cikin su ta yi kiran sunana
"Lokaci ya yi da ya kamata ka san duk abin da ake
ciki....."
"Me ya shafe ni?" Na katse mata hanzari.
"Qwarai kuwa ya shafe ka." Ta ce dani "In za ka
ba ni xan lokaci yanzu kuwa za ka ji abin da ya shafe
ka." Sannan ta ci gaba da cewa, "ka san Kanal
Mukhtar?" Na yi shiru na xan lokaci babu alamar
razana a fuskata, amma daga cikina har zuwa
qwaqwalwata sun daina amfani a lokacin.
Tun ranar da na baro Kano sai yanzu ne na tuna
da Amina, yarinyar da ta ke mutuwar sona, amma har
yanzu Allah bai sa min sonta ba, magana ma ina yi
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
20
mata ne don kar ta ce na wulaqantata. Duk da cewa
ban san abin da wannan 'yan biyu ke nufi ba,
murmushin dake yawan bayyana a fuskarsu, ba na
sonsa. Murmushi ne irin na mugunta, na kuma kasa
gane abin da suke nufi. Idan ba ka sani ba bari na
faxa maka ko wanene Kanal Muktar, fari ne xan
gajere kakkaura mai yawan tarin gashin baki, tsohon
Soja ne wanda a halin yanzu shekararsa goma da yin
ritaya daga aikin Soja. Mutane da dama suna jita-jitar
cewa shekarunsa saba'in a duniya, wasu kuma sunce
ya kusan tamanin, Allah ne kawai da mahaifiyar
Kanal Muktar suka san yawan shekarunsa a duniya.
Abu xaya da ya rage masa jin daxi shi ne ba shi da
xa ko xaya a duniyar nan, sai Agolansa xaya tal wacce
yake mutuwar so kamar ransa, wannan Agola tasa ya
xauke ta ne kamar 'yar da ya haifa. Amina ita ce
Agolan Kanal Muktar.
Xakin ya yi shiru, ba ka jin komai sai motsin
ganyayyaki da furannin fulawa da ke ta gugar tagogin
gidan. Haqiqa yanzu ne na fahimci sabon salon da na
ke shirin shiga, duk da cewa kuwa ban san abin da su
Badura ke nufi ba da ambatar sunan Muktar.
Na xago kaina muka haxa ido da su, sannan na ce
da ita.
"Mene ne to idan na san shi?" Ba tare da ta dube
ni ba sai ta ci gaba da cewa.
"Shekaru biyar da suka wuce, mahaifinmu Alhaji
Ahmad ya rasu, a sakamakon haxari Jirgin Saman da
ya ritsa da su. In za ka iya tunawa, yana xaya daga
cikin manyan masu kuxi dake Kano, yana xaya kuma
daga cikin manya-manyan marubuta littafi na
qungiyar 'RAINA KAMA'. Mun yi baqin ciki da
mutuwarsa, duk da yake yana nuna mana bambanci
tsakaninmu da 'yan uwarmu, ya mutu ya bar mata
biyu. Daga cikinsu akwai mahaifiyarmu Hajiya Binta,
dake zaune a unguwar Tarauni cikin birnin Kano, sai
kuma kishiyar babarmu Hajiya Asma'u."
Sannan ta dube ni ta ce da ni. "Hajiya Asma'u ita
ce mowar Babanmu, ya fi sonta a kan kowa, daga ita
sai 'yarta, sai abin da suka faxa shi ake yi a gidan.
Idan ba ka manta ba, babanmu ya rubuta wasu
littattafai guda biyu tun kafin ya rasu. Littattafan da
suka xaga harshen Bahaushe a duniya, sun sami
karvuwa cikin Najeriya gaba xaya, har ma waxanda
ba sa jin yaren hausa sun yi qoqarin koyonta domin su
sami damar karanta littafin. Akwai qasashen waje da
dama da suka yi murna da fitowar littafin,
musamman ma da ya ke yana taimakon su wajen
koyon harshen Hausa, an gabatar da littafin shekaru
biyar da suka wuce tun kafin mutuwar mahaifinmu,
ya samu kyaututtuka da dama daga manyan mutane
dake cikin birnin Kano. Xaya daga cikin kyaututtukan
ita ce wata sarqa ta zinariya wacce wani qwara ya bai
wa babanmu, shi wannan qwara yana mutuqar son
yaren Hausa, kuma ya koyi yaren Hausa ne saboda
yin hulxa da Hausawa, wajen cinikayya, mutumin
kuma da ya koya masa Hausa shi ne Babanmu.
Don haka lokacin da aka gabatar da littafin sai
qwaran ya tafi qasar waje, a can ya sa a ka qero masa
wannan sarqa ta zinare. A jikinta an rubuta kalmar
'R.K' da ruwan daiman, wato ma'anar kalmar raina
kama, dalili kuwa shi ne littafin ya fito ne ta qarqashin
qungiyar raina kama Kano.
A taqaice dai mahaifinmu ya raba gadonsa tun
kafin rasuwarsa da wata xaya mun sami dukiya mai
tarin yawa, sai dai kuma abin da ya baqanta mana rai
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
21
shi ne, bai yi rabon gado da sarqannan ba, da ya tashi
sai ya yi son kan nasa ya bai wa 'yar lelen 'yarsa
sarqar wato 'yar gidan Hajiya Asma'u kenan. Kada
ka yi tsammanin sarqar tana da wani kuxi ne mai
yawa, sam-sam kuxin ta bai wuce naira miliyan biyu
ba da dubu xari biyar."
"Fadil" Badura ta yi kiran suna na cikin wata
murya wacce ta ban tsoro.
"Ina son sarqar nan ta dawo wajena."
"Ta yaya za ta dawo wajenki?" Na tambaye ta, ta
dube ni sannan ta ce da ni.
"Har yanzu ba ka gane abin da nake nufi ba, in ba
ka gane ba to bari na qarasa ma labarin. Bayan
mutuwar Babanmu, Hajiya Asma'u ta yi aure. Bayan
shekara xaya, mutumin da aura kuma shi ne Kanal
Muktar, yana da gida a Sultan Road cikin jihar Kano
in ba ka sani ba kuma bari na faxa ma, duk cikin jihar
Kano in ka xauke gidan Gwamna babu inda ya kai
gidansa tsaro. A nan ne kuma na ke so kaje ka samo
min sarqar, shiga gidan wata sabuwar duniya ce,
amma shiga gidan ya fi shiga hannun 'yan sanda a
wajenka. Ko har yanzu ba ka gane abin da nake nufi
ba?"
Sannan ta qyalqyale da dariyar mugunta.
"Kada ka yi tsammanin shiga gidan Kanal Muktar
kamar shiga gidanku ne. Amma duk da haka gara
masu gadin gidan su harbe ka da a ce 'yan sanda sun
harbe ka a cikin jama'a."
"Me na yi 'yan sanda za su harbe ni?" Na tambaye
ta.
"Ba ka ma sani ba! Kana jin za ka kashe Zainab a
banza ne?"
"Ban kashe ta ba!!" na ce da ita cikin kaxuwa da
ihu, ban san lokacin da na tashi daga kan kujerata ba.
"Ka yi a hankali Fadil!" Badura ta ce "Domin dole
ne ka yi abin da na sa ka, domin ita ce hanya mafi
sauqi a gare ka, ita ce hanyar ka xaya tal da za ka iya
tsira. Idan ka kawo sarqar kuxin da za mu ba ka ya
isheka ka bar qasar nan, kaga ka tsira kenan."
Haqiqa yanzu daidai nake da na shaqe wuyan
Badura na karya shi saboda rashin qauna. Sannan na
dube ta na ce da ita.
"Idan an ce ba zan yi ba fa me za ki yi?"
"Kada ka vatawa kanka lokaci Fadil!" Ta ce da ni,
sannan ta miqe tsaye ta buxe wata loka ta xauko wasu
fararen takardu masu xauke da rubutu, ta jefo min su,
haxe da wata Jarida, sannan ta ce da ni.
"Ni zan tafi, sai ka yi qoqari ka san yadda za ka yi
ka isa birnin Kano." Sannan ta yi min murmushi, ta
ce da ni.
"Ba ka da mafita, dole ne ka yi abin da na sa ka
babu damar kaucewa. Ka san daman Hausawa sun ce,
'KIBIYAR AJALI FALKE BAYA KAUCE MA TA '
Sannan ta tura qofa ta juyo ta kalli su Salman da
xaya yarinyar da nake tsammanin ita ce Amira.
"Ku zo mu tafi." Ta ce dasu, suka bita qofar xakin
a daidai lokacinne Amira ta juyo ta ce da ni. "Mu
haxu a Daula Otel Kano, idan ka yi nasara, idan kuma
ba ka yi ba sai na ce mu haxu a filin sukuwa, wajen
harbe ka." Rufe qofar xakin ce ta tabbatar min cewa
sun tafi. Na dubi takardun nan da ban san abin da
suke nufi ba, ya zama dole na duba su, don haka sai na
gyara zama na buxa jaridar. Ban yi mamakin ganin
hotona ba a sha fin farko na Jaridar. A saman jaridar
an rubuta cikin manyan haruffa kamar haka,'wani
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
22
xan bindiga daxi ya harbe ma'aikaciyar Daba Otel
Kaduna....' guntun labarin kuma ba sai na faxa maka
ba, 'yan sanda suna ta nemansa ruwa a jallo, an kuma
rufe kowacce hanya da za ta fita daga Jihar Kaduna....'
Babu motar da za ta fita ba tare da 'yan sanda sun
yi mata bincike ba. Abin da ya fi bani tsoro shi ne xan
tsohon nan motsattse ya bada shaidar cewa ya ganni
na fito daga xakin da Zainab ta mutu, a qaryarsa cewa
ya yi wai har da bindiga a hannuna, wannan shaida ita
zata qara fitar da Badura daga zargin ko bakinmu
xaya da ita.
4
allai Kibiyar Ajali! Haqiqa yanzu nasan kibiyar
da Badura ta harben da ita, ta same ni a
maqogwaro, samun da ta yi min ina