tashi na yi kan xan sandan da gudu
kamar kibiya ya ga tahowa ta, don haka sai ya yi
qoqarin kai usir (abin busa) bakinsa, idan na sake ya
busa usir xin to ni ina buqatar addu'a kenan. Domin
na san wajen an iya cika da 'yan sanda cikin minti
xaya, na yi qoqarin kai kutufo bakinsa a daidai
lokacin da iskar bakinsa ta fara busa usir xin. Naushin
ya haxa da iskar bakinsa suka bada irin qarar da zak
aji idan tayar keke ta fashe. Xan sandan ya faxi
wanwar, hancinsa da bakinsa na tsiyaya, ban koma ta
kansa ba domin na san an gama masa aiki. Sai na
harba da gudu na nufi katangar lambun.
Ruwan saman da ake tafkawa kamar da bakin
qwarya ya fara tsagaitawa, shirun dake lambun a
halin yanzu ta fara rayuwa da hayaniyar gudun 'yan
sanda a cikin ruwa, daga can vangaren lambun usir
mai qaran gaske na tashi kamar algaita, lallai ina
ganin bala'i, amma duk wannan kaxan ne idan na
tuna da sato sarqa daga gidan Kanal Muktar, soja fa
ba xan sanda ba ne banbancinsu a bayyane ya ke.
Na yi tsalle na kama katangar lambun sai na ji an
riqe qafata, wani xan gajeren xan sanda ne, tsattsama,
tsawonsa bai wuce takun qafa biyar ba. Ya fizgo ni, da
wani irin zafin nama na mamaki, santsin ruwa ya
kwashe shi sai ya saki qafata, ni kuma hannuna ya
rabu da katangar na faxo kan tsakiyar cikin xan
sandan. Sai na ji kamar na faxo a kan qwallon qafa,
na yi tsalle gefe guda daidai lokacin ne xan sandan ya
tashi ya yi yo kaina, abinka da gajeren mutum tuni sai
ga shi a cikina. Ya yi sama da ni ya haxa ni da bango
ya matse ni qamqam da qyar nake numfashi, kamar
daga sama sai naga wani abu kamar katako ya taho
daga saman katangar, xan sandan bai kula ba yana ta
qoqarin fasa min ciki da matsa, katakon ya daki
tsakiyar kan xan gajeren xan sandan nan, sai ya yar
da ni ya faxi, ko motsawa bai yi ba. Na dube shi na
haxa masa naushi a fuska, qafafunsa suka mimmiqe
sannan yai shiru kamar matacce.
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
33
"Kama nan Fadil!" Wata siririyar murya ta ce da
ni daga saman katangar. Muryar sananniya ce a gare
ni, sai dai ba zan iya tunawa ba ko ta wacece a halin
yanzu.
A ka zuro min qafa sanye da takalmin ruwa baqi,
na kama ta na yunqura sannan na kama saman
katangar. Can qasan katangar wani siririn layi ne
wanda gidaje suka juya masa baya, wanda ya ziro min
qafar shi ya fara dira qasa, ni kuma na bishi a baya,
ya kama hannuna muka miqe cikin wani loko da
gudu. Wasu yara suna karatun Islamiya a cikin wata
rumfa, suka zubo mana ido suna kallonmu, bayan
wani xan lokaci sai gamu a bakin titi, motoci suna ta
zirga-zirga. Sai da na ga mun nufi wata baqar mota
Fasfanda sannan na gane mai ja na.
"Yi sauri ka shiga." Amina ta ce da ni, rigar
ruwan da tasa ita ta maida ita kamar namiji, fuskarta
na qyalqyalin farin cikin sake gani na.
6
duniyar nan gaba xayanta ban ga wand aya fi
masoyi ba. Lallai duk wanda ya ce yana sonka
ko da da wasa ne to ka rungume shi hannu biyu. A da
ban san haka ba sai da Aminatu ta tserar da ni daga
hannun 'yan sanda, sannan na fahimci cewa mai
sonka shi ya ke bada rayuwarsa wajen ceto taka
rayuwar.
Na yi tunani mai zurfi a lokacin da Amina ta ke
zura gudu damu a cikin motarta, duk cikin abokaina
ban ga wanda zai iya yi min abin da Amina ta yi min
ba, sai yanzu na gane irin son da Amina take yi min,
so ne na haqiqa. 'SON UWAR YARA BA' So irin na
Badura, a nuna ma so a lalata rayuwarka. A karo na
farko tun farkon haxuwarmu da Aminat sai na ji
qaunarta ta mamaye min zuciya, cikin minti goma sha
biyar sai ga shi ina nadamar qin karvar soyayyar
Amina da na yi. Haqiqa na wahalar da rayuwarta, na
kuma zalunci kaina, domin na san abin da ta yi min ta
gama karya min zuciya, ta sani na kamu da ciwon
A
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
34
sonta, ba tare da na shirya ba, in da ace Amina za ta
ce bata sona a halin yanzu, to da wahalar da zan sha
sai ta fi wacce tasha linkin ba ninkin.
Tunanina ya katse a daidai lokacin da Amina ta
taka birki, sannan ta sauka daga kan hanya ta tsaya,
tsakaninmu da Kaduna ya yi mil biyar. Tun lokacin
da muka shiga motar babu wanda ya ce da wani qala,
Amina ta juyo ta fuskance ni tana murmushi, sannan
ta dafa kaina ta ce da ni.
"Sannu Fadil, wallahi ka sha wahala! Kalli duk
yadda ka canza, kamar ba kai ba, yanzu da sun kashe
ka ni ya zan yi a duniyar nan Fadil! da ni ma qarshen
farin cikina ya zo kenan."
"Ki yi wa Allah godiya da ya sa har yanzu ina da
sauran numfashi." Na ce da ita. Wata mota ta zo da
gudu ta wuce mu kamar walqiya, cikin hasken fitilar
motar sai Amina ta kula da hannuna, inda gilas ya
yanke ni tun ina kan bishiyar gidan nan mai lambu,
nan da nan ta kunna 'yar qaramar fitilar dake cikin
motar da na kula sai naga hannun ya kumbura. Har
yanzu jini na zuba kaxan-kaxan.
"Bari na xaure ma." Amina ta ce da ni.
"Da me za ki xaure?" Na tambaye ta.
"Bari ka gani mana." ta ce dani, sannan sai ta cire
xan kwalinta, gashin kanta ya bayyana yana sheqi,
qamshin damina da kuma qamshin turaren da ke jikin
Amina suka haxu suka cika cikin motar, suka bada
wani irin qamshi mai faranta rai. Muka haxa ido da
ita sai kwarjininta ya sa na xauke idona, qaunarta ta
cika min zuciya, begenta ya mamaye qwaqwalwata,
ban san lokacin da ta xaure ciwon da kallabinta ba.
"Kin ga za ki vata xan kwalinki da jini." Na ce da
ita.
"Haba Fadil, lafiyarka ai ta fi komai a gare ni." Ta
sa siraran 'yan yatsunta masu taushi tana shafa saman
fuskata.
"Kalli duk yadda fuskarka ta kumbura."
Na matsa kusa da tagar motar na dubi fuskata
jikin madubi, sai na ga 'yan yatsun jibgegen xan
sandan nan guda biyar a fuskata, fatar bakina ma ta
qara girma.
"Babu komai Fadil." Amina ta ce, "Idan mun je
gida sai mu sami asibitin da za su duba ka."
"Kada ki damu." Na ce da ita. "Ke dai yi qoqari
mu tsira tukunna."
"Fadil!" Amina ta kira sunana, hannunta a cikin
hannayena, tana matsawa da na lura sai na ji 'yan
yatsunta suna rawa a cikin tafin hannuna, sannan ta ci
gaba da cewa.
"Na yi ma tambaya, za ka bani amsa?"
"Allah sa na sani." Na ce da ita.
"Fadil kana sona kuwa kamar yadda nake
sonka?"
Muryar ta na rawa. "Kada ka ce nayi rashin
kunya, wallahi sonka da na ke yi ya fi qarfin na voye
shi a zuciyata. Kai kuma na ga kamar ba ka damu da
ni ba Fadil, don Allah ina roqon arziqi xaya kafin mu
ci gaba da tafiya, ina son ka faxa da bakina ka cewa
kana sona koda da wasa ne. Sai na ji daxin tuqin, da
zan tserar damu daga sharrin maqiyanka, ya
masoyina, bana son ace kana kusa da ni amma ban
san matsayina a cikin zuciyarka ba."
Muka yi shiru na xan lokaci sannan na kalle ta na
ce da ita.
"Amina kwanakin baya da suka wuce, bana
tunanin zan tava qaunarki, amma yanzu sonki da
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
35
begenki sun zama ginshiqin rayuwata. Wallahi Amina
ina qaunarki, ba zan iya bayyana miki yadda nake jin
sonki a cikin zuciyata ba, na baki amanar kaina sai
yadda ki ka yi da ni, na zama naki.
Aminat ban sani ba ko kema kin zama ta wa?" Na
tambaye ta.
Ta yi min murmushin da na tabbatar na farin
cikin jin kalamai na ne.
"Daman ni taka ce Fadil, na gode da abin da na ji
daga bakinka koda kuwa bai kai zuciya ba."
Nima na saki murmushin kwatankwacin irin
wanda ta yi min.
"Kada ki yi shakkar abin da na faxa ya
masoyiyata, abar qaunar, kece tauraruwata ta
shekara, qauna, so, da bege a gare ki ba zan tava
dainawa ba." Muka haxa ido d aita. Abin da ta gani a
idona shi ya tabbatar mata da gaske nake, kunya ta
kama mu gaba xayanmu sannan ta lulluve idonta da
tafin hannayenta biyu.
"Wayyo rabin raina!" Amina ta ce dani cikin
murmushi.
Amina ta jijjiga kafaxa ta, na tashi firgigit, tun
lokacin da muka ci gaba d atafiya na fara yin barci,
saboda gajiya da kuma zazzavi da yake damuna.
Bayan da Amina ta gane zazzavi na damuna, sai ta
xauko gyalenta daga cikin wata baqar jaka, ta rufe ni
da shi, sannan muka ci gaba da tafiya.
Bana tsammanin Amina za ta tashe ni daga barcin
ba tare da wani dalili ba, don haka ba tare da tambaya
ba sai na tashi zaune. Kallo xaya na yi wa fuskarta na
tabbatarwa kaina babu lafiya, sannan na gansu a can
gaban mu suna tsattsaye cakare-cakare a bakin hanya,
ko wannensu na sanye da baqar rigar ruwa, duk da
yake kuwa an xauke ruwa, da bindigoginsu a maqale a
kafaxarsu.
Tun kafin mu qaraso suka fara dallo mana fitila
suna yi mana alamar idan mun zo mu tsaya, a can
gefen hagu kuma na titin sun balbalawa tayar mota
wuta tana ta ci, a kusa da wutar ne idona ya gane min
wani xan qaramin katako a jikin sa an rubuta, kamar
haka cikin harshen turanci 'STOP POLICED
CHECK' Amina ta taka birki muka tsaya.
"Ka koma bayan motar ka kwanta." Ta ce da ni
cikin sanyin murya. Ban yi mata musu ba, sai kawai
na faxa bayan motar na kwanta, Amina ta janyo wani
qaton tamfal ta rufe ni, sannan ta juya ta nufi 'yan
sandan bayan mun xan yi tafiya, sai na ji motar ta
tsaya, na yi mutuwar tsohuwa a cikin tamfal xin bana
ko cikakken numfashi saboda tsoron kar a ji ni,
zazzavin dake jikina na riga na manta da shi, a halin
yanzu ina ta kaina ne.
"Sannunki Hajiya." Wani gwarin xan sanda ya ce
da ita.
"Yauwa sannunka da aiki." Amina ta ce cikin
dariya, "Ya dukan ruwa.?" Xan sandan ya qyalqyale
da dariya, sannan ya ce.
"Haba Hajiya, ki na jin zamu zauna ne a nan ruwa
ya yi ta dukan mu, ai kinsan ba z ata yiwu ba."
Sannan ya ci gaba da cewa "Da za a fara wani ruwan
ma yanzu to da duk gida za mu gudu."
"Don cika aiki ko?" Amina ta tambaya cikin
dariya.
"Abar maganar." Xan sanda ya ce da ita. "Ina
zuwa ne Hajiya?" "Zan je Kanon Dabo." Amina ta
amsa masa.
"Ko za mu iya duba bayan motarki?"
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
36
"A'a ba za ku iya ba." Amina ta ce cikin dariya.
"Kai xan samariu kar ka vata min lokaci, ka je can
ka nemo wanda ya yi muku kisan kai, amma ba nan
ba. Ko kana tsammanin harkata har ta kai ta wadda
zan xauko mai kisan jama'a a bayan motata?"
"Kin cika surutu 'yanmata." Xan sandan ya ce.
"Oho! Wato yanzu an tashi daga Hajiya kenan na
koma 'yanmata, to nima bari in kira ka 'yallavai, idan
ba ka yarda da ni ba, to je ka duba. Amma kada ka
nuna ka sanni idan muka haxu da kai a Kano wata
rana, tun da sharri za ka yi min."
"Haba Hajiya, 'yanmata abin har ya zo da haka!
Kada ki damu daman wasa nake yi miki, wanda muke
nema ina tsammanin tuni ya bar Kaduna, mu ma
muna yi ne don dole." Sannan xan sandan ya daxa
marairaicewa muryar ya ce da ita.
"Idan na zo Kano ina zamu haxu?"
"A Daula Otel." Amina ta ce da shi cikin raxa.
"Wa zan tambaya idan na zo." Xan Sandan ya
tambaye ta.
"Ka ce kana neman Baby."
"To shi kenan sai na zo." Xan Sandan ya ce, "Za
ki iya tafiya." Amina ta taka motar muka yi gaba,
koda muka yi gaba, sai na ji qarar wata qatuwar mota
a bayanmu taja birki. 'lallai sun vatawa xan sandan
shiri' Na ce cikin zuciyata.
**
Tsakanin mu da Kano yanzu bai wuce mil ashirin
ba, mun wuce Qarfi da kaxan, tun da muka bar 'yan
sandan nan babu mai cewa komai. Aminatu tana ta
maka gudu damu kamar zamu tashi. Tun da muka
baro Kaduna har zuwa yanzu ban ga motar da ta
wuce mu ba, lokaci-lokaci Amina ta kan dube ni ta yi
min murmushi. Murmushin shi yake sani nake xan
manta halin da nake ciki, soyayya da daxi take, a
gurin wanda ya samu mai sonsa.
Duk rikicin da muka yi da 'yan sanda, jakar da
yayana ya bani tana bayana. "kada ka sake ka bar
jakar nan ta vata, ka tafi da ita duk inda za ka.."
MAganar da yayana ya yi ta jaddada min kenan da ya
bani jakar a lokacin da zan tafi Kaduna. Na gyara
xaurin jakar dake bayana, hannuna ya dunguri
aljihun gaban rigata, sai na ji qabarbar, na zaro wata
takarda daga ciki tasha ruwa, har ta fara bushewa,
amma har yanzu rubutun jikinta bai goge ba. Na
buxata rubutun saman takardar shi ya tuna min ko ta
mecece, tsarin gidan Kanal Mukhtar, shi ne abin da ke
rubuce a jikinta, takardar da Badura ta ba ni ce haxe
da jaridan nan tun ina gida mai lambu, na Kaduna.
Kada ka yi zaton zan bar Amina taga takardar, don
haka sai na saye ta a aljihuna.
Saura kaxan hancina ya daki gilas xin gaban
motar a sakamakon birkin da Amina ta ja, sai da
tayar motar ta yi qara qu!! Can gaban mu motoci ne
sama da guda biyar, an fito da mutanen ciki ana ta
bincike, muka yi shiru na xan lokaci muna kallon abin
da ke faruwa.
"Ya kamata ki kashe fitilar motar." Na ce da ita,
qwaqwalwata ta fara tunanin mafita, 'yan sandan
Kano fa ba irin na Kaduna ba ne, idan Amina ta
yaudari wani ya yarda to wani ba zai yarda ba,
sannan ne dabara ta faxo min, duhun gero ya rufe
ko'ina a bakin hanyar.
Na kalli Amina na ce da ita.
"Zan sauka na bi ta cikin gero, ke kuma sai ki yi
gaba idan sun gama binciken, ma haxu a gaba kar ki
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
37
tsaya sai kin bai wa mil xaya baya, sannan ki jira ni."
Na yi mata murmushin tabbatar mata abin da na faxa.
"Kada ki damu rabin raina." Na ce da ita, ban jira
wani abu ba sai kawai na buxe murfin motar na dira.
Amina ta bari sai da na shige duhun geron sannan ta
ja motar ta yi gaba.
Ruwan saman da aka yi a Kano bai kai na Kaduna
ba, amma hakan bai hana cikin duhun geron sanyi ba,
abin ka da mai jin zazzavi, nan da nan sai na fara
rawar xari. Na daure na ci gaba da tafiya cikin geron,
bayan 'yan mintuna sai na fara jiyo hayaniyar 'yan
sanda suna yiwa masu mota tambayoyi. Tsakanina da
su bai wuce taku shida ba, amma duhun gero ba zai
bar su su gane ni ba, na qaraso wata duhuwar gero a
kusa da wajen akwai wata qatuwar kuka, don haka sai
na bi ta bayan kukar da nufin ci gaba da tafiya,
sannan ne na yi tuntuve da wani abu, na wuntsila
gaba, na zo da fuska a kan tushiyar gero, da farko na
xauka kututturen bishiya ne ya taxe ni, amma qarar
razanar da na ji a bayana shi ya tabbatar min ba
kututture ba ne.
"Kana motsawa ina harbe ka." Xan sandan dogo
ne siriri, yana riqe da bindigarsa a hannun dama,
hannunsa na hagun kuma riqe da wandonsa, yana
barazanar sulluvewa. Duk da yake na tsorata sai da
abin ya so ya bani dariya, saboda ganin xan sandan
fitsari yake na yi tuntuve da shi, na tashi tsaye ina
rawar jiki, hancin bindigarsa a kan goshina.
"Babu mamaki ma kai ne mutumin da ya yi kisan
kai a Kaduna." Xan sandan ya ce cikin fushi, "me ka
ke yi anan.?" Ya daka min tsawa.
"Aikin da muka sa shi yake yi." Wata murya ta
amsa masa tambayarsa daga baya. "Idan ba ka aje
bindigarka