na farko da ya fara yiwa idona maraba, shi ne
manya-manyan Karnukan dake zagaya gidan suna
gurnani kamar saci babau, kamar yadda Badura ta
sanar da ni cikin wasiqarta, qofofi goma sha biyu ne
reras, kowaccen su tana fuskantar 'yar uwarta, idan
ka fita daga wannan sai ka shiga waccan. Daga kan
katangar da nake maqale ribda ciki, ina iya hangen
kowace qofa xauke da sojoji masu gadinta guda huxu,
kamar dai yadda Badura ta sanar dani. Ina iya kuma
hangen Karnukan uku-uku a kowacce qofa. Tsoro ya
daxa kama ni na yi matuqar tsorata da Karnukan
nan, hakan ne ma ya sa na fara tunanin abin da ya fi
haxari cikin abu uku, na farko dai Soja, na biyu
bindiga, na uku kuma Karnukan, duk da yake nasan
bindiga farat xaya zata hallaka mutum, amma hakan
bai sa zuciyata ta amince da cewa bindiga tafi kare
haxari ba. Na san dai bindiga bata harba kanta sai an
harbata, haka shi ma Soja sai ya ga abin harbawa zai
harba xin, to amma kare fa?
Na sunkuyo da kaina qasa, na sake nazarin gidan,
na yi sa'a saboda daidai inda nake saitin qofa ta
qarshe ne, daga nan babu wata qofa. Sai dai kawai
mutum ya tsinci kansa tsakar gidan wacce a haskake
take tsakar gidan na yi karo da kare. Sai dai kuma in
har abin da Badura ta faxa gaskiya ne to da wahala na
ci karo da kare ko kuma maigadi. Tunanin haka shi
ya baiwa zuciyata damar raya min cewa na yi qunar
baqin wake na faxa tsakar gidan, amma duk da haka
sai da na xan saurara a qalla mintuna biyar ina
sauraro tare kuma da kallon tsakar gidan. Duk
tsawon lokacin nan ban ji komai ba, ban kuma ga
wani abu da zai sani shakkar shiga gidan ba. A cikin
xan lokacin da na ke jiran ko zan ji motsin wani abu
daban ne, sai tunanin Amina ya faxo min, wacce
rabona da ita tun safe, da ta kawo min abinci, ta kuma
ce zata dawo da daddare amma bata dawo ba, wanda
a qarshe ma na gode wa Allah da ya sa ba ta dawo ba.
Saboda zuwan nata yana iya kawo min vata lokaci
wajen fitowa neman sarqar, sanin cewa yanzu fa
tsakani na da Amina bai fi taku kaxan ba shi ya jefo
da tunanin ta zuciyata, daman an ce rashin sani ya fi
dare duhu, don na tabbata da Amina ta san irin
haxarin da nake ciki yanzu, to da ta kawo min sarqar
har gida, to amma bata sani ba, nima kuma bana son
ta sani xin domin rashin sanin nata shi ya fi alheri a
gare ni.
Wani zakara ya yi kuka, na duba agogona, qarfe
xaya da minti xaya, alamu ne da suke nuna cewa, gari
ya kama hanyar wayewa. Nan da nan na yi tsalle, na
dira tsakar gidan, na yi sa'a ba a kan dandamali na
faxo ba, saboda gindin katangar a zagaye yake da
koriyar ciyawa tattausa. Ina dirga sai muka yi arba da
wani xaki, mai kyakkyawar qofa ta gilas sai dai kuma
gilas xin kamar madubi yake, idan ka leqa da niyyar
kaga abin da ke cikin xakin sai dai kaga fuskarka.
Na matsa a hankali ina sanxa zuciyata kuma tana
ta bugawa tsakanin haqarqarina, kamar dai yadda
Badura ta faxa, xakin daga vangaren hagu yake.
Tsakanin xakin da qofar gidan ta goma sha biyu zai
kai kimanin sawu na dogon mutum, ashirin daga inda
nake tsaye ina iya jin gurnanin mugayen Karnukan
dake gadin qofar. Idan kuma har ba hancina bane ke
faxa min qarya, to ina iya shaqar warin tabar da masu
gadin ke sha.
"Good morning Sir." Wani Soja ya ce da xan
uwansa. A can xaya vangaren na gidan, abin ya bani
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
54
mamaki. Don na lura da cewa shi Soja ba shi da dare
ba shi da rana. Ko yaushe safiya ce.
Na matsa kusa da qofar xakin gabana ya faxi,
wannan ya samo asali ne saboda sanin cewa tsakanina
da sarqar da ta jefa ni cikin bala'i bai fi taku uku ba,
sai dai kuma ba a nan gizo ke saqar ba, qofar ta gilas
ce shafaffiya babu alamar gurin buxewa a jikinta, ina
son na tava ina tsoron kada na jangwalo wani sabon
bala'in, to idan ma na tava xin ta yaya zan buxeta? Na
yi kimanin mintuna biyu ina zagaya xakin daga
qarshe ne na gano wata taga a bayan xakin daga
vangaren yamma, tagar 'yar qarama ce, ita ma kuma
a rufe take da gilasai, sai dai ita tana da wajen
buxewa, ina jan wani qarfe mai ruwan azurfa, sai
tagar ta bada wata 'yar qara ta buxe, sannan na leqa
cikin xakin, kamar yadda Badura ta sanar da ni a
zaune a tsakiya gilas xin wanka ke kan wani qaton
tebur mai ruwan gwal, sarqa ce tana qyalqyali kamar
waliqya. Hakan yana da nasaba ne da irin
matsanancin hasken dake zagaye da sarqar. Wanda
kuma Badura ta gargaxe ni da cewa kada na sake na
matsa kusa da gilas xin sai na kashe wutar xakin gaba
xaya, domin kamar yadda ta ce, wai akwai na'urar
qararrawa mai aiki da inuwa, kuma ita ce ke gargaxin
Sojoji da kuma Karnukan gidan cewa gida babu
lafiya.
Na daxa buxe tagar, sannan na zira qafata cikin
xakin. Zan xago qafata ta hagun kenan sai na ji wani
abu ya mari fuskata, ya kuma yi sama da wani irin
kuka. Da zaka tsaga jikina a lokacin ba zaka sami jini
ba don tsoro. Na yi qiqam ko cikakken numfashi bana
yi iya yi. Qafata xaya a ciki xaya a waje. Sai bayan da
na dubi tsakar gidan ne sannan abin ya ban haushi ya
kuma bani dariya a zaune akan katangar gidan, wani
kyakkyawan Aku ne shi da matarsa, yana kallona.
Yana wani irin kuka, ban ko qara komawa takansa ba
na faxa cikin xakin ta tagar. Xumi ya bugi fuskata,
saboda matsanancin zafin dake gauraye a xakin
sakamakon qwayayen wutar lantarkin da suka zagye
xakin a qalla goma sha uku. Na dubi gilas xin da
sarqar ke ciki, sannan na dubi hasken dake zagaye da
xakin, sannan ne na fara gaskata maganar Badura, zai
yi wuya ko kuma in ce ba zai ma yiwu ba ka gane
cewa gilas xin da sarqar ke ciki a jone yake da na'ura
mai qararrawa. Sai dai ko an faxa ma ko banza dai
Badura ta taimaken ta nan wajen, duk da yake kuwa
har yanzu ban amince da ita ba. Ni a ganina duk zaqin
bakin da ta yi na yaudara ne.
Shawara ta kasa yankuwa a gare ni na duba xaqin
sama da qasa ban ga wajen kashe qwan ba, sai bayan
da na yi minti guda ne ina dube-dube sannan naga
abin kunnawar (swich on/swich off) su na gani a
rubuce a jiki cikin harshen turanci, wajen kunnawa
da kashewa kenan. Sai dai kuma abin mamaki ko
kuma in ce abin baqin ciki wai aka rasa inda za a ajje
abin kunnawar sai a kan teburin nan inda gilas xin da
sarqar ke ciki yake, da farko har na matsa da sauri
domin na kashe, cikin da na fara nufar wajen sai
qwaqwalwata ta fara yi min ihun gargaxi. "kai wawa
baka ganin dabara ce aka haxa don kama marasa
gaskiya irin ku, baka ganin kana matsawa kan teburin
inuwarka zata faxa akai, bayan kuma an faxa ma
na'urar ce ke yiwa Sojojin gidan nuni, tana aiki kuma
ne da inuwar wanda ya zo kusa d aita? Na yi turus na
tsaya koda na dubi inuwata sai naga tsakaninta da
gilas xin bai fi takun hannu ba, na yi sauri na ja da
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
55
baya. To a daidai lokacin ne kuma qaddara tayi
halinta.
Ba zato ba tsammani sai ga xan tsuntsun Akun nan
ya faxo xakin kamar daga sama, ashe nine na yi
kuskure ban rufe tagar da na shigo ba, cikin qanqanin
lokaci qwaqwalwata ta fara yi min gargaxi da irin
aika-aikar dake shirin faruwa, nan da nan na kaiwa
Akun nan cafke, yin haka shi ya tsorata Akun, shi
kuma ya nufi kan gilas xin yana fuffuka da fika-
fikansa, a take a nan al'mura suka watse, inuwar
Akun ta yiwa gilas xin rumfa a loka ci guda kuma sai
duk na ji gidan ya xauki kukan jiniya mai firgitarwa.
'Ta faru ta qare' na ce cikin zuciyata. "Ina amfanin
baxi ba rai, tunda abin da nake gudu ya faru me kuma
zan ji tsoro?" A take a nan na nufi wajen gilas xin da
gudu, har yanzu jiniyar bata daina kuka ba, saboda
qarin inuwa da aka samu akan gilas xin. Ina zuwa sai
na buxe gilas xin na xauke sarqar na jefa a aljihu,
sannan na kashe wutar xakin gaba xaya, na nufo qofar
xakin da gudu, na manta da cewa ashe a rufe take ina
zuwa sai na ci karo da qofar, gilas xin ya tarwatse ni
kuma na faxo rubdaciki, a daidai lokacin na ji gudun
Sojoji sun nufo qofar gidan ta goma sha biyu, gidan ya
ruxe da hayaniyar Sojoji. Daga xaukan sarqar zuwa
ga fitowata na ji harbin gargaxi da bindiga ya kai xari.
Na yi sauri na miqe sannan na yi cikin gidan da
gudu da nufin na sami gurin vuya, amma abin ya ci
tura, filin gidan har yanzu a haske yake da lantarki,
kuma babu wajen vuya, da na lura da vangarena na
hagu sai naga wata 'yar siririyar hanya wacce bangon
gidan da wani ginin xaki suka qirqireta, da gudu na
shige kwanar da niyyar na sami wajen vuya ina zuwa
sai na ga ashe hanyar wani xaki take fuskanta.
Abubuwa suka taru suka rikice min, can kuma Sojoji
sai harbe-harben iska suke yi. A daidai lokacin ne
kuma na ji ana buxe qofa ta qarshe wace take
fuskantar gidan, ina tsammanin da qatuwar sarqa
suka xaureta. Don haka suka sami tangarxa wajen
buxeta. Na duba sama da qasa ko zan ga wajen vuya
amma babu, na san kuma ko wanne lokaci daga yanzu
Sojoji ne za su shigo farfajiyar gidan. Na kuma dubi
katangar sai naga duk tsallen da na yi ba zan kamo ta
ba. Idan ma kuma na yi nasarar kamota ma, to na
tabbata ba zan dira da yatsuna ba domin kaifafan
kwalabe ne da qusoshi akan katangar. Suna kuma
maraba da hannun duk wanda ya yi qoqarin tsallaka
katangar. Wauh! wauhn!!! Amsa kuwwar haushin
Karnukan ta dako dodon kunnena, haushin Karnukan
kamar duka da guduma ne a qirjina. Idan akwai abin
da na fi tsoro, bai wuce Karnukan nan, da ace
Karnukan nan sun kama ni gara ace da bindiga aka
harbe ni.
Qofar da Sojojin ke qoqarin buxewa ta fara yi
yowa gaba-gaba, tsoro ya sake kamani, saboda ganin
irin yadda Karnukan ke dukan qofar da jikinsu, tun
kafin ma Sojojin su buxe su har sun qosa su shigo.
"Fadil!!" Wata siririyar murya tayi kirana, qofar
xakin dake fuskantar siririyar hanyar da na biyo ta
buxe, tana sanye da doguwar riga ta barci kanta babu
xankwali, Amina ce.
"Shigo nan." Ta ce da ni, a daidai lokacin ne kuma
ta kama hannuna muka shige xakin sannan ta maida
qofar xakin ta rufe. Duk da yake ta rufe xakin hakan
bai hana ni jin gurnanin Karnuka a qofar xakin ba.
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
56
11
aba Fadil!" Amina ta ce da ni cikin
shesshekar kuka, "me yasa zaka yi min
haka? Yanzu tsakanina da kai har akwai wani abu da
zai same ka ka voye min, in da ka faxa min ka ce
sarqar ka ke so me zai hana na baka ita cikin ruwan
sanyi. Ka tuna fa irin son da nake yi ma, kafi qarfin
sarqar a wajena amma kuma......" Ta kasa faxar
kalmar da take son furtawa, sai dai kuma na gane
abin da take qoqarin faxi, tana son ta san dalilin da
yasa na hauro gidan ne, idan kuwa har bani da hujjar
hauro gidan to suna xaya ya dace dani 'Varawo'.
"Ba laifina ba ne Amina." Na ce da ita, "wallahi
tilasta min aka yi, aka kuma fi qarfina." Har yanzu
Amina ba ta daina kukan ba, amma jin cewa tilasta
min aka yi sai naga nan da nan ta xago kai ta dube ni.
Duba na nutsuwa, sannan cikin tattausar murya ta
tambaye ni.
"Wanene ya saka ka shigo gidan nan xaukar
sarqa?"
"Waxanda suka xora min laifin kisan kan da aka
yi a Kaduna." Na amsa mata kai tsaye.
"Kana nufin ka ce duk akan sarqar ne aka xora
ma sharrin?"
"Akan ta ne aka kashe Zainab." Na qarashe mata.
Amina ta yi shiru na xan lokaci, sannan ta xago kai
ta ce. "Su wanene Fadil? Ina buqatar jin su yanzun
nan, bana buqatar wani noqe-noqe kuma."
"Suna da yawa." Na ce da ita, "amma shugabarsu
ita ce kishiyar mahaifiyarki Hajiya Binta, yayarki
kuma Badura ita ce ke taimaka mata, ita da wani xan
ta'adda Salman sannan......" Na yi shiru cikin kaxuwa.
Kallon da Amina ke yi min shi ya sani rawar jiki, kallo
ne da zan iya fassara shi da kallon tsana. Tun da nake
da Amina ban tava ganin ta yi min irin kallon ba.
"Ci gaba mana." ta ce da ni cikin kakkausar
murya.
"Akwai xaya 'yar uwar taki Amira, sai kuma wani
xan tsoho da ban san ko wanene shi ba." Na ce da ita.
"Da wa kuma?" Ta sake tambayata.
"Su ke nan." Na tabbatar mata.
"Qarya ka ke!" Ta ce dani cikin kukan takaici.
"Sai wa kuma? Ka rage guda xaya, idan ba za ka
faxa ba bari na faxa ma xayan."
"Faxa min to." Na ce da ita bakina na rawa.
"H
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)
57
"QAI NE." Ta ce dani, "wallahi daman tun farko
sai da na yi zaton haka, nasan Hajiya Binta daman ba
qaunar mu take ba, baya ga haka ma....." Ta fashe da
kuka. "Ka cuce ni Fadil, wallahi ka cuce ni, an haxa
baki da kai domin a cuci mahaifiyata." Sannan ta yi
min wani irin kallo sannan ta ce.
"Fadil." Ta kira sunana muryarta a dusashe.
"Na'am." Na amsa, muryata na rawa.
"Me yasa ka yaudare ni.?" Ta tambaya.
"Ba yaudararki na yi ba." Na amsa mata.
"Haba Fadil!" Ta ce dani "Na fa karanta takardar
da Badura ta aiko ma ta soyayya, wacce a cikinta ne
har take faxa ma sirrin gidan nan. Ka ci amanata, ka
kuma cue ni, tunda ka so 'yar'uwata sannan kuma ka
amsa min wai kana sona."
"Ni ban ce ina sonta ba." Na ce da ita, "Amina kin
kasa fahimtata, wallahi ba laifina ba ne, kuma
takardar da ki ka karanta ba ki karantata har qarshe
ba ne da kin fahimci gaskiya."
"Kaima ka san ba zan iya karance ta ba, saboda
irin kalaman da Badura ke yin amfani da su, wai tana
qaunarka. Wallahi zuciyata ba zata iya daurewa ba,
kuma......" Muryarta ta sake dusashewa, ta fara kuka.
Sannan ta xago kai muka haxa ido da ita.
"Babu abin da zaka ce min, na yarda da kai Fadil,
tun lokacin da na sami takardar da Badura ta rubuto
ma nake tunanin irin baqin cikin da zan faxa in har
abin ya zama gaskiya. Sai gashi kuma ya zama xin.
Wai Fadil da kanka, da kuma hankalinka aka haxa
baki da kai don a cuci mahaifiyata ko? Wato wannan
shi ne sakayyar irin soyayyar da na nuna maka? Tun
da nake da kai Fadil ban tava nuna ma rashin qauna
ba, ban kuma tava tunanin cutar ka ba, duk da yake
ma na san daman can kai ba qaunata kake ba...."
"Kada ki faxi haka Amina." Na ce da ita. "Ke kanki
kin san da bana qau....." "kar ka vata bakinka." Ta ce
dani a lokaci guda kuma ta miqo min siraran
kyawawan 'yan yatsunta na hannu.
"Bani sarqar da ka xauka." ta ce da ni. "Nima ina
sonta kamar yadda Hajiya Binta ke sonta." Da farko
na yi niyyar qin bata, amma na san hakan bai biyuwa,
domin a lokacin daidai take data qwalla ihu, Sojoji su
cika xakin.
Muka yi shiru na xan lokaci muna kallon juna ko
qiftawa ba ma yi, na dubi Amina babu alamun qauna
a fuskarta, sai alamun tsana da kuma zargi da suka
fito qarara a kyakkyawar fuskarta, na xan yi jim
sannan na tura hannun nawa a aljihu na zaro sarqar
na miqa mata, Amina ta karvi sarqar ta buxa rigar
mamanta ta jefa ciki sannan ta ce da ni.
"Vace min da gani."
"Saboda me Amina." Na tambaye ta.
"Saboda ba na qaunar ganin mayaudari kuma
maqiyin mahaifiyata." Ta amsa min. "Me ya sa ki
tunani ni mayaudari ne kuma maqiyin mahaifiyarki."
Na sake tambayarta.
"Saboda an haxa baki da kai domin ganin an cuci
mahaifiyata, kuma ka yaudare ni,