x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 5 - KIBIYAR AJALI

  • 12001 words
  • 15000 words
  • Out of 49194 words

Category: Love Stories

Views 532

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
tsammanin shi ne
zai zamo ajalina, duk da ya ke har yanzu ina da
L

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

23
damar da zan zare kibiyar daga jikina ba tare da ta yi
sanadiyyar ajalina ba, sai dai kuma damar kaxan ce.
Mintuna biyar suka shuxe kamar wasa har yanzu
qwaqwalwata ba ta fara aiki ba. A duk lokacin da na
fara tunani sai tunanin abin da Badura ta ce da ni ya
ruguza tunanina, kamar yadda ruwa ke ruguza
tubalin yashi.
"Ina son sarqar nan ta dawo wajena..."
"Idan ka yi nasara ladan da zamu ba ka ya ishe ka
ka bar qasar nan, ka ga ka tsira kenan.."
Wannan su ne maganganun da suke rikita min
qwaqwalwa.
Haqiqa Badura ta so kanta, ta yi amfani da rashin
imaninta, wajen ruguza rayuwata. A cikin zavin da ta
bani babu wani mai sauqi, kamar yadda ta ce wai idan
na yi nasara zan bar qasar, wannan kuma wani abu ne
da ba zai yiyu ba. Idan na bar qasar wajen wa za ni,
shin kuma ni da sake haxuwa da 'yan uwana sai a
lahira kenan? Duk wannan mai sauqi ne a kan shiga
satar sarqa gidan Kanal Muktar, abin da na tabbatar
ma kaina shi ne kwanana ya zo qarshe.
Badura ta bani zavin shaixan, dole ne na kira shi
da zavin shaixan, domin kuw ababu mai sauqi daga
cikin biyun, idan na yi na sara, na bar dangina, 'yan
uwa da abokaina kenan har abada? Idan kuma ban yi
nasara ba. To wannan ba sai na faxa ma ba, na mutu
kenan, dole ne na samu zavin kaina na uku idan har
kuwa ina son tsira, ya kuma zama dole na rama abin
da Badura ta yi min, sai kuma na samo wanda ya
kashe Zainab in har ina raye. Wannan shi ne
alqawarin da na xaukar wa kaina lokacin da nake
zaune a cikin gidan nan wanda ban san ko a wacce
unguwa yake ba.
Abin da ya fi damuna yanzu shi ne, hanyar da zan
bi na je Kano. Na farko dai ko wacce hanya a cike
take da masu jajayen idanu suna nemana, ga shi kuma
ba ni da mota ba kuma kuxi, to idan ina da mota ma
ta ina zan bi? Kuma wajen wa za ni idan na isa
Kanon, domin na tabbata yanzu yayana ya san halin
da nake ciki a halin yanzu, na yi alqawarin, ba zan
tava tunkarar gidanmu ba sai na ga abin da ya ture
wa buzu naxi.

*
Sa'o'i biyu suka wuce ba tare da na sami wata
qwaqqwarar shawara ba, don haka sai na ga zama ba
zai yi min ba. Nan da nan na tashi na nufi qofar xakin
da nake tsammanin za ta fitar da ni har farfajiyar
gidan. Na buxe qofar ga mamakina sai na ga wani
makeken lambu, mai xauke da kayan marmari iri-iri
ya zagaye ginin xakin da nake ciki. Lambun yana
zagaye ne da wata makekiya r katanga wacce ba na
tsammanin zan iya tsallakata, sai dai idan na yi
amfani da tsani, ya kamata na xan zagaya na ga
tsarinsa. Don haka sai na rufe qofar xakin na fito waje
qafafuna babu ko takalmi, nabi wata 'yar siririyar
hanya wacce nake tsammanin za ta kai ni tsakiyar
lambun.
Koda na juya na kalli xakin da na fito daga ciki sai
na ga ya zama xan qanqani a cikin tafkaken lambun,
sannan na ci gaba da tafiya a hankali. Na bi wata 'yar
siririyar hanya wacce bishiyoyi suka yi mata inuwa ta
ko wanne vangare. Sai da na wuce bishiyoyin nan
sannan na hango wata tafkekiyar qofa wacce nake
tsammanin ita ce za ta iya fitar da ni daga lambun. Ba
tare da na yi tunani sau biyu ba, sai kawai na nufi

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

24
qofar da sauri tun kafin na isa qofar na fara jin qarar
motoci suna ta wucewa ta qofar lambun, qatuwar
hanya ce, motoci suna ta zirga-zirga, daga can kuma
tsallaken titin manya-manyan kantuna ne wasu ana
saida kayan masarufi, waxansu kuma an ta ciniki iri
daban-daban. Wata qatuwar mota, ta wuce kamar
guguwa, a daidai lokacin ne na hango wani shago,
wanda ganinsa ya sa gumi ya karyo min. Qaton shago
ne a shafe da farin fenti, an zagaye qofar da wasu
baqaqen qarafuna. Wani Inyamuri qato, fari, mai
kaurin wuya, yana zaune a qofar shagon, yana ta
girgiza kai kamar qadangare, ga dukkan alamu dai
yana sauraron kixan Turawa ne. A gefen hagun xinsa
kuma wani qaton katako ne fari yana xauke da rubutu
cikin harshen Turanci 'EMEKA BUSINESS
CENTRE' Daga qasan katakon kuma an yi zanen
wani mutum da wayar talfo a hannunsa. Ko ban faxa
maka ba, za ka iya tunanin cewa wannan shi ne
mataki na farko da ya kamata na xauka domin fitata
daga Kaduna.
Ba tare da na vata lokaci ba, sai na juyo a guje na
nufo xakin ina zuwa na buxe shi na shiga da sauri ba
tare da na rufe qofar ba. Agogon bangon xakin ya
nuna qarfe goma sha biyu na rana, na buxe cikin
jakata na xauko wata rigar sanyi mai haxe da hula na
sa. Har na juya zan fita daga xakin sai na ga wani
qaton baqin tabarau a kan tebur, na yi tsammanin na
Salman ne, nan da nan na xauka na sa, na dubi
fuskata a mudubi na yi murmushi, abin da na gani a
mudubi shi ya bani dariya za ka iya kirana Uce ko
kuma Cinedu, na zama kamar Inyamiri. Duk wannan
abin ya faru ne a cikin abin da bai gaza minti biyu ba.
Da gudu da sassarfa na isa qofar lambun, ina fata
dai ba za ka iya mamaki ba da irin shigar da na yi,
wani abu ne da ka sani. Kusan kowa a halin yanzu ya
san halin da ake ciki a Kaduna, ya kuma san
kamannina a hoto, to amma yanzu zai yi wahala ka
gane ni, in dai har ka yi la'akari da hoton da ke jikin
Jarida.
Ban yi mamaki ba da na tadda qofar lambun a
buxe, qofar ta yi qara, qir!! a daidai lokacin da na
maida ita na rufe, bayan na yi jira kamar na daqiqa
talatin, na samu na tsallaka titin.
Tun kafin na qaraso shagon sai na ga Inyamurin
ya shiga shagon ni kuma na bishi a baya, qaton shago
ne wanda ke xauke da manya-manyan kujeru uku.
Bangon xakin a lulluve yake da takarda ruwan gwal,
kana shiga xakin za ku yi ido huxu da kayuwan talfo
guda biyar, uku daga cikin su jajaye ne biyun kuma
farare. Duk wannan na kula da shi ne cikin abin da
bai wuce daqiqa huxu ba.
"Mene ne lambar ka?" Inyamirin ya tambaye ni
cikin harshen turanci.
Na zaro biro da wata guntuwar takarda daga
aljihuna na rubuta masa lambar talfon xin yayana
dake Kano, sannan na miqa masa.
"Zauna a can." Ya nuna min xaya daga cikin
kujerun da take fuskantar fararen kayuwan talfon
nan guda biyu. Ban yi cikakken minti xaya da zama
ba sai ya miqo min kan talfon.
Tun kafin na qarasa da kan talfon kunnena sai na
ji muryar Hajara, tana cewa "wanene?"
"Ni ne Fadil!" Na ce da ita.
Hajara matar yayana ce dake Kano, kuma a
wajenta na girma tun lokacin da iyayenmu suka rasu

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

25
a sakamakon haxarin mota, sai babban yayanmu ya
xauke ni ya kai ni wajen ta a lokacin shekararsu uku
da yin aure. Tana mutuqar sona, musamman ma da
yake ta ga ba ni da qiwa, da rashin jin magana.
"Fadil kana ina?" tausayinta ya kama ni saboda
shesshekar kuka da ta fara yi.
"Kada ki damu." Na ce da ita, "ke dai ki saurare
ni da kyau ki ji abin da zan faxa miki." Ba tare da na
jira ta sake tambaya ba sai na ci gaba da cewa.
"Don Allah Hajara ki yi maza ki tafi gidan Kanal
Muktar ki sami Amina, idan kin same ta ki ce mata ni
na aiko ki. Ki ce mata ina Tudun Wada Kaduna, ina
kuma buqatar taimako da gaggawa, domin ya zama
dole na bar Kaduna yau xinnan. Kuma ki ce mata
wannan ita ce damata ta qarshe ko na fice daga
Kaduna yau ko kuma 'yan sanda su kama ni, kina ji
na Hajara?"
Na tambaya, na ji shiru na xan lokaci sannan sai
na ji Hajara ta ce da ni "Fadil." Na ce "Na'am." Ta
sake yin shiru, jikina ya fara rawa.
"Hajara!" Nayi kiranta "Ya ya na ji kin yi shiru,
in wani abu ne ya faru ai sai ki faxa min, ba sai kin
voye min ba. Kin san dai wannan abu qaddara ce
kuma dole ne ta faru a kaina, amma abin da na ke so
ki gane shi ne ba ni na yi kisan kan ba sharri aka yi
min, ko kin yarda ni na kashe ta?" Wannan magana
da na yi ita ta dawo da Hajara cikin hankalinta.
"Haba Fadil!" Ta ce da ni. "Daidai da rana xaya
ban tava zaton za ka iya kashe Akuya da ranta ba,
balle mutum. Abin da ya sa ka ji na yi shiru shi ne,
Aminar da kake faxa ba ta nan, tun jiya da muka sami
labarin abin da ya faru, ta zo gidan nan da Jarida
wacce ke xauke da hotonka tana kuka. Ta ce da ni, za
ta tafi Kaduna wajenka ko na san inda za ta same ka?
Na ce ma ta wallahi ban san inda za ta same ka ba,
saboda kai ma ba ka san kowa ba. Shi ne ta ce ita dai
sai ta tafi neman ka, don ta ce wai akwai gidan 'yan
uwansu a Kaduna."
"Ba ta ce dake ga inda za ta ba?" Na tambayi
Hajara.
"Nima wallahi ba ta faxa min ba."
"Shi kenan to." Na ce da ita, "Saura kuma abu
xaya don Allah Hajara idan Yaya ya dawo kar ki ce
masa na bugo waya, saboda bana son hankalinsa ya
tashi, kema kuma kar hankalinki ya tashi kin san.."
Ta katse ni da cewa.
"To yanzu Fadil ya ya za ka yi ka tsira daga
wannan sharri? Kuma ta ya ya za ka fice daga
Kaduna?"
"Babu komai." Na ce da ita "Ke dai ki taya ni da
addu'ar nasara, sai na samo wanda ya kashe Zainab
na kai wa 'yan sanda shi a hannu."
"Ta ya ya Fadil?" Hajara ta tambaya.
"Haba Hajara! Kin sanni fa, ban tava cewa zan yi
abu na kasa ba."
Hajara ta fara kuka.
"Fadil don Allah kar ka yadda su kama ka, ka ga
in sun kama ka......" Na ajiye wayar talfon xin, ba zan
iya jure kukan da Hajara take yi ba, domin zai iya
karya min zuciya, ba sai an faxa ma ba kai kanka ka
san ba na buqatar karayar zuciya a halin yanzu.
**
Motsin wani abu da ban san ko mene ne ba shi ya
tashe ni daga nannauyan barcin da na ke yi. Na tashi
firgigit saura kaxan na faxo daga kan bencin da na ke
kwance, magariba ta yi duhu ya mamaye ko'ina cikin

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

26
lambun. In ka xauke wani farin kyandir da ya
haskake qofar xakin da su Badura suka kawo ni. Na yi
mamakin yadda aka yi har bacci ya xauke ni a
lambun, tun lokacin da na dawo daga wajen talfon
nan, sai na koma xaki na sako qaramar riga na dawo
cikin lambun na fara tunanin abin da ya kamata na yi.
Shawarar da na yanke ita ce, idan dare ya yi sai na
sulale na bar gidan, tun da a lokacin duhu bana
tsammanin akwai xan sandan da zai iya kama ni.
Hanya xaya da na ga za ta fitar da ni ita ce, na je
wajen wanzami ya aske min kaina gaba xaya, na sa
kaya masu datti. Idan duhu ya qara yi sai na je tasha
na shiga motar katako irin waxanda suke safara daga
Kano zuwa Kaduna. Na san in ba tsautsayi ba da
wahala su kama ni, domin irin waxannan motoci an fi
bincikar kayan da suke xauke da shi sama da mutanen
cikinsu. Yanke shawarar ke da wuya sai na ga ina
buqatar hutu kuma ga shi inuwar dake lambun tana
da sanyi, sai kawai na kwanta.
Motsin da na ji ya ba ni tsoro, na duba sai na ga
xakin a buxe, na kuma tabbata a rufe na bar shi
lokacin da na fito. Daxin da xawa kuma sai na ga
xakin gauraye da haske, haka ne ya tabbatar min da
cewa akwai wani a cikin xakin. Nan da nan na miqe
tsaye na nufi xakin da sanxa ta hanyar voye jikina a
bayan bishiyoyi da furannin da suka yi layi a lambun,
taku ashirin daidai ya kai ni qofar xakin. Sannan sai
na tsaya cak ina sauraron wani abu da ya sa tsigar
jikina ta tashi, in dai ba kunnena ne ya faxa min qarya
ba, to na ji kamar jiniyar 'yan sanda, kafin na qarasa
tunani tuni duk zagayen unguwar da lambun ya ke ta
gauraye da kukan jiniya ko'ina, kudu da yamma har
da arewa, ba ka jin komai sai kukan jiniyar 'yan
sanda, ba tare da sanin haqiqanin abin da zan yi ba sai
na xare wata bishiya dake qofar xakin na hau can
samanta na miqe tsaye ina hangen bayan lambun.
Ta faru-ta-qare, na ce cikin zuciyata, abin da na
hango ya kaxa hantar cikina, 'yan sanda sun zagaye
lambun kamar qasa, a halin yanzu kukan jiniyar ya yi
sauqi, ba ka jin komai sai qwat-qwat xin gudun 'yan
sanda. A iya hangena ina iya ganin kudu, arewa da
yamma, amma ba na iya ganin gabas saboda manyan
benayen da suka yi shinge a bayan lambun ta
vangaren gabas da suka zagaye lambun.
Qarar bindiga ya cika min kunne, ina tsammanin
'yan daxi-bindiga ne suke gargaxina da cewa sun zo,
harsashi ya daki gilas xin tagar xakin dake qasa na,
wani raxaxin zafi ya mamaye hannuna na dama, dake
riqe da reshen bishiyar da na ke kai. Na shafa sai na ji
danshi a hannuna, raina ya vaci da na tuna da
Badura, duk abin da aka yi min ita ta janyo min, kada
ka yi tsammanin zan tsaya su kama ni kamar mace, ni
ma fa ba qaramin shaixani ba ne idan aka takura min,
duk da yake na san ko wanene kai dole ne ka tsorata,
in dai har ka ga yawan 'yan sandan da suke jirana a
waje.
Tunanin Badura ya sake faxo min in dai akwai
yadda zan yi dole ne na yi qoqarin tsere wa
'yansandan nan ko ta halin qaqa, ina so a ce koda sun
kama ni. To ya zama na rama abin da Badura ta yi
min, na tashi tsaye na hangi cikin lambun sai na ga
kamar 'yan sandan sun fara shigowa, ga wanda bai
san me ake kira yaqi ba, idan ya ga yawan 'yan
sandan da suke jira na sai ya yi zaton wannan shi ne
farkon yaqin duniya na uku. Ba tare da na sake tunani
sau biyu ba, sai na saki reshen bishiyar na yi qasa, na

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

27
tabbata kowane ne ke cikin xakin ba xan sanda ba ne,
ya kuma zama dole na ga kowanne ne kafin na yi
shirin gudu. Abu xaya da ya ke ba ni qwarin gwiwa
shi ne 'yan sanda ba za su matso kusa da ni cikin
gaggawa ba, domin suna tsammanin ina da bindiga.
Na daki qofar xakin da qafa ta buxe na shiga ina
dube-dube banga kowa ba, qofar wani xaki da ke
fuskantata a buxe take, na nufi qofar da sanxa, tun
kafin na qarasa sai na ji kamar mutum ne ke
numfashi sama-sama a xakin, na tura qofar a hankali
na shiga.
Tana kwance a gadon da suka xaure ni, tasha
xauri da igiya kamar damin gero tana numfashi
xaixai, jajayen kayan da ta zo da su xakina a Otal xin
Daba, sune ke jikinta, sai dai yanzu duk sun yayyage,
alamun ta sha wuya a wajena.
Muka yi ido biyu da Badura, sai ta yi min
murmushi.
"Ina fatan yanzu ka gane abin da nake nufi da
kibiyar ajali?" Ta ce da ni. "Abin kawai da ya rage
yanzu shi ne, su zo su same ni a nan kwance, shi kenan
kai kuma ka zo hannu."
"Kina nufin ki ce za su yarda da cewa ni na xaure
ki?" Na ce da ita.
"Ba sai an faxa musu ba, shin mene ne amfanin
Jaridar da na ba ka? A tsammanin su, ka yi niyyar
kashe ni ne kenan. Ba ka da mafita,
End Ads