x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 14 - KIBIYAR AJALI

  • 39001 words
  • 42000 words
  • Out of 49194 words

Category: Love Stories

Views 528

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads

ki ka yi wasa da hankalina." Sannan ya ci gaba da
cewa "Sai na nuna miki iyakarki." Idan har Badura ta
xago ta kalle shi, to dutse ma zai iya kallon ka idan
kayi masa magana, take totur xin motar gaba xaya,
ruwan sama da ake yi kuma ya wuce yayyafi a halin
yanzu domin tuni gaban gilas xin motar ya jiqe, da
qyar Badura take ganin gabanta. Irin gudun da
Badura ke sheqawa shi yasa fuskar xan sandan ta
canza, cikin lokaci qanqani sai duk kamanninsa suka

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

69
sauya. Idanunsa suka firfito saboda tsoro da fargaba,
ya juyo ya kalle ni sannan ya juya ya kalli Badura
wacce tuni ta yiwa Kano nisa, ni kaina ban san ko
hanyar ina take bi da mu ba, ruwan saman da ake
sheqawa da kuma duhun daren su suka haxu suka
juyar min da qwaqwalwa, daxin daxawa kuma ga
ciwon dake hannuna shima ya tsananta.
"Tsaya na sauka don Allah." Xan sandan ya ce
cikin tsoro da fargaba. "Don Allah ki tsaya na sauka,
wallahi na tuba." Duk da yake hannuna na raxaxin
zafi hakan bai hanani yin murmushi ba, na yi qoqarin
yin dariya amma na kasa. Xan sandan ya yi mutuqar
bani dariya, wanda ke buga mana tsawa sai gashi yana
magiya.
"Ina za ki damu?" Xan sandan ya sake tambaya
cikin rawar murya.
"Inda ba zamu dawo ba." Badura ta ce dashi, a
daidai lokacin ne akayi wata tsawa mai qarfi, wacce
tasa motar mu ta girgiza, saura kaxan mutuqin motar
ya qwace daga hannunta, aka yi walqiya hakan shi ya
sani ganin fuskar Xan Sandan wacce ta haxe sharkaf
da gumi, gashin bakinsa sai xiga yake da gumi,
fuskarsa kuma ta koma launin gasasshen nama.
"Ka nuna min kai xan sanda ne." Badura ta ce
dashi. "Mene ne amfanin bindigar dake hannunka.?"
Ta tambaye shi tana murmushi. "Ko ka xauka ina
tsoron zungureriyar bindigar ka ne?"
"Zan kuwa nuna miki ni xan sandan ne." Xan
sandan ya xaga bindigarsa ya yi saitin kan Badura, na
rufe idona cikina na rawa cikin 'yan daqiqun da abin
ya faru, na xauka harbawa zai yi don haka sai nayi
kalmar shahada, na kuma runtse idanuna, ina jiran na
ji qarar bindiga. Abu xaya na tabbatarwa kaina,
nasan in har ya harbi badura, a cikin irin wannan
gudun da take da motar, to muma rayuwarmu tazo
qarshe kenan, hakan shi yasa wani irin sassanyan
gumi varkowa daga goshina zuwa kan fuskata. Na ci
gaba da kalmar shahada domin na tabbata mu tamu
tazo qarshe, tuni har zuciyata ta fara ayyanawa, wai
gani nan na mutu, an xauko ni a makara an nufi
maqabarta dani.
Minti guda ya shuxe ban ji qarar bindiga ba, ban
kuma ji motar ta hantsilar damu ba, don haka sai na
buxe idanuna domin naga abin da ke faruwa, ga
mamakina sai naga xan sandan ya maida bindigar,
hannayensa na rawa.
"Ka harba mana tsoron me ka ke ji 'yallavai.?"
Badura kenan take cewa cikin zazzaqar muryarta da
ba zan tava mantawa da ita ba. "Ka tuna fa kai namiji
ne, a cikin mazan ma kuma wai xan sanda." Tunda
nake ban tava ganin mace marar tsoro kamar Badura
ba. Na duba irin ruwan da ake tafkawa gami da iska
amma duk wannan bata sa ta rage gudun da take yi
da motar ba, maimakon hakan sai ta qara take totur
xin motar gaba xaya. Xan sandan dake zaune a gaban
motar ya zama kamar mutum-mutumi, ba ya ko motsi
saboda tsoron abin dake shirin faruwa, idonsa akan
sitiyarin motar, ya buxa baki kamar zai yi magana sai
ya yi shiru babu mamaki gani ya yi maganar tasa ma
ba za ta yi tasiri ba, xan sandan ya lumshe idanunsa,
hakan shi ya bani damar tunanin cewa babu mamaki
addu'a yake yi, can sai ya nisa ya ce da Badura.
"Ya kamata ki san abin da kike yi, ba ki san
wannan gudun da kike yi halaka zai kaimu gaba xaya
ba."

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

70
"Ina tsammanin halakar ita tafi dacewa damu."
Badura ta ce dashi idonta akan titin da muke bi.
"Xazun nan fa kake shirin kai masoyina ga halaka,
kasan kuwa in har ina numfashi a bayan qasa, babu
wanda ya isa ya hala min saurayi...."
"Wa ya ce zai hallaka shi?" Xan sandan ya ce
muryarsa na rawa, lokaci-lokaci kuma yakan kalli
malejin motar, wanda tuni an qure shi har qarshe.
"Laifi ne ake zarginsa dashi, don haka dole ne na
kama shi tunda na ganshi, ba laifina ba ne wallahi
'yanmata, don Allah ki tsaya na sauka." Ya fara
magiya.
"Kada kayi min magiya." Badura ta ce dashi, "ai
kasan cewa idan ka kai shi hannun mutananku
hukuncin kisa za a yanke masa amma ba ka damu ba
da rayuwarsa. Sai yanzu ne kuma kake tsammanin
zan damu da rayuwarka?" Sannan ta ci gaba da cewa
"Rayuwa bata da amfani a gare ni, in har na bari aka
hallaka min rabin rayuwata, akan laifin da ba shi ya
aikata ba, wallahi na gwammace ni na salwantar da
tawa rayuwar akansa." Sannan ta dubi xan sandan da
kyau, ta ce dashi "Mahaifiyata da kuma taimakona, su
suka jefa laifin kisan kan da ba shi ya yi ba akansa,
ina son ka zama shaida kaima." ta ce da xan sandan,
duk da yake kuma lokaci-lokaci motar takan xan
kufce daga hannunta, amma hakan bai hanata ci gaba
da maganar ba, ni kuma ban daina yin addu'a ba,
domin ni a tsammanina kowanne lokaci xan sandan na
iya yin fushi yayi qoqarin hana Badura tuqin, sannan
kuma sauran abin da zai biyo baya ba sai an bayyana
ba.
"Na maimaita, na sake maimaitawa da ace Fadil
ya halaka gara ni na halaka a hanyar kare tasa
rayuwar." Badura ta ce, "Don haka nayi niyyar tserar
da shi, daga sharrin da aka yi masa ban kuma ga
wanda ya isa ya hanani tserar dashi xin ba, sai ko
Ubangii mahalicci, amma ba dai mutum ba ko aljan,
ko kuma mutanenku 'yan sandan." Ta ce da xan
sandan cikin sassanyar murya. har yanzu xan sandan
bai ce komai ba, a tunanina bana jin yana saurarar
abin da take cewa ma, babu mamaki shi tunanin
hanyar da zai tsira da rayuwarsa yake, domin gudun
da Badura take ya wuce qima, nima kuma abin ya
fara bani tsoro.
"Ya kamata ki xan saurara haka Badura." na ce
da ita a karo na farko tun loka cin da muka baro cikin
garin Kano.
"Haba masoyina!" Ta ce dani "Baka ganin idan
muka tsaya anan ritsamu zai sake yi da bindigarsa ya
kama ka? Ni ban damu da kaina ba Fadil, inda dan
tani ce, to da sai na barshi ya tafi dani, amma kai a'a,
ba zai tava yiwuwa ba, in dai kaga har na tsaya ya
sauka, to sai ya yarda da sharuxaina guda biyu." Ta
dubi Xan sandan.
"Waxanne sharuxai ne? Faxi na ji, wallahi zan
cikasu in har za ki sauke ni."
"Sharaxin farko shi ne, ka jefa bindigarka ta tagar
motar nan, na biyu kuma shi ne ka koma bayan motar
ka kuncewa Fadil ankwar dake hannunsa."
"Na yarda." Xan sandan ya ce, nan da nan ya
sauke gilas xin motar ya jefa bindigar qasa, ta bada
wata irin qara lokacin da ta haxu da kwalta, sannan
sassanyar iska haxe da ruwa, suka feso cikin motar
saboda tagar motar da xansandan ya buxe, nan da nan
ya yi sauri ya rufe sannan ya juyo ta tsakanin kujerun
gaban motar ya ce "miqo hannunka."

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

71
Ban sami damar miqa masa hannun ba, saboda
abin da na hango. A gigice a tsakiyar titin muke bi,
wani gungumeman reshen bishiya ne, wanda kuma
cikin daqiqar da na ganshi qwaqwalwata ta sanar dani
cewa 'yan fashi ne suka gindaya shi. Na yi mamakin
ganin Badura bata ko rage gudu ba.
"Kalli gabanki!" Na ce da ita cikin qaraci,
Xansandan ya rufe idonsa, jikinsa na rawa. Badura ta
take birkin motar ta yi quli-qulin kubura damu, abu
na qarshe da na ji shi ne qarar Xan sandan nan cikin
gigita, a lokacinne aka yi jifa dani waje ta cikin gilas
xin motar.










14
a farka a gigice, sakamakon sassanyar ruwan
sanyin da aka kwara min a fuska. Ban san abin
da ya faru gare mu ba tun bayan lokacin da muka yi
haxarin, na yi qoqarin buxe idanuna amma abin ya
gagara. Matsanancin ciwon kan dake addabata, shi
yake barazanar raba kaina gida biyu a duk lokacin da
na yi qoqarin buxe idona.
Na fara qoqarin tunanin abin da ya faru a kanmu,
koda yake ban cimma nasara ba, qwaqwalwata ta
daina tunanin komai sai juyawa kawai take yi kamar
yadda hannun agogo manunin daqiqa ke juyawa.
Duk wannan bai tashi hankalina sosai ba, sai
bayan da na yi qoqarin xago hannayena domin na riqe
kaina wanda ke barazanar rabewa saboda tsananin
ciwo, gabana ya faxi da na ji hannayena a xaure suke
tamau a bayana. A lokacin wato qwaqwalwata ta fara
tunani sosai, na gane cewa haxari muka yi amma daga
nan ban iya tuna komai ba. Hakan shi ya tabbatar
min da cewa suma na yi, to idan suma na yi ina
Badura? Kuma a ina muke? Na tambayi kaina, kamar
amsar tambayata sai aka zungure min quguna da
wani abu mai tsini, wanda tuni zuciyata ta ayyana min
cewa mashi ne, sai bayan da na buxe idanuna ne sanan
na gane na yi kuskure.
Yana tsaye a kaina, xan qarere ne, wanda ganinsa
ya tuna min da Barbushe wanda na tava karanta
labarinsa a cikin (Kano ta Dabo ci gari), yana da
jajayen idanuwa, kansa shan qwalan qafa ne, a kuma
aske yake tas yana qyalli kamar madubi, ga
mamakina sai naga idonsa fari tas kamar madara,
savanin guntun ire-iren su waxanda su idonsu jajur
yake kamar garwashin wuta, voye kamanninsa masu
firgitarwa ba abin kawai da zan iya cewa sun qara
masa, shi ne sun fito da kamanninsa. Irin na kumurcin
maciji, kada ka ji anje idanunsa farare ne, ka xauka
kuma wai manya ne masu kyan gani, savanin haka shi
na sa qanana ne, kamar da reza aka yankasu. Yana
sanye da wando da riga baqaqe, tafkeken sawunsa
N

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

72
kuma sanye cikin takalmin qarfe, irin wanda Kafiran
da can suka yi yaqi dashi. Hakan shi ya tabbatar min
kuskurena a fili na tunanin wai da mashi aka soke ni.
Na dube shi babu alamar murmushi a fuskarsa,
murtuk yake kamar wanda aka sanar dashi adadin
kwanakinsa a duniya, na duba izuwa vangarena na
hagun, a nanne to na hango Badura akan kujera suka
zaunar da ita suka kuma haxata da kujerar suka
xaure, muka yi ido huxu da ita, idonta ya cicciko da
qwalla abin mamaki kuma shi ne, daga ni har ita babu
wanda ya yi koda qwarzane daga haxarin da ya faru
akanmu. Sannan ne to na tuna da cewa babu mamaki
ya mutu a sakamakon haxarin da ya faru. A karo na
biyu sai na sake gane kuskurena, ban qarashe tunani
na ba sai qofar xakin ta buxe, su uku ne suka shigo
xakin xauke da xan sandan suma danqara-danqara
ne, koda yake bana jin idan an haxa su duka ukun
zasu kai girman shugabansu.
Suka shigo xakin a hankali, sai dai kuma
kowannensu yana muzurai, suna zuwa sai suka yi jifa
da Xansandan ya gangaro ta matattakalar da fuska a
kan tsandaurin kataki, haxe da qarar data razanani.
Zaka yi mamakin jin cewa ina ta magana akan katako
amma nasan ba ka gane abin da nake nufi ba, to bari
na baka hoton yadda xakin da muke ciki yake a
bayyane. Da farko dai xan iya cewa bangon xakin da
kuma qasan xakin duk da katako aka gina shi,
tangameman xaki ne wanda ke da taga xaya da qofa
xaya, sai dai shi qofarsa da tagarsa ba xaya take da ta
sauran xakunan ba da ka sani, shi wannan xaki
tagarsa da qofar a sama suke, don haka ko su 'yan
fashin sai ta hanyar amfani da matattakala irin ta
bene suke shiga xakin. Hakan shi ya sani tunanin to
idan ana ruwan sama ya ya zasu yi kenan? Nasan dole
ne ruwa ya cika xakin, koda yake kuma banga alamar
zubar ruwan sama a xakin ba. In ka xauke wasu 'yan
tarkacen kayayyaki dake kusa da Badura duk sararin
xakin babu komai sai wasu kujerun katako guda uku,
biyu daga cikinsu a kakkarye suke, mai xan kyan daga
cikinsu ita ce mai qafa xaya.
Faffaxan bakinsa mai kama da saran adda ya
faxaxa izuwa abin da shi yake tunanin wai murmushi
ne, sannan ne na gane cewa ashe ba shi da haqoran
gaba guda uku, wawilon dake bakinsa shi ya tuna min
da bakin qadangare.
"Ka yi mamakin ganinka anan ko?" Ya tambaye
ni yana kallona tsigar jikina tayi yarr!! Ko kaxan
bana son murmushinsa.
"Ni ne (Dawaye)." Ya ce dani "Sana'ata kuma shi
ne fashi da makami, abin da na fi qauna a duniya
kuma shi ne na qwace kayan da ba halak xina ba."
Sannan ya qyalqyale da dariyar mugunta. Kukan Jaki
ya fi dariyarsa daxin ji, na dubi badura, jikinta na
rawa kamar mazari, xan sandan kuma da suka jefo na
kwance jini na fita ta baki ta hanci, haqiqa yana cikin
matsananciyar azaba, kuma na tausaya masa.
"Na yi farin ciki da kamaku." Xan fashin ya ce
dani yana murmushin mugunta. "Duk da yake kuwa
bamu sami komai a gurinku ba, amma a qalla mun
kama maqiyanmu." Ya nuna xan sandan da takalmin
qarfansa mai tsini. "Maqiyinmu ne." Xan Fashin ya ce
dani "Ku ne kawai da kuke neman halak kuke
tunanin masoyan kune, amma a zahiri maqiyanku ne
tunda yanzu ma babu mamaki yana shirin qulla muku
sharri ne."

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

73
Maganar dake fitowa daga bakinsa babu kai ba
gindi su suka sa na fara tunanin ko mahaukaci ne,
domin a gurina xan sanda ba maqiyina ba ne, duk da
yake kuwa suna nan babu adadi suna farautata, nasan
cika aikinsu suke yi rashin sani ne kawai yasa suka
kasa gane gaskiya.
"Kamar yadda suke kama mu suna harbewa, haka
muma idan mun kama su ba za mu yi musu ta daxi ba.
Zamu kashe duk wanda yazo hannunmu a cikinsu,
har da abokin tafiyarku." Ya nuna Xan sandan dake
kwance maganar ta yi mutuqar girgiza ni na kuma
zargi Badura cikin zuciyata. Saboda ita ta yi
sanadiyyar kawo shi ga halaka, duk da yake kuwa ni
take qoqarin tserarwa. A can ma xaya vangaren
Badura na ta zubar da qwalla jin cewa za a kashe xan
sandan nan shi yasa jikinta ya sake xaukar rawa.
"Kada ka damu.'' Xan fashin ya ce dani yana
dubana, "ba zamu kashe ka ba, amma zamu mai da
kai yaronmu. Ita kuma 'yar uwarka mai dafa mana
abinci." Sannan ya sake qyalqyalewa da dariyar
mugunta. "Babu mamaki gobe zamu kashe
maqiyinmu." Ya nuna xansandan, ''ba kuma kisan
bindiga zamu yi masa ba, kisan da zamu yi masa ba na
falan xaya ne ba." Sannan Xan Fashin ya sunkuyo
inda nake kwance, yana zazzare idanu. Daga inda
yake ina iya jin hucinsa kamar giwa.
"Da a yi maka irin kisan da zamu yi masa xan
samari." Ya ce dani, "gara a harbe ka da kibiyar
Aljali ka mutu lokaci guda. Sannan ya sake dosaro
gashin bakinsa kusa da fuskata, kasan irin kisan da
zamu yi masa?" Ya tambaye ni, ban amsa ba, ni ko
motsi bana iya yi don razana. "Da farko zamu yanke
kunnuwansa xaya bayan xaya sannan mu yanke
hancinsa, za kuma mu datsa hannunsa na dama da
kuma na hagun sannan kafaxunsa da haka zamu
kashe shi." Badura ta qwalla kukan razana, da
maganar da ya yi, xaya daga cikin yaran da suke a
tsaye a bayansa ya matsa gaba ya falleta da mari, har
sai da kanta ya yi baya. Xakin ya yi shiru na xan
lokaci, ba ka jin komai sai hucin qaton shugaban 'yan
Fashin nan, sannan ya dube ni ya ce da ni "ka yi mata
nasiha xan samari, idan ta sake yi mana kuka a nan
itama haka zamu kashe ta." Ban san lokacin da na
sami kaina ina amsa masa ba.

**
Idan ka xauke shesshekar kukan Badura, da kuma
numfashin xan sandan nan da ke kwance babu motsin
komai a xakin. Minti biyar kenan da ficewar 'yan
Fashin, ba su kuma fice daga xakin ba sai da nima
wani daga cikinsu ya falla min mari.
Dole ne na san yadda za a yi na tserar da rayuwar
xan sandan nan, koda kuwa idan na
End Ads