x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 16 - KIBIYAR AJALI

  • 45001 words
  • 48000 words
  • Out of 49194 words

Category: Love Stories

Views 529

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
Tuni sauran 'yan fashin sun

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

79
shige cikin xakin nan mai qofar sama, xayan da aka
harbe ne kawai ya rage bai shige ba yana saman qofar
ya zura qafarsa ta dama zai shige sai wani Kurtun xan
sanda ya hango shi sannan ya xaga bindigarsa a
hankali ya ja kunamar. Qarar bindigar ta yi amsa
kuwwa a cikin dajin, xan fashin ya yi taga-taga ya
faxa da fuska cikin xakin, duk da yake banga sauran
abin da ya faru gare shi ba, nasan cewa ya mutu, babu
wanda za a yi wa harbi uku xaya a hannu, wani a baya
sannan a qirji sannan ya rayu, zai yi wuya.

**
Baka jin komai a sararin dajin sai amsa kuwwar
qarar bindigogin 'yan sanda da 'yan fashi, suna ta
musayar wuta, wani xan siririn xan sanda fari wanda
nake tunanin bai daxe da shiga aikin ba, ya fito daga
mavoyarsa, ya buxewa xakin 'yan fashin wuta cikin
lokaci qanqani ya yi wa wani vangare na xakin
katakon kaca-kaca. Danqararen xan fashin ya leqo a
hankali ta wajen da xan sandan nan ya yi wa kaca-
kaca lokacin da ya leqo xan sandan na qoqarin lodawa
bindigarsa alburusai, abin ka da sabon shiga,
maimakon ya sunkuya a mavoyarsa, sai ya tsaya
qerere a tsaye shi a zatonsa 'yan fashin sun tsorata ne,
don haka suka daina harbi. Xan fashin ya saita kan
xan sandan sannan ya ja kunamar bindigarsa, xan
sandan ya yi sama ya faxo sannan cikin abin da bai
wuce daqiqa biyar ba jini ya rufe fuskarsa bai ko
shura ba. Ina jin lokacin da xan sandan dake kusa da
ni ya riqe numfashinsa cikin razana, shima ya ga abin
da ya faru. Badura na gefe guda tana kuka.
"Ya kamata na fita na taimaka musu." Xan
sandan ya ce dani.
"Kana jin zaka iya yin abin da ya gagari mutum
ashirin?" Na tambaye shi.
"Ba zan iya ba." Ya ce dani, "Kuma ba zan iya
tsaiwa a nan ba ina ji ina gani suna kashe mana 'yan
uwa, don me yasa ake biyana?" Kafin na yi qoqarin
yin wani abu tuni xan sandan ya banke ni, ya buxe
qofar ya fita, lokacin da ya banke ni sai na yi sauri na
kai idona wajen 'yar kafar dake jikin qofar domin
leqen abin da xan sandan zai yi, bai yi cikakken taku
biyu ba, sai ga kan xan fashin nan ya leqo, sannan kan
bindigarsa ya leqo.
"Zai harbe ka." Na gargaxe shi cikin qaraji, amma
na makaro, qarar bindigar xan fashin ta sake ratsa
sararin dajin, xan sandan ya yi taku biyu gaba sannan
ya faxi da baya bai ko shura ba.
Jin na qwallawa xan sandan kira shi ya sa Badura
ta nufi inda nake leqe ita ma ta leqa akan idonta aka
harbe shi.
"Fadil!" Ta kira sunana tana kuka "Don Allah ka
yi min wani abu mana, ina tunanin kuma abin shi ne
zai zama na qarshe."
"Mene ne?" Na tambaye ta cikin mamaki da
tausayin halin da ta shiga. "Faxi mana Badura, bana
son naga kina kuka, wallahi kukanki shi yake daxa
karya min zuciya." Ina son na ji wata kalma xaya ta
fito daga bakinka Fadil." Ta ce da ni.
"Wacce kalma ce?" Na tambaye ta.
"Ina son ka ce kana qaunata da bakinka, sannan
kuma ina son ka ce ka yafe min duk abin da na yi
maka a baya, don Allah Fadil ka taimake ni ka faxa
kar ka bari na mutu da ciwon sonka ban samu cikar
burina ba."

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

80
"Haba Badura, ki daina faxin haka, wa ya ce za ki
mutu? Na yafe miki Badura." Na ce da ita, "na kuma
gane cewa ba laifinki ba ne, laifin mahaifiyarki ce,
baki da laifi a gurina Badura har abada, ina roqon
Ubangiji kuma ya tserar damu masoyiyata, na yarda
da qaunar da kike yi min Badura, tunda ki ka
sadaukar da rayuwarki gurin ganin kin tserar da ni,
ina son ki Badura, ina sonki. Ke ce abar begena har
abada rabin rayuwata."
Badura ta yi ajiyar zuciya, bayanta yana fuskantar
qofar xakin, ni kuma bayana yana fuskantar cikin
xakin kowannenmu yana kallon abin qaunarsa,
soyayyar Badura ta motsa cikin zuciyata, sannan na
dube ta, sai ta sunkuyar da kai tana zubar da qwalla,
ban san ko kukan farin ciki ba ne ko kuma baqin ciki
ba.
"Fadil....!" Ta kira sunana cikin sassanyar
muryarta mai xaukan hankalin ma'abocin bege,
muryar da ba zan tava mantawa da ita ba ce har
abada a rayuwata bata qarasa faxar kalamin dake
bakinta ba, sai 'yansandan da ke waje suka buxewa
qofar xakin da muke ciki wuta. Babu mamaki
gargaxin xan sandan nan da na yi shi ya sa suka san
da wasu a cikin xakin, harbin kuma shi ya shuka
baqin ciki marar misaltuwa a cikin rayuwata a duk
lokacin da na tuna da mutuwar Badura sai na yi ta
zubar da hawaye, ruwan harasashin bindigogin 'yan
sandan, duk a bayan Badura suka sami matsu gunni,
ta qwalla qara sannan ta faxo qirjina.
"Wayyo Fadil! Wayyo Fadil!!....Amira! Amira..."
Sannan ta yi shiru, a haka ta mutu a jikina, ba zan
tava mantawa da ranar ba har abada.

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

81
16
ayan da suka harbe yarinyar da ta mutu tana
begena, sai suka tsaya da harbin, a zatonsu sun
gama damu gaba xaya, sannan sai na ji sun buxewa
xaya xakin 'yan fashin wuta, kasancewar qofar xakin
da muke ta zama kamar rariya saboda ruwan
albarusan da aka yi mata, sai na sami damar ganin
abin da ke faruwa. Badura rungume a jikina, ina
kuka. Ban motsa daga gurin ba, bana kuma tsoron su
sake harbi, domin ni yanzu na daina jin tsoron
mutuwa, ban damu ba na mutu koma na rayu. Sai
bayan da Badura ta mutu sannan na gane irin
matsanancin son da nake yi mata, sannan ne kuma na
gane cewa, duk da yake ita ce asalin faxawata a cikin
bala'in da ke faruwa a kaina, amma hakan bai hana
nafi sonta fiye da Amina ba, mutuwar Badura kamar
wata fitila ce aka kashe ta rayuwata.
"Fadil!!" Amsa kuwwar kalaminta da na ji a karo
na qarshe, shi yake ta kururuwa a kunnena. A koda
yaushe nakan tuna irin yadda take kiran sunanan a
duk lokacin da ta so sanar dani wani abu, don haka
tun farkon labarin nake cewa (muryar da ba zan tava
mantawa ba).
Gawar Badura a rungume a jikina ina leqe ta
qofofin da harsashi ya yiwa qofar hawaye na na
kwarara akan kumatuna. Lokacin da 'yan fashin suka
ga ruwan harsashin ya yi musu yawa, sannan suka ga
halaka qarara sai suka ruxe suka fara fitowa ta qofar
saman xakin. Yaran biyar suka fara fitowa, ba a ko
tava qasa ba aka gama da su babban su ne na qarshe,
hancin bindigarsa ne ya fara fitowa sannan varin wuta
ya biyo baya, nan da nan duk 'yan sandan suka koma
mavoyarsu suka vuya, hakan shi ya ba shi damar
fitowa fili har yanzu yana varin wuta, wani xan
gajeren xan sanda baqi kakkaura ya leqo da
bindigarsa, sannan ya harba harsashin ya wuce ta kan
xan fashin, lokaci guda kuma xan fashin ya ja
kunamar bindigarsa harsashin ya sami xan sandan a
goshi, nan take ya shure bai ko matsa ba, albarushin
kuma da ya kashe xan sandan shi ne ya zama harsashi
na qarshe a cikin bindigar xan fashin, lokacin da ya ja
kunamar bindigar sai bindigar ta qi tashi, ba a jima
ba da faruwar hakan, 'yan sandan dake voye suka
gane abin da ke faruwa. Nan da nan xan fashin ya
qwalla qara cikin razana.
"Kada ka harbe ni." Ya ce cikin qaraji, sai dai ya
xan makaro, wani Kurtun xan sanda tuni ya auna
qaffarsa, barinsa kuma yaga asara ne don haka sai ya
ja kunamar bindigarsa xan fashin ya qwalla qara mai
tsanani, duwatsu da qoramun da suka zagaye dajin
suka yi amsa kuwwa, sannan xan fashin ya faxi da
fuska, wannan shi ne ya kawo qarshen musayar wutar
da ake yi tsakanin 'yan fashin da suka kama mu da
kuma 'yan sanda. Mintuna biyu da harbe shi, sai 'yan
sanda suka fito daga mavoyarsu, suka xaure xan
fashin sannan suka buga masa ankwa a hannayensa.

**
Na ajje gawar Badura a hankali ina kuka, lokacin
'yan sandan sun fara warwartsuwa ko'ina cikin gidan.
Mene ne abin yi? Na tambayi kaina, shin bari zan yi
su kama ni, ko kluwa me ma zan yi ne? Na ce a
B

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

82
hankali muryata na rawa, sannan ne na kalli cikin
xakin sosai ga mamakina sai naga xakin yana da
tsayin gaske, da zan yi sa'a xakin yana vullewa ta cikin
wani, to da sai na bi ta nan in zurare. To idan na gudu
ma ina zani a wannan qungurmin dajin? Na tambayi
kaina. Sannan ne dabara ta faxo min, tunda
'yansandan basa tsammanin akwai wani sauran mai
rai a gidan, me zai hana na vuya a wani lungun idan
sun gama abin da za su yi sun tafi sai na fito, na san
dai da wahala ace sun tafi da motocin 'yan fashin gaba
xaya, sai dai...Tunanina ya katse a daidai lokacin ne
idona ya hango min wani teburi a can qarshen bangon
xakin, ba tebur xauki ne ya hankalina, ba abin da ban
tava sammanin zan gani ba ne a xakin naga ni, akan
teburin a ajiye a bayan mazauninsa kan talfon ne.
Haqiqa shi ne abu na qarshe da nake tsammanin zan
gani a gidan na yi mamakin abin da 'yan fashi suke yi
da talfon.
Cikin xoki da qaguwa, sai na matsa kusa da talfon
xin har na xauka, sai na tuna da cewa qofar xakin a
buxe na barta, kuma na san kowanne lokaci, daga
yanzu 'yansanda za su iya shigowa xakin, don haka sai
na koma ba tare da na dubi inda Badura take kwance
ba, bayan na rufe qofar. Sai na koma na xau kan
talfon xin sannan a karo na biyu tun sa'ar da na faxa
cikin masifar, sai na bugawa yayana waya.
"Wane ne?" Aka tambaya a can xaya vangaren
gabana ya faxi da na ji muryar Yayana ce da kansa.
"Ni ne Fadil." Na ce da shi, muryata na rawa.
"Fadil!" Yayana ya kira sunana muryarsa na
rawa.
"A ina kake?" Ya tambaye ni, "me kuma ke
faruwa.?" Ba tare da vata lokaci ba sai na bayyana
masa duk abin da ya faru a gurguje tun daga farko
har qarshen, sannan na ce da shi ga halin da nake ciki,
kuma Badura ma gata nan a gabana, sun harbeta,
yayana ya yi shiru sannan ya ce da ni. "Saurara da
kyau Fadil! Da farko ina son in yi maka albishir da
cewa, ka kusan fita daga sharrin da aka yi maka."
Ban gaskata abin da naji ba.
"Me kake nufi?" Na tambaye shi.
"Kwana biyu kenan yau da kama Hajiya Binta,
mahaifiyar su Badura, sannan Salman ma an kama
shi dukkan su tare da xan tsohon nan ma'aikacin
Durba otel."
"Amira fa?" Na tambaye shi cikin xoki.
"Amira bata da laifin komai ita da 'yar'uwarta
Badura."
"Ya ya aka yi aka gane ba su da laifi?"
"Ranar Talata xin nan da ta wuce wasu Jami'an
bincike na 'yansanda ciki dake aiki a Daba Otal
Kaduna, suka zo da shaidar da take nuna cewa Hajiya
Binta ita ce ta yi ummul'aba'isin faruwar komai,
sannan abin mamaki ma shi ne ita wannan yarinyar
ba a cikin otal xin aka kashe ta ba, saceta aka yi ta
hanyar haxa baki da xan tsohon nan mai aiki a otal
xin, bayan da suka kasheta ne suka shigo da ita cikin
dare tare da taimakon xan tsohon nan suka kwantar
da ita akan gadon, da ka tarar da ita. Lokacin da ka je
xakin mai lamba (3), daman kusan abin a shirye
yake..."
"Kana nufin ka ce ba a cikin otal xin aka kashe ta
ba?" Na tambaye shi.
"Ko kusa ba a ciki ba ne, kasan fa irin matakan
tsaron da ke otal xin ba zaka tava yin wani abu na
rashin gaskiya ba, ba tare da an kama ka ba, ita ma

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

83
wannan bindigar xan tsohon ne ya shiga da ita, saboda
hanyar da ma'aikatan otal xin suke bi babu na'ura
mai qwaqwalwa, wadda kuma ita ce take nuna duk
wani abu da mutum ya shiga da shi otal xin, saboda
haka xan tsohon nan shi ya shigarwa da Hajiya Binta
da bindigar ciki ita kuma ta shigo ta hanyar da kowa
ke shiga ta kama xaki a hawan benen na uku, shi ne ta
bari sai da asuba ta hayo hawan benen ku ta harba
bindigar domin ta saka ka fito ka kuma faxa
tarkonsu."
Na yi shiru cikin mamaki "To ta yaya aka yi ku ka
san wannan?" Na sake tambaya.
"Su Jami'an tsaron otal xin suna da wata na'ura
mai qwaqwalwa wacce take xaukar duk wani abu da
yake faruwa a otal xin, ko waya aka bugo sai ta xauka,
ba kuma a binciken abin da ta xauka sai qarshen
wata, to a irin binciken ne aka gane duk irin makircin
da aka shirya, hatta ita Badura da Amira duk xakinsu
xaya a nan otal xin da kake zaune, shi ma Salman a
nan Hajiya Binta ta kama masa xaki, don haka duk
lokacin da zasu tattauna, sai Hajiya Binta ta tara su a
xakinta, sai dai kuskuren da ta yi bata san da wannan
na'ura mai qwaqwalwa ba, wacce duk abin da suka
tattauna yana cikinta. Ka ga ke nan bana jin akwai
sauran wani abu da zaka ji tsoro."
"To 'yansandan da suka ritsa ni a nan yaya zan yi
da su?"
"Za mu bugo masu waya yanzu, tunda suna da
salula, sai mu sanar da su abin da ake ciki, sannan
wani abin kuma." Yayana ya ci gaba da cewa "tare
muke da Kanal Muktar yanzun nan ya zo domin bai
daxe da zuwa ba, ka bugo waya shima yazo akan
maganar ku da Amina da kuma yadda za a yi a tserar
da kai, to ina yi masa wannan bayanin da na yi maka
ne ka bugo waya yanzu ma gashi nan a kusa da ni."
Sannan ya xan yi shiru.
"Fadil ina Jakarka take?" Ya tambaye ni, gabana
ya faxi sai yanzu na tuna da Jakata da yayana ya bani
na yi shiru ina tunanin inda na yarda ita.
"Na manta inda...." Ya katse ni kafin in qarasa.
"Shi kenan." Yayana ya ce dani, ta cikin talfon
xin.
"Jiya muka tsince ta a cikin motar da ku ka yi
haxari, wataqila zaka so ka ji amfanin baka ita da na
yi, to dalilinta shi ne a qasanta akwai wata 'yar
qaramar rikoda mai xauke da maganganu, sanin
yaudarar masu aikata muggan laifuka ne, yasa na
baka ita saboda tun lokacin da na hanaka tafiya ka
nace sai ka tafi sai na ga ya dace na baka ita, domin na
yi tunanin wani abu sakamakon haka zai iya faruwa a
kanka, domin su daman yawancin mutane irin su
Hajiya Binta sun fi yaudarar 'yan yara samari kamar
ka, kuma jakar tana da muhimmanci domin tana xaya
daga cikin abin da zai fitar da a kotu kuma duk
maganar da kuka yi da Badura, Hajiya Binta da
Amira da kuma Salman duk suna ciki. Wannan ma
shaida ce da zata iya fitar da kai, daga qarshe bana
son na barka cikin duhu ita wannan jaka ta
'yansandan ciki ce (C.I.D)." Ya ce dani
"Kana nufin kace kai (C.I.D) ne Yaya?"
"Bana son irin waxannan maganganun ta talfon."
Ya ce dani. Abin ya yi matuqar girgiza ni, duk da yake
bai faxa min da bakinsa ba na tabbata Yayana xan
sandan ciki ne (C.I.D). Tav! abin da mamaki.
"GA shi nan Kanal Muktar yana buga musu
waya." Muryar yayana ta sake ratso talfon xin.

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

84
Mintuna biyar da yin magana da yayana ta talfon sai
abubuwa suka sake juyewa, a wannan karon daga
baqin ciki da quntata, zuwa farin ciki abin kawai da
ya rage farin cikin shi ne mutuwar masoyiyata
Badura. Aka qwanqwasa qofar xakin, ban yi fargabar
komai ba sai kawai na buxe, domin nasan su Yayana
sun gama aiki. Xansandan yana tsaye sauran
'yansandan kuma a bayansa.
"Zo mu tafi." Ya ce da ni, na juya na yi wa Badura
kallon qarshe, tana kwance lallausan
End Ads