x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - KIBIYAR AJALI

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 49194 words

Category: Love Stories

Views 517

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
ba?"
Na tambaya "lafiya kuma na gan ki haka cikin
wannan lokacin?" Ta yi ajiyar zuciya sannan ta xago
kai muka haxa ido "Wallahi Fadil wani abu ne ya ke
bani tsoro." Ta ce da ni "Tun jiya da safe wani mutum
yake ta bina a baya a baya, duk inda na yi sai ya bini.
Da farko na yi qoqarin vace masa amma na kasa, sai
na haqura na qyale shi na xauka irin samarin nan ne
masu bin 'yanmata a gindi. To sai kuma jiya muna
zaune a lambun nan, na gan shi yana ta kallonka yana
muzurai, na yi niyyar na faxa maka sai tsoro ya
hanani. Shi ne na ce maka zan tafi, kaga idan na tafi
sai ya bini domin ba na son abin da zai tayar maka da
hankali."
"Kamar yaya yake?" Na tambaya cikin mamaki.
"Baqi ne, dogo, kakkaura, yana sanye da koriyar
riga da farin wando." Tsoro ya kama ni cikina ya
kaxa. Tun sa'ar da ta fara bani labarin sai yanzu ne na
gane abin da take nufi, mutumin kenan da ya zo
nemana ba na nan shi ne kuma yake bin Badura.
"Bayan wannan fa? Shi ya hana ki zuwa wajena?"
Na tambaya.
"A'a, ba hana ni ya yi ba, ni ce dai na hana kaina,
domin bana so in jefa ka a cikin bala'i, gara in wani
abu ne ma ya same ni ni kaxai." Na tashi na matsa
kusa da ita, na qura mata ido.
"Kada ki ce haka." Na ce da ita "Ni masoyinki ne,
ki faxa min duk abin dake damunki, gobe zan yi
maganinsa." Abin da nake faxa ni ma kaina ya bani
mamaki, domin maganar da ta yi ta daxa tabbatar
min da qaunar da take yi min.
"Jiya da daddare..." Ta ci gaba da cewa "Na gan
shi ya zo otel xin nan a wata mota qirar Alfa Romiyo,
amma bai shigo ciki ba daga waje ya aje motar ya
shigo da qafa, da na ga haka sai na yi sauri na rufe
xakina ina leqensa ta tagar xakin.
Yana nan yana ta dube-dube har sha xayan dare,
da na ga haka sai na kulle tagar xakina na yi kwance.
To sai kuma can dare na ji ana ta tava min qofar xaki,
amma idan na leqa sai na rasa kowa, da haka dai har
gari ya waye. Da yamma tayi yau kenan, na yi shiri
domin na same ka a lambu, sai na ganshi kuma a
hawa na xaya na benen nan, yana jira na na fito don
haka sai na yi zamana har dare ya yi ban fito ba, shi
ne yasa ma kaga ban zo ba wajenka."
"A wanne xaki ki ke?" Na tambaye ta.
"Xaki mai lamba uku." Na yi mamaki don jin
cewa xakinta a kusa da nawa yake amma ban sani ba,
xaki mai lamba huxu shi ne nawa. Ta xago kai muka
haxa ido sai ta ce da ni. "Ina fata ban takura ma ka
ba, don nazo na yi ma bayanin abin da ya fa ru, kaga
jiya wallahi ban yi barci ba don tsoro, kuma yau ma
na kwanta kenan, sai na ji an fara gugar qofar xakina,
shi ne na ganka kana buxe qofar xakinka. Shi ne na ce
bari na zo na kwana a nan da safe sai na tafi."
"Ki tafi ina?" Na tambaye ta.
"Kano mana, ai canne garinmu."
"Daman a Kano ki ke?" Na ce da ita da sauri.
"E mana!" Za ka yi mamakin yadda aka yi ban
tambayi inda take zaune ba a Kano, ban kuma
tambaye ta abin da ya kawota Kaduna ba, haqiqa
al'amarin ne ya rikitar da ni ya kuma bani tsoro, don
hakan sai na qyaleta ban qara tambayarta komai ba.
"Sai ki kwanta da safe ma tattauna akan maganar."
Na ce da ita ban kuma ce mata ba nima xan Kano ne.

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

9
A haka muka kwanta, tana gefena daga jikin
bangon xakin, ni kuma ina kwance a gabanta, wato a
bakin gadon. Qarfe huxu da rabi na dare agogon
bango ya buga, otel xin tayi tsit ba ka jin komai sai
saukar ruwan sama a jikin tagogin xakin kamar da
bakin qwarya. Idona biyu tun qarfe goma sha biyu, sai
yanzu ne na ji idona ya fara lumshewa, na juya na
zubawa abar qaunata ido, ina kallon kyakkyawar
fuskarta har dai barci ya xauke ni.
Qarar abin da ban tava zato ba ta ratsa
qwaqwalwata, na tashi firgigit! Na miqo qafata qasa,
sannan na tashi tsaye barci ya fice daga idona. Nan da
nan kamar daman idona biyu, da farko na xauka
qarar tsawa ce, amma daga baya sai na kasa gaskata
hakan, na tabbata qarar bindiga na ji. Nan da nan na
nufi qofar xaki da gudu na buxe na leqa, a daidai
lokacin da na ga wani ko kuma in ce wata, ta nufi
qasan benen da gudu, sanye da baqaqen kaya. Zai yi
wuya ka gane mace ce ko namiji ne saboda rashin
isasshen hasken dake kwararon benen, sai da me
gudun ya zo shan kwanar da za ta kai shi hawa na
qarshe ne na gane mace ce, na tabbata ko wace ce ba
ta so a gane ta, a matsayin mace.
Cikin kaxuwa na juya zan koma xakina sai naga
xakin Badura mai lamba uku (3) a buxe, ban yi wata-
wata ba na kutsa kai cikin xakin. Na lalubi makunnar
lantarkin na kunna, xakin ya gauraye da haske,
sannan na ganta a kwance a kan gado, gaban farar
rigarta ya rine jawur da jini, tiriri na tashi daga ramin
da harsashin bindigar ya yi a qirjinta. Babu alamar
tsoro a fuskarta, duk da cewa ta riga ta mutu, hakan
bai hana Zainab yi min murmushin qarshe ba.





























2

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

10
intuna biyu suka shuxe ina tsaye a kan gawar
Zainab, ba na ko motsi kamar an da sa ni,
rigata ta jiqe sharaf da gumi, duk da yake ana xan
sanyi saboda ruwan da ake ketawa kamar da bakin
qwarya. A halin yanzu ruwan ya xan tsagaita, na yi
zaton qarar bindigar zai tashi jama'ar da ke kan
benen Otel xin amma koda mutum xaya bai zo ba, na
xan buxe qofar xakin na leqa sosai ko zan ga motsi
amma ban ji motsin komai ba, sannan na juya na yi
wa Zainab kallon qarshe na fice daga xakin na kuma
maida qofar na rufe. Na sa hannu zan tura qofar
xakina kenan sai na ji wata murya irin wacce za ka ji
idan ka je maqabartar da ake fatalwa ta ce min.
"Barka da asuba."
Na yi firgigit na juya a ruxe abin da idona ya gane
min ya ban haushi da kuma dariya, wani xan tsoho ne
fari mai motsattsiyar fuska, kamar matsatten lemon
tsami, yana sanye da shuxayen kaya, a qirjin rigar an
rubuta cikin harshen Turanci (Durbah Hotel) wato
sunan hotel xin da nake ciki kenan.
"Barka ka dai." Na amsa masa cikin wata murya
da bata fi tasa daxi ba. Girarsa mai kama da ta biri ta
xaga sama a yayin da ya ga fuskata ta haxu da gumi.
"Lafiya dai Malam ko ba ka jin daxi ne?" Ya
tambaya, na yi murmushin da bai ka idanuna ba, na
ce da shi "Wallahi wani abinci jiya ku ka bamu a otel
xinnan wanda ya rikita min ciki, shi ne ya ke ta murxa
min ciki. Yanzu ma na je wajen maqwabciyata ne ko
tana da magani ta taimaka min." na xan yi shiru,
sannan ya kalle ni ya ce, "Allah ya sauwaqe." na ce
"Amin."
Har zan shige xakina sai na ji ya ce, "Zainab ta
tashi kuwa ko har yanzu bacci take?" Saura kaxan in
kifa masa mari, fuskata ta canja kala jikina ya xau
rawa, lallai in tsohon nan ya san Zainab tana cikin
xakin nan, to kashina ya bushe, domin babu abin da
zai hana a xora min laifin kisanta.
"Malam ka ga kar ka vata min lokaci." Na ce da
shi cikin fushi "Ni ban san wata Zainab ba, Badura
dai ita ce mai xakin ita kaxai kuma na gani a ciki. In
babu sauran wani abu kuma ya kamata ka qyale ni da
shegiyar tambayarka, ka je ka yi aikin da aka sa ka."
"Allah ya ba ka haquri Mallam." Motsatten
tsohon ya ce da ni, "daman abin da ya sa na tambaya,
jiya ne kafin mu tashi daga aiki ta ce min idan aiki ya
yi mata yawa a xaki mai lamba uku (3) zata kwana
wai saboda idan dare ya yi ba a samun motar zuwa
unguwarsu."
Jikina ya sake xaukar rawa kamar ana yi min
kixan gangi.
"A wacce unguwa take?" Na tambaya.
"A unguwar Shanu take." ya ce da ni.
"Mene ne aikinta a otel xin nan?".
"Aikinata shi ne bada xakunan kwana da kuma
kula da waxanda ke ciki."
"Sai an jima ka ji ko." Na ce da shi, ba tare da na
jira wata amsa ba, sai kawai na shige xaki na janyo
qofar na rufe sannan na sa sakata.
Badura na zaune a kan gado tana shafa mai, koda
ganin fuskata sai ta tashi tsaye ta dafa qirji.
"Lafiya Fadil na ganka haka duk ka canja nan da
nan?".
"Haxa iya kayan da ki ka san zai yi miki amfani
kisa cikin Jaka". Na ce da ita ba tare da na kalle ta ba,
domin nasan kallonta a lokacin zai iya qara tsoratar
da ita. Na yi tsammanin za ta tambaye ni wani abu
M

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

11
amma sai ta ba ni mamaki. Nan da nan na ga ta fara
haxa kayanta kamar yadda na umarce ta. Na wuce ta
na bar ta anan tana ta haxa kayanta ni kuma na shige
banxaki.
Na duba kaina sama da qasa a cikin madubin dake
liqe a xakin, abin da na gani ya ban tsoro. Fuskata ta
yi sharkaf da gumi kamar wanda ya ga fatalwa, kar
ka yi mamaki da jin haka domin kuwa wannan shi ne
karo na farko da na tava ganin gawa qiri-qiri, kasan
kuwa ko jana'iza naje a lulluve nake ganin ta. Na
xauke kaina daga madubin sannan na je gindin famfo
na sheqawa kaina ruwa. A halin yanzu ba na buqatar
wanka, ita ma Badura rashin sanin abin da ya faru ne,
ya ba ta damar wanka, shin da ta san da gawa a
xakinta me kake jin zai faru? Na shasshare ruwan
dake kaina da wani qyalle, sannan na sake duban
kaina a jikin madubin, abin da na gani yanzu ya fi na
da kyawun kallo, da kaxan a qalla dai ba zan tsorata
yara ba, na buxe qofar ban xakin na shigo xakin tana
zaune a kan kujera tana kuka.
"Mene ne kuma ya same ki?". Na tambaya, ta yi
ajiyar zuciya sannan ta xago kai muka haxa ido da ita,
sannan ta ce. "Fadil don Allah in laifi na yi maka sai
ka faxa min bai kamata a ce kana korata don kawai
kaga ina sonka."
Ban ga lafinta ba domin kuwa ko kai ne ka kwana
a xakin wani ya zo ya ce maka haxa kayanka ba tare
da wani qarin bayani ba dole ranka ya vaci. Sai dai
kuma shirun shi ya fi amfani a halin yanzu, ba sai na
gaya ma ba halin mata. Ina faxa mata za ta rikice har
ta sa shirin da nake a halin yanzu ya ruguje. Ya zama
dole na bar otel xin kafin a sami Zainab a mace.
"Kada ki damu masoyiyata." Na ce da ita cikin
kalami mai daxi. "Idan mun je gida zan faxa miki
abin da ya faru". Sannan na ci gaba da naxe kayana,
tana zaune ba ta ce da ni uffan ba.
NA haxa kayana masu amfanin a Jaka xaya,
sannan na zuge na yi shirin gudu kenan, ko ban faxa
maka ba za ka fahimci bala'in da na faxa a halin
yanzu, gawar ma'aikaciyar otel xin da nake ciki a
xakin masoyiyata, kana jin idan a ka same ta
matacciya wa za a fara naxewa? Masoyiyata Badura,
kasan kuma ko ban faxa maka ba, ba zan tava barin
wannan ta faru a kanta ba, sannan abin da ya daxa
dagula al'amarin shi ne idan 'yan sanda suka far
abincike matsattsen tsohon nan zai ce ya ganni na fito
daga xakinta a daidai lokacin da ta mutu, me kake
tsammani? Kana jin 'yan sanda za su yarda da
qaryata cewa maganin ciwon ciki na zo karva a xakin
na taradda ita a mace?.
NA save Jakata a kafaxa sannan na dube ta na ce
da ita.
"Ina xan mukullin motarki, ko kuwa kin baro shi a
xakin?".
"A'a ga shi nan." Ta ce da ni, ta miqo min xan
mukullin na jefa a aljihuna sannan na ce "tashi mu
tafi." Ta xauki jakarta mai taya ta biyo ni zuwa qofar
xakin cikin mamaki da rashin fahimtar al'amuran
dake gudana, duk da yake dai na san, ta san babu
lafiya, amma ba zan tava haqura na faxa mata ba sai
mun fice daga cikin otel xinnan.
"Ba ni jakar taki sai ki riqe wannan." Na ce da ita
a yayin da na miqa mata tawa jakar, ni kuma na karvi
tata akwatin ita dai bata yi min musu ba ko kuma
tambaya. Kawai dai tana bi na kamar kuma mun

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

12
kawo hawan benen na qarshe kenan, sai na ga xan
motsattsen tsohonnan yana qoqarin shigewa wani
xaki. Na yi sauri na matsa kusa da shi, da farko na yi
niyyar na manta da shi amma sai na yi tunanin me
yiwa ya leqa xakin ya ga abin dake ciki don haka ne
yake qoqarin vace min sa'adda ya hango ni. Babu
mamaki ma yanzu 'yan sanda suna kan hanyarsu,
zuwa otel xin.
Na rarumi kwalarsa na haxa shi da bango
qafafunsa da qyar suke tava qasa, sannan na ce da shi
cikin fushi.
"Ka manta da duk abin da ya faru xazu, ka gane
ko?" Na buga masa tsawa, "Ko da an zo ana tambaya
to amsar ka ita ce ban ga kowa ba, in ka sake ka qara
cewa wani abu daga nan, ba sai na faxa maka ba." Na
sake shi ya faxo a kan tsintsiyar dake hannunsa. Ya so
ya bani tausayi amma da na tuna da masoyiyata
Badura da kuma bala'in da take ciki sai na dake
zuciyata, na sake buga masa harara.
"Ka ji ko." Na ce da shi "To". Ya amsa cikin irin
muryar da za ka ji yayin da ka shaqe zakara, abin da
na ke nufi na ce da shi "Koda 'yan sanda za su
tambaye ka ko ka ga wanda ya shiga xaki mai lamba
uku ko ya fita to amsarka ita ce ban gani ba." "To".
Ya sake amsawa. Ban damu ba na san ko ya leqa ko
kar ya leqa dole ne nan da awa xaya a sami gawar
Zainab xan tsurkun tsohonnan kuma dole ne ya ce ya
ganni, amma yanzu na san na yi maganinsa na xan
lokaci.
Badura na rave a jikin bango jiki na rawa, ba ta ce
da ni komai ba, na duba agogona da qyar na ga ko
qarfe nawa ne yanzu, sai na ga babu shi babu
labarinsa. Na juya na kama hannun Badura dake
tsaye kamar gunki muka nufi qasa, na san na makara
ban damu da na koma xakin Badura ba, domin duba
agogo. Na tabbata a nan na yadda shi ko yake na san
agogo ba wani abu ne ba dan 'yan sanda sun sami
agogo wannan wani abu ne da bai shafe ni ba, domin
kuwa ba ni kaxai ne mai sa agogo ba. Tunanina ya
katse, a yayin da na ji wani abu kamar kukan jiniya,
na fizgi hannun Badura muka yi qasa da gudu.
Muka fice ta qofar baya.
"Yi sauri ki kai mu inda motarki take." Na ce da
ita, ba ta yi min gardama ba, sai kawai ta wuce gaba
da gudu nima na bita, a halin yanzu ta fara gane
lamarin ba ta vata lokaci ba, duk da yake ba ta san
meke faruwa ba amma na san ta san muna qoqarin
kaucewa 'yan sanda ne. Kafin na qaraso inda motar
take tuni ta faxa ta tashi motar ta yi baya kaxan zuwa
saitin da nake, ban yi wata-wata ba sai kawai na buxe
gidan gaba na faxa na jawo na rufe. Duk wannan ya
faru ne a cikin daqiqa talatin.
Badura ta fizgi motar da gudu kamar walqiya
muka nufi qofar otel xin dake baya don kuwa na san
yanzu 'yan sanda sun cika xaya qofar. Wata mata ta
xauki qara a yayin da motarmu ta yi kan xanta da ke
wasa a tsakiyar titin otel xin, Badura ta xauke kan
End Ads