x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - KIBIYAR AJALI

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 49194 words

Category: Love Stories

Views 520

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
idan suka same ni
to na tsira kenan, abu xaya da ba zan sake na faxa
musu ba shi ne, in da gidan ku yake a Kano. Wannan
wani abu ne da za su nema da kansu."
Na kalle ta cikin haushi sannan na ce da ita.
"Kina tsammanin ni mahaukaci ne zan nufi gida a
halin yanzu."
Badura ta yi murmushi.
"Fadil!" ta ce da ni, "Kar ka vatawa kanka lokaci,
ka yi qoqari ka tsere wa abin da ke jiranka waje,
damar ka ta qarshe kenan." Sannan ta ci gaba da
cewa. "Idan kana ganin ba wani abu ne 'yan sanda su
san gidan ku ba to bari na faxa ma, ba abin wahala ba
ne na faxawa 'yan sanda cewa yayanka ya san inda
kake. Ka ga za su yi tsammanin shi ya voye ka." Ta
xan yi shiru sannan ta sake murmushin mugunta.
"Ba za ka so ace an azabtar da yayanka saboda kai
ba, kada kuma ka yi tsammanin idan 'yan sanda sun
saki yayanka, zai sami ci gaba da aiki a gidan rediyo.
Abin kunya ne ace ma'aikacin gidan rediyo ya voye
mai kashe jama'a da gangan kawai, don saboda xan
uwansa ne, idan muka bi ta fuskar siyasa wannan zai
janyo abin kunya da maganganu ga gidan rediyon.''
Na yi shiru ina tunanin lallai yarinyar nan ta gama
sanin sirrina ciki da waje, haushi ya kama ni, na yi
taku guda na gaggawa, na kifa ma ta mari, don qarin
haushi maimakon ta yi kuka sai ta qyalqyale da
dariya. Lokaci guda kuma, sai ta qwalla ihu, kamar
wacce ake zarewa ido, cikin daqiqa uku na gane abin
da ke shirin faruwa, na faxi rub da ciki a daidai
lokacin ne a ka fara ruwan harsashi ta cikin tagogin
xakin. In da na yi sa'a sai harsashi xaya daga cikin
dubun harsashen da ake zubowa xakin ya daki
qatuwar fitilar dake liqe a bangon xakin, fashewarta
ke da wuya sai xakin ya zama kamar qabari saboda
duhu.
Na manta da zancen Badura yanzu ta kaina nake,
duhun xakin shi ya ba ni damar yin wani abu, na ja
ciki ina laluben jakata, za ka ga wawanci na idan ka ji
cewa ina neman jaka cikin wannan lokaci. Maganar

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

28
yayana ita na bi, lokacin da zan taho Kaduna sai ya ba
ni wata jaka baqa ya ce da ni duk inda za ka ka tafi da
jakarka, kada ka sake kuma ta vata, ban san abin da
yake nufi ba, amma na san akwai ma'anar yin hakan.
Bayan xan lokaci na sami jakar na rataya ta a
bayana, na yi amfani da wasu igiyoyin roba dake
jikinta na xaure ta a bayana, ''lokacin gudu ya yi" na
ce cikin zuciyata. Na tashi cikin sanxa na leqa tagar
xakin dake gabas, banga motsin komai ba cikin
lambun ban yi tsammanin daman zan ga motsin wani
abu ba, amma vangaren kudu da arewa, nasan yanzu
ya zama tarkon mutuwa. Na yi shiru, tunanina ya
katse, wata qatuwar murya na magana cikin bututun
yin magana tana cewa.
"Fadil!! Fadil!! Mun san kana ciki, ka ajiye
bindigar ka ka fito hannunka a sama."





























5
un san kana ciki Fadil!!" Muryar ta sake
cewa, "Ka fito a hankali hannunka a sama,
muna so ka fito ta qofar xakin, za ka haxu da mutanen
mu guda uku, mun ba ka mintuna biyu ka fito, in
kuma ba haka ba to za mu sa yaranmu su kamo ka da
rai ko babu rai."
Gidan ya yi shiru, ba ka jin komai sai jefi-jefin
motsin 'yan sanda a bayan gidan, na lalubi bangon
gabas na tashi tsaye, na ja tagar xakin kaxan-kaxan
har ta buxe, wata sassanyar iska ta bugi fuskata, sama
tayi baqiqqirin da hadari, ana ta walqiya, iska na kaxa
rassan bishiyoyin da ke lambun, na qurawa cikin
duhun lambun ido, ina qoqarin ganin motsi, sassanyar
iskar dake lambun, tattare da duhunsa, su suka qara
razana daren, da barazana mai ban tsoro, kada ka yi
tsammanin hakan zai hani dirga cikin lambun ko kusa
“M

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

29
yanzu babu alamar tsoro a tare da ni raina ya gama
vaci.
Bayan idona ya tabbatar min babu kowa a kusa,
sai na kama qarfen tagar, na dafe a jiki, na xago
qafafuna biyu na zura su waje kaina na ciki, sannan
na juya kaina na kalli inda Badura take, na ce da ita
sai gani na biyu, amma kada kiyi tsammanin kin yi
nasara, ba a gane jarumi sai yaqi ya qare." Ba tare da
na jira wani abu ba sai na dirga cikin lambun
ganyayyakin bishiyoyin lambun, su suka hana 'yan
sanda su ji sautin dirga ta cikin lambun, duk inda ka
ta ka cikin lambun ganyayyaki ne, sun lulluve qasar
wajen kamar siminti ga dukkan alamu ya yi shekaru
rabonsa da shara.
Badura ta qwalla qara, qara ne irin wanda za ka ji
daga bakin wanda ake azabtarwa, a daidai lokacin ne
na ji qatuwar muryar nan ta ci gaba da magana ta
cikin bututun magana.
"Fadil!! Har yanzu kana da sauran minti xaya,
kada ka sake ka tava yarinyar nan ta wajen ka, idan
ka tava ta harbinka zamu yi." Na tsaya cak a inda
nake, wnai motsi a gabana shi ya xauke min hankali,
bayan daqiqu uku sai na ga wani xan tsamirmirin xan
sanda, yana sanxa ya nufo gindin bishiyar, na rave a
bayan ta, na gode wa Allah da ya sa baqar riga ce a
jikina, na tabbata bai ganni ba, ba ya kuma zaton ina
wajen a yadda ya ke tafiya da gadara, yana
tsammanin ina cikin xakin ne, xan sandan ya matso
kusa da ni, tsakaninmu da shi bai wuce taku xaya ba.
Ban tava ganin tashin hankali irin wannan a rayuwata
ba, xan sandan ya fara sanxa a tsammanina ba ya so
na gan shi ne domin yana tunani a kwance nake a
tsakar xakin, in dai haka yake tunani to lallai yana
buqatar sake sabon tunani, numfashina a halin yanzu
sama-sama ne.
Xan Sandan ya leqa tagar xakin a hankali ta
hanyar sunkuyar da kansa qasa-qasa, ya xan karkatar
da kunnensa yana sauraron ko zai ji inda Badura ke
qara, ban jira wani vata lokaci ba sai na takura na
daka tsalle cikin abin da bai wuce daqiqa xaya ba sai
gani a kansa muka faxi rica!! a kan matattun
ganyayyakin bishiyar, abin ya so ya bani dariya,
domin lokacin da na faxa kansa, na yi zaton zai faxi da
gwowowinsa ne amma abin mamaki sai na ji kamar
na faxa akan karmami, muka mirgina sau biyu a qasa,
na yi wuf na rufe bakinsa a daidai lokacin da yake
shirin ihu, na dunqule hannuna na kirva masa naushi
a muqa-miqi, ya yi wani irin kuka mai ban dariya, na
ta ka ruwan cikinsa sai ya tashi zaune kama sifirin da
na xauke qafata kuma daga kan ruwan cikinsa sai ya
koma ya baje, da farko na xauka na kashe xan
tsamirmirin xan san dan nan amma da na tava
qirjinsa sai na ji yana bugawa.
A halin yanzu an fara cida da yayyafin ruwan na
kama qafar xan sandan na ja shi kamar buhu har
qarqashin wata bishiyar goba mai yawan ganyayyaki.
A qalla dai zai kai sa'a xaya kafin a same shi.
"Ya isa haka." Wata siririyar murya irin ta
matsorata, ta ce daga bayana. "Ka ajje bindigarka ka
xaga hannayenka sama, kada ka manta." Muryar ta
ce da ni "Daidai nake da na harbe ka a gadon baya,
amma abin da muka fi so shi ne muka ma ka da ranka
motsin yaudara xaya daga gare ka, zai zama shi ne
motsinka na qarshe a duniya.
Aka fara iska mai qarfi haxe da ruwan sama,
hancin bindigarsa a tsakiyar gadon bayana, in dai har

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

30
na samu damar zillewa xan sandan dake bayan, to ina
da cikakken qarfin gwiwar cewa zan iya ficewa daga
lambun, amma abin da ya fi damuna shi ne, ban san
iya yawan 'yan sandan da suke gadin vangaren gabas
na lambun ba, duk da yake dai nasan har yanzu
guntun 'yan sandan ba su da masaniyar abin da ke
faruwa a vangaren gabas na lambun.
Addu'a ta xaya ita ce, Allah sa na samu damar
yaudarar xan sandan dake bayan tun kafin wani ya zo
ya tadda mu.
''Kada ka sake ka motsa." Ya ce da ni, ban san
abin da yake nufi ba, amma zatona yana jiran ruwa ya
tsagaita ne, mun ji qe sharkaf, amma ni duk da haka
zafi na ke ji, aka yi wata walqiya mai hasken gaske,
duk lambun ya haske, sannan wata tsawa mai qarar
gaske ta biyo baya, amsa kuwwar tsawar ta sake rikita
lambun. Xan sandan dake bayana sai ya yi zaton shi
za ta faxawa, yana rawar jiki sai na ji saitin bindigar
ya kauce daga bayan, ban jira wani abu ba sai kawai
na faxi rib da ciki, na sa qafa na doke shi a qirji,
bindigar dake hannunsa ta faxi can gefe guda, muka
tashi lokaci guda muka shiga tsere kowa na qoqarin
xaukar bindigar, ruwa ya daxa tsugewa da qarfi,
santsin cavin ruwa ya kwashi xan sandan sai gashi a
qasa kamar wanda aka jefo daga sama, bai yi wata-
wata ba sai ya riqe idon sawuna, nima na faxi kansa,
muka shiga kokowa cikin cavi, abin ka da wand aya
manyanta, kafin minti xaya sai ga xan sandan yana
numfashi sama-sama, na yi masa xiban karan
mahaukaciya na jefa shi bayana, idona ya gama
rufewa a halin yanzu, faxa kawai nake kamar
mahaukacin doki, domin na san idan sauran 'yan
sandan suka zo to fa kashi na ya bushe kenan.
Xan sandan da na jefar gefe guda ya yi qoqarin
tashi amma sai juwa ta xauke shi ya faxi, sannan sai
ya tashi na ga ya xora hannu aka zai yi ihu, na duba
inda bindigarsa ta faxi, na raruma kafin ihun nasa ya
gama fitowa sai na kwaxa masa gindin bindigar a
tsakiyar ka, ya yi taga-taga ya faxa cikin cavi da
fuska,'biyu kenan' na ce cikin zuciyata.

** **
Ko kaxan bana son faxa da xan sanda, ba dan
komai ba kuwa sai don doka ce mai tsanani, amma
kuma irin halin da na ke ciki ya zama dole na qwaci
kaina.
Rigata ta jeqi sharaf da ruwa, bayan na dawo da
numfashina daidai, sai na gyarawa jakar dake bayan
xauri, sannan na kama qafar xan sandan da na doke
na voye shi, shi ma a qarqashin bishiya. Lambun ya yi
shiru ba ka jin komai sai dirar zubar ruwa a kan
kwanukan gidajen jama'a dake bayan lambun, sai
kuma jefi-jefin caval-caval xin ruwa da na ke ji na
takalmin 'yan sanda, a can vangaren arewa ina
tsammanin sun fara tunkarar gidan, sai dai kuma
ruwan da ake yi shi ya vata musu lamari domin duk
takun da suke ina ji, har yanzu fa suna tsammanin ina
da bindiga.
Na sa gabana gabas ina sanxa halin yanzu na fara
hango katangar gidan, ta cikin wata bishiyar lemon
zaqi marar ganye da yawa, sai dai kuma kai wa ga
katangar shi ne ya ke da mutuqar haxari, domin babu
mamaki wani xan sandan na nan a gadin wajen,
kamar da bakin Mala'iku sai na ji na yi sama kamar
karmami, sai bayan da na faxa cikin cavalvalin ruwan
da fuska sannan na gane cewa ashe fa wai qafafuna a

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

31
ka kwarfe, na mirgina sau uku cikin cavalin ruwa
sannan na yi qarfin hali na tashi zaune ina qoqarin
gane me ya faru, qaton xan sandan wanda za ka iya
ganin jajayen idanunsa daga cikin duhun daren, na
tsaye a kaina. Jibgegen kakkaura mai faxin kafaxa,
kamar qofar gareji. Zai yi wuya ka banbance tsakanin
wuyansa da kansa, da farko sai ka xauka mutum-
mutumi ne, hannunsa da ya yiwo kaina kamar
harsashi shi ya tabbatar min da cewa ba mutum-
mutumi ba ne.
Qaton hannunsa mai kamar farantin waina ya
cakumi kwalata, ya xago ni safayau, kamar biredin
mahaukaciya. Qafata da kyar take tava qasa, ya
kwaxa min mari sau uku, idona ya gane min taurarin
wahala kamar tarin yashi, na ji kamar saman kaina
zai cire ya faxo.
"Sai ka san ka daki xan sanda." Ya ce da ni "Daga
yau ka sake kashe wani." Muryarsa mai kama da
kwarankwatsa, qafafuna sai reto suke falau-falau
kamar bulala mai baki biyu. Cikin gigita da takaici,
na kutufi hancin xan sandan, alamun da ya nuna
alamu ne na irin wanda aka doka da gudumar totuwa
a gadon baya.
"Ka je ka sake qwarewa a dambe." Xan sandan ya
ce da ni, a daidia lokacin ne ya saki kwalata, tare da
dukan qirjina, duka ne irin wanda zai iya kayar da
katangar bulon siminti, na faxi rica!! kamar wanda
iskar gas ta doka, hankalina ya fara fita daga jikina,
quguna kamar zai fashe, na yi qoqarin tashi abin ya
gagara, da na yunqura sai na ji kamar gini ya faxo
min.
Xan Sandan baya ko qoqarin fito da bindigarsa,
domin yasan zai yi wuya na tsira daga hannunsa, ya
yarda da kansa, nima kuma na yarda da naushinsa,
domin na fara tunanin da ya naushe ni gara ya harbe
ni da bindiga a kafaxa, naushin sa ya fi bindiga haxari,
don kuwa dukansa zai iya kashe mutum farad xaya.
Kada ka yi zaton abin da nafe faxa gaskiya ne, kai
kanka ka san wahala ce ta sa ni tunanin haka.
Caval-caval na ji qarar xan sandan na cewa, a
yayin da ya keto cavin ruwan da ke tsakaninmu da
shi, na yi ta maza sai gani a zaune. Dole ne yanzu na
san yadda zan yi na rage masa haukan qarfin dake
kansa, in kuwa na sake ya yi min irin dukan xazu to
na san yau bani da wajen kwana sai a gidan Yari. Ya
matso kusa da ni tsakaninmu da shi bai wuce takun
sawu uku ba, dabara ta faxo min. Sai na yanke jiki
kafin qibtawa da bismillah sai gani facal! cikin cavin,
duk da yake babu cikakken hasken da zan iya ganin
fuskar xan sandan sosai duk da haka zan iya cewa na
ga haqoransa suna murmushin mugunta. A zatonsa
sarewa na yi na faxi, in har yana tsammanin zan kamu
haka kamar wani jiqaqqen zakara, to yana buqatar
sake tunani sau dubu a cikin kowacce daqiqa xaya. Na
harbo qafata kamar 'KIBIYAR AJALI', jibgegen xan
sandan ya yi qoqarin kauce tunbinsa, amma ina ya
makara, gindin takalmina ya daki tunbinsa, sai na ji
kamar na daki salkar ruwa. Xan sandan ya yi qara,
irin qarar da za ka ji daga bakin kwaxo, da farko na
xauka ba zai ji dukan ba, saboda ganin naushin da na
yi masa ya shanye shi kamar wanda na daki bango.
Duk wannan rikicin ya faru ne cikin daqiqa biyar,
na sake yunqurawa gaba, na sake dukan cikinsa sau
biyu. Xansandan ya yi baya taga-taga kamar zai faxi,
sannan sai na ga ya tsaya cak kamar mashi, yana
fuskantata qaton cikinsa a hannu. Na ji kamar motsin

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

32
ganye a bayansa, wani xan siririn xan sanda ne yake
matsowa a hankali cikin sanxa, walqiyar da aka yi ita
ta bani damar ganinsa, qirjina ya fara dakan uku-uku,
dole ne yanzu na yi wani abu, na tabbata xan sandan
bai ganni ba.
"Xan uwa me ka ke yi haka ne?" Siririn xan
sandan ya tambaya cikin harshen turanci, nan da nan
na yi sauri na kwanta a hankali cikin cavalin, na
mimmiqe kamar fatalwa.
"Wayyo! cikina, ya kashe ni kawo min taimako
xan uwana." Na yi maganar ne cikin harshen turanci.
"Idan ba ka harbi qaton nan ba kashe ni zai yi."
Na sake cewa cikin harshen turanci, qarar harbin
bindiga da hasken wutar da ta fitar daga bakinta, da
kuma aradun da aka yi a daidai lokacin haxe da
walqiya, sai suka haxu suka kurumta kunnena,
jibgegen xan sandan ya yi kuka.
"Kashe xan uwanka kai wawa." Ya yi taku biyu
gaba sai ya faxi da baya a gabana, cikin hasken
walqiya sai na ga jini na vulvulowa daga gwiwarsa ta
qafar hagun, na yi ajiyar zuciya. "a qalla dai bai mutu
ba." na ce cikin zuciyata.
Qarar bindigar da kuma aradun da aka yi a
lokacin, su suka haxu suka ruxa matsoracin siririn
xan sandan nan da ya yi harbin, yana harbin sai ga
bindigar ta qwace daga hannunsa ta faxi qasa, a
tsammanina bai tava harbi da ita ba sai yau. Cikin
ruxanin nan na
End Ads