x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 1 - KIBIYAR AJALI

  • 1 words
  • 3000 words
  • Out of 49194 words

Category: Love Stories

Views 513

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

1
Qarar abin da ban tava zato
ba ta ratsa qwaqwalwata, da
farko na xauka qarar aradu ce,
barcin da idona ya zama tarihi a
halin yanzu, na tabbata qarar
bindiga na ji. Nan da nan na nufi
qofar xakin da gudu, a daidai
lokacinne na ga wani ya nufi
qasan benen da gudu, sanye da
baqaqen kaya. Cikin kaxuwa na
juya zan koma xakina, sai na ga
xaki mai lamba uku (3) a buxe,
ban yi wata-wata ba sai na faxa
cikin xakin, na lalubi makunnin
lantarki na kunna, sannan na
ganta a kwance gaban farar
rigarta ya rine da jini, babu
alamar tsoro a fuskarta. Duk da
cewa ta mutu, hakan bai hana
Zainab yi min murmushi ba......

-NAZIR ADAM SALIH











DAGA: Nazir Adam Salih (NAS)
Kibiyar Ajali
Me ya fi kuxi?
Ta leqo ta koma
Birnin Sarauniya
Naira da Kwabo
Kai Da Jini
Iska mai kaxa ruwa
Aci Bulus
Kuxin Da Maciji
.Linzamin Shaixan
Aziza
Aljani ya taka wuta
Bindigar Kwali
Mutuwar Kasko
Dare da Rana
Tsohon Alqawari
Murmushin Alqawari
Kura da kan Rago
Kisan Boko

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

2

Copyright (c) Nazir Adam Salih
Haqqin Mallaka (M) Sauqi Bookshop


An fara Bugawa: 1996
An sake Bugawa: 1997
An sake Bugawa: 2009



SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan littafi ga Iyayena



P.O. Box 4792
Abubakar Saddiq Islamiyya Dakata




TSARIN BANGO:
SANI SAUQI BOOKSHOP




Tsarawa da Bugawa a;
Na’urar COMPUTER:

NAFI’U SALISU
08038981211-07028573535

DON
KABIR ABUBAKAR MOH’D SHARIF (KAM)


Wannan littafi qagagge ne, an kuma qirqiro shi ne
ba dan cin zarafin wani ba sai don nishaxi, ba a kuma
yarda a juye shi ta kowacce irin hanya ba sai da izinin
marubucin.

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

3















KIBIYAR AJALI
NAZIR ADAM SALIH
(NAS)

























KASHI
NA XAYA

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

4



1
l'amarin ya faru ne, tun yammacin wata
Lahadi, misalin qarfe huxu da rabi, ba zan tava
mantawa da lokacin ba, domin kuwa lokaci ne da ya
zamo wani vangare na tarihin rayuwata. Ina zaune a
qofar gidanmu, sai ga wani yaro fari siriri yana sanye
da fararan kaya da baqar hula hana-sallah a kansa,
yaron bai wuce shekaru goma sha uku a duniya ba, ya
jingine kekensa a jikin bangon gidanmu.
"Ina wuni." Yaron ya ce dani.
"Lafiya lau." Na amsa.
"Wai kai ne Fadil?" Yaron ya tambaye ni.
"E, ni ne." Na amsa. Ya miqo min wata farar
jakar wasiqa an zane ta da furanni, tun kafin na buxa
na gane daga inda wasiqar ta fito, wannan ita ce
wasiqa ta uku da na karva a cikin kwana biyu. Haqiqa
ina tausayin rayuwar Amina, sai yanzu ne na gane irin
son da take yi min, amma ni har yanzu Allah bai sa
min qaunarta ba ko kaxan, kada ka yi zaton wai ko
don ba ta da kyau ne shi ne yasa ba na qaunarta, kada
ka yi mamaki idan na ce ma ina kyautata zaton tana
xaya daga cikin matan da za su cinye gasar
Sarauniyar kyau da za'ayi a nan Kano.
Na fito da wasiqar na karanta, sannan na ce da
yaron, "Ka je ka ce mata ina zuwa yanzu." Ya ce
"To". Sannan ya hau kekansa ya tafi. Tausayin
rayuwarta ne ya sake dawo min, amma ba don ina son
ta ba. Kyakkyawar tafiyar minti ashirin ta kai ni
unguwar, gidan Kanal A. Muktar yana xaya daga
cikin manyan gidajen da ke Sultan Road, Kanal
Muktar tsohon Soja ne wanda ya yi ritaya shekaru
goma da suka wuce. Ganin wasu sojoji biyar masu
jajayen ido da tarin gashin baki, shi ya sa ni na kafe
babur xina tun kafin na qaraso qofa r gidan, na tako a
qasa har na qaraso qofar gidan, na tsaya cak ina
shawarar abin da zan yi, shin sallama zan yi wa
sojojin ko kuwa sannunku zan ce musu? Sannan
kamar daga sama sai na ji an yi kiran sunana, tana
zaune a kan wata fasfanda na yi mamakin yada aka yi
ban gane ta ba.
"Sannu da zuwa." Ta ce da ni. "Na ji ance gobe za
ka tafi Kaduna hutu, shi ne na ce bari na kirawo ka
mu yi sallama." Tausayinta ya qara kama ni a karo na
farko kenan tun lokacin da muka fara haxuwa da
Amina a wajen wani fati da aka yi a unguwarmu, sai
na ji ta fara karya zuciyata.

**
"Kina nufin kice wani ya zo nema na?". Na
tambayi yarinyar a daidai lokacin da zan buxe qofar
xakina dake Daba Otal Kaduna, kwanana biyu a
cikinta, kuma na ji daxin zama. Babbar otel ce mai
xauke da kayan jin daxin rayuwa, ana jita-jitar cewa
duk Najeriya babu irinta, in ka xauke guda xaya
wacce ba sai na faxa ma ba.
"Ke mene ne sunanki?". Na tambayi yarinyar da
ke gabana.
Ta yi murmushi sannan ta ce.
A

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

5
"Sunana Zainab, kuma ni Ma'aikaciya ce a nan
Otel xin". Sannan ta sake yin murmushi.
Na dube ta sannan na ce, "Don Allah kin san abin
da za ki yi.?" Ta ce, "A'a." "Idan ya dawo ki ce masa
ya bar miki sunansa, ko kuma ya jira ni har na
dawo."
"Kamar yaushe za ka dawo, in ya zo na faxa
masa?"
"Zan dawo kamar bakwai da rabi na dare. Na
gode kin ji ko. Don Allah mene ne sunanki? Kin faxa
min amma na manta." Na tambaya.
"Sunana Zainab, idan kuma kana son ganina, za
ka iya zuwa hawan benen nan na uku ofis mai lamba
(6)."
"Na gode." Na ce da ita, sannan ta tafi ta bar ni
nan cike da mamakin wannan baqo nawa wanda bana
tsammaninsa, yanzu haka ma ba ni Fadil xin ya ke
nema ba, na ce cikin zuciyata, sannan na fitar da
maganar daga cikin raina, na tura qofar xakin na
shiga.
Sanyi ya bugi fuskata a yayin da na shiga xakin,
babban xaki ne wanda ke xauke da gado xaya, kujeru
biyar da kuma tebur xaya mai xauke da wata
qaramar bidiyo da talabijin mai faxin fuskar da ba ta
wuce faxin bangon sinima ba, za ka iya kiran xakin
'Aljannar Duniya', ko kuma in ce Aljannar Najeriya
saboda tsabar tsaruwarsa, ni dai wajen hutu na kira
shi.
Duk zuwan baqon mutumen nan bai dame ni ba,
har yanzu ni ina murna da hutuna da na fara a nan
jihar Kaduna. Kullum fatana shi ne idan na gama
makarantar gaba da Firamare (wato Sakandire) na
tafi Kaduna na kashe lokacin jiran da zamu yi na
fitowar sakamakon jarrabawarmu. Yayana wanda
nake wajensa a can jihar Kano, bai so na tafi hutun
ba, saboda babu wanda na sani a Kaduna, amma da
na takura masa sai ya amince ya kuma kama min
wannan xaki, da kuma wa'adin wata xaya zan yi,
bayan wata guda ya ce kada na qara koda kwana guda
na koma gida.
Na zage labulen tagogin biyu dake xakin sannan na
cire rigata da wandona na xaura qyallen tsane ruwa,
na shiga wanka. Bayan na fito na dubi agogo na ga
qarfe huxu saura minti biyu, sannan na buxa
akwatina na xauko wata riga baqa marar nauyi mai
buxaxxen hannu, na kuma xauko wani farin wandona
shima na sa na tsefe kaina, na xaura agogo na kuma
qwama takalmina, na shiga duba xan littafina na
rubutu. Bayan lokaci qanqane na gano inda na ajiye
shi, shi da alqalamin rubutuna, sannan na fito na rufe
xakin. Har zan tafi sai na dawo da baya na sake
buxewa na shiga domin na tabbatarwa hancina abin
da ya shaqa a daidai lokacin da nake qoqarin rufe
qofar, na miqa kaina ina daga waje na shaqi iskar
dake xakin. Ni dai na san ban sa turare ba, na kuma yi
mamakin yadda aka yi har na shigo na yi wanka ban
ji qanshi ba sai da na zo fita. Haqiqa wani ya shigo
xakin xazu bayan fitata. Na tabbatar da hakan ta
hanyar kula da tsarin inda takalmana suke daga
vangaren arewa, amma yanzu sun dawo vangaren
kudu na xakin, akwatin kayana ma ba'a bar shi a
baya ba.

**
Idan ka xauke wajen da na ke zaune ko'ina cikin
lambun shaqatawar otal xin cike yake da mutane

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

6
maqil, waxansu na wanka, wasu kuma suna wasa da
jajayen 'ya'yansu a bakin ruwa, wannan shi ne xaya
daga cikin abin da ya sa jama'a suke zaune a otel xin.
Na xauki biro da littafina na xora akan tebur, sannan
na jingina da kujerar na fara tunanin abin da zan fara
rubutawa.
Idan ba ka sani ba ya kamata ka sani, na zo hutu
Kaduna ne da niyyar rubuta littafi a kan soyayya
kamar yadda abokaina ke yi a nan Kanon Dabo. A
duk lokacin da na yi niyyar fara rubutawa sai na ji
duk na rasa ta inda zan fara wannan shi ne babban
abin da ya sa na nacewa yayana ya bar ni na zo
Kaduna hutu, domin idan ina ni kaxai zan fi ba da
qwazo da nutsuwa. Don haka ma da na zo wajen
shaqatawar otel xin, sai na zavi vangaren arewa da
lambun, daga jikin katanga wacce zai yi wuya ka gane
cewa katangar bulo ce saboda korayen furanni da
ganyayyakin fulawowin da suka yi yaxo a kanta gaba
da baya. Abin ba acewa kome, domin duk inda ka
taka a otel xin kore shar yake da ciyawar nan mai
kama da kilishi.
Saura kaxan biron dake hannuna ya qwace ya faxo
qasa a sakamakon firgitar da na yi. Na tabbatar da
cewa lokacin da na zauna babu kowa a kusa da ni, sai
wata bishiya taku biyu daga inda nake, to amma
yanzu juyawar da zan yi sai naga wata yarinya tana
zaune a kan wata kujera mai kyawun gani, ga dukkan
alamu ita ta zo da kayarta.
"Sannunka." Ta ce da ni cikin wata murya
lallausa, muryar da ba zan tava mantawa da ita ba
har abada a zuciyata, da qwaqwalwa ba za su iya jure
irin kyawun wannan yarinya ba.
"Yauwa sannun ki dai kyakkyawa." Na amsa
mata. Wannan shi ne farkon rikicin, sa'adda na juya
na tafi daga wajen da duk wannan bai faru a kaina ba.
Na miqe tsaye a yayin da tabar kujerar da take
zaune ta matso kusa da ni, sannan sai tattausan
leventa ya faxaxa izuwa murmushi, fuskarta na
qyalqyali, haqoranta kamar nono, tana sanye da riga
suwaita baqa da kuma jan wando Jeans da baqin
takalmi kambos, ta xaure mararta da wani faffaxan
belt mai qyalqyali, ga sarqa mai kamar walqiya na ta
qyalqyali a wuyanta. Sai bayan da ta yi murmushi ne
na kula da wani xigon baqi a kumatunta na hagu,
wanda shi dai ba xiga shi a kai ba, halitta ce kawai.
'Yammata da dama suna da kyawawan fuskoki da
kuma halittar da za ka daxe kana sha'awarta, ka kalle
su sama da qasa ka gane wa kanka cewa lalle
waxannan su ne irin matan da duk wani saurayi ke
burin mallaka, sannan da zarar kun rabu sai ka
manta dasu da xai kamar ma ba a halicce su ba.
Amma wannan yarinyar ba za ka tava mantawa da ita
ba, kada ka tambaye ni me yasa? Akwai wani abu
dake tattare da kyawunta, ita dai daban ce daga cikin
mata kamar yadda kalanzir yake daban a cikin ruwa.
"Kina buqatar taimako ne?" Na tambaya cikin
muryar da na kasa ganewa, ko tawa ce ko kuma ta
wani. Ta girgiza kai sannan ta ce, "A'a, daman dai na
ga kai kaxai ne shi ne na ce bari na zo na xebe maka
kewa. Kasan nima ban cika son surutu da hayaniyar
jama'a ba."
"To ai shi kenan." na ce cikin rawar jiki.
Ta janyo kujerarta ta zo gaban tebur xina ta
zauna, a duk lokacin da ta kalle ni sai na ji kamar na
xauke ta na haxiye domin qauna, na tabbata yanzu na

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

7
kamu da ciwon so, wanda ban san maganinsa ba. In
dai har yarinyar nan ba ta amince min ba.
"Mene ne sunanki 'yanmata?" Na tambaya.
"Sunana Badura." Ta ce da ni cikin lafazi tattausa.
"Hutu ka ke a nan ne, na ga alamar kamar kai baqo
ne?"
"Qwarai kuwa." Na ce da ita "Yau kwanana biyu
kawai a nan, kuma sunana Fadil."
Badura ta kalle ni na kalle ta, muka yi shiru na
xan tsawon lokaci, wajen ya yi tsit domin a lokacin
mutane sun fara watsewa. Ta xan duba agogo ta miqe
tsaye.
"Zan tafi Fadil, sai kuma yaushe kenan?"
"Haba Badura! Tun yanzu?" Na ce, "Ki bari
mana shida ta qarasa." Yayin da nake bin ta da ido.
"Akwai abin da zan yi ne, gobe ma rana ce, zamu
iya haxuwa kamar wannan lokacin." Sannan nan da
nan ta dafa kafaxuna guda biyu ta qura min ido,
nasan ta gane na kamu da ciwon sonta, ta kuma san
nima na san ta kamu da ciwon sona.
"Fadil!" Ta ce da ni cikin rarraunar murya kamar
za ta yi kuka. "Kar ka ji komai, don Allah idan na
vata ma rai kayi haquri zan dawo gobe kamar yau.
Kai ne mutum na farko da na fara jin sonsa a cikin
zuciyata." Kafin na farga har ta saki kafaxuna ta faxa
motarta ta ja kamar hayaqi ta nufi qofar lambun.

**
Qarfe uku ta yi, huxu tayi, ban ga alamar Badura
ba, na tashi na fara hange-hange amma ban hango
kome ba, sai masu hannu-da-shuni ne su da 'ya'yansu
ke ta shagali a bakin ruwa. Tun misalin qarfe biyu na
sauko daga xakina zuwa lambun na zauna zaman jira
amma har yanzu shiru kake ji. Biyar ta yi, shida ta yi,
sannan na fitar da rai, na tabbata yau ko bacci ba zan
iya ba. Haka na kwana ina tunani jiya, ga dukkan
alamu yau ma haka zan kwana. Na miqe na nufo
qofar lambun ina dube-dube shiru, kamar na tsaya na
sake dubawa sai dai na haqura, na hau sama na shiga
xakina, na buxe tagogin xakin sannan na kwanta
amma barci ya kasa xaukata. Na dubi agogo na ga
qarfe goma saura kwata. Haqiqa tunani, da begen
Badura sun mamaye duk wani sashe na zuciyata. Abin
da ya fi tsoratar da ni ma shi ne, yadda aka yi har na
kamu da ciwon sonta cikin xan qanqanin lokaci. A
yanzu kam babu wani abu da ba zan iya ba wajen
ganin na mallaki abar begena Badura. Kada ka ga
laifina, abin da ido ya gani zuciya ta amince masa dole
ne rai ya so shi. Na juya da niyyar na gyara
kwanciyata, sai na ji kamar ana qwanqwasa qofar
xakin. Na yunqura na tashi tsaye cikin mammaki ina
tunanin ko Zainab ce ta kawo min abinci, to amma
kuma ai na sanar da ita cewa yau a wajen zan ci
abinci, na dai buxe qofar.
A tsaye a bakin qofar, fuskarta tana walwali
kamar mudubi, tana sanye da riga ruwan hoda da
wandonta, akwati mai taya baqa a hannunta kanta
babu kallabi, Badura ce. Cikin mamaki da kaxuwa na
matsa ta shige cikin xakin ba tare da ta ko dube ni ba,
abin da na tabbatarwa kaina shi ne, wannan zuwa
nata ba na kwanciyar hankali ba ne. Na qara
tabbatarwa da kaina haka a lokacin da na kunna
lantarkin dake xakin, haske ya gauraye ko'ina, sai na
ga fararen idanunta sun yi jajur kamar ta wuni tana
kuka, ko kuma ba ta sami cikakken barci ba.

KIBIYAR AJALI_______________________________Nazir Adam Salih (NAS) KIBIYAR AJALI______________________________Nazir Adam Salih (NAS)

8
"Me ya faru Badura, na yi ta jiran ki ba ki zo
End Ads