x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 9 - TAJMAHAAL

  • 24001 words
  • 27000 words
  • Out of 37284 words

Category: Love Stories

Views 137

29 May 2025
Start ads
After Image Ads
har na tsawom tarihi"

Murmushi yayi yana binta da ido cikin shauki yace, "Maharani meyesa kike kira na da d'an sarki??
Suna ne wanda ba nine na dace dashi ba tinda mahaifina ba sarki bane"

Dafa kafad'ar sa tayi cikin sassanyar murya tace, "Rajkumari kai ma fa jinin Sarauta ne, abunda yayi mahaifin ka shine yayi mahaifi na kaga kuwa da kai wannan sunan ya dace, kai fa k'ani na ne Raj ka kasance kamar ni mana"

Murmushi yayi yace, "zanyi k'ok'arin hakan kamar yadda kike so sarauniya"

Murmusawa kawai tayi bayan an kammala suka koma gida.

Farin ciki a wajen Raj ba kama hannun yaro idan ya tuna kalamanta gareshi sai yaji tamkar shine mutum mafi sa'a fiye da kowa a duniya.

Bayan kwana biyu.

Cikin sauri sauri take tafiya cikin wasu lunguna wanda babu kowa a wajen sai d'ai-d'ai d'in dakaru,
Kamar da wasa taji kukan wucewar mashi ta gefen kunnen ta,
Da mamaki ta juyo domin ganin ko waye sai dai bata ga kowa ba, ta cigaba da tafiyar ta.

Ba zato ba tsammani taji an k'ara kawo mata hari da wasu guda uku a lokaci d'aya, sai a lokacin ta gane abun ba na wasa bane koma waye maharbin kibiyar nan to ita yake hari, waige waige ta farayi ko zata ga wani amma bata ga kowa ba,, tana cigaba da tafiya kuma zataji an k'ara watso mata su.


Takawa tayi da wani mugun gudu, yayin da aka shiga harbo mata su akai-akai cike da k'warewa da kuma son cimma wata manufa.......




*INDO CE..*
[21/03, 7:10 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠*

(Masarauta)


Mallakin

*INDO CE..*



🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼


*Page~12*


بسم الله الر حمن الر حيم



*Ga masu buk'atar shiga group na musamman domin jin k'arshen Labarin Naira 100 ne kacal😂 ku hanzarta ku mallaki naku kar a barku a baya🤣 domin k'arin bayani ku neme ni tanan 👉🏻 08146838480*





Cikin zafin nama ta k'arasa ga takobin da aka yiwa mazauni a jikin bango, ta zaro ta cike da k'warewa ta juyo tareda kai masa wani mugun hari,

Cikin zafin nama ya kauce mata tareda farmakar ta da tashi takobin,
Karewa tayi cike da zullumi da kuma tsananin son taga ko waye dan kuwa ko farce be bari a waje ba face idanuwa wanda take ganin kamar tasan me su amma ta kasa ganewa, gashi iya k'arfin sa yake kai mata hari sai dai beyi nasarar samun ta ba saboda k'warewar da tayi.

Ba tareda ya gajiya ba ya cigaba da farmakar ta.

'Dan k'aramin yak'i me d'auke da babban gumurzu sukayi har sai da ya kai ta k'asa warwas sannan ya bud'e fuskar tasa gami da mik'a mata hannu alamar ta rik'e shi ya tashe ta.

Sai da numfashin ta ya kusa tsayawa saboda mamakin abunda idon ta ya gane mata, cikin kad'uwa tace, "Aruuful'Ansaaar!!!!!"

Gyad'a kai yayi tareda cewa, "ni ne"

Cikin sauri ta tashi tana karkad'e jikin ta, kanta ya fara kullewa duk yadda tunanin ta yaso bata abun ya gagara, cikin tsananin mamaki tace, "kenan mahaifin ka k'arya yayi min??? Kai d'in gwarzon jarumi ne wanda kai tsaye zaka amsa suna Khiladie Yonkha khiladie (Jarumin Jarumai) amma yace min baka iya rik'on takobi ba amma har ka kai ni k'asa???"

Jinjina kai yayi yace, "wannan kad'an ne daga cikin ikon Allah, tabbas Abu Ansaar yayi miki k'arya sai dai kuma ba shine da Alhakin ta ba saboda yayi ne dan tsoron ki da yakeji, ni kuma bana shakkar ki Lakhshmie hakan ne yasa na yanke hukunci bayyana miki asalin zahiriyya ta, ni ma'abocin irin wannan abunda kika gani ne, ina wasa da makamai sosai, ba ni kad'ai ba har mahaifiya ta mukanyi irin wannan wasan da ita haka Abu Ansaar, muna rik'e makami amma mu ba dan zubda jini muke rik'e shi ba abun wasa muka d'auke shi"

Ido ta zuba masa cikin k'unar rai, ta d'an jima tana kallon sa bayan ya gama maganar,,, sannan tace, "kuma har kakejin kana da zarrar da zaka iya gwada wasan ka dani?? Kuskure na biyu kenan wanda ka aikata kuma ka sani bazan k'yale ka ba"

'Dan murmushi yayi tareda cewa, "Naji kuma na d'auka nayi kuskure kuma bazaki k'yale ni ba,, sai dai ki sani ni hakan ba'a gaba na yake ba tinda dai sak'o na ya riga ya isa gareki, kuma na sanar dake abunda nake son sanarwa"

Da d'an mamakin tace, "meye kenan?? Ansaar ya kamata ka shiga tai-ta-yin ka yanzu, ka sani nan fa ba a dajin Allah kake ba masarauta ta ce ka gane???

Girgiza kai yayi yace, " idan ban gane ba zaki iya ganar dani??
Kin san meye abunda nake son sanar dake???
Kaifin kafirci da izzar mulki da k'arfin iko gami da ji da kai da girman kai harda rashin sani sun tare miki sun sa kina ji da ganin cewa duk duniya kece tauraruwa mafi haskawa, gani kike kinfi kowa k'warewa jarumta da wayo,
Kin nuna bajintar ki akan ragwayen mazancan, ba Ramraj ba kawai shi kansa Arveen ban yarda da jarumtar sa ba,
Kin nuna dukan su kece tauraruwa a cikin ku,
Hakan ba kuskure bane tinda hakan ta faru, gaskiya ne a cikin su kinfi kowa jarumta sai dai ki sani duniya fa da fad'i, baki ta'ba kawowa zan shigo rayuwar ki ba sai gani katsidim kuma kece kika gayyato ni,
Kinga kuwa tinda ni kaina baki sanni ba hakan yana nufin akwai dubun ki kuma akwai wanda baki ishe su komai ba,
Ki dena d'auka cewa kinfi kowa domin kuwa dukan mu bayin Allah ne,
Gashi duk wannan ji da kan naki nazo na rusa shi domin kuwa abun kaico ne ace na shigo masarautar ki na ciki da yak'i,
Na kai ki k'asa abunda a rubuce jikin littafin tarihin masarautar ba'a ta'ba yi ba,,,
kisan da a cikin jama'ar ki ne sai sunyi tunanin wani abu??,
Ki dena jijji da kai d'innan bashi da amfani,
Kinga yanzu na isar da sak'o na,
Amma fa ke jaruma ce duk da hakan, sai dai kinsan duk iyawar ka akwai wanda ya fika"

Daga haka ya bar mata gurin ba tareda ya k'ara cewa komai ba.

Da ido ta bishi har ya 'bacewa ganin ta sannan ta cigaba da tafiya, koda ta dawo turakar ta ko maganar kasa yi tayi tunanin ta be wuce Ansaar ba, kalaman sa sunyi matuk'ar sosa mata rai, ga kuma cin galaba da yayi a kanta sai taji duk hankalin ta ya tashi, bata da burin da ya wuce nuna masa iyakar sa.

Arveen kallon Waziri yayi cikin salon fusata yace, "Baba wai yarinyar nan me takeji dashi ne??? Taci mutunci na a gaba dubban jama'a, haka inaji ina gani kenan Raj ze k'wace kambu na?? Shine fa wanda bata saurara a daa amma yanzu gaba d'aya ta mayar da nutsuwar ta kan sa ne"

Waziri ya dafa kafad'ar sa cike da manyance yace, "yaro na fad'a min gaskiya shin kana son Maharani ne??"

Ture hannun nasa yayi tareda cewa, "a'a amma dai kasan daa duk cikin masarautar nan daga Farhana sai ni, amma yanzu bata bin ta kaina, hakan yana min ciwo Baba"

Waziri yace, "d'ana kayi tunani sosai karka 'batawa kanka lokaci indai kana son ta ni me baka duk abunda kake so ne kaji ko?? "

Girgiza kai yayi yace, "nifa nace bana son ta"

Waziri yace, "to shikenan, indai wannan ne matsalar ka zata warware, ni nace ma zan ajiye matsayi na na d'ora ka a kai, tinda kaga kai matashi ne sabon jini inaga idan taga haka zata dinga tsoma ka cikin wani abunda ya shafi masarautar nan, na gaji da yanke hukuncin da takeyi kai tsaye bayan ga manyan masarauta amma tana y'ar yarinya ta dinga juya mu"

Da sauri Arveen yace, "da gaske?? Naji dad'in hakan, ko babu komai zan dinga yin kutse cikin lamarin ta koda bata nemi hakan ba"

Waziri yace, "yauwa d'ana ai nasan kanada fahimta"

Hadima Farhana ce zaune a gefen k'afafun ta tana taunar kayan marmari cikin kwanciyar hankali.

Maharani tana kwance kan d'an madai-dai-cin gadon ta na hutawa, ba abunda take tunanu sai Ansaar lamarin sa yana matuk'ar d'aure mata kai, d'an kallon Hadima Farhana tayi ta kauda kai sannan tace, "Hadima Farhana na rasa ta inda zan shawowa Aruuf ya nuna min iyaka ta, ya nuna min gazawa ta, ina buk'atar d'aukar fansa akan hakan domin kuwa raina ya k'onu da yawa"

Hadima Farhana ta gyara zama kafin tace, "Maharani, nagode Allah da ya kawo min wanda ya iya fahimtar dake way'annan abubuwan da kika kasa fahimta, kinga yanzu ma sai ki gane ba wai jarumin ki ne kad'ai jarumi ba akwai dubun sa"

Girgiza kai tayi tace, "jarumi na daban yake, kuma idan ya dawo zaki gane hakan"

Farhana tace, "Maharani da bakida tabbacin cewa yana raye? Baki sani ba ko ya mutu ko yana nan, kedai kawai lokacin dawowar sa kike jira"

"Ruhin sa da nawa aminan juna ne, da ya mutu tabbas zanji hakan a jiki na, damuwa d'aya kawai bansan a wane hali yake ba, amma nasan ze dawo Farhana"

Ta'be baki tayi tace, "bayan zuwan sa Tajmahaal ban k'ara saka ido na a kansa ba ina son ganin sa,
Amma Kinsan ya zakiyi ki rama?? Kawai kiyi amfani da k'arfin ikon ki hakan ne ze sa ya gane akwai tazara a tsakanin ku"

Murmushi tayi ba tareda tace komai ba.

Raj yana kwance bisa hamshak'in gadon sa ya kalli sama sai tunane tunane yake, Gimbiya Sunaya ce ta shigo tana cewa, "Raj!! Wai kai baka da aiki sai kwanciya ne?? Tashi zakayi fa ka dena wannan kwanciyar dan a haka bazaka ta'ba cimma burin ka ba, kai naga yanzu ma baka da burin da ya wuce ka mallaki soyayyar ka, mahaukaci ka ma manta da rashim Albarkar da yarinyar nan tayi maka, ta kashe maka mahaifi amma kai ba ta wannan kake ba, ni buri na kawai d'aukar fansa yaro gara ma ka gane, ta maida kai shashasha bafa wai matsayi ta baka ba dan tace ku shiga farauta tare, kawai tana so taci zarafin ka ne"

Mik'ewa yayi ya zauna kafin ya rik'o hannun ta yace, "zauna Mama"

Zama tayi tana binsa da ido.

Murmusawa yayi sannan yace, "koda ita bata d'auki hakan a matsayin komai ba ni na d'auka, bazan manta da hakan ba domin yana d'aya daga cikin babban abu na tarihin rayuwa ta, batun d'aukar fansa kuma bana ta ita domin kuwa shi ya riga ya mutu, kinga gara mu k'yale batun sa mu gina sabuwar rayuwa, idan ba haka ba kuma kema zaki bishi ne domin kuwa kashe ki a wajen ta ba komai bane sai dai nasan ni bazata kashe ni ba, Mama ki bi a sannu dan kuwa bana so na rasa ki"

Shiru ta d'an yi kafin tace, "wannan haka ne amma gaskiya bazan hak'ura ba idan kaga na janye to nayi bakin k'ok'ari na har na gaza"

Raj yace, "to Mama ina miki fatan Nasara"

Tsaki tayi tace, "tashi kaje ka kai mata wannan abincin kace inji ni kaji ko??"

Kallon ta yayi sama da k'asa kafin yace, "in kai mata abinci inji ki? Anya kuwa ba guba kika zuba mata ba???"

A razane tace, "rufamin asiri d'ana idan na zuba mata wani abun ai zata gane kuma k'arshe tawa ce baza tayi kyau ba, na rantse da abun bauta Ram ban zuba mata komai ba kwata kwata ba da niyyar cutarwa na bata ba, kawai gani nayi a masarautar nan mune dangin ta amma bama kulawa da ita shiyasa"

A ranta kuwa cewa take "kai yaro ne fa Raj baka da wani wayo, sai abunda ka gani dai kawai kai dai kaje ka kai mata, idan kuma da rabon ka kashe masoyiyar taka da hannun ka to"

Jinjina kai yayi yace, "to zan kai mata"

Kar'ba yayi ya kama hanyar sashin nata, ko ina ya ratsa kallon sa ake domin kuwa kowa yasan kai tsaye sashin ta ya nufa kuma da kayan abinci hakan shine na farko dan haka abun yazo musu a bazata.

Yana cikin tafiya yaji an kirashi.

"Hee!!!! Nirbal"

Duk da ba sunan sa bane amma yaci amsa sunan dan shine rago dan haka ya gane cewa dashi ake, tsayawa yayi yana waige- waige, can ya hango shi yana tawo wa cikin k'asaitaccen takun sa, ido Ya zuba masa yana k'ara kad'aita buwayar wanda ya halicce shi, shi ba jinin sarauta ba amma yanda kasan sarki Ganesh haka yake da k'asaita, sai dai indai kana da nutsuwa zaka gane halittar sa ce a haka bawai jinin sa ba.

yayi zurfi a cikin tunani hakan yasa besan ya k'araso ba sai ji yayi yace, "Nirbal, kana namiji meyesa ka bari Lakhshmi ta fika jarumta"

Ido ya zaro tareda mai-mai-ta "Lakhshmi??"
Cikin sigar tambaya.

Gyad'a kai yayi tareda cewa, "eh Lakhshmi"

Cikin tsoro da firgici yace, "Hazoor, Maharani Lakhshmi, kuskure ne kiran sunan ta haka kai tsaye, kai fa bak'o ne kuma karka manta fa kana da mahaifi a wannan masarauta ka samu ka lalla'ba ka bita a sannu har ku rabu lafiya ka samu ka d'auke mahaifin ka ku tafi, amma baka gama biyan wani abun ba karka d'aukarwa kan ka wani, ni ma fa ta kusa cire min kai"

Murmusawa yayi yace, "kana tsoron ta da yawa, kamata yayi ka zama jigon ta ba wai ta zama naka ba domin kuwa a ko ina namiji shine aka sani da jajircewa ba mace ba"

Raj yace, "kanayin kuskure fa, baka san wacece Maharani bane shiyasa, ni yanzu abinci akace na kai mata dan haka karka 'bata min lokaci ka bani guri na shige"

Aruuf yace, "k'warai na san fuskar ta amma bansan 'boyayyen halinta ba, zaka ganar dani abunda ban gane ba???"

Da sauri yace, "eh gobe mu had'u a bayan masarauta cikin lambu yanzu sauri nake"

Bashi hanya yayi tareda cewa, "zaka iya tafiya zamu had'u goben"


Ya wuce da sauri...





*INDO CE..*
[22/03, 10:51 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠*

(Masarauta)


Mallakin

*INDO CE..*



🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼


*Page~13*


بسم الله الر حمن الر حيم



*Ga masu buk'atar shiga group na musamman domin jin k'arshen Labarin Naira 100 ne kacal😂 ku hanzarta ku mallaki naku kar a barku a baya🤣 domin k'arin bayani ku neme ni tanan👉🏻 08146838480*



Har ya d'an yi nisa sai kuma ya juyo yace, "karfa ka manta"

Shafar sumar kansa yayi kafin yace, "Nirbal Aye wahan, ( zo nan)"

Dawowa yayi ba musu dan kuwa shakkar sa yake tin daga lokacin da ya zumbud'awa Maharani mari kai tsaye.

Mik'a masa hannu yayi tareda cewa, "bani tarkacen nan kaji ko?? "

Nok'e kafad'a yayi yace, "a'a bazan bayar ba, babu ruwa na aike na akayi"

Dafa kafad'ar sa yayi yace, "ka bani sai kace mata yana guri na kace mata nace ta fad'a min inda mahaifi na yake sai na baka ka kai mata, idan kuma kayi min gardama yanzu zan tumurmusa ka"

Da sauri ya mik'a masa yana cewa, "gashi amma ba ruwa na kai da ita kuma zance mata kaine ka kar'ba"

Jinjina kai yayi yace, "dama ai dan ka fad'a d'in na kar'ba kace mata ta fad'a min inda Abu na yake"

Gaba yayi yana cewa, "ni ba ruwa na"

Cike da fargaba ya k'arasa sashin ta kafin ayi masa iso wajen ta tuni ya fashe da kuka ra'be-ra'be,
Ba 'bata lokaci Hadima Fadya ta dawo tace ya shiga amma tana can gurin hutawar ta,
Cikin tsoro ya shiga ya ratsa ya wuce, ya same ta zaune bakin wani d'an k'aramin ruwa wanda aka k'awata shi da adon furanni jajaye da Farare, ta zubawa ruwan ido tayi zugum da alamu tunani me zurfi take.

Shashshekar kukan sa ce ta dawo da ita hayyacin ta da sauri ta dawo da nitsuwar ta gare shi cike da kulawa tace, "Raj!! Kya huwa?? ( Raj Me yake faruwa??) .

Cike da ga'bonci yace, " Aruuf, Mama ta bani abinci na kawo miki shine ya k'wace yace sai kin fad'a masa inda mahaifin sa yake sannan ze baki"

Ido ta zuba masa har wani lokaci kafin ta kauda kai, kamar baza tayi magana ba sai kuma tayi murmushi tace, " haka ne?? Ka fad'a masa yana masaukin bak'i sashi na musamman, amma ya cinye abinci ni na k'oshi shine yake da buk'ata"

Cikin sauri Raj yace, "kina nufin kin hak'ura ba zaki yi min komai ba??"

Murmushi tayi gami da rik'o hannun sa cike da manyance tace, "Mera bhai!! Kuma shine abun kuka? Bazance komai a kai ba domin nasan ba yin kanka bane,
ba nace ka zama jarumi ba wai??"

Gyad'a kai yayi alamar "eh"

Ta murmusa kafin tace, "sai yaushe kenan??"

K'asa yayi da kai cikin k'asa k'asa da murya yace, "nima ban sani ba"

Y'ar dariya tayi tace, "ka saba da shagwa'ba, da na sani tin kana yaro na kar'be ka daga hannun Maman ka domin kuwa be kamata ace kana jinina ka kasance haka ba,
Da ka taso a hannun Uwa Urmiy nasan zaka zama jarumi kamar yaro na Abdulkareem, Farhana ma da aka haifa a bayan ka kuma ita mace gashi ta zama jaruma, ya kamata kai ma ka zama namiji ba me tsoron mata ba"

Gyad'a kai yayi tareda cewa, "to"

Shafa kumatun sa tayi kamar k'aramin yaro tareda cewa, "ka nutsu Raj, tashi kaje"

Da sauri ya mik'e tareda amsa mata, yayi hanyar fita har neman yin tuntu'be yake.

Yana fita taga an harbo wani mashi ya sauka a gefen ta, ido warwaje take kallon mashin ganin wasik'a d'aure a jikin sa, zuciyar ta fal fargaba ta d'auka ta warware ta ta fara karantawa.

"Lakshmie Mahalakhshmiey, Lakhshmie Ganesh
End Ads