Shi kuwa Aruuf kansa ya gama kwarkwancewa mamaki ya lullu'be shi da ya akayi Maharani ta samu d'a??
'Dayan ne ya kalli d'an uwan sa cike da rashin imani yace, "idan fa bamu kashe su yau ba bamu da sauran lokaci"
Cikin tsawa Aruuf yace, "Ku dakata!!! Akan me zaku kashe su?? Laifin me sukayi muku??? To zanga wanda ze iya ta'ba su"
'Daya yace, "wannan Fa Aruuful Ansaar ne zefi sauk'i mu gudu kafin ya gano mu"
Kafin yayi wani yunk'uri sun bar wajen da gudu kowa yayi ta kansa.
Hadima Urmi tace, "na gode maka d'an nan ka cece ni daga wannan azzaluman mutanen"
Ido ya zuba mata yana mai-mai-ta sunan ta Hadima Urmi, jinjina kai yayi yace, "karki damu, kece Uwa Urmi ko??"
Tace, "eh nice"
Yace, "ko zaki iya bai labarin abunda ya faru cikin nutsuwa ina son sanin d'an waye wannan"
Zama tayi sannan ta fad'a masa iyayen yaron har zuwa barwa Maharani shi da sukayi, cikin tausayi ta cigaba da cewa, "Maharani tana son yaron nan sosai hakan nema yasa ake son kashe shi sabo da indai ta rasa shi zataji ba dad'i yanzu nima kaina ina cikin wanda suke son ganin bayan mu, rayuwar mu tana cikin had'ari, haka suke kawo mana farmaki a ko wane lokaci ba zato ba tsammani Allah ne kawai yake temakon mu"
Jinjina kai yayi yace, "zan yi mata magana, amma wace masarauta ce suke son sace ta"
Da sauri tace, "Marudha ce"
Jinjina kai yayi tareda cewa, "karki damu komai ze wuce insha Allahu"
Cikin farin ciki tace, "nagode sosai d'an nan Ubangijin ka yayi maka Albarka"
Murmusawa yayi har cikin ransa yana mamakin k'arfin kafirci irin na mutanen masarautar ace duk yawan su ba musulmi.
Tana zaune a wata haraba had'ad'd'iya
Tasha ado, Arjula ce ta sakko kusa da ita tana karkad'a jela.
Ganin hakan yasa ta gane akwai magana, hannun ta mik'a mata, ta haye,
Kallon ta tayi a marairaice tace, "Arjula?? Fad'a min me yake faruwa"
Shiru tayi na d'an wani lokaci kafin ta zaro ido tareda cewa, "Aruuf ya baki wasik'a ki kai masarautar Marudha kuma??
Me yace?"
Daga masarautar Purlasirie.
Na shirya tsaf domin taren ko wane k'alu bale da zan fiuskanta daga gareku, sai dai fitina ba itace a gaba na ba yanzu, zefi mana sauk'i muyi sulhu tsakanin mu kuma mu had'e kan mu, be cancanta mu zauna muna raba gari ba bayan kuma akwai wanda suke son ganin bayan mu mu duka, kamata yayi mu had'a k'arfi da k'arfe mu yak'e su kuma mu nema kan mu da mutanen mu y'anci, nakasta junan mu ba shine mafita ba, kiyi tunani Maharani Sameena, idan baki hak'ura da d'aukar fansa akan abunda nayiwa d'an ki ba? To ki zo har inda nake ki rama, ni na zubar da makamai na bana shirin yak'ar ki domin hakan bashida wani amfani, daga Maharani Mahalakhshmi"
Muryar sa ce ta tsinkaye ta,
Da sauri ta zuba masa ido cikin ranta tana mai-mai-ta abunda bakin sa yaje furtawa har ya kammala kafin ta mik'e cikin gadararren takun ta ta k'araso gaban sa, a dake tace, "me kake nufi da hakan??? Karanbanin ka har ya kai nan koma ya wuce?? Har kana ganin kayi isar da zaka rubuta wata wasik'a da yawun masarauta ta?"
Murmushi yayi yace, "dad'i na dake bakya cin riba, ni a nawa tunanin hakan shine dai-dai ina amfanin fitina Lakhshmi?? Ni bansan ana irin wannan yak'in da ake karkashe mutane ba, kuma Marudha zata iya temaka miki akan way'an da suke hak'on su cimmi ki, dad'i na dake girman kai amma idan kinyi tunani zaki gane hakan shine dai-dai addu'ar da zakiyi a yanzu itace Allah yasa su amince da hakan"
Shiru tayi tana d'an tunani kafin tace, " idan aka samu matsala ka yarda ka d'auk hukunci na??"
Yace, "na amince, tinda Allah yasan da kyakkyawar niya nayi hakan, amma mutanen ki suna cikin wani yanayi, Mahalakhshmi me ze hana ki dawo da Abdulkareem kusa da ke? "
Ido ta zuba masa kamar wadda take shirin had'iye shi sun ja lokaci suna kallon kallo kafin tace, "a kan wane dalili??"
Ba tareda shakka ba yace, "akan ana son kashe shi!!! a gani na ki dawo dasu nan har Uwar Hadimai Urmi "
Murmushi tayi tace, "na amince da hakan ka nemo min Hadima Farhana"
Juyawa yayi ba tareda yace mata k'ala ba ya bar wajen.
Ta raka shi da ido tanajin wani yanayi yana riskar ta, har ya 'bacewa ganin ta bata dena kallon hanyar da ya tafi ba, lumshe ido tayi tareda sauke wata sassanyar ajiyar zuciya, akan la'b'ban ta ta mai-mai-ta "AruufulAnsaar "
*Ga masu buk'atar shiga group na musamman domin jin k'arshen Labarin Naira 100 ne kacal😂 ku hanzarta ku mallaki naku kar a barku a baya🤣 domin k'arin bayani ku neme ni tanan 👉🏻 08146838480*
Kallon Arjula tayi cikin nutsuwa tace, "Arjula? Meyesa Aruuf yake kiran suna na haka kai tsaye?? Jarumi na ne kawai yake kirana Lakhshmi ko Mahalakhshmi kai tsaye, yana da abun Al'ajabi a tattare dashi"
Da sallama ya shiga inda Abu Ansaar yake ya same shi zaune ya zuba tagumi hannu bibbiyu, da sauri ya k'arasa yana cewa, "Abu lafiya kuwa?"
Tatta'be baki yayi cike da rigima irin ta tsoho ya fara hawaye yana cewa, "d'a na ni dai kazo mu tafi gidan mu mubar wannan masarautar ina jin tsoro, akwai abubuwa sosai a cikin ta harda marasa kyau,
Yau wata mata tazo tace min in gaggauta d'auke ka mu tafi idan ba haka ba sai ta kashe mu duka, kuma shak'e min wuya tayi banyi tunanin ma zan zo yanzu a raye ba, d'a na ka rufa min asiri ka tashi mu bar wannan masarauta tin kafin su kashe mu"
Ido Ansaar ya zuba masa zuciyar sa tana wani irin harbawa,
Baki a sake da tsananin mamaki yace, "Abu na wacece??'"
Abu Ansaar yace, "ban santa ba yaro amma duk inda taje tazo y'ar cikin masarauta nan ce, tayi ado irin na sarauta sosai amma ni ban santa ba bata fad'a min sunan ta ba kawai tace min na d'auke ka mu tafi wai kana yi mata shigar kutse a cikin rayuwar ta"
Aruuf yace, "Abu dan Allah zaka iya kwatanta min yanayin ta? Ina son sanin ko wacece, ni dai a sani na bana shiga hurumin ko wace mace idan ba Lakhshmi ba ta yaya kenan zan shiga rayuwar wata?? Ko dai Farhana ce? Abu babba ce ko yarinya??"
Abu Ansaar ya ta'be baki kafin yace, "naga duk ka firgice ne, da alamu dai bakayi musu laifin komai ba, kawai ganin ka ne basa son yi, dama su mutane haka suke dan haka d'ana kawai mu bar musu masarautar su, ita babba ce ba yarinya bace, nima ba dan nasan lakhsmi Maharani d'in ba da zance ko itace dan tayi ado irin nasu amma ita wannan babba ce dan kuwa zata iya kaiwa tsarar mahaifiyar ka, tace wai rayuwar ta da d'an ta kake shiga shiyasa"
Shiru yayi yana d'an tunani kafin yace, "tace ina shiga rayuwar ta da d'an ta?? Kenan wannan wacece? Kuma kace tayi ado irin na Lakhshmi ko? Ba kuma mahaifiyar Ramraj bace?? Ita kuma bata da gatan da zatayi irin wannan adon sosai a masarautar nan, kuma ita ba wata babbar macece ba,
Abu kai na ya kulle anya kuwa ba Gimbiya jusi bace??
Idan haka ne kenan ita ma tana da wani k'uduri mummuna akan Lakhshmi??
Kuma a hakan kake cewa na bar masarautar nan Abu??
Kasan had'arin da mutanen cikin ta zasu fuskanta idan bana nan??
Lakhshmi duk tunanin ta yana ga wani da take jiran zuwan sa ta rasa yadda zatayi komai ina son temaka mata sosai Abu"
Jinjina kai yayi yace, "nima ina so ka temaka mata d'ana amma rigimar sarauta sai y'an sarauta su d'in ma ba kowa ne yake iya ta ba, kuma wadda kake zato be zamo lallai ace itace ba domin kuwa nasan gimbiya Jusiyya sosai ba itace tazo guri na ba, wata ce daban,
'Dana kayi k'ok'ari kamar nan da kwana uku kayi abunda zakayi mu gudu kaji ko?? Ka nema mana alfarma a wajen Rani"
Jinjina kai Ansar yayi yace, "shikenan,
amma ni yanzu duk na kasa fahimta, na zauna ina hira da wani tsoho Udday yace ba d'an masarautar nan bane kai ma gashi wata tazo wajen ka kuma bana jin itama y'ar wannan masarautar ce, gaskiya akwai rikici"
Abu Ansar yace, "d'ana ni dai duk inda ka shiga ka dinga addu'a Allah ze warware maka komai"
Ya gyad'a kai tareda amsawa da "to"
Arveen da Waziri suna zaune suna tattaunawa akan abunda ya shafe su, Arveen yace, "Baba ni fa har na fara kwatanta yadda zan gudanar da mulki na, kowa sai ya tabbatar an samu canji ni bazanyi yadda Maharani Mahalakhshmi takeyi ba, zan bawa kowa damar sararawa da y'an mata ba tareda hukunci ko doka ba,
Amma fa bayan wannan babu wani abu me sauk'i, hukunci na kuma sai yafi nata tsauri"
Waziri yace, "idan ka zama sarki ita kuma ya zakayi da ita??"
Kai tsaye yace, "zan maida ita baiwa ta ko kuma na kulle ta a kurkuku ko Baba??
Ko kuma ta zauna a me kula da matata"
Waziri ya shek'e da dariya yace, "lallai d'ana mulkin ka zo ze da abun mamaki, ina son ganin wannan ranar ni kaina sai na dinga gwangwajewa ta"
Arveen yace, "karka damu baba"
Wani matashin ba fade ne ya shigo yana kai gaisuwa suka amsa tareda bashi umarnin ya fad'i abunda yake tafe dashi.
Da sauri yace, "ranka yadad'e Shugaban mu na gobe wato Aruuful Ansaaar dai ya aikawa Masarautar marudha wasik'a akan neman sulhu a yanzu zancen nan da muke Sarauniya Sameena ta amince da hakan haka itama Sarauniyar mu ta amince yanzu gaf suke da had'e hannayen su guri guda su zama tsintsiya mad'aurin ki d'aya, sannan wannan Aruf Ansar da kuke gani makirin mutum ne yanzu ya riga ya gama mamayar zuciyar sarauniyar mu, abubuwa da dama shine yake tsara mata yadda zatayi, sai kun tashi tsaye a kansa idan ba haka ba ze baje tsarin ku kuna zaune, kuyi hanzarin sanin abunyi ranka yadad'e"
Tini zuciyar Arveen ta fara tafasa yayi kicin kicin da rai.
Waziri ne ya kalli bawan yace, "yanzu ka zo da labarin da ya fusata d'ana dan haka ba kai ba samun kyauta yau ka tashi kaje"
Sim sim ya tashi ya fice, ko babu komai ya isar da abunda yake son isarwa.
Waziri ya kalli Arveen cikin son kwantar masa da hankali yace, "haba jarumin d'ana be kamata abu kad'an ya dinga fusata ka ba,
Zamu san abun yi"
A harzuk'e yace, "kar in bari abu kad'an ya fusata ni wannan kake kira abu ka d'an??
Haba kace ka samo mana mafita ashe hanyar da bata 'bullewa ka kai mu,
A memakon masarautar Marudha ta tarwatsa ta yanzu sai su had'e kai dan temakon juna? Meyesa hakan???"
Yayi tambayar a tsawace.
Waziri ya dafa kafad'ar sa tareda cewa, "yi hak'uri d'ana kwantar da hankalin ka ni nasan hakan ma baze yuwu ba"
Maharani tana zaune Ansaar ya iso inda take, ba tareda ya jira umarni ba ya nemi kujera ya zauna kusa da ita.
Ido ta zuba masa tana jin wata irin kibiya tana sukar zuciyar ta.
Da d'an murmushi akan fuskar sa yace, "ba abu ne fa me wuya ba Lakhshmi, ki bawa masarautar Marudha hak'uri baya nufin kin fad'o, domin kuwa shi shugaba da son zaman lafiya aka san shi, hakan da zakiyi shine ze k'ara kankaro martabar ki a wajen wasu, kiyi k'ok'arin danne zuciyar ki karki bari girman kai yasa ki fad'a halaka, ki rubuta wasik'a yanzu yanzu Lakhshmi,
Gobe ki tashi mutanen ki suyi tafiya zuwa can domin isar da sak'on, kiyi komai da tsari kuma da mutuntawa"
Daga haka ya tashi yana shirin barin wajen.
Sunan sa da ta kira ne yasa ya fasa tafiyar ya juyo yana kallon ta.
cikin murmushi me cike da shauki tace, "Aruuful Ansaar, Tumhara har kaam bahut khub hota hai"
(Aruuful Ansaar Ko wane aiki naka yana kyau)
Murmushi yayi tareda d'an rissinawa.
Hakan ya sumar da ita a zaune, yau ne rana ta farko da ta ta'ba ganin ya risina mata, hakan ya sata cikin nishad'i, ita kad'ai tayi ta murmushi tana tunanin irin yanayin sa da d'abi un sa.
Da daddare ta kaiwa Ummee ziyara,
Cikin sanyi ta zauna kusa da ita tareda rik'i hannun ta, a marai-rai-ce tace, "Ummee na yak'i dawowa gare ni gashi har wani yana nema ya gaje fadar sa, ko dai ya mutu ne??"
Girgiza kai tayi alamar a'a ko kuma bata sani ba.
Murmushi tayi tace, "Ummee mutum d'aya ne ya ta'ba sanya shauki a cikin tunani na bayan shud'ewar wani lokaci"
Duk da irin yanayin da take ciki be hana kyakkyawan murmushin ta bayyana ba, ta lumshe ido tareda had'iye wani mugun yawu.
Maharani tace, "zan iya tafiya?"
Gyad'a mata kai tayi.
Ta tashi tana murmushi ta koma turakar ta.
Hadima Urmi ce ta shigo hannun ta rik'e da Abdulkareem wanda yayi wayo ya girma har ya fara irin gwaranci na yara.
Tana ganin sa fara'ar ta ta k'ara fad'ad'a da sauri ta taso ta kar'be shi tana cewa, "Abdulkareem!!
Ido ya zuba mata ko k'iftawa baya son yi.
Ta saki murmushi tareda hura masa iska a fuska sai kuma ya k'yalk'yake da dariya.
Sake rungume shi tayi tareda sumbatar goshin sa tace, " ina fatan nasara wa rayuwar ka Abdulkareem "
Uwar Hadimai Urmi tace, "Ranki yadad'e naji kamar yana buk'atar ganin ki ne shiyasa na shigo miki dashi ina godiya k'warai da gaske da ya kasance kin dawo damu kusa da ke, anan zamu fi samun kwanciyar hankali"
Ta murmusa tareda cewa, "uwa urmi ai wannan ba komai bane gareki, kije kawai yau zan kasance tareda Abdulkareem"
Tayi godiya sannan ta fice.
Yau ta kasance rana ce wadda ake lullumi babu rana sai hazo da hadari da suka zagaye sararin samaniya iska tana kad'awa kad'an kad'an,,, sakamakon Albarkar shuke shuke da tsirrai da suke dasu a yanki yasa k'amshin su yake tashi yana bazawa ko ina.
Cikin nutsuwa take shiryawa cikin wani Sari ruwan makuba (coffee ) wanda aka yiwa ado da ruwan gwal (golden ) yayi matuk'ar dacewa da jikin ta yayi mata kyau sosai,
ta d'auki wata dank'areriyar sark'a ta zuba a wuya har sai da ta kai kan cikin ta kallo d'aya zakayi mata ka gane ta madarar gwal ce sai shek'i da walwali take, haka tayi ta saka kayan ado ta ko ina sosai tayi kyau kamar sabuwar amarya, tana gama shiryawa ta zura takalmin ta,
Wajen taga ta nufa tana lek'awa, sassanyar iskar da take kad'awa ta shak'a taja numfashi kafin ta sauke ajiyar zuciya, murmushi ta saki saboda tunanin da ya fara bijiro mata,
A duk lokacin da yanayi ya kasance irin wannan takan kasance a mak'ale dashi domin kuwa tana matuk'ar jin dad'in irin wannan yanayin yayin da ta kasance a tareda shi, idan bazata fita ba haka shima bazata barshi ya fita ba sai dai ya rungume ta kawai, tayi bacci ta farka shi kuma yana ta gadin ta, idan kuma zata fita ko a ina take ko a wane yanayi take ko yawan mutanen da suke guri baya hana ta shigewa jikin sa, amma sauyin rayuwa ya sa itace me fita ko wane irin lokaci ana ruwa ana rana ana sanyi ko ana iska baya hana ta fita domin al'umar ta.
A take wata muguwar kewar sa ta tsirga mata tin daga sama har k'asa , idanun ta suka cicciko da k'wallah, tafukan hannun ta tasa ta goge su kafin ta fara takawa cikin nutsuwa tayi hanyar waje.
Ko ina ta ratsa d'iban gaisuwa ake da mik'o jinjina, da kyar take iya amsa musu saboda yanayin da ta tsinci kanta a ciki,
Haka ta cigaba da ratsawa har ta isa bayan masarautar,, bakin tank'amemem ruwan da yake gudana ta tsaya tana kallon furrai da tsirrai tana matuk'ar jin dad'in daddad'ar iskar da take gudana.
Ta dad'e anan tana tunanin rayuwar baya da kuma wadda zata kasance nan gaba, tana jin zuciyar ta na mata barazana akan irin abunda yake shirin faruwa, duk da tana da k'warin guiwa amma tana matuk'ar tsoron wannan Azzalumar masarautar domin kuwa d'aukar fansa ce zata dawo dasu wajen ta.
Tana cikin tunanin taji an rungume ta,
Wani bahagon numfashi ta fizga tareda zazzaro ido a razane.
Muryar sa ce ta daki dodon kunnen ta cike da kulawa yace....
(Su o'o har an baza kunnuwa aji me yace hhh😂😜😜a dena sa ido😎)
*Ga masu buk'atar shiga group na musamman domin jin k'arshen Labarin Naira 100 ne kacal😂 ku hanzarta ku mallaki naku kar a barku a baya🤣 domin k'arin bayani ku neme ni tanan 👉🏻 08146838480*
"Mad'aurin rigar ki ne ya kwance shine zan gyara miki"
Duka ta tattaro k'arfin ta ta bangaje shi, a zafafe ta yarfa masa wani shigaggen mari, fuska a had'e tace, "ka shiga tai-tayin ka Aruuf,,
Maharani Mahalakhshmi ni ba kamar ko wace mace bace, bana buk'atar gigi, ban amince wani ya kusanci kusa