x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 8 - TAJMAHAAL

  • 21001 words
  • 24000 words
  • Out of 37284 words

Category: Love Stories

Views 133

29 May 2025
Start ads
After Image Ads
dubawa kafin ta mik'e cikin sauri ta nufi wata sark'ak'iya dake cikin Masarautar, cikin wani madai-dai-cin gida wanda akayi sa ginin dutse da dutse, ta shiga babu komai sai duhu a ko ina kamar gidan fatalwa loko loko a gidan anan ne fa ta rasa ina zata dosa,
Wata murya ce ta katse mata tunanin ta da cewa, "Barka da zuwa, ki biyo ni"

Cikin sauri ta marawa budurwar wadda ta rufe fuskar ta ruff baya cike da fargaba da tunanin ina aka kawo ta haka?? Duk da tasan waye me kiran nata tasan bazata samu matsala ba.

Wani lungu suka shiga suna fita sai gasu a wani babban d'aki wanda hasken kendir da fitulu ya wadata, can ta hango shi a kashingid'e kan wata hamshak'iyar kujera irin ta sarauta sai lumshe ido yake da alamar yana tunanin wani abun ne ko kuma wani abun yayi masa dad'i.

Murmushi ta saki kafin ta k'arasa gefe ta tsaya tareda cewa, "Sannu da hutawa magajin izza"

Wani sukurkutaccen murmushi ya saki tareda jinjina kai ba tareda yace komai ba.

Murmushi tayi tace, "da alama yau Sarautar ta motsa ne"

Budurwar ce ta kar'be zance cike da kishi tace, "k'warai Sarautar ce ta motsa kinsan abunka da jinin abun sai anyi hak'uri"

Ta k'arasa maganar tareda zama kan makekiyar kujerar da take kusa da ita ta hard'e k'afa d'aya kan d'aya, cike da izza taci gaba da cewa, "naga ma kina da matuk'ar amfani gareshi har da yake iya shareni ya saurare ki, ina kishi da hakan gaskiya"

Murmushi Hadima Farhana tayi cike da jarumta tace, "wai ke wacece ke ne?? Naga koda yaushe fuskar ki tana rufe ne, bansan wace fuska bace bare na gane ta ishe ni kallo ko bata ishe ni ba, ki zauna a iya matsayin ki domin ba take nake ba"

Cike da takaici tace, "me kike tak'ama dashi ne da har kike fad'a min duk maganar da tazo kan harshen ki??

Zatayi magana ya dakatar da ita da cewa, " barka da zuwa Hadima Farhana zaki iya zama anan"

Ya fad'a yana yi mata nuni da gefen sa.

Cikin gadara ta k'arasa ta zauna ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya.

Cikin sauri ta sauke ta-ta k'afar ta kalle shi rai 'bace tace, "meyesa haka Kumar?? Wannan fa baiwa ce a wannan Masarautar meyesa zaka bata y'ancin da har zanyi abu tayi??

Rausayar da kai yayi tareda sakin wani malalacin murmushi yace, " kwantar da hankali mana,
Farhana karki damu akanta tana da kishi ne sosai"

Farhana tace, "ohh ita d'in matar ka ce??

Girgiza kai yayi tareda cewa, " bazance a'a ba kusan hakan dai"

K'asa Hadima Farhana tayi da kai cikin ranta tana wasu y'an maganganu.

Gyara zama yayi tareda cewa, "game da zuwan wancan Bawan, yanzu wane hali shugabar taku take ciki?

Hadima Farhana tace, " indai akan wannan ne tabbas tana cikin damuwa domin kuwa marin ta da yayi da kuma nuna mata iyakar ta hakan ba k'aramin tayar mata da hankali yayi ba"

Kumar yace, "ya batun zuwan ta Masarautar Maruda?
Da kuma auren da Waziri yake son shirya mata?

Lumshe ido tayi ta bud'e kafin tace, " bana jin wannan k'udurin nasu ze kai ga cin galaba akanta, zuwan Ansaar ya tarwatsa komai ya tarwatsa manufofi da shirye shirye da dama ni kaina zuwan sa ya rusa min shirin da na tsara, yanzu nasan ita kanta Maharani Sameena tana can cikin rud'ani da tashin hankali, domin kuwa tarihi ne yake k'ok'arin mai-mai-ta kansa kamar yadda kuke fad'a"





*(Kuyi hak'uri da wannan dan Allah,, ina bala'in yin ku VIP grp musamman Ummu Taslim Ummu Sulaiman Maman Najwa sai kuma Waziriya ta ta hannun daman wato Salmaji Ce, sai kuma babbar Aminiya ta Jiddah Shajarafi y'ar Mutan KT da sauran su,,, ina godiya Allah yabar k'auna)*




*INDO CE..*
[20/03, 11:03 a.m.] INDO CE..: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhUTxJ28ext83rI6uvV1xB

*🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠*

(Masarauta)


Mallakin

*INDO CE..*



🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼


*Page~11*


بسم الله الر حمن الر حيم




*Ga masu buk'atar shiga group na musamman domin jin k'arshen Labarin Naira 100 ne kacal😂 ku hanzarta ku mallaki naku kar a barku a baya🤣 domin k'arin bayani ku neme ni tanan 👉🏻 08146838480*



Jinjina kai yayi tareda cewa, "k'warai haka wannan yake sai dai dole akwai matakin d'auka kafin abu ya rinca'be amma yanzu bamu da makama ya zame mana dole mu dakata na wani lokaci kafin mu gane bakin zaren"

Hadima Farhana tace, "na yarda da hakan"

Zaune yake ya zuba tagumi yayi zurfi cikin tunani, sama ta ka yaji muryar ta ta ratsa dodon kunnen sa,
Yamutsa fuska yayi ba tareda ya kalli inda take ba,

K'arasawa tayi kusa dashi ta tsaya tana kallon sa har wani lokaci kafin ta durk'usa dai-dai shi sannan tace, "Sannu da hutawa Aruuf"

Ba tareda ya kalli inda take ba yace, "Barka da fitowa"

'Dan murmusawa tayi tareda lumshe ido sannan tace, " da fatan babu wata damuwa"

Gyad'a kai kawai yayi ba tareda yace komai ba.

Cikin nutsuwa tace, "Aruuful''Ansaar ko zaka iya fad'a min ina mahaifiyar ka???"

'Dan kallon ta yayi ya kawar da kai sannan yace, "na rasa ta tin ina k'arami"

"Kenan baka san lokacin da ta mutu ba??"

Girgiza kai yayi tareda cewa, "a'a na rayu da ita na wani lokaci har na fara girma sannan ta mutu"

Tace, "ooh na taya ka bak'in cikin rasa ta domin kuwa rashi abu ne me tsanani ga wani sai dai kuma wasu garesu rashin shine abunda yafi dad'i, babu yadda muka iya tinda mu dai mun riga mun rasa,
Banji dad'i ba Ansaar, kenan yanzu kana tareda mahaifin ka ne??

Kai tsaye yace, " hakan ne ma yasa nakejin ba dad'i saboda tsallake umarnin sa da nayi"

'Dan kallon sa tayi ta gefen ido cike da son gane gaskiya da kuma banbance tantamar da take tace, "kenan bazaka iya sanar dani sunan sa ba??

Ba tareda ya jira wani abu ba yace, " Abu Ansaar, da haka nake kiran sa dan haka kema ki kira shi da hakan"

Jinjina kai tayi tace, "na yarda da hakan,
To amma a wane yanki kuke zaune??
Kace a daji kuke rayuwa baka san mutane ba kuma wai da gaske ne hakan??

Gyad'a kai yayi yace, " muna rayuwa ne a cikin wani daji da yake mak'ota da wannan k'asar mu ba'a cikin ko wane yanki muke ba, cikin wannan dajin shine kawai duniyar mu banida wasu abokanai sai dabbobi da tsuntsaye, nasan ma yanzu suna can cikin damuwa suna nema na,
Ki barni na koma ga mahaifi na"

Jinjina kai tayi tace, "na gamsu da maganar ka, amma na kasa yarda cewa kanada mahaifi kuma shi mahaifin naka shine wanda ya haife ka da gaske, ka tabbatar iyayen ka ne su d'in?? Kuma baka da dangi ko da guda d'aya bayan iyayen ka?"

Zuwa yanzu ya fara gajiyawa da irin tarin tambayoyin da take aza masa, a k'agauce yace, " sune suka haife ni idan ba haka ba ai bazanyi miki k'arya ba domin ni na yarda da hukuncin Addini na duk wani mak'aryaci yana kan hanya mara kyau shiyasa na za'bi fad'en gaskiya akan k'arya, kuma banida wasu dangi Ummu Ansaar da Abu Ansaar sune kawai dangi na, ina fa da hankali na meye kike tunani ne a kaina?? Banajin yin surutu amma kin sani magana, ki fitar dani daga wannan kurkukun ki barni na tafi gurin Abu na"

Girgiza kai tayi tace, "zan k'ara tsananta bincike akan ka, idan kuma na gane k'arya kake wani ne ya aiko ka ko kuma kai d'in wani ne ba wanda ka fad'a ba ka sani ni a guri na gutsire maka kai abu ne ne sauk'i, idan kana son fita daga nan ya zama dole ka cike sharrud'a na bin dokar masarauta ta sahu da k'afa, haka yin abunda duk wani bawan wannan masarauta yakeyi,
Girmama na sama da kai a cikin bayi na ya zama dole kai d'in k'ask'antacce ne a cikin su domin kuwa ranar ka ta farko a cikin yankin da bakasan suwaye suke rayuwa a cikin sa ba, ka aikata kuskuren da ze ta bibiyar ka har k'arshen rayuwar ka,
Ka yarda da sharrud'ai na sannan na fitar da kai daga sijn idan ba haka ba rayuwar nan ta kama ka, zan aikawa mahaifin ka wasik'ar gayyatar sa zuwa wannan masarauta kuma koda yazo bazan bari ka ganshi ba"

Shiru yayi yana nazari har wani d'an lokaci sannan yace, "na amince zan zama bawan naki indai zaki fitar dani daga nan, ban saba irin wannan rayuwar ba, kuma ina son ganin Abu na"

Mik'ewa tayi tareda cewa, "kayi tunani me kyau"

Daga haka ta fice zuciyar ta tana sak'a mata abubuwa daban-daban.

Kai tsaye wajen Ummee ta nufa.


Tana tsaye ta jingina a jikin bango idanun ta a lumshe,
Cike da sa ran jin muryar ta wanda ze tabbatar mata da cewa jarumin ta ya bayyana tace, "Ummee????"

Shiru batayi magana ba hakan yasa taji zuciyar ta tayi wani wawan zillo lokaci d'aya taji ta fara sarewa,
Cikin rawar baki ta k'ara furta " Ummee??"

Idanun ta kawai ta bud'e ta zuba mata, har lokacin bakin ta gum kamar bata ta'ba magana ba.

Maharani ta k'ara ware Ido tana kallon ta a razane, cikin kad'uwa tace, "Ummeeh? Hakan yana nufin kenan baze dawo ba?? Kenan Ansaar ba shine Jarumi na ba???
Na shiga rud'ani na kasa ganewa Ummeeh dan Allah yau dai kiyi magana"

Ta k'arasa maganar a ma-rai-rai-ce.

Jin Ummein ba tace komai ba yasa taji wasu zafafan hawaye sun gangaro kan fuskar ta, tafin hannun ta tasa ta goge su, cike da tausayin kanta tace, "zan cigaba da zaman jiran sa har lokacin da ze zo, bazan ta'ba gajiya ba har lokacin da ze bayyana gare ni, nasan baze guje ni ba ko Ummee??"

Ummi kam ta kasa magana sai wasu hawaye da suke ta gudu kan fuskar ta.

Cikin sanyin jiki ta koma sashin ta, cikin ranta taji gaba d'aya Ansaar ya fice mata a rai tamkar wani babban mak'iyin ta takejin sa.

A ranar tasa aka fito dashi daga kurkuku sai dai duk da haka yana tareda tsaro a duk motsin da yayi, har mamakin yadda ta mayar dashi kamar wani dabba yake.

Lokacin da aka zauna a fada ta rubuta sak'o ta aika dakaru suyi tafiya zuwa inda Ansaar yayi mata bayani ba dan komai tayi hakan ba sai dan ayi mata bincike sosai banda haka da Arjula kawai zata aika.

Da gudu gudu gimbiya Sunaya ta shiga turakar ta tareda k'walawa Raj kira.

Da sauri ya tashi yana tambayar ta lafiya.

Jikinta har rawa yake tace, "Raj yau Maharani tace ka shirya zaku shiga daji tare, hakan ya sani farin ciki sosai"

Cikin rashin fahimta yace, "Mama wai dajin gaske?? Nifa tsoro nakeji"

Tsaki ta rafka cike da takaici tace, "kai kuwa anyi soko Raj, a memakon kayi murna zakace wani tsoro kakeji?? To ai kuwa tace jarumtar ka take son gwadawa sai ka shirya kafin ranar zata sa gasa tsakanin kai da ita, kuma na rantse idan ka tsaya jin tsoron nan sai na shak'e ka ka mutu"

Cikin sanyin jiki yace, "Shikenan Mama zan shirya amma dai gaskiya inajin tsoro"

Dafa kafad'ar sa tayi tace, "kwantar da hankalin ka yaro na kar kaji tsoron komai ai nasan baza ta cutar da kai ba,
Kawai kayi k'ok'ari sosai kaji??"

Gyad'a mata kai kawai yayi ba tareda ya gamsu ba.

Hannun ta hard'e a bayan ta tayi tsaye tana tsammanin zuwan sa,
Bayan wani lokaci dattijon ya k'araso bakin sa d'auke da wasu Addu'o'i
Sai da ya kai matsaya sannan ya dakata cike da kulawa yace, "Maharani Mahalakhahmi"

Cikin sanyi tace, "Guru banyi zaton cewa wanda ya shigo cikin mu a yanzu ba jarumi na bane, shin da gaske ne hakan??

Jinjina kai yayi yace, " k'warai ba shi bane, sai dai kiyi hak'uri Amma wannan ba shine wanda kike jira ba, amma wata rana shi d'in ze bayyana"

Kamar zatayi kuka tace, "kenan wannan waye???"

Yace, "kamar yadda ya fad'a miki haka gaskiyar sa take,
Sai dai wani abunda baki sani ba, koda jarumin ki baya tare dake to tabbas wannan ma bango ne a gareki shi d'in abun bauta ya jefo shi gareki ne domin ya temaka miki"

Murmushi tayi tace, "nagode amma bana jin akwai wani, wanda ze iya maye min gurbin sa dan haka bani da wata alak'a da Aruuful'Ansaar bana buk'atar ko wane temako nashi,
Ya zauna a matsayin sa na bawa,
Na barka lafiya guru"

Daga haka ta juya ta fice zuciyar ta cike da takaici.

A can dajin kuwa sun tarar da Abu Ansaar cikin kid'ima da tashin hankali duk ya rame yak'i cin abinci yayi kuka har ya gaji ya bari,
Ba k'aramin farin ciki yayi ba da yaji inda d'an sa yake se dai yaji takaici sosai da suka sanar dashi hukuncin da Maharani ta yanke masa na zama bawan ta,
Babu yadda ya iya haka ya tarkato y'an komatsen sa ya biyo su suka dawo cikin masarauta.

Tinda suka shigo ta zuba masa ido tana daga sama a kishingid'e kan wani madai-dai-cin gado wanda yaji ado irin na tambarin masarautar, jinjina kai tayi kafin ta mik'e ta ta taka zuwa gaba, cikin d'aga murya tace, "ina yi maka barka da zuwa wannan masarauta Abuu Ansaar da fatan zaka kar'bi hukunci na"

Da mamaki yace, "wane irin hukunci kuma ranki yadad'e??

Murmushin gefen baki tayi tace, " hukuncin da na yanke akan d'an ka sannan ina buk'atar jin dalilin ka na turo shi cikin masarauta ta ya tayarwa mutane na hankali"

Dafe goshi yayi cike da tsoro yace, "ranki yadad'e ba da nufi ne hakan ta faru ba, ba nine wanda na turo shi ba domin kuwa babu abunda ze iyayi gareku yake wannan Sarauniya,
Ni yaro na ragon maza ne ko rik'on wuk'a be iya ba face wuk'ar da ze yanka nama,
Bare kuma ya iya rik'on takobi ko kuma wani mugun makami,
Shi ba wani jarumi bane kamar yadda kukayi zato, bashi da k'arfi haka kuma bashida wata dabara, amma ubangijin mu Allah yayi masa halitta irin ta jarumai amma sam ba haka yake ba, ki gafarce shi Sarauniya, a bisa rashin sani ya shigo yankin ki, be ta'ba shiga duniyar da mutane suke rayuwa ba sai yanzu, yana cikin wasa ne ma akan dokin sa har ya shagala yayi nisan da ya kai ga shigowa nan dan haka zan d'auke shi mu tafi ba fad'a ba tashin hankali, ni ban iya fitina ba bare na koya wa d'ana, dan Allah kiyi hak'uri"

Jinjina kai tayi tace, "Na yarda da abunda ka fad'a, amma barin ku wannan masarautar ya sa'bawa k'a'ida ta, d'an ka dole ze kasance anan domin kuskuren da ya aikata kuma kai ma ta shafe ka"

Rai 'bace Ansaar yace, "wannan zalumci ne, meye abunda mahaifi na yayi miki? Ni nayi miki laifi dan haka karki sake ki ta'ba mahaifi na"

A yatsine tace, "ba'a musayar yawu dani Aruuf ka kiyaye"

Abu Ansaar durk'ushewa yayi a wajen ya fashe da kuka tareda cewa, "haba d'ana koda ka tsallako iyakar duniyar mu meyesa ka za'bi wannan duniyar ka shigo cikin ta, kazo duniyar da ake zubda jini ake yin zalumci, gashi ta raba ni da kai"

A hankali ya durk'usa gaban Abu Ansaar zuciyar sa na rad'ad'i, cikin son kwantar masa da hankali yace, "karka damu Abu na, babu abunda waccan yarinyar ta isa tayi maka indai ina nan, na amince zanyi komai da ta sani indai har zan k'waci kimar ka Abu na, ka dena kuka Allah yana tare damu"

Rungume d'an nasa yayi cike da k'auna irin ta d'a da uba,
A hankali ya shiga shafa bayan sa yana cewa, "Abu Ansaar dan Allah karka damu ko ina ne zata kai ka ka sani zanzo gareka, kuma idan ta cutar da kai to fa bazan ta'ba k'yale ta ba"

Abu Ansaar yace, "yaro na nasan ma bazata cutar dani ba, kawai ina tsoron kar ta wahalar min da kai ne"

Murmushi yayi tareda shafar kumatun Abu Ansaar yace, "indai a kaina ne kar ka damu babu abunda ze faru kaji Abu na??"

K'ok'arin raba sun da dakarun suka shiga yi ne yasa ya janye jikin sa ya mik'e yayi gefe, yana kallo suka tafi da mahaifin sa, duk da ransa baya so haka nan ya hak'ura"

Ko ina ciki da waje ya d'auka Maharani zata shiga daji tareda Raj.

Tana cikin shirye shirye Arveen ya sanar mata da buk'atar sa ta shiga gasar, ba dan taso ba tace ta amince.

Tana cikin tafiya ta dawo daga wajen Abdullkareem taga ya sha gaban ta,
Da tsananin mamaki ta zuba masa ido ba tareda tace masa komai ba.

Tini sojojin ta suka zagaye shi suna shirin kai masa hari tayi saurin dakatar dasu.

Gyara tsayuwar sa yayi yace, " a gani na tinda masu shiga gasa sun zama biyu ke ba girman ki bane kice zaki gwada dasu ki hak'ura ki bar su su biyu"

Shiru tayi na wani lokaci kafin ta d'an murmusa tace, "nan masarauta ta ce, mutanen cikin ta mutane na ne, Arveen da Raj su kuma jini na ne, kaga baka da alak'a da tsara min yadda zan tafiyar da komai nawa, kuma in jaddada maka ba'a shiga gaba na idan ina tafiya nakan sa yankewa mutum k'afa, to amma kai bak'o ne kana buk'atar uzuri ka kiyaye gaba"

Murmushi kawai yayi yana mamakin yadda take d'aukar kanta kamar itace tayi kanta, yana mamakin yadda mulki yasa takejin gaba d'aya itace sama da kowa a duniya.

Anyi gumurzu sosai tsakanin su biyu ita da Arveen sai dai duk da hakan itace ta kayar dashi a gasar ya rage daga ita sai Raj,
Bayan sunyi nisa ta kalle shi cike da kulawa tace, "Raj kasan meyesa nace mu shiga daji tare domin farauta??

Girgiza kai yayi yace, " a'a"

Tace, "mahaifiyar ka ta haife ka ana tsaka da yak'i ne, a memakon kazo a jarumi sai ka zama tamkar mace, Rajkumari?? Ina so ka zama jarumin namiji wanda masarautar Purlasiri zatayi Alfahari da kai
End Ads