x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 5 - TAJMAHAAL

  • 12001 words
  • 15000 words
  • Out of 37284 words

Category: Love Stories

Views 132

29 May 2025
Start ads
After Image Ads
jini,
Kina kallo take irin wannan aikin,,,,,,,,
Hadima Farhanaa kinsan wacece mahaifiyar ki??????

Girgiza kai tayi cike da k'agara.

Yace, " mahaifiyar ki itace wannan matar da take d'aure a kurkuku, kullum azabar safe daban ta dare daban karki zata kawai kulle ta tayi a gurin nan, a'a azabu take mata iri-iri, mace me kyau ga hankali da nutsuwa, amma zalumcin Mahalakhshmi ya mayar da ita mahaukaciya,
Mahaifin ki kuma mutum ne me daraja amma yarinyar nan ta zubar masa da mutuncin sa tasa yayiwa mahaifiyar ki fyad'e har aka haife ki, bayan tasa ya aikata wannan mummunan abu sai ta kashe shi,
Ita kuma mahaifiyar ki tasa aka kulle ta ake wahalar da ita,
Ke kuma take amfani dake wajen bata kariya da biyan buk'atun ta, ita muguwa ce muguwar da ta wuce duk zaton masu zato,
Kar kiyi tunanin mutanen gari suna binta ne saboda nagartar ta, su sunsan halinta ne shiyasa, kawai saboda tsabar zalumcin ta ne yasa idan kana son zaman lafiya ka nuna mata so amma badan suna sonta bane,
Farhana ki zo mu had'e mu yak'e ta domin mu kawar da mulkin zalumci daga wannan yanki namu me tsohon tarihi"

Cikin kuka Hadima Farhana tace, "kana nufin ba ta hanyar halak iyaye na suka haife ni ba???

Yace, " k'warai da gaske itace tayi sanadin hakan, shiyasa tak'i baki labarin suwaye iyayen ki, haka take ce miki ma itace ailar zuwan ki duniya.




*INDO CE..*
[01/03, 6:28 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠*

(Masarauta)



Mallakin

*INDO CE..*

Marubuciyar
SIRRIN K'ETA.
A JINI 'DAYA.


🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼


*Page~7*


بسم الله الر حمن الر حيم



Free page



*Tajmahaal na kud'i ne Naira 100 kacal cikin rahusa😄*

*Domin magana dani ta prvt ga link👇*

https://wa.me/message/45UKV47T7IM2F1


*(Sanarwa!!! Assalamu'alaikum masoya littafin TAJMAHAAL na fara kar'bar kud'in sa daga yau (1 March 2022) 100 ne ba yawa😊 ku hanzarta mallakar naku tin kafin ya koma 200 😅 Domin neman k'arin bayani ku tuntu'be ni ta wannan link na sama👆sai na jiku🥰)*



Ya k'ara da cewa baya ta wuce kiyi tunani akan goben ki, idan kika k'waci mahaifiyar ki daga wannan k'uncin nasan zatayi matuk'ar farin ciki"

Girgiza kai tayi tana cewa, "sai naji kamar k'arya ne kamar hakan bata faru ba, meyesa zatayi min haka?"

Murmushin gefen baki yayi yace, " dama ba lallai ki yarda ba domin kuwa ta riga ta tirke ki, amma kiyi tunani sosai duk hukuncin da kika yanke ina jiran ki- ki same ni anan"

Daga haka ya cigaba da tafiya ba tareda ya k'ara cewa uffan ba.

Kuka ne ya kufce mata ta shiga rero shi.

Dai-dai lokacin hadarin da ya had'o ya fara wani irin rugugi yana tsawa gami da walk'iya tareda iska, ruwa me k'arfin gaske ya sakko lokaci d'aya.

Mik'ewa tayi domin gudun dukan ruwan dan kuwa sanyi takeji saboda zazza'bin da ya rufe ta saboda mugun jin da tayi,
Cikin sauri sauri take tafiya kamar daga sama ta fara jin kukan Abdulkareem,
Hankalin ta ne ya k'ara tashi ta shiga dube dube a gurin cike da rashin tsoro,
Tana cikin dubawa tayi karo dashi an yasar dashi a sararin Allah ruwa sai jibgar sa yake,
Cikin sauri ta k'arasa ta d'auke shi ta rungume tana k'ara rarraba ido, gilimin mace ta gani ta wuce da gudu ba tareda da tabari ta shaida ta ba, taso binta amma sanin bazata iya ba saboda rawar sanyin da take yasa ta fasa,
Kai tsaye sashin Maharani ta nufa zuciyar ta na tsinkewa fargaba da tsoron irin yadda Maharani zata fuskanci abun ya cika mata zuciya,
A bakin k'ofa ta durk'ushe cikin rawar murya tace, "Maharani??"

Cikin nutsuwa ta sakko daga kan gadon ta ta nufo inda take zuciyar ta na wani irin bugawa a dari da sittin,
Hannu ta mik'a mata ba tareda tayi magana ba.

Cikin sauri ta bata shi tareda cewa, " a gafarce ni Ranki yadad'e"

Ido ta tsura masa har wani lokaci kafin tayi magana cikin matuk'ar razani tace, "waye???

Hadima Farhana tayi k'asa da kai cikin sanyi tace, " bansan ko waye ba Hazoor (Ranki yadad'e) kawai na tsinkayi kukan sa ne ina cikin tafiya koda na duba shine na ganshi cikin wannan halin ruwa yana dukan sa, sai kuma naga gilmin wata mace amma ban shaida ko wacece ba, wannan shine iya abunda na sani, ki fuskance ni dan Allah kar kiyi min gurguwar fahimta"

Jinjina kai tayi tace, " kenan akwai masu son ganin bayan sa??

Hadima Farhana tace, "sosai duk wanda yake son ganin bayan ki ze iya ta'ba yaron nan domin hakan yana girgiza ki.

Rungume shi tayi tsam a jikin ta tana k'ara zuba masa ido, murmushi me tafe da hawaye ne ya su'buce mata cikin sanyi tace, " duk abunda yayi tsanani yana tareda sauk'i, wata rana hakan ze zama tarihi kamar yadda abubuwa da dama suka zama,
Ya zama dole a ninka tsaro akan sa, ki nemo min Uwar Hadimai Urmi kuma ki had'o min da Subbhu Da Uddaiya gobe ina da magana dasu a k'aramar fada ta, sannan ki kula da kanki kema"

Mik'ewa tayi tana cewa, "ina godiya Sarauniya, zanyi kamar yadda kikace"

Batace komai ba sai ma komawa da tayi ta kwantar dashi kan gado, Arjula ta kalla cikin rauni tace, "wai sai yaushe ne ze dawo Arjulah??
Tin inada sa rai har na fara karaya, tabbas idan be zo ba mak'iya zasu hallakar dani sannan su cutar da mutane na, bana son abunda ya faru a baya ya k'ara faruwa, ya kamata yazo gareni tin kafin k'arfi na ya k'are, Na mallaka rayuwar wannan yaro gareshi ne a matsayin mahaifi idan be zo ba tayaya Abdulkareem ze san yana da uba?,
Ina son yaron nan kamar yadda nake son sa hakan ta faru ne tin lokacin da na fara d'ora ido na akan sa, idan aka cutar dashi tabbas anyi min matuk'ar illa a rayuwa ta, bana so hakan ta faru Arjula, yanzu shikenan ya gujeni??"

Wasu zafafan hawaye ne suka gangaro kan kumatun ta,
Goge su tayi kafin ta fara k'ok'arin bawa Abdulkareem temakon da ze dawo hayyacin sa.

Washe gari kamar yadda tace hakan akayi, tattaunawa ta gaggawa sukayi yayin da ta tuhumi Hadima Urmi akan abunda ya faru, sai dai itama lokacin da za'ayi hakan make ta akayi ta fad'i a sume, hakan yasa ta bar zancen domin kuwa batajin Hadima Urmi zata bada kai wajen cutar da ita.

Waziri.
Zaune yake kan wani k'awataccen lilo ya kashingid'e sai wani irin murmushi yake me cike da tarin manufofi.

Arveen ya kalle shi cike da k'aguwa yace, "Baba wai wane irin tunani kake haka wanda yake sa ka wannan murmushin???

Kai tsaye yace, " farin ciki, inaji a jiki na lokacin nasara ta ya fara, amma idan muka bari Gimbiya Sunaya ce zata cike mana ramin da muka dad'e muna ginawa ba tareda mun cimma ruwa ba, yanzu kuwa mun fara ganin idon ruwa tayaya zamu bari ta dawo mana da aiki baya?? Wannan tunanin nayi kuma na gano mafita shiyasa nake murmushi yaro na"

Shima murmusawa yayi tareda cewa, "na san kaci dubu sai ceta Baba na, ni kuwa ban ta'ba tunani akan Sunaya da d'an ta ba, kuma tabbas zasu rushe mana tubalin mu, ya zamuyi dasu Baba??

Waziri yace, " yarinyar nan ta cika ta tumbatsa hallau kuma ta shahara, tinda ta hau mulki bata ta'ba nema na a matsayin wazirin wannan masarauta ba komai ita take yankewa da kanta, tayi fatali da dokokin masarauta da tsare tsaren ta babu rawan ta da shawartar wani sai wannan d'iya musulmar nan Farhana, to nima a wannan lokacin na yanke mata hukunci a matsayi na na yayan uban ta zan nemo mata auren wani yarima d'an Sarauniyar da takeji da kanta take takara da ikon Mahalakhshmi, yaron yana da mugun son mata kuma ita d'in macece wadda kowa yake sha'awar ta dan haka idan na had'a su sai na koma gefe na zuba ido, idan ya aure ta kaga shikenan mu kuma sai mu shigar da k'udurin mu"

Dariya Arveen ya farayi kamar sabon mahaukaci.
Cikin rashin ganewa Waziri yace, "yaro na?? Meye kuma na irin wannan dariyar???

Arveen yace, " Maha? Mahalakhshmi ce zata amince kayi mata za'bin aure ina ai bazata amince ba"

Waziri yayi murmushin manyan ce ya rausayar da kai kafin yace, "Yaro na ka girmi Mahalakhshmi sai dai kuma duk da hakan nine na haife ka, na haifi kamar ka ma bare kuma ita?? Na riga na shirya tin kafin na fito, shiyasa nace maka shi d'in yana da son mata bare kuma ita, nasan a nashi gigin dole ze kai hannu jikin ta, kasan meye abunda zatayi?? Y'ar k'aramar wuk'ar da take sokewa a k'ugu zata zare ta yanka masa tafin hannun sa, ta yuwu ma harda wani hukuncin zata had'a masa idan yayi wasa ma a ranar ba lallai yaga uwar sa ba, kuma kana ganin mahaifiyar sa zata amince??? a lokacin da ta haruzuk'o tace bazata yarda ba nasan zatayi ta tunanin hanyar da zatabi don ta rama abunda Mahalakhshmi tayi mata zata shiga tashin hankali dan tasan Maha tafi k'arfin ta, ni kuma a lokacin zan tunzura ta akan cewa idan bata aurawa d'an ta Maha ba bazata ta'ba rama abunda akayi mata ba, kaga daga haka na had'a hatsaniya tsakanin manyan masarautun nan guda biyu idan yaso su kashe kansu, mu dama ai dukan su adawa muke dasu domin kuwa sunyi mana tazara sun nuna mana iyakar mu"

Arveen yayi dariya tareda cewa, "lallai Baba na kana da matuk'ar basira wannan abu yayi"

Farhana ce tsugunne a gaban Mahaifiyar ta idanun ta suna zubda k'walla, cikin rawar murya tace, "Mama???

'Dago zararrun idanun ta tayi ta zuba a kanta tana binta da kallo irin na mamaki.

Farhana ta rik'o hannun ta gami da Fashewa da matsanancin kuka, sai da ta sassauta sannan tace, " Mama kiyi hak'uri a bisa shareki da nayi shekara da shekaru, bansan cewa ke d'in mahaifiya ta bace amma yanzu insha Allah zaki samu kulawa daga gareni bazan k'ara barin ki ba Mama, dan Allah kice wani abu, kiyi min magana ko zanji dad'i kice kin yafe min Mama ko kina fushi dani ne???

Girgiza kai tayi alamar a'a idanun ta suna zubar da hawaye kamar famfo sai dai ko motsa baki batayi ba bare sa ran magana.

Hadima Farhana tasa gefen mayafin ta tana goge mata k'wallar cike da k'auna gami da tausayawa.

Mik'ewa tayi tana cewa, "zan dawo na k'ara duba ki Mama bazan k'ara bari a zalumce ki ba"

Raj.
Yana kwance ya tada kai da cinyar Gimbiya Sunaya yana kallon sama sai murmushi yake.
d'an dukan sa tayi a kafad'a gami da cewa, "kai d'ana na lura yanzu soyayya tasa ka fara zauncewa, wannan murmushin da kake sunan sa me??? Bana son lalaci fa, kasan ita sarauniya sai dai jarumi amma kai gaba d'ayan ka rago ne, bana so ta saka gasar shekara ka kasa cin gasar hakan ze zubar maka da martaba da kimar ka kaji ko?? Dan haka kayi k'ok'arin zama jarumi kafin lokacin"

Dariya yayi yace, "Mama?? Ai nasan tana so na ko banci gasa ba amma dai zanzama jarumi kamar yadda kike so Mama ta"

Dariya tayi tace, "shashashan d'ana"

Kamar yadda yace su had'u haka suka k'ara had'uwa a gurin waccan ranar.

cikin k'unar zuci da 'bacin rai Hadima Farhana tace, " na amince da buk'atar ka, zanyi duk yadda zanyi na k'wato mahaifiya ta daga wannan mugun k'arnin bazan iya cigaba da kallon ta a haka ba, na yarda na had'a hannu da kai domin kawo k'arshen zalumci, daga yau na dawo tsagin ka, tin yanzu ma a fara daga wane mataki zamu d'ora???

Jinjina kai yayi yace, babu shakka kinyi tunani me kyau Hadima Farhana fatan zaki cigaba da bada k'ofa, yanzu abunda zaki fara shine jiyo mana sirrin ta da duk wani shirin ta haka ne ze sa musan ta wace k'ofa ya kamata mu shigo mata"

Hadima Farhana tace, "zanyi hakan ba tareda na nuna mata wata alama ba, zan zauna a matsayin yardarjiyar ta sai dai kuma ba hakan bane yanzu bakin alk'alami ya riga ya bushe, zata gane kuren ta tabbas tinda abun nata haka yake nima bazanji tausayin ta ba"

Da haka suka rabu kai tsaye ta koma wajen ta domin lokacin cin abinci ta yayi.

Bayan an kammala zaman fada waziri ya taso ya dawo kusa da ita, cikin nutsuwa da nuna kulawa da kamilanci yace, " y'ata? Be kamata ki zauna ba aure ba har yanzu,ya kamata kiyi aure kodan mu k'ara samun k'warin guiwa akan ki, baza mu so rasa jinin ki ba y'ata, ki manta da abunda ya wuce ki gina rayuwar ki ta gaba"

Girgiza kai tayi tace, "waziri ka tsaya a matsayin ka karkace zakayi kutse a cikin lamari na domin baka da wani amfani gareni banajin zanyi wani aure dan haka ka k'yale ni"

K'ara marairaice fuska yayi yace, "haba y'a ta? Gimbiya Jusiyya kina jin abunda y'arki take cewa?? Ke kad'ai ta yarda dake dan haka kiyi mata bayani yadda zata fahimta, ya kamata tayi aure domin shine cikar y'a mace"

Gimbiya Jusiyya taja dogon numfashi gami da jinjina kai sannan tace, "shikenan zanyi nazari akai"

Sosai Gimbiya Jusiyya tayi tunani akan goben y'ar ta a take taji ta aminta da shawarar Waziri, hakan yasa ta lalla'ba Maharani Gami da binta da nasihu masu ma'ana har ta amince.

Waziri jiki na rawa ya aikawa masarautar sakon gayyata, abunka da me jiran kad'an ba 'bata lokaci suka amsa tareda tsayar da ranar zuwa.


*Karku manta ku biya domin ku karanta cikin Aminci😊*



*INDO CE..*
[03/03, 11:56 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠*

(Masarauta)



Mallakin

*INDO CE..*

Marubuciyar
SIRRIN K'ETA.
A JINI 'DAYA.


🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼


*Page~8*


بسم الله الر حمن الر حيم



Last Free Page



*Tajmahaal na kud'i ne Naira 100 kacal cikin rahusa😄*

*Domin magana dani ta prvt ga link👇*

https://wa.me/message/45UKV47T7IM2F1



*(Sanarwa. Ga masu buk'atar siyan littafin TAJMAHAAL har yanzu k'ofa a bud'e take ku gaggauta mallakar naku ku karanta cikin aminci da kwanciyar hankali😊 Kuyi min magana ta wannan link na sama👆 sai na jiku😊)*


*(k'arshen shafin kyauta, daga yau indai kuka ga littafi na a waje to ba da izini na ba, ku daure ku siyi naku 100 ba yawa)*



Kamar me tsoron taka k'asa haka take takawa har ta isa cikin kurkukun.

Kamar yadda ta saba tana ragu'be a gefe ta kifa kanta cikin guiwoyin ta tareda rungumo k'afafun ta da hannayen ta.

Cikin nutsuwa ta k'arasa, a kanta ta tsaya gami da zuba mata wadatattun idanun ta,
Ta dad'e a haka kafin ta durk'usa kan guiwoyin ta tana fuskantar ta,
Cikin wata irin murya me cike da aminci tace, "Ummeeh???

'Dago idanun ta da sukayi jajur tayi ta zuba su a kanta.

Kallon kallo suka fara yiwa juna ido cikin ido babu wanda yayi alamar janye kowa kallon tuhuma yake watsawa kowa, (Maharaniey Mahalakhshmiey,,) ce, (Sarauniya Mahalakhshmi ) ce ta katse shirun cikin maraitacciyar murya tace, " Ummeeh!?? wannan ne karon farko da na fara karya miki alk'awari, kiyi hak'urii nima ba'a son rai na hakan ta faru ba, Farhana ta matsa ne shiyasa amma ba da son rai na bane Ummeeh, karkiyi fushi dani,
kiyi magana karkiyi shiru kice min wani abu Ummeeh!!

Ba tace komai ba sai zuba mata idanun ta da tini hawaye suke zirya a cikin su tayi.

Hannu tasa tana share mata k'wallar sannan ta Dafa guiwar ta cikin rauni tace, "kenan?? Bazan k'ara jin muryar ki ba? Shikenan bazaki k'ara ce min komai ba?? Kiyi magana Ummeeh dan Allah,
Magauta zasuyi nasara a kaina sun fara cin galaba ta ,
Na fara gajiyawa komai ya fara k'are min, sun kusa yin nasara a kaina, Ina jin bak'in ciki sosai zuciya ta tana k'una idan na ganki ina tuna abubuwa da dama,, na kasa mantawa, komai ya juya min yanzu, na kusa sarewa Ummeeh kiyi magana,
Idan na 'bata miki rai ne akan Farhana kiyi min hukunci amma karkiyi fushi dani, hakan ze k'ara jefa rayuwa ta cikin yanayi , yanayi mara dad'in gaske, idanun ki suna zubar da hawaye Ummeeh, ashe akwai wannan ranar? Da zata zo min da irin wannan barazanar tana nuna min hawaye a idon ki???????, ki dena kuka Ummeeh , meyesa zuciya ta take gaya min abu da dama?? Yaushe ne komai ze dawo dai-dai??
Surutu na bashi da amfani gareki kenan?? Ko meye zan fad'a baza kice komai ba?

Fad'awa tayi jikinta tana kukan zuci me tsananin rad'ad'i da k'una.

A hankali ta d'ago hannu ta d'ora a kanta tana shafawa har zuwa gadon bayan ta cikin sigar rarrashi.

A hankali ta fara sauke sassanyar ajiyar zuciya har wani lokaci kafin ta janye jikin ta tana kallon ta kallo me tarin ma'anoni,
Cikin sanyi tace, " Ummeeh inaji a jiki na kamar baya zata dawo"

Mik'ewa tayi tana goge fuskar ta ba tareda ta k'ara cewa uffan ba ta juya tabar wajen..


Kamar yadda suka tsara haka komai ya tafi dai-dai,
Ba dan taso ba suka shirya komai, kamar yadda waziri yayi zato hakan ta faru Maharani kuwa ta balle tace bata san zance ba,
Mahaifiyar sa kuwa ranta yayi bala'in 'baci,
haka aka tashi wasu da farin ciki wasu akasin haka.

Bata tsaya cikin masarautar ba har sai da ta danga da waje sannan ta tsaya tana kalle kalle zuciyar ta na zafi, bak'in ciki da takaicin abunda Waziri yayi mata ya
End Ads