ta fara had'a mabiya ta hanyar nuna musu tausayin ta a zahiri hakan yasa suke son ta kuma suke girmama ta sosai.
Abu Ansaar yana zaune dafa'an akan Sallaya bayan ya idar da sallah ya 'buge da kuka domin kuwa tin safe yasa a nemo masa d'an sa sai dai shiru ba'a ganshi ba ba labarin sa, hakan ba k'aramin tayar masa da hankali yayi ba dan ya riga ya saba basa iya nesanta da juna.
Yana cikin wannan yanayin Aruuf ya shigo sai k'asa k'asa yake da ido.
Da sauri ya tashi ya nufi inda yake yana cewa, "d'ana meyesa zaka tafi ka barni??? Yanzu har ka iya yawon da zaka dinga nesa da mahaifin ka?? Karfa ka manta kai kad'ai ne d'ana kaine nake kalla naji dad'i gashi na rasa matata bare nasa ran zata haifa min wani, idan na rasa ka komai ya k'are min d'ana"
Rungume shi Ansaar yayi yana d'an bubbugar bayan sa alamun rarrashi,
Cikin salon kwantar da hankali yace, "Abuu ka dena cewa haka dan Allah bazan nesanta da kai ba fa, koda yaushe ina tareda kai, ni d'a ne kawai a wajen ka amma ni kaine duniya ta ban canja ba har yanzu Aruuf d'in ka ne ni"
Turo baki yayi kamar me shirin sake fashewa da wani kukan, yace, "d'a na to ai naga baka tafiya ka barni ne yau kuma naga ka tafi baka dawo ba ina ta neman ka"
Jan hannun sa yayi ya zaunar dashi sannan yace, "Abu kana da abun mamaki sosai, baka tsufa sosai ba sannan kuma kai ba yaro k'arami bane amma kana da irin abun yara ko tsafaffi ai bazan 'bata ba kawai dai na d'an shiga gari ne"
Ya fad'a yana goge masa k'wallar cike da kulawa.
Abu Ansaar yace, "yaro na ba dai kana so na ba?? To ai kuwa yanzu zaka shirya gobe mu fita da assubuh mu bar wannan k'asa na gaji da zaman cikin ta yana da kyawu mu koma yankin mu, karka manta muna da y'an uwa muna y'ay'a da abokai a can kuma sun shak'u damu bazasu ji dad'in rashin mu ba, ko ka manta dasu ne?? Tsuntsayen ka da dabbobin ka??"
Jinjina kai yayi yace, "Abu meyesa baza mu cigaba da zama anan ba?? Nifa naji dad'in zama tareda su"
Da sauri Abu Ansaar yace, "o'oo yaro na nan fa rayuwar su ba irin tamu bace, kar kace haka, kar ka fara jin dad'in zama dasu ni kam tsoron su nakeji, ni dai mu tafi kawai nasan Sarauniya baza ta hana mu ba"
Aruuf yace, "Abu kwana biyu fa??"
*(Last Free Page)*
Dafe goshi yayi ya rashe da kuka yana cewa, "yanzu Aruuful Ansaar jindad'in ka da zama da mutane har yasa kana tunanin baza mu koma dajin mu ba? Ni kuwa ina zan kai Alk'awarin da na d'aukarwa mahaifiyar ka??
Me kake so in gaya mata idan nima na mutu??
'Dana ka biyo ni mu koma inda muka fito anan nafi jin dad'in rayuwa bana son mutane, kuma yanzu duk sun tsane mu duk cewa suke ka addabe su, bana so su kashe min kai Aruuf"
Shiru yayi yana nazari har cikin ransa yakejin k'unar kukan mahaifin nasa, hannun sa ya rik'o cikin nutsuwa yace, "Zamu tafi Abu amma ba da wuri ba, zan sanar mata kar mu tafi ba'a son ranta ba a samu matsala kasan ta zubar da jini baya yi maya wahala, idan na gaya mata ko zuwa da yamma sai muyi tafiyar mu, nima bana son zama anan tinda baka so Abu, mu koma muyi rayuwar mu tareda tsuntsayen mu da dabbobin mu, sune abokanan mu be kamata muyi tarayya da mutane ba, ka kwantar da hankalin ka Abu"
Share hawayen yayi yana murna, cikin fara'a yace, "to d'ana bazan kuma kuka ba amma indai bamu tafi gobe ba zanyi kuka na gaji da zaman nan ba'a yawo ba'a zuwa ko ina ba'a farauta ba'a wasa koda yaushe ina a wannan turakar jinake kamar ta d'aure ni ne, ai nasan ma zata bar mu mu tafi ai laifin da kayi mata tayi naka hukunci nasan yanzu ta hak'ura"
Aruuf yace, "eh mana ai yanzu ta hak'ura kuma zata bar mu mu tafi"
Washe gari, fitowar ta kenan daga turakar ta ta nufi fada,
Cikin hanzari ya tari gaban ta, ba tareda ya jira shan k'amshin ta ba ya fara isar mata da sak'on Abu Ansaar.
Ido ta zuba masahar wani lokaci kafin ta rik'o hannun sa ta fara jan shi.
Tin yana tirjewa har ya gaji ya bita zungui zungui.
Har sai da ta dangana da turakar ta sannan ta tsaya ta saki hannun sa, a tsawace tace, "mai-mai-ta abunda ka fad'a"
Ba tareda shakka ba yace, "mahaifi na baya son zama a cikin mutane kuma nima ba tareda su na taso ba dan haka muna son komawa yankin mu, Abu Ansaar yace na nemi Alfarmar ki ki bari mu mu koma"
Zuwa yanzu tini jikin ta ya d'au wata irin kakkarwa idanun ta har sun fara canja kamanni, takobin ta ta zaro a fusace ta tsarga rigar da take jikin sa,, a take faffad'an k'irjin sa ya bayyana..
Cikin tsananin mamaki da al'ajibi ya tsaya yana binta da ido.
Itama k'are masa kallo tayi sama da k'asa, ganin bata ga abunda zuciyar ta da idanun ta suka dad'e suna muradin gani ba yasa tayi wurgi da takobin tareda fashewa da wani gigitaccen kuka ta durk'ushe kan k'afafun ta.
Zuwa yanzu abun ya fara zame masa kamar almara ko motsawa ya kasa yi sai binta da ido kawai da yake ya kasa fahimtar komai.
Sai da ta d'ebi d'an lokaci tana kuka kafin ta tsagaita, be ankara ba sai jiyayi ta rungume shi tsamm tana sakin wani sabon salon kukan.
Take yaji yanayin bugun zuciyar sa ya canja shi kanshi jin sa yake kamar ba shi ba, da kyar ya iya cewa, "Maharanie Me yake faruwa??? "
Sakin sa tayi ta juya masa baya cikin shashshekar kuka tace, "kowa cewa yake Mahalakhshmi ta samu me temakon ta ashe ba haka bane?? Meyesa ka za'bi tafiya ka barni bayan ka bari zuciya ta ta shak'u da kai???
Baka ta'ba tunanin dalilin da yasa kowa yake ganin kai jigo ne gareni ba??
Idan bazaka iya tausaya min ba Aruuf ka tausayawa dubban mutanen da suke baya na kuma suka dogara dani suka d'auki yardar su suka d'ora ta a kai na, kaji tausayin su karka tafi ka bar mu Aruuf ka kasance tareda mu, zuciya ta ta Alak'antu da kai fiye da yadda zaton ka yake baka, Aruuf ka tausaya min banida kowa,, bayan wani lokaci kaine wanda zuciya ta ta k'ara amincewa dashi, ina ji tamkar na samu wanda zan dinga gani ina jin farin ciki ashe kai a gurin ka ba haka bane, idan abunda nayi maka ne ka yafe min,
Bana so ka tafi ka barni zan shiga wani yanayi, kayi tunani akan goben mu yadda zata kasance, gaff suke da tarwatsa sansanin mu zasuyi min illah Aruuf kowa yana farin ciki an samu canji daga zuwan ka, ashe tafiya zakayi ka bar mu""
Sake rungume shi tayi tareda fashewa da wani sabon kukan.
Kamar bishiya haka ya tsaya kyamm, take yaji kansa yana wani irin juyi, wani wahalallen rauni ya ziyarci zuciyar sa kukan da take ya dasa masa miki a cikin ransa, lokaci d'aya yaji duk duniya bashi da za'bin da ya wuce ya zauna tareda su..............
*(Karku manta shine shafin k'arshe na kyauta🥰)*
*(shafin yau page 26 ni kaina nasan yayi wuta🔥🔥🔥🔥🤣😂😂😂)*