Gimbiya Jusi ce ta k'araso wajen cikin sanyi tace, "Maharani! Ina ma baki aikata abunda kika aikata ba?
Meyesa baza kiyi aure ba?
waziri gaskiya yake fad'a ba k'arya ba a gani na hakan ze fi mutumci da daraja gareki,
Meyesa kuma zaki ta'ba yaron mutane? Shifa ba d'an Tajmahaal d'in mu bane
Kuma Kin sani masarautar su jiran k'iriss sukeyi akan mu sun dad'e suna neman abunda ze had'a su da mu da kin k'yale shi ai ba kuskure ya aikata me girma ba"
A zafafe tace, "na k'yale shi kika ce??
Laifin sa ma ba babba bane!!
Dama ba kowa ne ze kalli abun da girma ba amma ni a waje na babban laifi ne kuma ba sai d'an wannan masarautar ba ko d'an waye dole ne ya kar'bi hukunci na idan yayi kuskure a duk inda yake bare kuma masarauta ta ya shigo, babban kuskure ne mutum ya kai hannan sa kaina dan kuwa hakan yana ta'ba jikima ta k'warai da gaske, kuma ko kece kikayi hakan tabbas bazaki tsira ba"
Jinjina kai Gimbiya Jusiyya tayi tace, "Maharani Maha gaskiya ne kina da darajar da kin wuce hakan to amma ina fargabar abunda muguwar matar nan zatayi bata da mutunci ko kad'an musamman ga duk wanda ya ta'ba d'an ta,
Tabbas waziri ya fad'i gaskiya da yace kiyi aure matsalar da ta faru da ba d'an mutunci yaso had'a ki dashi ba,
Amma Maharani? Sai yaushe ne zakiyi aure kuma waye za'bin ki??
Kallon ta tayi kafin ta maida hankalin ta kan ruwan da yake ta gudana, girgiza kai tayi tace, " ni bani da za'bi face za'bin Allah,
Ban sani ba ko yana raye ko ya mutu? Ko yana duniya ko akasin haka?? Ta yuwu ma a k'addara ta babu aure a ciki,
Na kasa gane meyesa kuke da son shiga sharafin da babu ku a ciki , ni bana tsoron ta haka bana shakkar ta duk abunda zatayi ina tsammatar ta,
Amma sai dai inaji a jiki na kamar hakan shiri ne, anyi ne domin a samu makamin tarwatsani"
Murmushi tayi ta k'ara da cewa, "Sai dai bana jin hakan zata yiwu abun bauta ze kawo min makamin da zan yak'i duk wani me shirin yak'a ta ko a gida ko a daji"
Gimbiya Jusi taja numfashi kafin tace, "naji dad'in jin hakan daga gareki, dama tsoro ba na jarumi bane, ina alfahari dake y'ata,
Zan wuce ciki sai kin shigo ko zaki zo tare dani!?
Girgiza kai tayi tareda cewa, " ki turo Farhana"
Murmushi tayi tace, "Sarauta izzarki tana burge ni yarinya ta, zan turo ta"
Daga haka ta juya ta nufi ciki.
'Boyayyar ajiyar zuciya ta sauke tareda dafe kanta da yake juyawa, tabbas wata rayuwar tana shirin kutso kai cikin rayuwar ta shin wane abu ne ze bayyana haka??
Suna zaune suna tattaunawa Farhana ta k'araso wajen a tsaye ta tsaya kafin tace, "meye shirin ka na gaba yanzu?? Maharani yanzu a cikin matuk'ar tsoro take domin kuwa abunda ya faru bazaka shigar da wani abu ba??
K'asaitaccen murmushi ya saki kafin yace, " gaggawar me kike ne?? Zuba ido zamuyi muga ta ina zasu fara 'bullo mata mu ma sai mu samu hanyar shiga hakan shine a tunani na bansan a naki ba amma meye ke abunda kike gani??
Farhana tace, "muguwar mata ina da wani mummunan kwanto a kanta zamu tsara komai a nutse, ni fa nace bazan iya k'yale ta ba, hankali na baze ta'ba kwanciya ba indai da ita a cikin gidan nan"
Kowa hada hadar sa yake a masarautar kowa yana ta kai kawo,,
Tana sama tana shan iska yayin da take kallon abunda yake faruwa a k'asan cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, jefi jefi idan ta tuna wani abu takan sauke gwauruwar ajiyar zuciya,
Gefen ta kuwa Fadya ce ta zuba mata idanu kamar wadda zata had'iye.
Jin ana kallon ta yasa ta juyo,
Da sauri Fadya tayi k'asa da kai tareda rintse idanun ta da k'arfi,
Cikin mamaki Maharani tace, "Meye abunda kike ne anan?? Na riga na iso inda zanje ai zaku iya tafiya domin kuwa ina son kad'aici ba buk'atar zuwa ku sani gaba"
Cikin rawar jiki Fadya tace, "Ranki yadad'e a gafarce ni, aikin mu ne tsaron ki sai dai bamu san hakan bakyaso ba da tini mun tafi, ina godiya sarauniya"
Jinjina kai tayi kafin tace, "zaku iya tafiya"
kafin su kaiga tafiya wani tsuntsu ya nufo inda suke, tsayawa sukayi kallon sa da mamaki,
Kai tsaye wajen da Maharani take tsaye ya nufa yana bud'e fuka-fukai.
Zuciyar ta na dukan tara tara tasa hannun ta ciri wasik'ar da yake tafe da ita tana cirewa ya juya yabar wajen,
Da ido ta bi wasik'ar cikin zuciyar ta tsoro da firgicin abunda zata gani ya gama lullu'be ta sai dai ko da wasa bata nuna alamar hakan ba.
Cikin nutsuwa ta fara warware ta, idon ta ya fara sauka kan Hatimin Masarautar Maruda,
Bugun zuciyar ta ne ya k'ara tsanan ta cikin k'aguwa ta k'arasa bud'e ta tafara karanta sak'on ciki.
"Maharani Mahalakhshmi tabbas kin aikata kuskure akan d'a na, kamar yadda baki aminta a ta'ba jama'ar ki ba sai kin d'au mataki haka nima ban amince a ta'ba tawa ba bare kuma d'an ciki na, ya zama dole ki biya abunda kika d'auka shine cikar kwanciyar hankalin ki, yanzu ne lokacin da zaki nunawa jama'ar ki son su kike ko kuwa kinfi son kanki ne, zasu fuskanci mummunan iftila'i daga gareni idan kin za'bi hakan idan kuma ba haka ba ki amsa kira na ki shigo cikin Masarauta ta ba tareda kowa naki ba, sai kinzo zaki iya banbancewa zaki fita ko kin shigo kenan,
Sannan idan zaki zo kiyi shirin amarci domin kuwa auren ki da d'ana shine kawai ze iya biya miki bashin da kika d'auka,
Kiyi tunani akan kanki da kuma mutanen ki za'bi ya rage naki duk hukuncin da kika yanke ki sanar dani,, kuma ki sani ko a yanzu akwai mutane na a cikin masarautar ki idan ma baki zo ba to tabbas za'azo a d'akko min ke har cikin fadar ki"
Dafe k'irji tayi saboda wani irin kad'uwa da tayi ta jigina jikin bango gami da lumshe ido.
Jiki ba k'wari ta koma turakar ta zama kawai tayi tana k'ara zubawa wasik'ar ido tarasa meyesa take jin gaba d'aya ta rasa wani karsashin ta da k'warin guiwar ta duk wata jarumtar ta ta k'wace mata sai wani mugun tsoro da firgici da ya sako ta gaba.
Tin daga ranar bata da wani kwanciyar hankali ko abinci bata iya zama taci duk da an k'ara tsananta tsaro a masarautar tana tsoron kar wani abu ya samu mutanen ta a dalilin ta,
Gashi har lokaci yana tafiya ta kasa tsayarwa zuciyar ta hukunci d'aya.
Kamar macijin da babu dafi take tafiya sululu har ta isa kurkukun tana shiga d'akin ta fad'a jikin ta tareda fashewa da wani hatsabibin kuka, taja lokaci tanayi kafin ta sassauta cikin rawar murya tace, "Ummeeh idan ban dawo ba dan Allah karki cigaba da irin wannan rayuwar yanzu zan saka kaina a kasada domin ceton jama'a ta duk sun ta'allak'a ne gareni bazan bari a cutar dasu ba, yanzu lokaci yayi wanda k'arfi na ya gama k'arewa zan amsa kiran Sarauniya Samina duk abunda tayi min zan d'auka ko zan fito ko bazan fito ba, banida masaniya akai nidai buri na d'aya ne kiyi min magana kafin tafiya, lokaci ya k'ure babu wani abu da ze iya dakatar da wannan abu da ya tinkaro ni, kuma na tabbata Waziri ne ya shirya min komai, nasan ke kin fahimta Ummeeh Amma Mama Jusiyya ta kasa fahimtar wanene shi,
Amma nasan indai har yana raye komai daren dad'ewa ze dawo kuma shine ze ceto rayuwa ta daga ko wane irin k'angi, ki gazgata min haka Ummeeh"
Mik'o mata wani abu tayi tana Gyad'a kai alamar haka ne,
Kar'ba tayi tana kallon abun kamar Rakhee da d'an mamaki tace, "menene wannan??
Bata magana dan haka bata da hanyar da zata iya yi mata bayani.
Share k'wallar ta tayi tana murmushi tace, " Nagode Ummeeh"
Cikin sauri ta tashi tabar kurkukun wani lungu ta shiga wanda ko mutane babu sojojin ma sai d'ai-d'ai da tafiyar tayi zurfi kuwa sai ya zamana babu kowa a wajen.
Wata Babbar k'ofa ce ta zallar k'arfe ta bayyana a gaban ta, cikin sauri ta shiga gurin take wani gunki ya bayyana a ciki, k'arasawa tayi a hankali tana kallon gunki fuskar ta cike da hawaye, durk'usawa tayi a gaban sa zata fara kuka kenan taji wata murya ta dakatar da ita da cewa, "Mahalakhshmiey Sarauniya ce kuma ita d'in jaruma ce wadda abun bauta be amince da zubar hawayen ta ba, hakan kuskure ne kike aikatawa abun bauta be amince ki zubda k'walla ba domin kina da k'arfin dantse da kuma k'arfin iko, ke d'in kin kasance jigo ce ga dubban Al'uma kece k'arfin su kuma k'warin guiwar su, idan suka ga hawayen ki hakan yana nufin kin gaza kenan hakan zesa su rasa duk wani karsashi, meye yayi zafi yasa ki cikin wannan hali yake wannan Sarauniya??
Da sauri ta tashi tana murmushi gami da goge hawayen, da farin ciki tace, " Guru Ummeeh "
Da sauri yace, "meye ya same ta??
Girgiza kai tayi tana murmushi, tayi taku biyu sannan ta juyo mik'a masa abun tayi tareda cewa ta bani wannan amma ta kasa magana sai yaushe zata fara magana Guru???"
Kar'bar abun yayi ya lumshe ido tareda damk'e Rakheen a hannun sa yana karanto wasu yan abubuwa, bud'e ido yayi ya mik'o mata cike da k'warin guiwa yace, "wannan naki ne a duk inda yake ze kasance tare dake,
Kuma ita d'in baza ta k'ara magana ba har sai ranar da ya bayyana a cikin Masarautar Purla a lokacin ne komai ze dawo mata dai-dai indai kikaji maganar ta to tabbas yazo, ki rik'e wannan duk inda kika shiga karki bari ki rabu dashi shi d'in kariya ne gareki"
Jinjina kai tayi tace, "Nagode kuma yanzu na samu k'warin guiwa amma Guru zan shiga Masarautar Maruda ban sani ba ko zan fito"
Kai tsaye yace, "kar kije, akwai matsala a shigar ki wannan Masarautar ki jira lokaci"
Had'e fuska tayi tana girgiza kai alamar a'a cikin k'asaita tace, "Guru iya abunda kake iya gani kenan ni kuma ina ganin goben mutanen wannan yanki nawa ne, zanyi komai domin na zama kariya garesu dan haka bana buk'atar ka dakatar dani ko meye ze faru zanje"
Yasan ba'ayi mata musu dan haka yace, "ina miki fatan nasara a rayuwa"
Juyawa tayi ta fice ba tareda ta k'ara tanka masa ba,
Tana dawowa turakar ta ta d'akko Alk'alami da abun rubutu domin rubata wasik'a zuwa ga Masarautar Maruda, Arjulaa sai k'ok'arin hana take amma tak'i ji har ta gama rubutawa sannan ta aika Arjulaa domin isar da sak'on, babu yadda Arjulaa ta iya haka taje ta isar.
Yau ce ranar da zata amsa kiran ba tareda ta bari kowa ya sani ba daga ita sai Farhana sai kuma d'ai-d'ai daga cikin wanda ta aminta dasu.
Farhana tashin hankalin ta ya kasa misaltuwa kwata kwata bata son zuwan Maharani amma ta rasa yadda zatayi ta dakatar da ita.
Tana zaune tana shiryawa ta zuba kayan ado a jikinta ta ko ina sai k'yak'yali take tayi kyau kamar ba gobe, fuskar ta fayau sai kwalli rad'au a idanun ta,
A zahiri mutum baze iya gane irin fargaba da tsoron da take ciki ba amma a zuci har yanzu addu'a take akan za'bi mafi kyawu ko zuwan ko akasin sa.
Wani irin bugawa zuciyar ta ta fara yi duff duff d'aya bayan d'aya,
A razane ta kalli Arjulaa tana cewa, "Arjulaa kina jin abunda nake ji?? A cikin Bugun zuciya ta nakejin Takun sawun gwarzon Doki tamkar a cikin zuciya ta yake tafiya, meye hakan yake nufi Arjulaa ki fita maza kiyi min bincike ki gane abunda yake faruwa.
Waziri yana kwance akan gadon sa suna hira shida d'an sa cikin farin ciki da nishad'i, lokaci d'aya ya fara jin bugun zuciyar sa ya fara canjawa ta ko ina yake jin takun Doki yana tinkaro sa da mugun k'arfi har gadon da yake kai yana amsawa, cikin sauri ya rik'o Hannun Arveen yana cewa, " Arveen duhu nake gani duhu!! duhu!!! Arveen, zuciya ta zata tarwatse jiki na rawa yake ka rik'e ni d'akin ya fara girgizawa Arveen"
Arveen kuwa ya kasa yin komai ga mahaifin sa saboda shima tini wannan iftila'in ya afko masa jikin sa ya d'auki wani mugun zafi.
Gimbiya Sunaya tana rik'e da abinci ta nufo turakar ta yayin da Raj yake kwance yana baccin sa cikin kwanciyar hankali, wata muguwar Tsawar da ta ratsa kunnuwan su ce tasa suka firgita a lokaci d'aya,
Watsi tayi da kayan abinci ta nufu Raj da gudu suka rungume juna a matuk'ar tsorace,
Raj da yake yana da mugun tsoro ga ragon ta tini ya fara kuka yana cewa, Mama Ido na ya dena gani Mama zuciya ta tana bugawa tamkar Takun fusataccen doki, ko dai yak'in da za'a rusa Tajmahaal yazo Mama??
K'ara rungume shi Gimbiya Sunaya tayi tana cewa, "'dakin mu yana girgizawa ko ina yana amsawa Raj wane irin Duhu ne yake tinkaro mu??
Nima inajin abunda kake ji d'ana karka damu kanka ko mutawa zamuyi tare zamu mutu bazan bari komai ya same ka ba"
Zamewa Gimbiya Jusiyya tayi yiifff ta fad'i a tsayen da take babu alamar numfashi a tattare da ita.
A firgice Hadimar ta tayi kanta tana kiran sunan ta amma ina, jijjiga ta ta shiga yi tana cewa ki tashi karki mutu banyi miki komai ba"
'Jakadiya ce tayi saurin k'arasowa tana cewa, "Ranki yadad'e me yake faruwa ne suma kikayi ko mutawa"
Hadima tace "bata numfashi anya ba mutuwa tayi ba???
Shiru sukayi suna kallon ta saboda bugawar da zuciyar ta ta farayi lokaci d'aya dufff dufff dudufff, kallon kallo sukayi take tsoro ya k'ara ziyartar su, a firgicr Jakadiya tace, " Takun Doki kuma Jarumin Doki tareda mugun duhu Hadima kinga mu tashi muyi ta kan mu domin kuwa mu abun bauta ya tseratar damu bamu shiga irin wannan hali ba dan haka kar laifin ya hau kan mu mu tashi mu gudu"
Kafin Jakadiya ta k'arasa magana tini Hadima taje wajen k'ofa suka rufa da gudu gudu suka bar sashin"
Tsananin Hargitsewar da kansa tayi da kuma irin rikicin da zuciyar sa ta shiga yasa ya fara fizge fizge da tirjiya yana ihu, da sauri tayo kansa tana furta sunan sa tareda tambayar lafiyar sa amma kafin ta k'araso ta yanke jiki ta fad'i,
Da kyar ya iya furta, "Zuciya ta zata fashe"
Hayaniyar da taji Masarautar ta kaure dashi ne yasa tayi saurin tashi ta d'akko abun hangen nesa ta lek'awa.
Hadima Farhana ce ta zuba a gaban ta tana haki tace, "kiyi sauri ki fito Hazoor akwai babbar matsala a Tajmahaal ki fito ki gani masarauta ta hargitse.
Da gudu gudu ta fito tana numfarfashi.
Inda take hawa domin yin sanarwa ta hau cikin d'aga murya tace, " kowa ya nutsu, maza a shirya Tarko akan ko wace hanya ta ko wace kusurwar Yankin purlasiri sannan a kulle ko wace k'ofa a bar guda d'aya itama a saka tsaro a kanta sannan a tura sojoji Dari uku wajen Masarauta domin yin bincike akai, a kad'a k'ararrawar yak'i domin tabbatarwa wanda basu sani ba, masu kibiya su dai-dai-ta kowa ya kasance cikin shiri domin fuskantar ko wace irin k'ura ce take tinkaro mu, muyi k'ok'arin bawa junan mu kariya"
Zuwa yanzu ta kasa magana saboda k'ara tsananta da bugun zuciyar ta yayi.
Bayan wani d'an lokaci...
*(karku manta wannan shine K'arshen shafin kyauta indai kuka ga littafi na a waje daga yau to ba da izini na ba, kuyi k'ok'arin mallakar naku kar ku bari a abar ku a baya )*
*INDO CE..*
[16/03, 8:37 p.m.] INDO CE..: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GhmvkCVguNJ004XgclluXD
*🎠🎠🎠TAJMAHAAL🎠🎠🎠*
(Masarauta)
Mallakin
*INDO CE..*
🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼
*Page~9*
بسم الله الر ØÙ…Ù† الر ØÙŠÙ…
*(k'orafe k'orafen da kuke min akan cewa na k'ara free pages yasa na k'ara muku😊😊 ina fatan zakuyi farin ciki da hakan🥰🥰)*
Arjula ta dawo tareda nufar inda shugabar ta take ta sauka kan kafad'ar ta.
Ido Maharani ta zuba mata cike da k'aguwa da son jin abunda take tafe dashi, lokaci d'aya jikin ta yayi wani mugun sanyi.
K'ara hargitsewar da masarautar tayi ne yasa ta matso domin ganin abunda yake faruwa.
Wata K'ararrawa aka shiga bugawa wadda ta k'ara gigita duk ilahirin mutanen cikin masarautar na ciki da waje kowa sai da ya bayyano kuma kowa ya mayar da hankali kan k'ofar masarautar domin kuwa k'ararrawar da aka kad'a tana nuni ne da cewar wani babban abu ya tinkaro cikin masarautar.
Kar'bar takobun ta wadda take cikin wani kyakkyawan kube tayi a hannun Hadima Farhana cikin sauri ta sakko k'asa cikin shirin ko ta kwana.
Dakaru kusan talatin ne rik'e da wasu mazajen sark'ok'i wanda suka yiwa wani mutum dabaibayi da su sai fizge fizge yake yana cewa su sake shi,
Har sai da suka dangana da gaban Shugabar su sannan suka tsaya.
Subbhu ne ya kalle ta cikin ladabi yace, "Ranki yadad'e wannan da kike gani wani bak'o ne ya shigo cikin yankin ki ba tareda izinin ki ba kuma ba tareda yabi dokoki ba ya shigo kai tsaye kuma gadan gadan a kan dokin sa ya razana duk mutanen mu dake wajen masarauta kuma shi d'in mutum ne me matuk'ar kafiya, fuskar sa a rufe take amma ya tirje ya hana mu bud'e ta gashi bamu san wane irin mutum bane, munyi amfani da tarkunan da kika bamu umarnun had'awa ne mun kama shi da kyar, ranki yadad'e yanzu wane hukunci kika yanke akansa??
Lumshe ido tayi tareda jan wani gwauron numfashi tana karanto addu'o'i
Bud'e ido tayi ta zuba su a kansa sannan ta kalli Subbhu a k'asaice tace, "ku sake shi"