x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 12 - TAJMAHAAL

  • 33001 words
  • 36000 words
  • Out of 37284 words

Category: Love Stories

Views 135

29 May 2025
Start ads
After Image Ads
dani ba shine zakayi min irin haka saboda ka samu fuska?"

Hannun sa dafe da kumatun sa cikin wata sassanyar murya yace, "kenan har ranki ya 'baci!?? Bana son hakan kiyi hak'uri, a bisa kuskure ne na aikata hakan nima kaina na sa'ba doka da k'a'ida ta, wannan baya d'aya daga cikin d'abi'a ko ak'ida ta ina neman afuwar ki"

A tsawace tace, "rufe min baki Ansaar!!! idan zuciya ta ta riga ta buga batajin magiya bata gane meye hak'uri bare ta tausayawa mutum iya abunda ta sani kawai hukunta duk wanda yayi mata kuskure, ka cancanci mummunan hukunci sai dai bazan iya yi maka shi ba, kuma hakan ya samo asali ne saboda ina mutunta addinin ka da kuma duk wani mabiyin addinin banda haka tabbas kai da kwanan farin ciki daga yau sai dai tarihi, Aruuf"

Kallon ta yake ido cikin ido a dake yace, "tabbas nayi kuskure amma irin hukuncin da kike yankewa mutane wani laifin sa be kai girman hukuncin ba, kin mayar da zubda jini tamkar ado ko kuma wani abu me kyau,
Na tsani wannan d'abi'ar taki,
Mutum ya aikata kuskure kad'an kiyi masa hukuncin kisa kin mayar da takobi abun k'arar da rayuka,
Ki jaraba koda sau d'aya ki dena irin wannan hukuncin ki samu jituwa da kusanci da jama'ar ki na tabbata hakan ze sa kiji sauyi sosai a tareda ke,
Bayan wanda kike so kuma kike jiran zuwan sa kin kasa sakin jiki da kowa,
Ba dole sai ahalin ka ne zasu ji'banci lamuran ka ba idan da kina jansu a jiki sosai nasan zaki fi haka samun salama domin nasan zaki samu masu d'ebe miki kewa ba adadi,
Nayi bincike akan mahaifin ki wato Sarki Ganesh, tabbas shi shugaba ne me adalci wanda yake iya zama yaci abinci tareda bayin sa, yakan zauna yayi hira ta fahimta dasu ya d'auki kowa a matsayin d'an uwa yana kyakkyawar kyautatawa gare su baya zargin kowa haka ya d'auki yarda ya bawa kowa, tunane tunane ba aikin sa bane ya mik'a lamarin sa ga ubangiji, meyesa bazaki kwaikwayi baban ki ta wasu 'bangaren ba??"

Shiru tayi tana nazari kafin ta girgiza kai tace, "baka san komai ba dan haka ka janye jikin ka, duk da cewar na d'an yi mamakin yadda ka zayyano min wasu daga cikin halayen mahaifi na, amma wannan kad'an ne tunanin ka baze iya d'auka ba kwanyar ka bindiga zatayi idan aka fara karanta maka tarihi na da na mahaifi na har ma da mahaifiya ta Sarauniya Rukhshah, Rukhshahnaa, tunani kuma abu ne wanda ya zama wajibi ga wanda yake tafiya ba gaba ba baya kuma hanya ta k'ure masa ya zama dole yayi nazari akan meye mafita, ka dinga tunanin abunda ze yuwu Bin Abu Ansaar "

Daga haka ta fara takun ta me matuk'ar jan hankali da shagalarwa da nufin komawa ciki.

Cikin zafin nama ya rik'o hannun ta tareda finko ta tayi baya, dai-dai inda wata k'orama take kwararar da ruwa ya tara ta,
Sai da ta jik'e jalaf har ta fara kakkarwa saboda sanyi da kuma yadda ruwan ya ratsa k'ok'on kanta sannan ya sake ta.

Cikin hanzari ta fito tana girgiza kanta tareda k'ok'arim shak'ar kyakkyawan numfashi, ta d'auki lokaci kafin numfashin ta ya dai-dai-ta sai sauke ajiyar zuciya take a kai a kai ta furzar da wata sassanyar iska ta bud'e idon ta garass a kansa tana binsa da wani kallo me cike da tuhuma da kuma tsantsar 'bacin rai.

'Dan murmusawa yayi yace, "Lakhshmi nasan ba lallai idan kin fahimci me hakan yake nufi ba, ni nayi ne dan na sa kiji sanyi har cikin zuciyar ki ba da wata muguwar niya nayi ba,
Ranki ya 'baci sosai a dalili na be kamata in bar hakan ba, kuma yawan tunanin da kike ya jefa ki a damuwa hakan ne ma yasa nazo gareki domin nema miki salama, tin zuwa na da haka naso in iso miki sai dai kuma ban samu damar hakan tin farko ba,
Idan kika d'aga murya kece zakiji dan kuwa mutanen ki zasu raina girman ki,
Idan kuma kika koma cikin Tajmahaal a haka mutane zasu d'auka kinyi wankan Al'ada ne na addinin ku, ni kuma nayi ne kawai dan rage miki damuwa, na barki lafiya"

Daga haka ya juya ya bar wajen cikin takunsa irin na cikakken jarumi.

Ido ta bishi dashi take tunani ya k'ara bijiro mata, a zahiri tace, "yanayin takun sa yanayin salon sa haka ma tafiyar sa murmushin sa da kuma yadda yake gudanar da komai cikin kyakkyawar manufa da k'wak'k'warar hujja Sakkk,.

Murmusawa tayi tareda cewa, " na k'aunaci hakan Aruuf, kuma salon ka yana burge ni"

Wani shauki ne ya shiga d'ibar ta sai murmushi take ita kad'ai,,
Cikin nutsuwa ta shiga cikin masarauta kamar yadda ya fad'a kuwa kowa yayi zaton tayi wankan Al'ada ne shiyasa suke ta kwasar tabarraki,
Gaf da zata shiga sashin ta tayi karo da Gimbiya Jusiyya hannun ta rik'e da wani d'an abu na zuba wuta, fuskar ta d'auke da murmushi ta saka mata Albarka sannan taja hannun ta suka shiga ciki,
Kaya ta ta d'akko mata ta bata tareda cewa, "y'a ta kisa kaya kinji ko!? Kar sanyi yayi miki yawa"

Gyad'a kai tayi ta kar'ba tana murmushi.

Cikin hargagi Arveen yace, "Baba wai me yarinyar can take nufi da mu ne a wannan masarautar??? Ta d'auki wancan k'azamin bawan tamkar wani abun bautar ta, kusancin su yayi yawa, ina jin zafin hakan Baba"

Waziri yace, "yaro na? Nace ka dena saurin fushi dan kuwa mutum me saurin fushi be cika tunani ba,
Ka zauna kayi nazari sosai akan abu shine mafita ba kai ta fusata ba, karka damu d'ana"

Tsaki yayi yace, "haba Baba na, haka kake ta cewa kar na damu gashi yanzu duk ka lalata komai kwata-kwata ma yanzu ba ta mu take ba, zanyi abunda nake ganin shine dai-dai fa"

Waziri yace, "d'ana kwantar da hankali bana son ganin 'bacin ran nan naka, na gaya maka sannu sannu bata hana zuwa"

Arveen ya juyar da kai tareda cewa, "haka dai"


Gimbiya Jusi ce ta kalle ta cike da kulawa tace, "Maharani?? Naga kwanan nan kina cikin damuwa duk kin canja me yake faruwa ne?? Me yake saki irin wannan yanayi Maharani??"

Lumshe ido tayi tareda kamo gefen le'ben ta ta taune shi, kamar baza tayi magana ba sai kuma tace, "Mama Jusiyya masarautar da muka yak'a a baya tana son dawowa garemu domin d'aukar Fansa na tabbar yanzu magajin masarautar ne yake k'ok'arin tinkara ta abun bazeyi kyau ba domin kuwa nasan ya girma ne da muradin fansar jinin mahaifin sa"

Gimbiya Jusi iya tashin hankali ta gama kaiwa k'ololuwa, ko motsin kirki kasa yi tayi sai girgiza kai da take idanun ta sun cicciko da k'wallah.

Da sauri Maharani ta dafa kafad'ar ta tareda cewa, "Haba Gimbiya Jusi meyesa kuma zaki tashi hankalin ki haka shiyasa fa nak'i fad'a muku gara na shiga tashin hankalin ni kad'ai k'anwata Farhana ma ban gaya mata ba saboda bana son ku shiga irin rud'anin da nake ciki ina fata a cikin wannan k'adamin masoyi na ya dawo Gimbiya Jusi daga nan ne duk wani k'warin guiwa ta ze dawo, rashin sa ya sa rayuwa ta ta samu babban nakasu, Mama Jusi dan Allah ki dena damuwa babu abunda ze faru sai Alkairi, ubangiji baze basu ikon cin nasara a kan mu ba, domin a koda yaushe gaskiya itace a sama"

Gimbiya Jusiyya ta share k'walla cikin tausayi da juyayi tace, "y'ata ke me nasara ce kuma zaki cigaba da nasara a rayuwar ki, har yanzu jinin masoyin ki yana bibiyar jikin ki, akwai abu me matuk'ar daraja a tsakanin ke dashi, darajar wannan abun baze bari ya nisan ta da ke ba, yana tareda ke y'ata"

Murmushi ne ya su'buce mata ta lumshe ido a k'asaice tace, "naji dad'in hakan Gimbiya Jusi"

Farhana tana zaune gefen sa suna hira kad'an kad'an mafi yawanci ma tambaya ce yake mata sai ta bashi amsa,
Wannan budurwar me rufaffiyar fuska ta shigo kai tsaye Kumar ta fara kira,
Yayi saurin bud'e mata hannu ta fad'a jikin sa tareda sauke wata zazzafar ajiyar zuciya.

Cike da kulawa ya rungume ta yana kallon ta cikin muryar sa me cike da jin kai yace, "kyaa hua??"

Numfashi ta sauke kafin tace, "masarautar da ta dad'e tana bibiyar Maharani itace yanzu take k'ok'arin jefo harin ta gidan nan, yanzu lokacin da ze d'auki fansar sa yayi"

Kece yayi da dariya, har sai da yayi me isar shi sannan ya tsaya, cikin k'warin guiwa yace, "ban damu da kashe kashen da za'ayi ko 'barnar da za'ayi ba, ban damu ba idan an rushe masarautar nan ni dai buri na a wulak'anta Maha"

Farhana tace, "wannan gaskiya ne Khumar nima babban buri na shine naga an tarwatsa ta, ban ta'ba muradin mulki ba kawai naga an kawo k'arshen ta shine cikar buri na"

Devi tace, "shikenan to yanzu me kuke ganin za'ayi??"

Khumar yace, "baku da damuwa a kan wannan yanzu hukuncin da na yanke shine za'a bi zanyi nazari naga abunda ya kamata, sai mun cika muradhen mu"

Zaune take a bakin gado ta rufe fusksr ta da tafukan hannun ta duka biyun, ta dad'e a haka kafin ta tashi ta fice.

sashin da aka mayarda Hadima Urmi ta nufa, ta tarar da ita zaune tana yiwa Abdulkareem wasa.

Tsayawa tayi tana kallon sa har cikin rai tana yaba wa irin mugun wayon da yaron yake dashi, a hankali ta tsungunna dai-dai shi cikin sassanyar murya ta kira sunan sa, ya dawo da kallon sa gareta yana fara'a.

Murmushi tayi tareda shafar kansa tace, "zanje kurkuku na duba Ummee na ko zaka raka ni??"

Hadima Urmi ta murmusa tareda cewa, "me zamani y'ar mulki yaro Abdulkareem be iya magana ba, zan iya amfani da yawun sa??"

Kallon ta tayi ta kauda kai sannan tayi mata alamar eh.

Hadima Urmi tace, "godiya nake uwar marayu ta dai Abdulkareem yana son ya bi Ummeen sa alamun sa ma sun nuna hakan"

Hannu ta mik'a masa tana murmushi tareda cewa, "kana da son yawo kenan??
Yanzu ma kaci girman da zaka fara sanin ciki da wajen masarauta zan dinga d'aukar ka nayi komai tareda kai dan ka fahimci komai"

Shi kuwa cikin sauri ya mak'ale mata sai rarraba ido yake.

Hadima Urmi tace, "Abdulkareem ya gode haka ma me rainon Abdulkareem ta gode"

Bata kula ta ba ta d'auke shi suka fita.

Tana kwance can gefe ta tsakure sai d'an numfashin ta da yake fita a hankali ne ze tabbatar maka da tana da rai.

A hankali ta k'arasa ta durk'usa a gaban ta, cikin sanyi tace, "Ummeen mu!!! Ki tashi nazo ki tashi kiga Abdulkareem, cikin hanzari ta bud'e ido tareda mik'ewa ta zauna tana kallon su.

Mik'a mata shi tayi tana cewa, " daga Udday da Surekha"

Rungume shi tayi tareda gyad'a kai cikin nuna kulawa da zallar k'auna, sumbatar goshin sa tayi take waye suka shiga jerangiya akan fuskar ta kamar famfon da ya lalace.
Maharani bata hana ta ba sai ma nata hawayen da suka fara zuba.....




*INDO CE..*
[27/03, 11:08 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠*

(Masarauta)


Mallakin

*INDO CE..*



🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼


*Page~17*


بسم الله الر حمن الر حيم




*(WANNAN SHINE K'ARSHEN SHAFIN KYAUTA DAGA YAU NA GAMA FREE PAGE. KI BIYA KI KARANTA CIKIN AMINCI😊)*


*Ga masu buk'atar shiga group na musamman domin jin k'arshen Labarin Naira 100 ne kacal😂 ku hanzarta ku mallaki naku kar a barku a baya🤣 domin k'arin bayani ku neme ni tanan 👉🏻 08146838480*










Cikin sanyi ta dafa ta kafin ta share k'wallar ta tana murmushi tace, "ba kuka zakiyi ba Ummee Addu"a zakiyi mana wata rana muma zamu haifa miki y'a me kama da ke nasan zakiyi farin ciki sosai musamman idan ta kasance me sunan ki, nasan zatayi irin halin ki da kyawun ki Ummee, kuma zata kasance jaruma sak jinin mahaifin ta, ina son ganin Murmushi a fuskar ki ba hawaye ba, idan ina ganin kina kuka nakaniji gaba d'aya bazan iya yafewa kaina ba,
Gashi kin k'i magana Ummee kin kasa fad'a min kin yafe min ko kuwa??
Duk da ko kin yafe min ba lallai ubangiji ya yafe min kuskure na ba, Ummee idan kinso zan iya bada raina fansa akan abunda nayi, Farhana ta kasance me karaga nasan koda bana raye indai hakan ta faru tabbas ruhi na ze samu salama Farhana nasan zatayi fiye da abunda nayi a wannan k'asar bare kuma da temakon ki, za'a shimfid'a mulki na adalci, Ummee meyesa baza ki za'bi hakan ba?? Meyesa sai zaman kurkuku kika za'bawa kan ki?? Mu kuma iyalin ki meye makomar mu Ummee??
Dan Allah ki dena kuka kiyi farin ciki a koda yaushe nasan wannan yaron tabbas ze zamo Fansar wasu daga cikin rayukan da muka rasa, ki kalle shi sosai duka yanayin jinin Abdulkareem ne dashi hakan ne yasa naji ina k'aunar sa domin kuwa Ahalin Abdulkareem ba abun k'i bane,
Kiyi Murmushi Ummee na"

Share hawayen ta shiga yi sai dai tana sharewa wasu suna k'ara zubowa, ido ta zubawa Abdulkareem wanda yake kallon ta kamar wanda yake mata kallon tuhuma, wani yalwataccen Murmushi ne ya buwayi fuskar ta, jinjina kai tayi tareda mik'awa Maharani shi, cikin ranta tanaji kamar tayi magana sai dai bakin ta yayi nauyi ya rik'e gamm baza ta iya motsa shi ba indai da sunan tayi magana ne, girgiza kai kawai take yayin da wasu zafafa hawaye suke kwararowa daga cikin idanun ta, tabbas tana da abun fad'e tana da muhimman abubuwan da ya kamata ta sanar mata sai dai k'addara ta hana ta wannan damar"

Jin tana neman fashewa da kuka ne yasa tayi saurin tashi tana rungume da Abdulkareem ta fice daga wajen tana tafiya cikin sanyi da tsanani tausayin rayuwar su"

"Lakhshmi"

Muryar sa ce ta doki dodon kunnen ta,,, tsayawa tayi cak ba tareda ta juya ba kuma bata cigaba da tafiyar ba.

K'arasowa yayi cikin nutsuwa da kamala yace, "Lakhshmi bana jin jefa kanki cikin wani k'angi shine mafitar damuwar ki, da haka me yasa baza ki baza sojojin ki ba tinda suna da yawa su je su nemo miki wanda kike so???
Kuma ina so ki tattara nutsuwar ki guri d'aya indai baki yi hakan ba banajin zaki iya yin tunani me kyau,
Akwai jarrabawa a rayuwa haka kuma akwai k'alu bale, wani tashi k'addarar zalla ce wani kuma tayi gauraye, rashin nutsuwa yana gusar da hankali kuma idan hakan ta faru k'arshe bata bada abu me kyau,
Ya kamata ki dinga nutsuwa ki bawa zuciyar ki damar yin tunani me kyau"

Sai da ya gama maganar sannan ta d'ago idanun ta wanda suka cika tafff da hawaye zuba a kansa ta d'an kwashi lokaci tana kallon sa kafin ta bud'i baki a hankali tace, "Zanyi amfani da abunda ka fad'a amma sai nayi dogon nazari kafin na amince na bar mutane su shiga inda basu sani ba, domin kuwa ta ko ina farauta ta ake, kuma mutane na sune komai nawa idan na bari aka ta'ba su tamkar zubar da kimar iyaye na ne nayi Alk'awari gare su bazan gushe ba zan tabbatar da adalci ga mutanen su,
Wasu suna ganin kamar abunda nake zalumci ne, a zahiri hakan ne sai dai wanda yasan ciki yasan waje yasan gaba da baya ze gane meye amfanin hakan, ni ina da k'wak'k'waran dalilin da yasa bana yin afuwa,,, Ansaar kayi min addu'a kawai domin kuwa bani da matemaki sai ubangiji, shine kawai yasan asalin halin da nake ciki"

Jinjina kai yayi ba tareda yayi magana ba yabar mata wajen, yau ce ranar farko da ya ta'ba jin tsananin tausayin ta ya bulale shi.

Lumshe ido tayi tareda sauke 'boyayyar ajiyar zuciya sannan taci gaba da tafiya.

Ba tareda ta ankare ba sai ganin mutum tayi a gaban ta, idanu ta waro masa tana binsa da kallon tuhuma.

Ya sosa k'eya cike da makirci yace, "Sarauniya Mahalakhshmi ki gafarce ni a bisa shigar sauri da nayi miki kai tsaye, ina son gaya miki ne cewa Mahaifi na yana Son magana da ke, yazo sashin ki ne ko kuwa zaki zo sashin mu,, ko gurin had'uwa??"

Kauda kai tayi cikin k'asaitacciyar murya me nuna tsantsar isa da izza tace, "Arveen, ya same ni a k'aramar fada ta sai dai yau bani da lokacin ganin sa sai zuwa gobe, yanzu lokacin yaro na ne"

Har cikin ransa abun yayi masa k'una sai dai be nuna alama ba dan kuwa yana son gyara hanyar sa ne dole sai ya jure, murmushin yak'e yayi tareda cewa, "ranki ya dad'e Sarauniya Malakhshmi y'ar sarki Ganesh da Sarauniya Rukhshanah , duk abunda kika ce haka za'ayi domin kuwa girman ki da darajar ki har sun wuce nan, a isa turaka lafiya me gadon izza"

Ko kallon sa batayi ba tayi gaba cike da rashin damuwa da kulawa.

Da wani mugun kallo ya bita yana jin kamar ya shak'e ta ta mutu ya huta .

Ta kasa zaune ta kasa tsaye tunanin maganganun Aruuful Ansaar ne kawai suke dawo mata, ta rasa gane me ya kamata tayi amincewa ko akasin haka, kwata-kwata zuciyar ta ba dad'i gashi bata da wanda zata fad'awa ya taya ta kuka,,, Abdulkareem da Arjula kawai sune wanda tasa gaba tana zubawa magana iri da kala.

Farhana kuwa yanzu ba koda yaushe take shiga inda take ba, taci gashin kanta kawai shiga gari take ta ko ina a cikin masarautar har ta fara gina ta-ta fadar domin kuwa
End Ads