Ture ta yayi daga jikin sa a burkice ya mik'e yana cewa, "Me ne??? Kika ce ta rad'a AbdulKareem????? Meyesa!?????
Ya jefo mata tambayar cikin tsawar da sai da ta razana.
"K'warai yaron Udday yaci wannan sunan"
Jingina yayi jikin garu yana maida numfashi a take wani gumin wahala ya shiga keto masa, ya lumshe idon sa ya bud'e sannan yace, "meyesa ta kasa sallamewa kanta wannan masoyiya??
Wadda ya kira masoyiya ta gyara zama kafin tace, " dad'i na da magajin karaga saurin fushi, da kayi shiru baka firgita ba da sannu zakaji mafita ta fara zuwar maka cikin tunanin ka"
Dawowa yayi ya zauna kusa da ita cikin salon yaudara ya rik'o hannun ta yana d'an murzawa cikin sassanyar murya yace, "fad'a min menene??
Murmushi tayi tace, " zamuyi amfani da hakan mu jefa rud'ani cikin zukatan mutane ta yadda zasuji sun tsane ta"
Yace, "kin kawo magana yaci ki samu kyauta me kike so na baki??
A kunne ta rad'a masa kafin suka kwashe da dariya sannan suka ci gaba da shirya yadda zasuyi su rusa Maharaniey.
Idanun ta a lumshe suke yayin da take k'ok'arin d'aure gashin ta da wata kyakkyawar sark'ar azurfa har ta kammala, Hadima Farhanaa tana gefe ta zuba mata ido har ta gama sannan tace, " gaskiya Maharanie ke kyakkyawa ce"
Murmushi kawai tayi ba tareda tace uffan ba.
Hadima Farhanaa taci gaba da cewa, "Hazoor kenan yanzu ina zakije???
Jin batayi magana ba yasa Hadima Farhanaa ta canja magana dan kuwa tsananin baiwar surutun da Allah yayi mata baze barta tayi shiru ba.
Cike da son k'arin bayani Hadima Farhanaa tace, " Maharaniey?? Shin meye dalilin da yasa kike hidimtawa Addinin muslumci lokaci lokaci???
Sannan kuma waye Abdullkareem??
Akwai abubuwa da dama wanda na kasa fahimtar su daga gareki har sai yaushe zakiyi min bayani?? Kin barni a cikin duhuwar da na kasa gane gaba da baya"
Kamar baza tayi magana sai kuma ta murmusa sannan tace, "baya tarihi ce gaba kuma gwagwarmaya, gani yafi ji dan haka ki tsammaci zuwan lokacin da zaki gani da idon ki, tarihi kuma ba abunda ya zama wajibi bane kiyi k'ok'arin yin tunanin gobe ba jiya ba dan ta riga ta wuce tariyar ta ba amfani, idan ta riga ta dawo kuwa ba lallai abun yayi kyau ba"
Ta k'arasa maganar tana zuba mata idanu.
Gyad'a kai Hadima Farhanaa tayi tace, "kenan dai ba dama?? Haka zan ci gaba da rayuwa kenan ba tareda nasan iyaye na ba?? Bansan wacece ni ba kenan a haka zan gudanar da rayuwa ta?? Ina buk'atar sani musamman akan mahaifi na"
Kamar wadda take tsoron yin magana tace, "da haka kika taso idan kin ci gaba da rayuwa a haka ba damuwa"
Mik'ewa tayi tana takun ta irin na giwa cikin nutsuwa ta nannad'e jikin ta da k'aton mayafin Sariey wanda ya sha ado ko ta ina ba ta kalli inda Farhanaa take ba sai ma kiran Arjula da tayi suka doshi hanyar fita.
Da sauri Hadima Farhana ta biyo bayan su.
Suna fitowa kowa ya d'au saiti.
Kai tsaye wani ke'bantaccen guri ta nufa wanda kai tsaye za'a kira shi da kurkuku, cikin nutsuwa take takawa har tabar harabar kurkukun ta shiga wani d'aki bayan me gadin d'akin ya bud'e mata.
K'arewa d'akin kallo ta shigayi kafin ta k'arasa a hankali ta tsugunna a wani waje.
Duhun da d'akin yayi yasa ba'a ganin komai bazaka iya gane menene a ciki ba.
Cikin wata irin murya kamar ba ta-ta ba tace, " Yaushe???
"Yaushe ne zakiyi magana???
Meyesa bazaki bani amsa ta ba??
Sai yaushe ze zo???
Kinyi shiru ki fad'a min!!!"
Tayi maganar a tsawace.
Me gadin gurin ne ya shigo da fitila yana haskawa..
Wata Mace ce a tsakure a jikin bango ta had'e kai da guiwa gashin ta yayi buzu-buzu kaca-kaca ga tarin datti,
Tsawar da Maharaniey, (Sarauniya) ta daka ce tasa ta d'agowa tana zuba mata firgitattun idanun ta wanda sukayi jajur,, daka ganta ka ga mahaukaciya saboda irin d'aud'ar da take jikin ta da kuma yanayin ta.
Ido ta zuba mata suna kallon kallo ba tareda tayi magana ba.
Maharaniey ta k'ara da cewa, "kiyi magana kafin ranki ya 'baci, ki fad'a min mana, meyesa kika dena magana ki bud'e baki kiyi min bayani"
Jijjiga ta ta shiga yi tana cewa, "kiyi magana ki fad'a min yaushe ne???
Hadima Farhana ce ta matso zuciyar ta na k'una cikin 'bacin rai tace, " gaskiya ranki ya dad'e ta wata fuskar ke muguwa ce, sai yaushe zaki dena azabtar da wannan matar??? Meyesa zaki za'ba mata wannan rayuwar?? Shin menene abunda kike so daga gareta da har kika kasa jin tausayin ta dan tak'i fad'a miki?? Wannan be dace ba"
Da mamakin maganganun da Hadima Farhanaa ta gaya mata ta juyo a fusace tana zazzare mata manyan idanun ta, cikin Hasala tace, "ki rufe min baki, kece zaki fad'a min abunda ya dace ne?? Yaushe ne kika samu matsayin da zaki duba tsabar idanu na ki fad'a min irin wannan maganar??? Me kika taka ne Farhanaa????????
Hadima Farhanaa tace, " ban taki komai ba tinda ni bani da mulki bani da dalilin sa, amma gaskiya ce nake fad'a miki me wannan matar tayi miki da zaki kulle ta anan shekara da shekaru?? Kuma ace bazan fad'a ba ya kamata kiyi adalci, kullum kin takura mata da tambaya, shin ranar mutuwar ki kike tambayar ta ne ko meye????
A fusace Maharaniey (Sarauniya) ta zaro wata takobi da akayi mata mazauni a jikin bangon d'akin wanda aka gina shi da zallar dutse,
Cikin tsananin Fushi ta kai mata Takobin da niyar raba kanta da gangar jikin ta ba tareda tunanin kuskuren da take shirin aikatawa ba.
Wani irin gurnani matar tayi tareda yunk'urawa ta mik'e tana girgiza kanta da iya k'arfin ta tana fizge fizge, tana wani irin ihu, kamar me cutar iska.
Dakatawa Maharaniey, (Sarauniya) tayi jikin ta na rawa saboda tsabar 'bacin rai, ta dad'e a haka kafin tayi wurgi da takobin ta kalli Hadima Farhanaa, cikin Izza tace, "Farhanaa ki dinga banbance matsayi na da naki, karki manta nice silar zuwan ki duniya, ki dena d'aukar kanki a wata abu ke ba komai bace face baiwa ta"
Daga haka tasa kai ta fice daga kurkukun a fusace, kai tsaye bayan masarautar ta nufa bakin wani k'aton kududdufi k'oramu suna ta gudana da ruwa ta ko ina ga sanyi da yake tashi a wajen tsuntsaye sai yawo suke suna lelewa, tsayawa tayi ta rungume Hannuwan ta cikin k'irjin ta tana babbaza ido, har wani lokaci kafin zuciyar ta ta fara yin sanyi.
Hadima Farhanaa ce ta k'araso wajen cike da nadamar abunda ta aikata, durk'ushewa tayi kan guiwoyin ta- ta maida hannuwan ta baya ta hard'e su, kanta a k'asa tace, "Hazoor, (Ranki ya dad'e) ki gafarce ni idan har zuciyar ki zata iya hakan, idan baki huce ba ki d'auki mataki a kaina na d'auka, tabbas nayi kuskure ama sharrin zuciya ne ba da son rai na ba, kwata-kwata bani da niyar 'bata miki rai bansan hakan zata faru bane"
Lumshe ido tayi tareda sauke wani zazzafan numfashi, ba tareda ta kalle ta ba tace, "ina Abdullakareem???
Hadima Farhanaa tace, " yana nan cikin kwanciyar hankali ba abunda yake damun shi"
Jinjina kai tayi ba tareda tayi magana ba ta juya ta koma cikin Tajmahaal.
Da tsakar dare ta tashi ta shiga wani d'aki,
babu haske sosai sai kad'an-kad'an, tarkace ne na abubuwan da suka fi kama da na tarihi, kan kujerar da ke tsakiyar gurin ta zauna ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tana d'an karkad'a ta a hankali, k'arewa d'akin kallo ta shiga yi kafin janyo wata akwati ta bud'e ta, zuba wa akwatin ido tayi har wani lokaci kafin ta saki murmushi, cikin wata maraitacciyar murya tace, "yaushe zaka dawo??? Meyesa zaka guje ni?? Sai yaushe zaka zo gareni???
Murmushi tayi ta k'ara cewa, " nasan zaka zo, ko ba dad'e ko ba jima, nasan fushi kake dani, nima yanzu na canja na dawo kamar yadda kake son gani na meyesa bazaka zo ba??
Ita kad'ai take y'an surutan ta har wani lokaci sannan ta tashi ta koma turakar ta.
Babbar Fadar Masarautar Phurlasirie,
Cike take mak'il da jama'ar masarautar yayin da kowa yake hirar sa cikin nishad'i da walwala hayaniya ce kawai ke tashi.
Shiru fadar tayi kamar wucewar tsawa, sakamakon busar da ta iso cikin fadar wadda take nuna alamar Maharaniey mahalakhshmie ta doso cikin fadar,
Kowa tashi yayi tsaye ya k'ame tareda sunkuyar da kansa k'asa gami da dunk'ule hannuwan su na dama suka d'ora gefen k'irjin su,
ba babba ba yaro haka tsoho da tsuhuwa haka maza da mata, kowa mik'a ban girma yake gareta.
Tsaye tayi a bakin fadar ta lumshe idanun ta, cikin wata irin siga take motsa bakin ta a hankali ba tareda sautin abunda take fad'a ya fito ba, sai da ta d'auki d'an lokaci a haka kafin ta bud'e idanun ta, take suka k'ara rikid'a suka k'ara wani irin kwarjini da razanar da duk wanda yayi gigin tsoma nasa idon cikin su,
Idan baka lura sosai ba bazaka ta'ba cewa tana k'ifta su ba sai in kayi mata kallon k'wak'waf hakan kuwa ba kowa ne yake iyawa ba,
Cikin takun ta me cike da zallar izza da gadara ta saka k'afar ta ciki tareda k'ara rarraba idanu tana kallon mutanen da suka koma kamar basa motsi,,
Har sai da ta dangana da kyakkyawar kujerar mulkin ta ta zauna sannan kowa ya zauna.
Kowa yayi shiru yana tsammanin abunda ze fito daga bakin.
An kwashi lokaci sosai kafin tayi magana cikin d'aga murya tace, "ina buk'atar sanin duk abunda yake gudana a ciki da wajen masarauta"
Da sauri Wanda suke da Alhakin hakan suka taso tareda hawa kan tudun da ke gefen kujerar wanda aka tanada saboda su.
Subbhu ne yayi gyaran murya kafin yace, " Ranki ya dad'e wasu daga cikin mutanen masarauta suna cewa sun kasa gane dalilin da yasa kika rad'awa yaro Abdulkareem sannan kuma kin enta Udday fiye da ko wane bawan ki ta dalilin haihuwar wannan yaro basu fahimci meye hakan yake nufi ba, har wasu suna cewa ko dai kina da alak'a ta jini da yaron"
Jinjina kai tayi tareda zubawa Hadima Farhanaa ido.
Hadima Farhanaa ta sunkuyar da kai cikin sanyin jiki.
Kamar baza tayi magana ba sai kuma ta mik'e, ta fara takawa cikin k'asaita hannun ta rik'e da gefen mayafin Sarin ta,
Juyowa tayi tana fuskantar jama'ar ta, cikin d'aga murya tace, "abu ne me kyau kaso wanda ya so ka da gaskiya, kyautatawa ga wanda ya kyautata maka abune me matuk'ar muhimmanci, kar ku manta da waye Abdulkareem kar ku zama butulu saboda wasu y'an tsirarun mutane suna son hure muku kunnuwan, ku tsarkake zukatan ku a koda yaushe kar ku bari wani yayi tasiri a zuciyar ku, ya kasance kuna yin komai da yak'ini ba tareda bin fad'ar wani ba, idan kun kasance wanda basu san waye shi ba kuyi tambaya ga iyayen ku da kakannin ku, nasan ma ba lallai ne ace baku san da hakan ba,
enta wanda ya enta ka shima abu ne me kyau, be zama dole sai wanda ka had'a jini dashi ba zaka kyautatawa, akwai su da yawa wanda su d'in jini na ne amma a hakan sune suke tunzura ku dan su jefa ku cikin wasi-wasi,
Komai na yiwa udday ban biya shi ba domin kuwa shi kyautar d'an sa yayi min, har gobe shi mutum ne me daraja a idon masu daraja, yaro kuma na d'auka a matsayin d'ana ne, kuma wani abunda baku sani ba, koda bana raye ku sani Abdulkareem bin Abdulkareem shine magajin karaga ta,
Yafi kyau ku maida hankali wajen kishin kanku da y'ancin masarautar ku da kuma yankin ku domin dubban halittu suna son ganin bayan Tajmahaal wadda kuka taso cikin ta tin kakannin kakannin ku,
Ni dai na aminta kuma na tsaya ga al'uma ta na fansar da raina gurin kare su da basu y'ancin su, ban yarda da zalumci ko nakasu a wannan masarauta ba, duk wanda yayi k'ok'arin hakan?? Yasan meye hukuncin duk wani kaifi a fadar nan"
Shiru tayi tareda k'ara taku biyu zafafa tana kallon su d'aya bayan d'aya.
Shiru fadar ta k'ara yi kowa da tunanin sa, jikin su yayi sanyi matuk'a domin kuwa sun san a cikin zantukan ta babu na watsarwa.
Wasu kuwa furucin ta na mallakawa Abdulkareem karaga shine ya k'ara hautsina tunanin su yayin da zuciyar su ke raya musu duk yadda akayi Abdulkareem d'an ta ne.
Babbar tambayar kuma itace da wane mijin ta haifi Abdulkareem????? Kuma a yaushe????
Subbhu ne ya d'akko wata takarda yana dubawa, cikin d'aga murya yace, "ku saurari k'orafin da Shugabar mu zata saurara da kuma hukuncin da zata yanke a yanzu"
A take nutsuwa ta k'ara wanzuwa a gare su kowa ya cigaba da sauraron su.
Subbhu yace, "Hazoor !! ( Ranki ya dad'e) "Janela tana d'auke da juna biyu wanda ya kasance ya samu asali daga Narayan,
Sakamakon keta haddin ta da yayi saboda son zuciyar sa ba tareda son ranta ba, iyayen ta sun mik'o kukan su gareki tareda sa ran samun adalci"
Udday yace, "wanda suka san dasu ake su fito gaban shugaba"
Fitowa sukayi suka durk'usa kamar yadda tsarin masarautar yake suna tsammani daga gareta.
Zama tayi tareda lumshe ido ta sauke 'boyayyar ajiyar zuciya kafin ta bud'e su ta juye akan Narayan wanda jikin sa yake kyarma saboda tsabar tsoro da fargabar azabar shugabar tasu, a Take wani abu ya fara kwaranyowa cikin tunanin ta,
Jinjina kai tayi tace, "wajibi ne auren ta gare shi bayan yayi zaman kurkuku na adadin lokacin da zata rabu da abunda yake jikin ta, kullum ze d'auki hukuncin bulalai hamsin ba tareda ya motsa ba,
Bayan wata d'aya sai a koma yi masa duk mako d'aya,
Ban da shan ruwa sai me zafi abinci kullum sau d'aya,
Kulawa da d'an sa da matar sa ya wajabta a kansa indai ya 'bata mata rai ko ya goranta mata koda na lokaci d'aya hukuncin kisa ta hanyar jifa ya tabbata gareshi"
Daga haka ta mik'e da niyar fita daga fadar jiki a muce.
Tashin hankalin abunda take fad'a ya hana shi aiwatar da abunda yaso k'addamarwa akan ta, idanun sa sun kad'a sunyi jajur saboda azabar rad'ad'in da zuciyar sa take masa ya kafe ta da idanu yana wani irin huci, zuciyar sa tana raya masa irin mummunan matakin da ya dace ya d'auka a kanta.
Da sauri mahaifin sa ya rik'o hannun sa wanda yake kakkarwa, cikin razani da shakka yace, "Arveen wannan be dace ba kasan wacece yarinyar nan kuwa??? Kai kad'ai ne ka rage min a yanzu dan haka karka sake kayi abunda zata cire maka kai a banza"
Yana shirin yin magana ta juyo tana kallon su saboda ji a jikin ta da tayi ana firar ta.
Ganin haka yasa sukayi saurin fuskewa dan gudun matsala.
Kawar da idon ta tayi daga kansu kafin tace, "Arveen ka kula da hukuncin da na zartar, karka bari a samu matsala"
Daga haka ta juya ta fice ba tareda ta k'ara kallon sa ba.
Fizgewa yayi daga rik'on da Waziri yayi masa, a fusace yace, "wai yaushe ne har yarinyar nan tayi girman da zata iya ja dani???
A gaban mu fa aka haife ta, amma Baba ka kalla yadda kowa yake jin tsoron ta, idan haka ne meye amfanin rashin iyayen nata??
Da sauri waziri ya shiga jansa dan kuwa akwai mutanen ta a kusa,, da wani yaji abunda yake fad'e ze rattaba mata kuma yasan hukuncin baya wuce kisa, baza tayi duba da cewa d'an uwan ta bane kawai gamawa zatayi dashi.
Sai da suka koma sashin su sannan ya sake shi,
Yaja tsaki tareda cewa, " Arveen kana da matsala meyesa kake haka ne??? Kasan halin yarinyar nan, ina ruwan ka da zancen yarintar ta tinda dai har ta riga ta girma??.
Yanzu abunda yake gaban ka shine wanda ya dace ba wai hurumin ta ba.
Arveen ya zuba dogon tsaki cikin k'unar rai yace, "yarinya duk ta addabi kowa?? Kenan mu haka zamu k'are a bayin ta??
A k'a'ida ma fa sarautar tawa ce, Kaji fa abunda take cewa wai nine zan kula mata ma da hukuncin da ta yanke wa wannan yaron, saboda tsabar zalumci ai ni banga laifin shi ba, ai kuwa wata rana hakan zata faru akanta itama sai muga me dakatar dani idan zata iya"
Waziri yace, "Arveen tinda dai na tabbatar baka son ta shikenan kawai kayi shagalin ka d'a na"
Ya fad'a yana wani irin murmushi me cike da ma'anoni da yawa iri da kala.
Cikin nutsuwa ta zauna a bakin makeken gadon ta tana maida numfashi saboda irin bugawar da zuciyar ta takeyi, cikin sassanyar murya tace, "Arjula?? "
Cikin sauri Arjula ta k'araso kusa da ita ta sauka tana kallon ta.
Itama kallon ta take har wani lokaci kafin tace, "Farhana"
Tashi tsuntsuwar tayi ta fice daga turakar cikin sauri,
Ba tareda wani 'bata lokaci ba sai gata