x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - TAJMAHAAL

  • 9001 words
  • 12000 words
  • Out of 37284 words

Category: Love Stories

Views 144

29 May 2025
Start ads
After Image Ads
wani muradi nasu ne"

Waro mata gwaragwaran idanun tayi cikin kausassar murya tace, "karki k'ara, koma meye d'an uwa na ne, na gani da ido na irin halin da yake ciki kina nufin ba gaskiya bane?? Ko kuma zata bashi guba ne kawai dan wani abu????

Rissinawa tayi tace, " naga kamar ranki ya 'baci ina neman afuwa ranki ya dad'e"

Zazzafar iska ta furzar kafin tace, "yau ne karon farko da naji na damu da damuwar wani, ashe dama ina da tausayi haka? Nayi zaton na barbad'ar dashi kamar yadda aka tambad'a min farin ciki na, ban zata zan iya ji'bantar lamarin wani cikin sauk'i haka ba "

Hadima Farhana tace, "Hazoor kina da kyakkyawar zuciya ta wata fuskar, amma rashin yafiyar ki shine yasa bana jindadi, shin wacece wadda kika kulle a kurkuku? Bakya tausayin ta,, ko meye tayi miki yaci ki yafe mata ta wahaltu ta bautu tin da hasken ta har ta koma mahaukaciyar k'arfi da yaji,,
Bana jin dad'in azabtarwar da kike wa matar nan shin wane zunubi ta aikata miki kika rufe ta har kika kasa yafe mata??????

*INDO CE..*



๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒน

*AURAN DIJAN GALA*

๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒน



*Shaharar ran book din nan mai matukar nishadantarwa ga fadakarwa hadi da ilimantarwa*

```ni oum siyama nashirya tsaf domin nishadantar daku, akan farashi mai sauki 200 kada kibari abaku labari```

*indai ba ki karanta AURAN DIJAN GALA anbarki baya yar uwa*, *maza Ku garzayo domin nishadinku*

*200 only*


*Ku tuntubeni a 08100437976 domin kira kuma ๐Ÿ‘‰08108353370 sainaji Ku*

```koda kudinki saida rabonki```

*Oum siyama ce*



Tinda ta fara maganar ta tsura mata ido har takai k'arshe, jikin ta yayi wani mugun sanyi lokaci d'aya, mik'ewa tayi tana taku d'aya bayan d'aya,
A wajen taga ta tsaya tana lek'a waje , a take yanayin ta ya canja, taja dogon numfashi kafin tace, "Banida abunda zan gaya miki Farhana nima kaina bana jindad'in hakan sai dai ya zama dole ne ba yadda na iya, d'an murmushi tayi ta k'ara da cewa, " ke yarinya ce Farhana, kije kawai na gaji da magana, wancan yaron Raj ya saka ni surutu, Abun beyi ba gaskiya yanzu bana son hayaniya lokacin buk'atar huta yayi"

Tashi Hadima Farhana tayi tana cewa, "zancen dai d'aya ne kullum ba amsa, sai yaushe ne kuma zaki bani labari akan iyaye na??"

A zafafe ta juya tana kallon ta fuska a had'e ba alamun wasa a tattare da ita.

Duk da rashin tsoro da jarumta irin ta Hadima Farhana sai da ta tsora tayi waje da sauri tana cewa, "Allah ya huci zuciyar Sarauniya"


Tin daga wannan lokacin kulawar ta da nutsuwar ta ta karkata zuwa ga Abdulkareem da kuma Ramraj,
Musamman Abdulkareem irin bada hankalin da tayi a kansa har ya wuce inda mutanen ta suke zato abun har ya fara girgiza su sun kasa gane wace irin k'auna ce tsakanin ita da yaron da ya kasance d'an bayin ta.


Mahaifiyar Ramraj kuwa sun samu mafaka a gefen Maharani,
Ita ta d'auke shi a matsayin d'an uwan ta wanda ya dace ya samu kulawar ta,,,, yayin da su kuma suke mata zagon k'asa suna k'ara ganin sirrin ta suna shiri dan ruguza ta.

Arveen ne ya kalli Mahaifin sa cikin 'bacin rai da bak'in ciki yace, "Baba kana kallon fa abunda yarinyar nan takeyi, meyesa kake tsoron ta ne??? Ni idan bazaka iya ba ka barni na tinkare ta muyi gaba da gaba meyesa haka ne?? Haba Baba ni nagaji kana cewa komai lokaci ne sai yaushe ne zan samu wannan k'arfin ikon??? Tayaya ne zan zama me mulki a wannan fada me tsohon tarihi???
Su kuma mutane kowa ita suke so sun kasa juyuwa ta riga ta shigar da tsoron ta a cikin zukatan su, ni kuma zan gusar da wannan tsoron nata da sukeji, shakka babu nine magajin Masarautar Purlasiri Baba"

Dafa kafad'ar sa waziri yayi yace, "ah d'ana kwantar da hankalin ka ba dai ina nan ba?? Sai dai amma ka sani tinkarar yak'i da wannan yarinya dai-dai yake da sadaukarwa gunki jinin ka, ba shakka sai tayi fata fata da kai, dan haka yanzu muna buk'atar wanda zasu taya mu yak'ar ta"

Arveen yace, "to yanzu ya za'ayi kenan Baba?? Ka duba ka ga yadda take kula da yaron nan Abdulkareem babu tantama yaron nan d'an ta ne dan kuwa abun ya wuce tunani, tsoro na d'aya kar sai tafiya tayi nisa kawai baya ta bayyana a gaban mu, Baba ka tabbatar ya mutu?????
Kar muje ta mutu ta bar mana baya da k'ura"

Dariya waziri yayi sosai kafin yace, "lallai yaro na ka girgiza da wannan lamarin, ya riga ya mutu, duk da cewar ita d'in yarinya ce me dabara amma Baban bazata iya dawo dashi ba,
Na rik'e maka kan macijin d'ana kayi wasa da jelar sa yadda ranka yake so,
Yaron nan kuma ya zama dole dama mu kashe shi domin kuwa jarumi ne tinda har kaga ta k'aunace shi sosai har ta rad'a masa wannan sunan tabbas yaron nan ze bamu matsala,
Kamar yadda tak'adirin Aljani ya gaya min wannan d'an shine bak'in duhun da muka dad'e muna ganin ze bayyano a garemu, dan haka ya zama dole ne mu kawar dashi"

Arveen yace, "k'warai Baba"



Kwance yake ya tayar da kai da cinyar ta yayin da fuskar ta take lullu'be da bak'in k'yalle.

Dariya yayi yace, "gaskiya kin cika shaid'aniya ina jin dad'in ki kina yi min aiki yadda ya kamata,
Yanzu waye na gaba a shirin mu???
Ya zama dole mu tashi tsaye,
Sai mun kashe wannan yaro Abdulkareem sannan haske ze bayyano mana a lokacin ita kuma duhu ze lullu'be ganin ta, amma duk da hakan sai mun nemi matemaki wanda ya kasance jigon ta,
Wa kike ganin zeyi mana haka???
Ko mu nemi matar Uddaiya??

Girgiza kai tayi tace, " a'a ba wannan ba, Hadima Farhana, ita zamu nema ta dawo tsagin mu indai hakan ta faru shikenan mun karya lagon ta, to amma ta wace hanya zamu biyo wa Hadima Farhana???
Indai dukiya ce bata da matsalar ta ba abunda zamu bata wanda zata yarda damu, idan kuma kayi mata barazanar kisa ko wani abu hukuncin Maharani Mahalakshmi ze tabbata ne gareka"

Mik'ewa yayi ya zauna tareda janyo ta jikin sa yana cewa, "ke kad'ai ma gayya ce kina shiga jikinta ba tareda ta sani ba ganin ki take kamar wata ta kirki batasan nan makashin ta take tare dashi ba,
Zanji da Hadima Farhana dan haka ki cigaba da abunda ya dace, goben nan zanyi maganin ta"



*INDO CE..*
[28/02, 7:43 a.m.] INDO CE..: *๐ŸŽ ๐ŸŽ ๐ŸŽ  TAJMAHAAL๐ŸŽ ๐ŸŽ ๐ŸŽ *

(Masarauta)



Mallakin

*INDO CE..*

Marubuciyar
SIRRIN K'ETA.
A JINI 'DAYA.


๐ŸŒผELEGANT ONLINE WRITER'S๐ŸŒผ


*Page~6*


ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑ ุญู…ู† ุงู„ุฑ ุญูŠู…



Free page



*Tajmahaal na kud'i ne Naira 100 kacal cikin rahusa๐Ÿ˜„*

*Domin magana dani ta prvt ga link๐Ÿ‘‡*

https://wa.me/message/45UKV47T7IM2F1


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒน

*AURAN DIJAN GALA*

๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒน



*Shaharar ran book din nan mai matukar nishadantarwa ga fadakarwa hadi da ilimantarwa*

```ni oum siyama nashirya tsaf domin nishadantar daku, akan farashi mai sauki 200 kada kibari abaku labari```

*indai ba ki karanta AURAN DIJAN GALA anbarki baya yar uwa*, *maza Ku garzayo domin nishadinku*

*200 only*


*Ku tuntubeni a 08100437976 domin kira kuma ๐Ÿ‘‰08108353370 sainaji Ku*

```koda kudinko saida rabonki```

*Oum Siyama*



Maharani.
Tana zaune kan k'ayatacciyar kujerar ta tana hutawa,
Haka kawai takejin zuciyar ta tana bugawa ba tareda tasan meye fa'idar hakan ba.

Hadima ce ta kutso kai tareda nemawa kanta iso.

Ba tareda tayi magana ba tayi mata alamar ta shigo.

Ta shigo tana cewa, "ranki ya dad'e, nice dai wadda aka kawo ni domin iso da mutanen ki gareki,
Sunana Fadya, Gimbiya Jusiyya tana son isowa ni kuma na hana ta, da fatan banyi laifi ba domin kuwa ta tabbatar min da cewar ba'a yi mata shamaki da shiga duk inda kike"

Zaratan idanun ta ta d'aga ta juye akan ta cike da tuhuma tace, "ban tambaye ki bayani akan ki ba, na sanki, meyesa zaki hana Gimbiya Jusiyya shigowa?? Shin ba'a wannan masarautar aka haife ki ba??? Baki san wacece Gimbiya Jusiyya a guri na ba???

K'asa tayi da kai tana cewa, " A huce ranki ya dad'e, akan aiki na nake ni sabuwa ce a wannan fannin nayi zaton shigowar ta kai tsaye ne ze sa nayi laifi amma a yafe ni kuskure ne bazan kuma mai-mai-ta shi ba"

Ko kallon ta batayi ba sai ma lumshe ido da tayi.

Da sauri Hadima Fadya ta tashi ta fice.
ba 'bata lokaci wata mace ta shigo, babbar mace ce me kamala da dattaku, tasha ado ta ko ina, fuskar ta d'auke da murmushi ta k'araso kusa da Maharani, cikin ladabtacciyar murya tace, "Maharani Mahalakhshmi?? Sannu da hutawa zan iya zama???

Gyad'a kai tayi ba tareda ta kalli inda take ba.

Gimbiya Jusi ta saki yalwataccen murmushi ta zauna a bakin gado,
Kallon Maharani Mahalakhshmi tayi cikin amintacciyar murya tace, " Yarinya ta kinci abinci kuwa??

Girgiza kai tayi alamar a'a.

Da sauri gimbiya Jusi tace, "meyesa??? Ki dena damuwa ki bari komai ya wuce be kamata kina zama kina saka tunani a zuciyar ki ba har ya hana ki cin abinci,
Idan baki inganta kanki ba taya kike ganin zaki iya inganta wasu??
Be kamata ba, komai da maslaha akeyin sa, meye damuwar ki yanzu???

Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke kafin tace, " Gimbiya Jusiyya babu abunda nake tunani"

Dafa kafad'ar ta tayi cikin sanyi tace, "haba y'a ta?? Ina ganin damuwa k'iri k'iri a tare dake amma kice min baki da damuwa?

Rausayar da kai tayi tace, " damuwa ta d'aya ce kawai ita kuma ba buk'atar kowa ya sani, zanci abincin amma ba a lokacin da kikace naci ba"

Murmusawa tayi tace, "har yanzu kin kasa sauyawa y'a ta, babu wanda ya isa yasa kiyi babu wanda ya isa yasa ki bari,
Ni dai ki rufamin asiri Maharani ki dena damuwar nan,
Duk alhakin ki a kaina yake, har sai na tabbatar na saki farin ciki sannan ruhina ze samu salama, kin cire yarda da kowa, amma ina so ki sani ni bazan iya cutar dake ba, duk wanda naga yana shirin hakan sai inda k'arfi na ya k'are,
Koda bazaki yarda dani ba Na rok'e ki ki dena kallo na amatsayim wadda zata cutar dake"

Ta k'arasa maganar tana sharar k'walla kamar me shirin durgujewa da ihu.

Dogon numfashi Maharani taja bata ce uffan ba.

Mik'ewa gimbiya Jusiyya tayi tana cewa, "kar na cika miki kunne bari na koma sashi na, ki kula da kanki"

Lumshe ido tayi ba tareda tace komai ba.

Hadima Farhana.
Tana cikin tafiya wata kuyanga tasha gaban ta,
Tsayawa tayi tana kallon ta cikin rashin fahimta, ita da ba'a ra'bar ta saboda tsoron hukuncin Maharani kuma yau itace wadda za'a tarewa gaba, mamaki sosai abun ya bata.

K'arasowa tayi a ladabce tace, "A gaida Hadimar Hadimai"

Gyad'a kai kawai tayi tareda zuba mata ido.

Tace, "kiyi hak'uri na tare ki a hanya, sak'o ne akace in isar miki wannan wasik'a ce"

Tayi maganar tana mik'o mata wasik'ar dake hannun ta.

Kar'ba tayi cikin tsananin mamaki, gaba d'aya kanta ya kulle ta kasa gane me hakan yake nufi.

Kafin ta farga taga kuyangar har ta 'bace tayi nata guri.

Cigaba tayi da tafiya cikin sanyin jiki da kuma rud'ani gami da firgici, waye wannan wanda bata sani ba????

Ko alamar shiga batayi ba ta kutsa kai turakar Maharani ,
Tana zaune suna had'a wasik'ar jaki ita da Arjula suna hira cikin kwanciyar hankali,
A k'asa tayiwa kanta mazauni tareda yiwa Maharani Sannu.

Amsawa tayi gami da binta da ido zuciyarta tana tsalle, kai tsaye tace, "Ina Abdulkareem??!

Hadima Farhana tace, " ranki ya dad'e Abdulkareem yana cikin k'oshin lafiya da kwanciyar hankali"

A zahirance ta sauke ajiyar zuciya gami da lumshe kyawawan idanun ta, k'ara bud'e su tayi kafin tace, "kina da damuwa! Meyesa???

Hadima Farhana tayi k'asa da kai.

Kamar yadda ya buk'ata da daddare ta kimtsa tsaf harda shirin ko ta kwana sannan ta nufi inda akace mata taje,
Shi kad'ai ta tarar dashi sai surutu yake kamar wani Aljani,
K'arasawa tayi cikin tsoro tsoro tace, " Meyesa kake nema na???

Kallon sa ya mayar gareta yana dariya tareda cewa kinzo??

Kawar da kai tayi tace, "a'a"

Kwashewa yayi da dariya ya mik'e ya nufo inda take ya tsaya gaf da ita yana kallon ta,
Sassauta dariyar yayi kafin yace, "kema fa kyakkyawa ce tamkar mahaifiyar ki"

Ido ta zaro a kansa tana mai-mai-ta abunda ya fad'a a cikin ranta.

Hannun ya kai ze ta'ba ta tayi sauri daka masa tsawa.

Ba shiri ya janye hannun sa yana cewa, "to ai shikenan tinda bakyaso ba matsala,,, abunda yasa na nemo ki dama ina so ki dawo tsagi na ne"

A kausashe tace, "a matsayin ka na wa?? "

Kai tsaye yace, "magajin izza, ina so ki rabu da uwar d'akin ki -ki dawo guri na mu had'a kai don nemawa kan mu y'anci"

Ba tareda ta tsaya k'arasa jin zancen shi ba ta yarfa masa wani kyakkyawan mari.

Raj.
Suna zaune shida gimbiya Sunaya suna tattaunawa,
Rausayar da kai yayi yace, "Mama gaskiya aikin mu yayi kyau inama ze d'ore a haka"

Dariya tayi tace, "haba d'ana kwantar da hankalin ka mana!! Ai tukunna ma wannan ai farko ne ka zuba ido kaga k'arshen, ai in gaya maka mu ai mun riga mun haye yanzu bamu da wata damuwa tinda har muka samu kusanci da ita,
Yaro na mahaifin ka dalilin kashe shi kenan akan gaskiyar sa, dan yace ze k'waci sarautar sa, ai sarautar tamu ce ba ta-ta ba amma muguwar yarinyar nan sai ta kashe mana shi gashi yanzu ta bar mu mu kad'ai ai nayiwa kaina alk'awarin bazan k'yale ta ba har sai na d'auki mummunar fansa akan ta, yaro na ka bita a hankali kayi mata ladabi har zuwa lokacin da zamu gama jefa ta cikin tarkon mu a lokacin ne zata rasa gabas ta rasa yamma,
Mu kuma lokacin mun zama masu karaga"

Ta'be baki Raj yayi yace, "sune basu kashe ta sun huta ba,, da tini ba wannan zancen ake ba, munafukar mata,
Ni dai wannan d'an da tasa ake bashi kulawa irin ta y'ay'an sarakai shine yafi tayar min da hankali ba akuya ta lullu'be mana da fatar kura ba kuwa??

Dafa kafad'ar sa tayi tareda cewa, " sa ranka a inuwa d'ana ai mun riga mun kusa zurma ta, ni a guri na jariri ba komai bane, cikin sauk'i zan talitse shi wuyar abun kawai ita d'in amma dan ta jariri ai me sauk'i ce"

Raj yace, "to shikenan, ni dai yanzu jindad'i na nake ba abunda ya dame ni tinda ina samun kulawa"

Tsaki Gimbiya Sunaya tayi tace, "kaji kai dama ai ba'a abun arziki da kai, na lura kwata-kwata baka damu da jinin mahaifin ka da aka zubar ba, lusarin namiji"

Tayi magana cikin nuna alamar fushi.

Dariya yayi ya tashi yana cewa, "bari ma ki gani tafiya zanyi"

Tsaki kawai ta raka shi dashi batace masa k'ala ba.

*Indo ce..*


Dafe kumatunsa yayi tareda rintse ido,, zuciyar sa ta fara tafarfasa lokaci d'aya,,, ji yake kamar ya hau kanta da duka amma sanin hakan ba riba yasa ya k'wak'ulo murmushin yak'e,
'Dan girgiza kai yayi yace, "banji dad'i ba, ba haka naso ki fahimta ba, ya kamata ki nutsu ki saurare ni,,
Ki dawo guri na hakan zefi miki kwanciyar hankali da nutsuwa idan ba haka ba kuma zakiji a jikin ki ne zanyi maganin ki"

Murmusawa tayi tace, "barazana kake son yi min??? Ai ba sai ka bi ta wannan hanyar ba, me kake so kayi min??? Kana so ka rabani da Shugaba ta ko??
To ka bada k'ok'ari,
Har ni zaka tsora, meye kakeji dashi??
Kashe ni zakayi?? Ko kuwa lalata ni zakayi??

Shiru yayi cikin k'unar rai ya kauda kai daga gareta cike da rashin sanin abunyi.


Ta k'ara murmusawa tace, " duk wata barazana da zakayi min baza tayi amfani ba sai dai ma ta hallakar da kai, nace bazanyi abunda kace ba duk abunda kaga zakayi ina jiran ka, ka jaraba ka gani ko akwai riba"

Daga haka ta juya zata bar masa wajen.

Da sauri yace, "yarinyar nan a zahiri take nuna miki son ki take amma a zuci ba haka bane, ita d'in muguwar yarinya ce wadda duk irin halaccin da kayi mata bazata ta'ba ganin sa ba haka zata sakanya maka da sharri,
Nasan kina son sanin suwaye iyayen ki,
To ni nasan su"

Tsayawa tayi cakkk tana saurarar maganganun sa, a take jikin ta yayi sanyi zuciyar ta ta kwad'aitu da son taji labarin iyayen ta,
Dawowa tayi ta nemi guri ta zauna sannan tace, "ina sauraron ka"

Mugun Murmushi ya saki kafin yace, "iyayen ki sun kasance bayi ne a wannan masarauta tin asalin ta,
Amintattun mutane ne masu gaskiya da kuma bin umarnin na sama dasu, basa ta'ba cutar da mutum,
Rana tsaka wannan yarinyar tazo ta zama sarauniya, muguwar shugaba kenan, tayi kashe kashe ta zubda jini, nima a lokacin na rasa mahaifiya ta,
Mahaifina dan yayi magana akan kashe masa mata da akayi shina sai ta tsira masa mashi a k'ahon zuciyar sa, ina kallo akan ido na ta kashe min iyaye na"

Shiru yayi yana share k'walla cike da tausayawa kanshi.

Jikin Hadima Farhana ya k'ara d'aukar zafi ga tasa nan in tausayin sa da ya lullu'be ta, jinjina kai tayi tace, "Ka dena kuka kayi hak'uri"

Share k'wallar yayi yace, "Bayan tayi wannan ta'asar ta zama shugaba haka take gudanar da mulkin ta tin asali duk wanda ya ta'ba ta koda kuwa dangin ta ne sai tasa a gutsire masa d'an yatsa, haka take wannan zaluncin har yanzu bata dena ba,
Nima a wannan hannun nawa na dama har yanzu akwai tabon ta wanda taje fad'uwa na rik'o ta tana juyowa ta keta min hannu ta zubar min da jini har sai da nayi kamar bazan rayu ba,
Ai kema kin gani dai har yanzu bata dena ba,
Wanda yasha gaban ta kuwa sai tasa a d'aure shi da sark'ok'i ai ta jansa a k'asa har sai anji masa munanan ciwuka jikin sa yayi ta zubda
End Ads