Da sauri ta durk'ushe a wajen tareda cewa, "Hazoor, (Ranki ya dad'e) na amsa kiran ki"
Ido ta zuba mata har wani lokaci kamar wadda bata ta'ba magana ba da kyar ta iya cewa, "Abdulkareem a nomo min Hadima Urmi"
Hadima Farhana ta jinjina kai ta tashi da sauri tana cewa, "yanzu kuwa Ranki ya dad'e, amma kafin na fita ya kamata kisha ruwa, abunda dai bakya so d'in ni kuma karanbani yayi min yawa bana son ganin ki cikin wani yanayi, kisha ruwa zuciyar ki zata samu salama Insha Allah"
Kamar bazata kula ba sai kuma ta jinjina kai tace, "zan sha amma bayan na ganshi"
Hadima Farhana tasan halin kayar ta dan haka tace, "yadda kika ce haka za'ayi, nagode da amsa tayi na"
Bata kalle ta ba sai ma hannu da ta mik'awa Arjula, ita kuwa tayi d'araf akai.
Basu 'bata lokaci ba suka dawo tare.
Uwar Hadimai Urmi ta mik'a gaisuwar ta.
Bayan ta amsa ta mik'e ta nufi hanyar fita.
Hadima Farhana tace, "Uwar Hadimai Urmi Shugaba tana son ganin d'an ta ne"
Hadima Urmi ta mik'e tana cewa, "zan cika aiki ya shugaba ta"
Sashin gaba d'aya yara ne wasu sun tasa wasu k'ananu ne.
suna ganin ta suka fara murna,,
d'aya bayan d'aya suke zuwa suna ta'ba k'afar ta ita kuwa sai sa musu Albarka take,
Masu kula dasu ma sai mik'a gaisuwa suke.
Hadima Urmi ce tayi gaba zuwa cikin wani d'aki k'ayatacce wanda yaji ado da dukiya me yawan gaske ko ina tsaf sai walk'iya yake.
Da murmushi akan fuskar ta ta shiga kai tsaye wajen d'an madai-dai-cin gadon da aka kwantar dashi yana shan baccin sa ta nufa, tsayawa tayi ta zuba masa ido tana k'ara jin k'aunar sa tana ratsa duka sassan jikin ta, a hankali tasa hannu ta shafi kansa har zuwa fuskar sa tareda furta, "Masha Allah"
Ta'ba shin da tayi ne yasa yayi firgigit ya bud'e idon sa yana waro su a kanta.
Yalwataccen murmushi ta sakar masa ganin yadda ya k'ara wayo ya girma, hakan ya tabbatar mata yana samun kulawar da ta dace, cikeda kulawa ta d'auke shi ta rungume shi tareda binsa da addu'o'i har wani lokaci sannan ta mik'a shi ga Hadima Urmi,
Hannu tasa ta share y'ar k'wallar da ta fara k'ok'arin sakkowa daga cikin idanun ta,
A zuciyar ta tana cewa, "ranar kuka bata zo ba tukunna"
Ficewa tayi daga shashin ta koma nata.
Ramraj ne zaune gefen k'afafun mahaifiyar sa, Kallo d'aya zakayi masa ka gane yana cikin damuwa.
Rausayar da kai yayi yace, "Mama Shikenan Maharani Mahalakshimi bazata saurare ni ba???
Wani shu'umin murmushi gimbiya Sunaya ta saki kafin tace, " ina ta murna na haifi namiji, namijin da ze iya yak'ar masarautar nan dan cika muradin mahaifin sa amma sai dai kashh, be cika namijin ba,
Raj a yanzu ba soyayyar ta ya kamata ka nema ba, Fansar jinin mahaifin ka ya kamata ka nema kuma ka nema masa cikar burin sa ko da ze samu salama,
Idan baka sani ba Maharani Mahalakhshimiey,
(Sarauniya Mahalakshmi) itace ta kashe maka Mahaifin ka ta ruguza cikar burin sa, wannan yarinyar shaid'aniya ce da suffar mutum a memakon muyi k'ok'arin kawar da ita sai kuma kace kana sonta??
Nace ka hak'ura ka k'i kaga yadda take wahalar da kai har yau tak'i saurarar ka bata ta taka ma baki d'aya, amma da Arveen ne na tabbata da zata saurare shi,
Kana kallon fa idan aka zauna a fada ma wuyacin abu ne bata bashi abunda zeyi ba, kaga wannan ma matsayi ne wanda kai baka same shi ba,
Mu bata d'auke mu matsayin jinin ta ba tafi ganewa Waziri da d'an sa saboda shi yafi mu nuna mata k'auna da kulawa, motsi kad'an idan kayi sai ta hukunta ka amma shi bata yi masa haka,
Ka dawo nutsuwar ka Raj kisan mutum a gurin ta tamkar shan ruwa ne bana so ta kashe ka ba tareda mun cika muradin mu ba"
Shiru Raj yayi maganganun Mahaifiyar sa suna ratsa shi, ya d'an d'ebi lokaci beyi magana ba sai kuma yace, "ita d'in ba wai wadda zamu kawar bace domin kuwa mutanen da suka fi mu k'arfi harda iko suna sun hakan amma sun kasa, Lakhshmie sarauniya ce wadda ta gagari duniya manyan masarautu suna da irin wannan buk'atar ta son kawar da ita dan haka idan muka kawar da ita kawai munyi yak'in ne amma ba mune da nasarar ba, sune zasu zo suyi kane kane akan komai,
Fansar jinin mahaifina ta hanyar kashe ta ko nakasta ta ba shine mafi kyawu ba, sai dai ta haifa min wani,, auren ta zanyi kawai kuma yadda tsarin yake wanda ya aure ta shine da mulki dan haka wannan ne ya dace damu,
Kiyi tunani akai sosai, yanzu lalla'ba ta zamuyi mu shiga jikinta sosai mu nuna mata komai ya wuce sai mu dinga binta a sannu muna hak'e jijiyoyin ta lokaci d'aya sai dai taji ta fad'a tarkon mu"
Dariya sosai Gimbiya Sunaya take sai da tayi me isarta sannan ta rungumo shi tana cewa, "ashe kana da fasaha d'ana gaskiya kai jarumi ne na dena ce maka ba jarumi ba kaji ko?? Bari ma gobe zanje nace mata baka da lafiya dan haka ka zauna gobe kar kaje ko ina kaji ko??
Zanje ma na nemo sa'a"
Yace, " ai kuwa ta haka zamu fara kama ta kinyi shawara me kyau"
Zaune take ita da Arjula suna hira sai surutu take zuba mata duk da cewar tsuntsuwar bata magana amma hakan be hana ta zama ta fad'a mata damuwar ta ba har ta bata labari,har abunda ya wuce baya ma suna tattaunawa,
Koda baza ta ce komai ba takan nuna alamar amsa ga abunda Maharani ta fad'a mata, idan na damuwa ne zata nuna alamar damuwar ta haka idan na farin ciki ne zata nuna,
Tsuntsuwa ce me ban mamaki sai dai kowa kawai ganin ta yake be san sirrin dake tattare da ita ba.
Kallon ta tayi tana murmushi tace, "Arjula!! Kin tuna a Fadar Maharanie Abunda ya faru?
Karyar da kai tayi hakan ke nuna alamar bata tuna ba.
Maharani tace, " kina nan fa Har maa take min dariya? Lokacin da yayi min..
Da sauri Arjula ta baza fuka-fikin ta tana fiki-fiki dashi,
Hakan yasa Maharani tayi shiru tana kallon ta fuskar ta d'auke da murmushi tace, "Yanzu dai kin tuna ko??
Kare kanta tayi da fuka-fikin ta ta cusa shi ciki tana karkad'a jela.
Dariya Maharani tayi tana cewa, " oh kunya ta ma kike ji?? Ni banji kunyar ki ba?
Sassauta murya tayi tace, "Arjula na kasa manta wannan ranar tana yawan dawowa cikin tunani na ko meyesa hakan??
Rausayar da kai tayi tareda yin kalar tausayi.
Maharani ta gyad'a kai kafin tace, " lokacin lek'en sirri yayi Arjula ki zagaye ko wane sashi na Mahaal kizo min da labarin abunda yake faruwa, ki tabbatar babu wanda ya ganki, ki bi iska yadda ko kusa da mutum kika je baze sani ba
"
Tashi Arjula tayi ta fice cike da son cika umarni.
Hadima Farhana ta k'araso tana d'an murmushi tace, "Sannu da hutawa Shugaba"
Bata ce komai ba sai Jinjina kai tayi ba tareda ta kalle ta ba.
Hadima Farhana tace, "Ranki ya dad'e taya kike iya yin magana da Arjula? Shin tsuntsuwar tsafi ce ko kuwa?? Naga bama ita kad'ai ba kema kina iya jin maganar ta"
Mik'ewa tayi daga kishingid'en da take ta d'ora k'afar ta d'aya kan d'ayar,
Cikin Izza tace, "daga ina kike??? "
K'asa tayi da kai tareda cewa, "ina neman afuwar shugaba, naje Sashin marayu Abdulkareem ya girma sosai, daga nan na wuce 'bangaren bayi dan kula da abunda suke aikatawa na tarar ba matsala, amma wata daga cikin manyan bayi na 'barin ciyar da mutane abinci na kama ta da laifin hantarar na k'asa da ita gami da wahalar dasu ko tayi musu horon yunwa haka kuma abincin sai son ranta take bawa mutum bata ba su wanda zasu ci ya k'osar dasu, sun bani k'orafi ne sai kuma nayi bincike na gane hakan nayi shigar bayin ne na shiga cikin su sai kuma naga hakan tana faruwa nima ta faru a kai na"
Jinjina kai Sarauniya tayi a hankali ta bud'e baki tace, " kin nuna mata kanki?? Wane mataki kika d'auka??
Da sauri tace, "Maharani ban d'auki mataki ba bata san ma naje ba"
Gyad'a kai tayi tace, "ki mayar da ita 'barin share share ba'a matsayin wata ba itama ta shiga cikin wanda shugabar su zata dinga basu umarni, a wajen abinci kuma ki nemi wata ki d'ora sannan ta dinga yi mata kamar yadda itama ta yiwa mutane,
Bayan haka idan ta k'ara yin hakan ga wani zata kar'bi tsatstsauran hukunci"
Hadima Farhana tace, "Zanyi hakan ranki ya dad'e"
Wata Hadima ce tayi gyaran murya a bakin k'ofa tareda cewa, "zan iya shigowa Ranki ya dad'e???
Hadima Farhana tace, " shigo"
Shigowa tayi tana d'ibar gaisuwa cike da ladabi tace, "nice Sabuwar Hadimar da zata dinga nemawa mutane iso zuwa gareki Hazoor"
Jinjina kai tayi alamar ta gamsu, ta k'ara zuba mata ido alamar tana sauraron abunda zata fad'a.
Godiya tayi sannan ta cigaba da cewa, "Hazoor gimbiya Sunaya matar Tsohon Galadiman wannan masarauta tazo hankali tashe tana son ganin ki"
Shiru tayi na wani lokaci kafin ta gyad'a kai.
Hadima Farhana tace, "a iso lafiya"
Tashi tayi ta fita cikin sauri.
A hargitse gimbiya Sunaya ta shigo fuskar ta yare yare da k'walla ta zube a wajen k'afafun Maharani tana cewa, "ya shugaba ta d'a na ya kamu da cuta mara warkewa yana cikin tsananin rashin lafiya, ki tausaya masa kije ki duba shi na rasa me zanyi masa ya warke"
Kauda kai tayi a yatsine tace, "Hadima Farhana kije ki duba shi"
Baki Gimbiya sunaya ta saki tana kallon Sarauniya saboda jin abunda ta fad'a, a ranta tana cewa, "wannan gallababbiyar yarinyar fa ta fini dubara, ai kuwa yanzu zan shawo kan ki"
Fashewa tayi da kuka tana cewa, "Maharani Mahalakshmi, sunan ki suna ne me daraja da kima abar bauta me matuk'ar tausayi da jink'ai, Hazoor d'a na maraya ne bashi kowa sai ni sai ke mune dangin sa kece y'ar uwar sa mahaifin sa ya riga ya mutu,
Bamu sani ba ko shima ciwon ajali ne ya kama shi kije kuyi ban kwana kar ya mutu be samu kulawar ki koda sau d'aya ba, yana son yaga kin kula shi a matsayin sa na d'an uwan ki amma be samu hakan ba,
Nasan ze mutu ne da bak'in cikin wannan, ki tausaya masa shifa jinin ki ne Maharani,
Yanzu yana mutuwa shikenan na rasa kowa wayyo abar bauta Mahalakshmi ki sassauta min wannan bak'in cikin"
Ta k'ara rushewa da kuka tana kallon Maharani dan ganin matakin da zata d'auka, shin zata amince ko kuwa??
Cikin zuciyar ta kuwa tana k'issima, "ai kin gama yawo Lakshmi indai kika sake kika amince kina zuwa aikin gama ya gama burin mu ya cika "
Ba tareda jan lokaci ba ta tashi jikin ta har rawa yake saboda farin ciki, sai da tayi godiya sannan ta fice,
Tana komawa sashin su ta fara rawa saboda tsabar farin cikin da take ciki,
Raj da yake gefe kwance yana shan wahala da kyar ya iya cewa, " nifa Inajin ba dad'i meyesa zaki bani guba saboda kawai cikar burin ki Mama idan kuma ta kashe ni fa???
K'arasawa tayi gurin shi tana murmushi cike da rawar kai tace, "kai ragon maza ka shanye kawai, idan ba haka ba kasan dai zata gane ciwon k'arya kake dan haka na baka wannan gubar ai nasan bazata cutar da kai ba, ba abunda ze faru, ka daure kawai kai fa matsalar ka rashin juriya rago kawai"
Maida kai yayi ya kwanta cike da azaba ba tareda ya k'ara ce mata uffan ba.
Ita kuwa cigaba tayi da murna.
Lokacin da Maharani ta iso ya gama galabaita,
Sai a lokacin Gimbiya Sunaya ta nuna tsantsar damuwar ta akan sa sai kuka take kamar na fitar rai, duk a tunanin ta ba abunda gubar zatayi masa a ganin ta kawai ragonta ce take sa shi yana mata wai-wai.
Cikin nutsuwa ta k'arasa kansa ta zuba masa zaratan idanun ta.
Gimbiya Sunaya ta zube a wajen ta dafe kai tana kuka tareda cewa, "Maharani kina ganin halin da d'ana yake ciki kice wani abu dan Allah"
Kallon ta tayi cikin tsawa-tsawa tace, "meye abunda yaci???
Ido ta zazzaro a firgice zuciyar ta ta fara tsalle tana dako sama ta dawo k'asa, cikin razani ta saki wata yar dariyar tsoro wadda batasan lokacin da ta su'buce mata ba tana cewa, " ha ah aha Maharani ai babu abunda ma yaci kawai kinsan da yake rago ne"
Kafe ta tayi da ido kamar wadda take shirin cinye ta.
Irin mugun kallon da take watsa mata yasa taji hantar cikin ta ta fara hargitsawa, cikin rashin sanin abunyi tace, "uhm ,Maharani ki dena min irin kallon nan yana da ban tsoro"
Tayi magana tana y'ar dariya.
Kauda kai tayi daga gareta ta maida kallon ta ga Raj wanda zuwa yanzu ko idanun sa ma ya kasa k'i bud'ewa, ganin irin matsanancin halin da ya shiga yasa taji zuciyar ta tafara harbin iska,
A kausashe tace, "Ram!!!"
Da kyar ya iya d'aga ido ya kalle ta a wahalce.
"Kayi magana mana tashi ka fad'a min"
Yunk'urawa yayi ya tashi da k'yar dan k'arfin hali da kuma shakkar ta da yake,
Jiri ne ya d'ebe shi ya fara wata irin shak'uwa yayi baya ze fad'i.
Cikin sauri ta rik'o hannun sa a razane tareda cewa, "RajKumari!!!!!"
Ba Gimbiya Sunaya da shi kad'ai ba ita kanta Hadima Farhana sai da mamaki da al'ajabi ya kashe ta.
Zama tayi gefen sa tana rik'e da hannun sa, k'ara zuba masa ido take tana binsa da kallon tuhuma.
Shi kuwa k'amewa yayi ya bita da ido ko motsi ya kasayi.
Gimbiya Sunaya kuwa farin ciki yasa takejin kamar ta nutse a wajen, yau d'an ta ya samu matsayin da Sarauniya ta kira shi da suna tsadadde haka,
Ba dan kar ta gane lumbu lumbu tayi mata ba da ta taka rawar murna.
Lumshe idanun sa yayi tareda sauke 'boyayyar ajiyar zuciya.
Cikin sassanyar murya tace, "Kumari?? Me kaci ne?? Me yake damun ka haka??
Girgiza mata kai yayi alamar babu komai, cikin ransa kuwa yana mamakin yadda akayi ta damu dashi lokaci d'aya, abunda ko da sunan wasa bata ta'ba nuna tasan da shi d'in d'an uwan ta bane,
Abun mamakin ma yadda tayi saurin kai hannun ta jikin sa matar da ko ra'bar gefen ta mutum yayi sai ta hukunta shi koda sunan tsautsayi bare kuma ya ta'ba jikin ta shikenan tashi ta k'are sai dai Allah ya tseratar dashi, amma yau itace da kanta ta rik'o hannun sa,
Duk da ya fara fita hayyacin sa amma mamakim wannan be barshi ba.
Kallon Hadima Farhana tayi a tsawace tace, " ki nemo masu kula da lafiya mana!!"
Da sauri ta juya tana cewa, "Yanzu kuwa ranki ya dad'e"
Maida kallon ta tayi gareshi cikin sanyi tace, "Rajkumari karka damu zaka samu lafiya"
Duk da wahalar da yake sha bata hana shi sakin murmushi ba.
Gimbiya Sunaya ce ta matso kusa tana cewa, "abun wasa ya zama gaske?? Raj?? Ya naga kamar kana cikin mugun hali ne?? Me yasa haka?? Karfa kace min ka illatu"
Tsawa Maharani ta doka mata da cewa, "yi min shiru!! Koma menene ai laifin ki ne, yaro d'aya a gurin ki kin kasa kulawa dashi???
Tatta'be baki tayi ta fara k'walla cikin k'issa tace, " Hazoor, ina kulawa dashi sosai kawai tsautsay ne"
Cikin 'bacin rai tace, "kuma kika barshi yaci guba Meyesa zaki barshi yaci abunda ze cutar dashi waye ma ya bashi gubar???"
Goge k'wallar ta shiga yi tana cewa, "Maharani!! tashin hankali da rud'ani yasa na fara kasa gane ina na dosa, ance min fa gubar bata cutar da mutane shin ba da gaske bane??
Da mamaki Maharani tace, " kenan ma kina sane da abunda ya faru kece kika bashi ko kuwa da hannun ki a ciki???
Zuwa yanzu lamarin ya fara bata tsoro jikin ta ya hau kyarmar tsoro ganin abun ya fara rinca'be mata gashi Maharani tana son gano ta ga irin halin rayuwa ko mutuwar da d'anta ya shiga, wanda da take ganin wasa amma yanzu ta gane gaskiyar lamarin hakan yasa hankalin yayi tsuntsuwa zuwa sama..
A diririce tace, "haba Maharani meyesa zan bawa d'an ciki na guba?? Na rantse da abun bautar mu bansan anyi ba, Hazoor ki duba ki gani fa yadda aka mayar min da d'ana"
Jinjina kai tayi tace, "ko waye kuwa na gane shi to bazeji dad'i ba,
Kuma idan bazaki iya kulawa da RajKumari ba zaki iya mayar dashi gareni, shi jinina ne dan haka ki kula dashi, bayan yau idan na k'ara jin wani abu ya same shi zan d'auki mataki akan ki"
Da sauri tace, "to ai kuwa zan kula dashi da gudu. ma Kuwa"
Maganin gargajiya ne aka shiga yi masa ba ji ba gani domin ceto rayuwar sa.
Bata da lokacin 'batawa a wajen dan haka ta barsu tareda basu umarnin bashi kulawa ta musamman.
Sai da sukayi da gaske sannan suka samu kansa bayan ya amayar da gubar ya dawo dai-dai sai dai rashin k'warin jiki da d'an abunda ba'a rasa ba.
Hadima Farhana ce ta kalle ta tayi k'asa da kai cikin ladabi tace, "Maharani ki gafarce ni, amma ina ganin kawai duk shiryawa sukayi ita da d'an nata, a gani na suna son cimma