x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 7 - TAJMAHAAL

  • 18001 words
  • 21000 words
  • Out of 37284 words

Category: Love Stories

Views 142

29 May 2025
Start ads
After Image Ads
k'aramin lokaci suka warware shi daga zargen da sukayi masa,, mutum ne kamar kowa amma duk da fuskar sa a rufe take kallo d'aya zakayi masa ka fahimci cikar haiba da zallar kwarjini gami da k'arfin dantse a tattare dashi.

Ido Maharani ta zuba masa zuciyar ta fall tunane tunane kala-kala,,, bayan shud'ewar lokaci me tsayi yau ce rana ta farko wadda ta d'ora idon ta akan abu kuma taji bata son saukewa"

Ajiyar zuciya ta sauke tareda lumshe zaratan idanun ta, takawa ta shigayi har sai da tayi taku uku sannan ta tsaya cikin zallar zarra tace, "bud'e min fuskar ka"

Shiru kamar ba dashi take ba ko motsawa beyi ba.

Ba tace masa komai ba dan bata son jayayya cike da jarumta ta k'arasa inda yake ta shammace shi ta janye abunda yayi nad'in dashi, take kyakkyawar fuskar sa ta bayyana,
Ido ya zuba mata kamar yadda itama ta zuba masa,
Suka shiga yiwa juna kallo na rashin tsoro da kuma rashin shakkar juna.

Sun d'ebi lokaci cikin wannan yanayi kafin ta sauke numfashi, murmushin izza tayi tareda cewa, "Ya kai me wannan fuska ma'abociyar kwarjini ina son sanin waye kai"

K'asa yayi da kai ya d'ago ya k'ara kallon sannan ya koma kallon gefe cikin kamalalliyar muryar sa yace, " bawan Allah"

Har cikin ranta sai da maganar ta ratsa ta lokaci d'aya ta tafi da bugun Zuciyar ta, jinjina kai tayi ta k'ara da cewa, "Dani da kai dasu duk bayin sa ne sai dai mun kasance muna addini mabanbanta, masarautar Purlasiri tana cike ne da mutane iri iri kuma masu addinai daban daban
Ba mu kasance mabiya addini d'aya ba, irin lafazin bakin ka kai tsaye ya tabbatar min da cewar kai d'in mabiyin addinin islam ne,
Sai dai kuma mabiya addinin nan babu su yanzu a wannan masarauta sun riga sun shud'e cikin wata tafiyar ruwa da ta ta'ba wanzuwa a cikin wannan masarauta,
Daga ina kake???
Ya sunan ka????

Kamar da dutse take magana yayi mata banza ko kallon ta baya yi bare ta gane yasan tana magana.

Murmushi tayi gami da yin tattaki sannan tace, " Kana da jinkai, sai dai kuma nan fada ta ce, kai d'in baka yi min kama da wani d'an sarakai ba, kafi kama da irin mutanen dajin nan"

Kai tsaye yace, "tunanin ki ya baki dai-dai ni na rayu ne a daji"

K'ara ware masa idanu tayi cikin gadara da tsantsar izza tace, "sunan ka"

"ARUUF''!!!!!!!!!!! ARUUFUL-ANSAAR!!!!!!!!!!!!!!!!

Ya fad'a cike da karsashi.

Sai da tsigar jikin ta ta yarfa saboda yanayin yadda yayi maganar me bala'in tsargawa mutum lokaci d'aya, akan la'b'ban ta ta mai-mai-ta "Aruuful'Ansaar " ta fad'a tana jefa idanun ta cikin k'wayar idon sa.

Shima kallon ta yake cike da jarumta.

Matsowa ta k'arayi kusa dashi sannan tace, "Aruufu'Ansaar? Tabbas wannan suna ne me dad'i sosai, uhm, ya sunan baban ka????

Kafin ta rufe baki yace, "Abu Ansaar "

Girgiza kai tayi tace, "sunan sa nake magana"

Ya k'ara mai-mai-ta mata cewar "Abuu Ansaar"

Ganin nema yake ya 'bata mata lokaci yasa tace, "mahaifiyar ka fa???

Kara tsaye yace, " Ummu Ansaar"

Zuwa yanzu zuciyar ta ta fara turnuk'owa ranta ya fara 'baci amma sai ta danne ta jinjina kai kafin tace, "dangin ka fa??

K'asa yayi da idon sa tareda cewa, " Ummu Ansaar Abu Ansaar sune kawai dangi na ban rayu tareda kowa ba sai su, sune na sani"

Jinjina kai tayi tace, "na yarda da hakan amma dole mahaifan ka suna da cikakken suna na gaskiya kowa ya shaida su d'in iyayen ka ne ba buk'atar k'ara mai-mai-tawa,
Meye sunan ta?

Sai da ya kalli cikin k'wayar idon ta sannan yace, " Ummu Ansaar "

Zuwa yanzu ji take kamar ta zaro takobin ta daga cikin koben ta ta falle masa kai saboda 'bacin rai gaba d'aya ji take ya gama zubar mata da mutunci kimar ta ta gama ta'buwa,
Mik'awa Hadima Farhana Takobin tayi ta k'ara matsawa kusa dashi, ba tareda shakka ba tasa hannu ta tallafo ha'bar sa tana cewa, "ya kamata ka gane cewa kaifa ba yaro bane da za'ace sunan Maman kawai ya sani"

Cikin zafin nama da zafin zuciya ya yarfa mata wani shigaggen marin da sai da taji duniyar ta tsaya mata cakkkk lokaci d'aya.

Cike da k'warewar aikin su sukayo kansa har sun fara zarge shi cikin sark'ok'in suna shirin hukunta shi.

Cikin tsawa tace, "ku dakata!!!!!

Dakatawa sukayi kamar yadda ta buk'ata, tasa hannu ta kwashe gashin ta da ya rufe mata fuska sakamakon hargitsuwar da tayi saboda azabar marin,
Cikin d'aga murya tace, " shi d'in ya kasance bak'o ne yayi kuskure a bisa rashin sani tabbas ya kamata yasan wacece Sarauniya Mahalakhshmi yana da kyau kuyi masa bayani yadda ze iya fahimta amma tabbas yayi kuskure"

Kallon ta yayi tareda cewa, "mafi girman kuskure shine wanda kika aikata,
Ni musulmin k'warai ne kuma addini na be baki damar d'ora hannu a kaina ba, ina ke'ban ce kaina da duk wata mace dan haka ki shiga taitayin ki"

Murmushi tayi cikin k'asaitacciyar muryar ta tace, "Aruuful'Ansaar kasan hukuncin duk wanda ya d'ora hannun sa a kan Maharani Mahalakhshmi koda kuwa macece?? Za'a yanke masa babban d'an yatsa indai da niya yayi, a rashin sani kuma ko a kuskure? Za'a yanka tafin hannun sa ne yadda ze gane kuskuren sa,
Yau ce ranar farko da na ta'ba yiwa wani mutum da ya d'ora hannun sa a kaina sassauci ka godewa Allah"

Cikin d'aga murya tace, "ya cancata da zaman kurkuku har zuwa lokacin da na umarci a fito dashi, ku d'akko jadawalin dokokin masarauta a karanta masa da yadda ze iya fahimta ko na rana d'aya kar ku barshi yabar wannan masarauta daga yau ya zama bawa na"

"Yarinya ce ke baki da hankali shiyasa kike irin wannan tunanin, daga ni sai Mahaifina muke rayuwa kuma yanzu sai in zama bawan ki shi kuma in barshi kenan? Ke sarauniya ce ban damu da hakan ba, ban aminta ma da wata halittar mutane a duniya bayan ni da mahaifi na da mahaifiya ta ba bare kuma nasan akwai wata sarauniya,
Abu Ansaar yana can yana jirana dan haka zan koma gare shi"

Murmushi tayi tace, "Abu Ansaar ma kansa laifin Ansaar ya shafe shi dan haka babu kai babu komawa amma idan ka damu da ganin sa shi ma ze zo kuma yadda ka kasance bawana haka shima ze kasance, zan waiwaye ka cikin lokaci, koda yaushe ka tsammaci zuwa na"

Daga haka ta juya tabar wajen cikin takun ta me nuna zallar jinin sarautar dake yawo a cikin jikin ta.

Kafin yayi wani yunk'uri sun d'aure shi cikin hanzari dan kuwa sun tsorata da lamarin sa duba da yadda ya basu bak'ar wuya kafin su same shi, kamar yadda tace haka sukayi suka wuce dashi kurkuku.

Zuciyar sa kawai k'una take, tinda yake be ta'ba fitowa tudun k'asa cikin mutane ba, yau ce ranar da ya fara tozali dasu amma sun saka masa da wannan rashin albarkar, tunanin irin halin da Abu Ansaar ze kasance kawai yake yasan yana can hankalin sa tashe, ko yawo ya shiga yaga ya d'an jima yanzu hankalin sa zeyi k'ololuwar tashi gashi ba da sanin sa ya fito daga dajin su ba kullum cikin gargad'ar sa yake da fita cikin mutane amma yau tsautsayi yasa dokin sa ya jawo shi garin wasa,
Ashe dai Abu Ansaar yasan halin mutanen ne shiyasa yake cewa koda wasa kar yayi marmarin zuwa domin cakud'ad'd'iyar rayuwa sukeyi,
Kamar ya zunduma ihu haka yakeji"


Raj da jikin sa yake ta tsuma har yanzu yayi lakur a bayan mahaifiyar sa,
A razane tace, "Raj meye yafaru ne haka? Waye shi wannan mutum da ya tinkaro mu mukayi wannan girgizar? A tsorace nake har yanzu"

Raj yace, "Mama kema kinji tsoro bare kuma ni? Nima ban san ko waye ba kuma har ya d'auki hannu ya mari Maharani kuma ba'a yi masa hukunci ba"

Gimbiya Sunaya tace, "Gaskiya ne Raj nima tsoron sa nakeji"

Arveen ya kalli mahaifin sa cikin rud'ani yace, "Baba na wai meye dalilin faruwar hakan ne? Ya zama dole ka shiga d'akin tsafin ka yanzu domin ka dubo mana shin wannan na asalin ne ko kuwa wani ne? Tabbas mutumin nan ya kasance me k'warin zuciya da matuk'ar kwarjini, shi d'in jarumin jarumai ne, tinkaro mu da yayi yasa masarautar mu tayi girgizar da ko yak'i ne ya taso sai haka, lallai na dasa alamar tambaya ta akan sa Baba, kuma yanzu k'iyayyata ta dawo gareshi na tsane shi"

Bakin makeken gadon ta ta zauna tana k'ara mai-mai-ta tunanin abunda ya faru, na dak'ik'a d'aya ji take bugin zuciyar ta yana k'ara tsanan ta, ta rasa inane inda zata sa kanta taji sanyi, tana matuk'ar jin zafi idan ta tuna yadda ya d'ebi yatsun sa biyar ya tarfa mata tafi a fuska, take taji zuciyar ta ta gaya mata idan bata wahalar dashi ta mayar dashi k'ask'antaccen bawan ta ba baza ta ta'ba hucewa ba, idan ta tuna shid'in musulmi ne kuma takanji wani abu yana sukar k'ahon zuciyar ta.

Farhana ce ta matso kusa da ita cikin sigar rarrashi tace, "Hazoor dan Allah ki yi hak'uri ki yafe masa shi d'in yayi kuskure ne a rashin sani amma ze gyara da zarar yasan wacece ke, ni dai ba ta shi ma nake ba, wannan 'bacin ran naki ne na tsani ganin sa bana so maharani ki dena dan Allah"

Jinjina kai tayi kafin ta mik'e ta shiga takawa har zuwa wajen taga, murmushi tayi tace, "Farhana ta?? Afuwa ga wanda yayi kuskure hakan yana sawa ne ya k'ara mai-mai-tawa rayuwa ta koyar dani darasai masu tarin yawa, karki damu a kaina indai kina son ki dena ganin fushi na to sai kin dai-dai-ta nutsuwar jama'a ta, sannan zaki gane kaina"

Hadima Farhana tace, "ni kuwa zan jarraba Ranki yadad'e"

Daga haka tasa kai ta fice ta barta.

Hannu ta mik'awa Arjula tareda cewa, "meye kike gani game da Ansaar yanayin sa yana nuni da......



*INDO CE..*
[18/03, 9:36 a.m.] INDO CE..: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JhUTxJ28ext83rI6uvV1xB


*🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠*

(Masarauta)


Mallakin

*INDO CE..*



🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼


*Page~10*


بسم الله الر حمن الر حيم



*ga masu buk'atar shiga group na musamman ina nan ina cigaba da posting kullum domin jin k'arshen labarin Naira 100 ne kati kuma 200 domin k'arin bayani ku neme ni ta wannan number 08146838480 gani ya kori ji kar ku bari a baku labari😂*




Da Cewa shi d'in jarumi ne, yanayin sa da yadda yake tafiyar da komai tamkar jarumi na, a lokacin da na fara ganin fuskar sa naso ace ba wannan fuskar na gani ba,,, ba dan na riga na sani ba da babu abunda ze hanani cewa shi d'in jinin Abu Abdulkareem ne, sai kace shine,, amma kuma ba shid'in bane, nasan shi a koda yaushe ze kasance yana kama dani ne"

Ta k'arasa maganar tana y'ar dariya kafin ta cigaba da cewa, "Ya matuk'ar girgiza ni, zuwa yanzu na riga na yankewa kaina cewa, Alhinin bayyanar AruufulAnsaar ne yasa nakejin bak'on yanayi, Arjula a lokacin da na riga na d'ai-d'aita imani da tausayi na banyi tunanin cewa a duniya akwai wani d'an adam wanda ze zo yafini zarra ba, ban ta'ba kawowa akwai wanda ze iya kallon tsabar ido na ya zabga min mari haka ba, tabbas ina jin rad'ad'i da k'una Arjula, ban zaci akwai mutum wanda yake jin kansa kuma yake da matuk'ar jarumtar da ze iya ja dani akan ido na gaba da gaba, Waye shi Arjula??
Na gigita kuma na k'agu da matuk'ar buk'atar sanin tarihin sa da asalin sa, sai dai ko sunan iyayen sa yak'i furta min bare nasan inane bakin zaren,
Arjula yana da kafiya ni kuma inaji da izza da zamu sauke wannan tabbas da zamu iya kawar da matsalar cikin k'aramin lokaci, amma bazan iya ba, babu wanda yake iya samun kaina sai shi kad'ai har mamakin yadda akai na mallaka masa rayuwa ta gaba d'aya nake, gashi yanzu na kasa yarda da kowa na kasa samun kusanci da kowa shi kuma ya riga yayitazara dani,
Lokaci lokaci nakanji tamkar ni marainiya ce abu d'aya nake tunawa ya gusar min da duk wannan tunanin tabbas bazanyi kukan maraici ba nan gaba,
Arjula ina ta surutu ni kad'ai baza kice komai ba??


Wunin yau ko abinci Waziri be tsaya yi ba ya duk'ufa wajen gano waye Ansaar sai dai har rufewar Almuru manufar abun bata bayyana gareshi ba har sai da ya k'ara raba dare,
Zazzafar iska ya furzar tareda zubawa Arveen ido.

Cikin sauri Arveen yace, Baba na ka fad'a min shine ko?? Me yake faruwa??

Waziri yace, "Arveen ba shi bane!!! Tabbas wancan ya mutu sai dai yabar baya da hazo!!! Wancan ya mutu mma ta samu wani wanda ze kasance bango a gareta kuma makamin ta, kaico, shi d'in ba kamar ko wane mutum bane dole ne mu san takun mu Arveen yanzu canja Salo zamuyi tabbas"

Arveen yace, "Baba na tabbas ina bayan ka indai zebamu matsala kawai mu kawar dashi mu huta"

Gimbiya Jusiyya tinda ta farko take faman numfarfashi jikin ta yayi zafi d'auu sai da temakon Jakadiya suka mayar da ita turakar ta sai bata fifita ake ita kuwa tana faman nishe nishe.

Hadima Fadya ce ta shigo bayan ta nemi izini, zubewa tayi tana gaisuwa kafin ta k'ara da cewa, "Ranki yadad'e Uwa Jusiyya tana cikin matsanancin yanayi na rashin lafiya"

Ido ta zuba mata har wani lokaci kafin tace, "su waye masu kula da ita?

Kafin ta rufe baki Hadima Fadya tace, " Ranki yadad'e Hadimar ta da kuma jakadiya sune suke kula da ita yanzun haka hadima ce tazo ta sanar dani kuma tace in sanar miki"

Wata rikitacciyar tsawa Maharani ta doka mata, "karki k'ara gauraya maganar ki da tawa, duk saurin da kike ki jira sai nayi shiru sannan ki d'ora karki k'ara musayar yawu dani"

Tsananin firgitar da tayi yasa ba shiri taji fitsari ya fara zubowa jikin ta ya d'au kakkarwa gumi ya shiga keto mata ta ko ina, da kyar ta iya cewa, "tuba nake ranki yadad'e sarauniya a gafarce ni a rashin sani ne hakan ta faru na rantse da abun bauta kuma nayi Alk'awari da Maharaja Bazan k'ara kuskuren nan ba"

Bata ko kalle ta ba bare tasa ran samun amsa hakan yasa ta tashi tayi waje har tana shirin yin tuntu'be.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta tashi ta gyara mayafin ta ta nufi hanyar fita,
Kai tsaye sashin Gimbiya Jusiyya ta wuce ta same ta kwance ta kishingid'a da filo sai maida numfashi take,
Ido ta zuba mata kamar bazata d'auke ba sai kuma ta kawar da kai ba tareda tayi magana ba.

Gimbiya Jusiyya tace, "jakadiya kuje waje zan neme ku"

Jakadiya tace, "Ranki yadad'e yanzu ma kuwa"

Sai da suka fita sannan ta nemi guri ta zauna a bakin k'aton gadon, kamar wadda take fizgo maganar da k'yar tace, "Mama Jusi? Meye abunda ya faru dake haka??

Gimbiya Jusiyya tace, " Yarinya ta waye wannan?? Wanda ya shigo wannan Masarauta tamu??

Mayar da kallon ta tayi zuwa gefe a fiffik'e tace, "Ba shine abunda ya kamata ki furta ba ya dace ki bani amsa ta tukunna ki tsirko naki zancen,
Aruuful'Ansaar shine sunan sa bayan haka bansan ko waye shi ba, sai dai daga yau zaki iya kiran shi da bawa na a cikin wannan masarauta domin kuwa bashida matsayin da ya wuce wannan"

Zazzafar ajiyar zuciya Gimbiya Jusi ta sauke kafin tace, "Kiyi hak'uri a bisa rashin baki amsa da nayi, amsar itace tinda Aruiful'Ansaar ya nufo wannan masarauta naji duk na fita daga cikin nutsuwa ta, na rasa gane neye sirrin hakan, har yanzu na kasa dawowa dai-dai"

Numfashi taja sannan tace, "na dasa ayar tambaya a kanku, Gimbiya Sunaya da Gimbiya Jusiyya tabbas naji abunda kuka fad'a sai dai ban shiga irin wannan tashin hankalin ba, tabbas Aruuf mutum ne me tasiri, zan saka wannan a cikin tunani na, ki mayar da hankali akan maganin da ma'aikatan lafiya suka d'oraki a kai dan yanzu kin manyanta dole ki kula da kanki, karkiyi k'ok'arin jefa kanki Hurumi na hakan ze wulak'anta kimar ki"

Daga haka ta tashi tana k'ok'arin fita,
Dakatar da ita tayi da cewa, "zaki iya fad'an komai a kaina domin kuwa rashin sani yafi dare duhu,
Na sani k'warai Aruuf yana da tasiri sosai hakan ne ma yasa zuciyar ki ta fara son yarda dashi tin kafin ki gane ko shi d'in waye,
Ki sani kece sarauniyar da kika gagari kowace masarauta ta duniya haka kuma wanda suke son mallakar duniya, mutane ne daban daban a ko wane yanki daga ko wane sassa na duniya haka kuma k'abilu daban daban kowa yana iya k'ok'arin sa dan ganin ya mallake ki ko kuma ya rusa ki,
Haka kuma kina da abokan gaba,
Ni bana yarda da kowa yanzu sai ke tin daga lokacin da aka tarwatsa farin ciki na aka tarwatsa ahali na haka miji na ma ba'a k'yale shi ba haka d'an cikin ciki na shima be tsira ba,
Mahalakhshmiey tabbas idan na zamanto me cutar dake na zama babbar asararriya, bazan iya hakan ba,
Zuciya ta tana shiga k'unci idan na tuna yadda kike d'auka ta tamkar wani abu me cutarwa, ni jinin ki ce Maharani Mahaa,,
Amma bazance dole sai kin fahimce ni ba nasan zaki gane hakan a duk lokacin da kika zauna kika nutsu,
Amma bana so ki yarda da Ansaar cikin lokaci kad'an kiyi bincike me tsauri akan sa, zansha magani na, ki kula da kanki yarinya ta"

Shiru tayi tana d'an tunani kafin ta saki wani yalwataccen murmushi sannan tace, "zanyi hakan"

Gimbiya Jusiyya ma murmusawa tayi a ranta tana tausayin yarinyar ta-ta.

Zaune take ta dafe goshi sai tunane tunane take, ji take kamar kwanyar ta zatayi bindiga saboda irin rud'ani da rikicin da take ciki,
Ji tayi an dafa kafad'ar ta ta juyo a hankali,
Wasik'a kuyangar ta mik'a mata ba tareda tayi magana ba,
Kar'ba tayi ta fara
End Ads