x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 10 - TAJMAHAAL

  • 27001 words
  • 30000 words
  • Out of 37284 words

Category: Love Stories

Views 134

29 May 2025
Start ads
After Image Ads
Maharaj,
Hahahaha lokaci. Ya gabato da zan rushe Masarautar Ganesh Maharaja"

Idanun ta ne suka k'ara girma yayin da gudun zuciyar ta ya ninku lokaci d'aya, wani razanannen numfashi taja kuma ta kasa mayar dashi ya dai-dai-ta,
Kamar hoto haka ta koma, idanun ta suna kan wasik'ar bata fasa kallon ta ba, ta karanta ta mai-mai-ta ba adadi.

hadima Farhana ce ta shigo a ladabce tace, "Ranki yadad'e, ganin ta a firgice yasa ita ma ta firgita tayi saurin k'arasawa tana cewa, " Hazoor kaise hai?, (ranki yadad'e ya akayi?)"

Jin shiru yasa ta mik'a hannu da nufin kar'bar wasik'ar.

Cikin sauri ta dunk'ule ta tareda luma hannun ta cikin ruwan, girgiza mata kai tayi tareda cewa, "Farhana kar kiyi bincike akan wannan baze amfana miki komai ba"

Cikin sanyi tace, "kiyi hak'uri Hazoor, ki huta lafiya"

Daga haka ta tashi tayi nata waje.

Koda ya koma ya sanarwa Aruuf abunda tace yayi mamaki sosai dan kuwa be ta'ba zaton hakan ba, take tunanin sa ya bashi da alama bata cin abincin kowa, kuma ba sune suke bata abincin ba shiyasa bata damu da shi ba,
A gefe guda kuwa farin cikin matsayin da Abun sa ya samu ya lullu'be shi a tunanin sa Kurkuku ta kai shi ko wani gurin dai mara kyau, amma da yaji haka sai yaji hankalin sa ya kwanta,
Komawa yayi can gefe ya bud'e abincin, ko d'aya daga ciki babu abunda ya burge shi domin kuwa irin abunda ya saba ci ba shine wannan ba,
'Daya daga cikin magunan da suke gurin ya fara kira,
Ta'be baki yayi yace, "kuma mage baza'ayi babu ku ba dan haka kuzo kuci abinci ni kam bazan iya ci ba"

Sauran duk sunyi gaba sai d'aya ce ta tsaya tana kuka da alama tana jiran abunda ze bata ne, mik'a mata yayi duka, ita kuwa ba jira ta fara ci.

Tana cikin ci ta dakata tana wata irin shak'uwa lokaci d'aya kumfa ta fara fita daga bakin ta idanun ta suka firfito sukayi guru-guru, kallo d'aya zakayi mata ka gane tana shan bak'ar wahala.

A razane ya zuba mata ido,, ya kalle ta ya kalli abincin cikin mamakon mamaki, yana kallo ta fad'i a wajen tana shure shure daga haka tayi lak'was alamar ranta baya tareda ita,
"Subhanallah"
Shine abunda ya fito daga bakin sa yana k'ara binta da kallon mamaki, zuciyar sa sam babu dad'i, ji yake kamar shine ya kashe ta kai tsaye ma shine silar mutuwar ta, kamar yayi kuka dan kuwa yana matuk'ar son dabbobi,
Tattare sauran abincin yayi yaje ya watsar a inda babu wani abu da ze gani yaci,
Da tambaya ya samu inda mahaifin sa yake.

cikin gata da wadatacciyar kulawa ya same shi, a sashin da yake komai yaji ko 'bangarorin wasu daga cikin wanda suka ji'banci gidan be kai nan kyau da tsaruwa ba,
Ko ina dukiya ce kamar banza.

Da murna ya k'arasa wajen sa yana cewa, "Abu na kana lafiya?"

Rungume shi yayi cikin farin ciki da tsantsar k'auna yace, "ina lafiya d'a na Allah yasa kaima haka ne"

Yayi murmushi tareda gyad'a kai yace, "nima ina lafiya, ina cikin farin ciki sosai"

Yayi dariya tareda cewa, "ina farin ciki a duk lokacin da naga farin cikin ka, Sabse Baada khiladie, (Babban Jarumi) naji dad'in zuwan ka"

Murmushi yayi yace, "farin cikin ka shine nawa, Abu indai bakayi farin ciki ba nima bazan yi ba"

Da sauri ya janye shi daga jikin sa yana cewa, "Allaah!!! Sabse baada Kiladi, meye yasa zuciyar ka take bugawa?
Wani abun mara dad'i ya tsinkaye ka d'a na"

Ya k'arasa maganar cike da yak'ini akan abunda ya fad'a kamar ze fashe da kuka.

Cike da kulawa yace, "Abu Kuch nahi hai, (Abu Babu komai)

Girgiza kai yayi yace, " kar ka 'boye min d'ana Alk'awari be ce haka ba"

Murmusawa yayi yace, "Abu na Sarakan Alk'awari, Abu an bawa yaron wannan masarauta ya kaiwa Sarauniya abinci shine na kar'ba dan ta fad'a min inda kake tsautsayi yasa na bawa mage shine ta mutu"

Abu Ansaar ya dafe goshi tareda cewa, "ya Allah, d'a na ka kwantar da hankalin ka babu komai tinda ba da sani ka bata ba, tabbas yaro na kai d'in daban kake daga cikin mutane, zuwan ka kenan masarautar nan amma Allah ya baka ikon ceton rayuwar Sarauniya Lakhshmi, Allah ya albarkaci rayuwar ka har bayan bayan ka yaro na"

Murmushi yayi tareda cewa, "Amin"

Shiru yayi yana tunanin abun, lallai akwai surkulle a cikin masarautar wanda ba lallai ya waru cikin dad'in Rai ba, kaida dangin ka amma kana neman kashe ta,
Kenan itama duk wannan girman kan nata ana nan ana shirye shiryen ganin bayan ta,
Da ita taci abincin nan fa da tuni ta mutu ko??

Ya jefawa kansa tambaya.

Abu Ansaar yace, "k'warai d'ana da tuni itace a matsayin wannan magen, Allah be k'addara mutuwar ta a dai-dai wannan lokacin ba"

Aruuf yace, "Abu kenan d'an uwan mutum sai ya nemi kashe shi a kan mulki??? Indai haka ne kuwa na tsani mulki,
Bare kuma Lakhshmi tana had'awa da son zuciyar ta,
Abu sai naji na kamu da tsanani tausayin ta, shin zan iya temaka mata?? Tinda nazo na lura akwai damuwa da yawa a tareda ita wanda bata bayyanawa, akwai babban abunda ya faru da ita kuma take 'boyewa ,, idan nayi bincike na gane damuwar ta-ta na temaka mata, banyi kuskure ba Abu???"

Abu Ansar yace, "bakayi kuskure ba Aruufu, a koda yaushe temako shine abu me kyau, Allah yace mu temakawa wanda suka gaza yin abunda mukayi temaka musu yana da kyau domin kuwa dama ce ta kyawawan ayyuka, ka jaraba da iya k'arfin ka da baiwar da Allah ya saukar maka Aruuful'Ansaar"

Murmushin jin dad'i yayi yace, "zanyi k'ok'ari sosai Abu na"

Da yamma suka halacci gurin da Raj ya fad'a domin had'uwar su.
cikin sanyin jiki Aruuf yace, "Raj waye yace ka kaiwa Lakhshmi abinci??"

Kai tsaye yace, "Mama ta ce, yayi dad'i ko?? Ai Mama ta iya abinci sosai"

Ido ya zuba masa yana jinjina kai ya lura da yanayin sa shi be san abunda mahaifiyar tasa ta shuka ba dan haka ya yanke shawarar baze fad'a masa ba domin shi zuciyar yara gareshi.

Ganin yayi zugum ne yasa yace, "Aruuf lafiya"

'Dan murmusawa yayi cikin son kauda zancen yace, "kai tsaye?? Aruuf babu d'an rissinawa??"

K'asa yayi da da kai tareda cewa, "a'a mantawa nayi"


Yace, "to ina jin ka"

Gyara zama yayi kafin ya fara cewa, "Ganesh Maharaja shine mahaifin ta, Gimbiya Jusiyya k'anwar sa, Baban Arveen da Baba na yayyen sa ne, kuma su baban su be basu mulki ba saboda yasan bazasu iya ba, Ganesh Maharaj ya fisu jajircewa da jarumta kuma ya ma fisu Adalci su ta kansu kawai suka sani basu damu da talakawa ba shiyasa baban su ys bawa Ganesh Maharaj mulki, bayan sun Haife ta aka zo akayi yak'i aka kashe su tin daga lokacin ita kuma ta koma hakan nan da kake ganin ta duk ta rikid'a ta koma kamaf muguwa to amma maganar gaskiya idan ka fahimce ta ba haka take ba, sai dai bata yafiya ba kuma ta sassauci ga duk wanda ya karya mata doka, idan kayi kuskure babba kuwa kashe ka zatayi hakan ne ma yasa ta kashe mahaifi na shima Arveen ta kashe mahaifiyar sa, amma Mama bata gaya min asalin laifin da sukayi mata ba,
Ni kuma a yanzu so nake kawai naga ta dawo mutum kamar kowa idan ta zama kamar mahaifin ta nasan duniya ma sai tayi alfahari da ita, amma a yanzu ko wace masarauta tsoron ta kawai akeji"

Numfashi Aruuf ya sauke kafin yace, "shikenan abunda ka sani??"

Yace, "eh mana amma dan Allah idan kasan cutar da ita zakayi kawai ka tafi ka barta"

Murmushi yayi tareda dafa kafad'ar sa yace, "karka damu k'ani na Lakhshmi zata canja kamar yadda kake so"

Da mamaki yace , "to taya kenan?"

Yace, "da ikon Allah kasan yafi k'arfin komai, fad'a min to ta kashe wanda suka kashe iyayen ta??"

'Dage kafad'a yayi ya nok'e ta alamar be sani ba. sai kuma yace, " eh ta kashe shi tabbas a cikin masarautar nan ma ta k'ona gawar sa"

Aruuf yace, "shikenan tashi kaje wajen Maman ka, sannan ka tsarkake zuciyar ka a koda yaushe karka bari duniya ta rud'e ka ka aikata kuskure kamar yadda iyayen ka suka aikata"

Gyad'a kai yayi yana maimaita kalaman nasa ya tashi yabar wajen.

Dafe kai yayi cikin juyayi da al'ajabi lallai ashe besan komai a duniya ba face daji, ashe ana irin wannan rayuwar a duniya be sani ba?.

Yana nan zaune yaji an dafa kafad'ar sa, be motsa ba sai mayar da hankali da yayi akan wanda ya dafa shin yana fahimtar yanayin sa domin gane da me yazo masa,
Fahimtar da yayi babu komai yasa ya juya suka had'a ido, kauda kai yayi tareda cewa, "Udday babban amintaccen Maharani meye kuma zakayi min??"

Zama Udday yayi cike da damuwa yace, "d'an uwa Aruuf kaji kad'an daga cikin labarin shugabar mu sai dai a yanzu haka tana cikin rud'ani da tashin hankali, bazaka iya temakon ta ba??"

Da d'an mamaki yace, "tashin hankali name?? Kuma tayaya zan iya temakon ta??"



*( masu yi min k'orafi ta prvt akan bana saka yaren su a cikin labarin, to sai dai fa ku d'an yi hak'uri an bani shawarwari ne akan cewar rubuta labarin da hausa yafi shiyasa, amma ko jefi jefi ne zan dinga sakawa insha Allah, amma fa ba irin sosai d'in nan ba, ina godiya da k'aunar ku gareni Allah ya saka da khairan)*


*Alk'alami na abun Alfahari na😊*




*INDO CE..*
[24/03, 8:51 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠*

(Masarauta)


Mallakin

*INDO CE..*



🌼ELEGANT ONLINE WRITER'S🌼


*Page~14*


بسم الله الر حمن الر حيم



*Ga masu buk'atar shiga group na musamman domin jin k'arshen Labarin Naira 100 ne kacal😂 ku hanzarta ku mallaki naku kar a barku a baya🤣 domin k'arin bayani ku neme ni tanan 👉🏻 08146838480*




Udday yace, "kwantar da hankali d'an uwa amma tabbas lamarin akwai rud'ani, wata azzalumar masarauta ce wadda take kiwon shugabar mu tin yarintar ta har zuwa yanzu, a wannan k'adamin kuma sun turo da wasik'ar zasu fara kawo mata hari,
Mun kasa gane yadda zamuyi d'an uwa, muna da buk'atar ka a wannan masarauta karka gujemu"

Jinjina kai yayi ya ta'be baki yace, "wannan tsakanin su ne ni kam bata shafe ni ba ni kuma indai ba itace tace na temaka mata ba to fa banida hannu a wannan lamarin, da zarar ta bani Abu na tafiya zamuyi yankin mu, inda bamu da wani shugaba bare ya kafa mana sharud'a"

Udday yace, "kar kayi haka d'an uwa Aruuf tabbas Sarauniya Lakhshmi tana da jin kai bazata yi abunda kake so ba"

Kai tsaye yace, "ashe bazan dai saka hannu na ciki ba"

Daga haka ya tashi ya bar wajen.

Hadima Farhana tana cikin tafiya sukayi arangama,
Da ido ta bishi har cikin k'ashin ta take jin wani irin yanayi ya tsinkaye ta, take zuciya ta fara raya mata abubuwa da dama da masu kyau da marasa kyau"

Tin be gane tana kallon sa ba har ya fuskanci hakan, cikin shirin ko ta kwana yace, "ke baki iya kallon hanyar ki bane kike bin mutum da ido?? Bana son rashin kamun kai"

Sosai maganar sa ta sosa mata zuciya, a sarari tace, "har wannan bawan ne ze dinga fad'a min wannan maganar banzar?"

Sake kallon sa tayi cike da jarumta tace, " ban iya ba, baka san cewa ra'bar gefe na ma kuskure bane?? Yanzu zansa ayi maka hukuncin da baka shirya ba,
Ku dinga sanin ya kamata ku gane tsaran ku da kuma wanda ba tsaran ku ba"

Cike da mamakin tsageranci irin nata yace, "Farhana!!! Ni bawa ne amma ba bawan wani ko wata ba bawan Allah ne, ra'bar kusa da ke kuma banga abun burgewar ma da ze sa na ra'be ki ba, idan arziki ne ban damu dashi ba dan ban san ma amfanin sa ba, mulki kuma kema baki da gado a kansa, ke kawai ta kusa da masu mulkin ce ba wai d'aya daga cikin su ba, kema ki dinga banbancewa mana"

Sosai ranta ya 'baci musamman da ta duba taga yadda ake kallon su, k'wafa tayi tace, "zaka gane kuma ka tabbatar da abunda na fad'a maka"

Daga haka ta wuce ta bashi guri,
Tana zuwa wajen Maharani ta zube a wajen sai had'e fuska take, da kyar ta iya yi mata sannu tana kaiwa ta fara zayyana k'orafin ta k'arya da gaskiya ta had'a ta fad'a"

Jinjina kai Maharani tayi kafin tace, "hukunci ya tabbata ga Aruuful Ansaar domin kuwa yana da yawan kutse cikin lamura na kuma hakan babban kuskure ne wanda yakan iya jawowa mutum zaman kurkuku na har abada ko kuma hukuncin kisa,
Yanzu kuma yazo ya tozarta ki Farhana, wai me yake tak'ama dashi ne?? Ina ganin fa sai na nuna masa iyakar sa, tin kafin ya wuce sa'ar sa"

Hadima Farhana tace, "ranki ya dad'e ina bayan ki d'ari bisa d'ari"

Cikin ranta kuwa farin ciki ne ya lulllu'be ta domin kuwa haka take so burin su ya cika na son muzanta shi a wajen Maharani, indai aka cigaba da hakan to wata rana da kanta zata kashe shi"

Washe gari bayan kammala zaman fada ta yanke hukunce hukunce ga duk wasu masu laifi haka shima ta yanka masa nasa hukuncin, sharar wata k'atuwar haraba da take a sashin bayi da tsakiyar rana idan ta bud'e tayi k'walll ba takalmi sannan baze tsaya ba har sai ya gama, kuma sai yayi har tsawon kwanaki goma"

Tin daga wannan ranar Maharani ta samu hanyar cin karen ta ba babbaka akan Aruuf,, wahala da bautuwa iri iri babu wadda bayayi mata, yawancin ayyukan wasu bayin musamman tsofaffi duk ta yaye musu ta mayar kansa, lokaci d'aya yayi bak'i kallo d'aya zakayi masa ka gane yana shan bak'ar wahala, tak'i bashi dama koda sau d'aya ya ida nufin sa na son temakon ta,
Tsananin tausayin da yake dashi yana kyautatawa talakawa da marasa k'arfi da gajiyayyu a cikin masarautar hakan yasa suke bala'in tausayin sa, gaba d'aya sai ya zamana duk shine kusan shugaban bayin kamar su bauta masa haka sukeji saboda nuna k'aunar su gare shi, yawanci suna kiran sa abun k'auna.

Yana kashingid'e kan lafkekiyar kujerar sa sai lumshe ido yake,, gefe kuwa Farhana ce zaune fuskar ta fayau da alamun farin ciki a tattare da ita.

Tana murmushi tace, "Ranka yadad'e hak'ar ka tana gab da cimma ruwa"

Cike da gadara da jin kai yace, "dama nasani ai nasan dole zanyi nasara, yak'in da aka fara shi tin bata da wayo ai dole ne a gama shi bata isa ta dakatar dashi ba"

Hadima Farhana tace, "wannan haka yake yalla'bai idan da ace banyi k'ok'arin jefa Aruuf cikin wannan halin ba nasan da yanzu komai ya warware mata,
Shiyasa nayi wannan k'ok'arin domin kuwa Aruuf mutum ne,
Kuma kowa cewa yake shine makamin ta,
Ina ta tunanin ko shine wanda take jiran zuwan sa sai yanzu na gane ba shine ba"

Yace, "gaskiya ina jin dad'in aiki dake Farhana kinsan abunda kikeyi, naji dad'in hakan"

Murmushi tayi ba tareda da tayi magana ba.

Yawan turo mata wasik'un da akeyi daga masarautu biyu yasa ta shiga tashin hankali, yanzu kwata kwata ba ta mutanen masarauta take ba, Aruuf d'in da tak'i shine me basu kulawar da ta dace, da lura da duk abunda sukeyi,
Hadima Farhana dama tini ta tsame hannun ta, yanzu duk nutsuwar ta tana ha Kumar duk abunda zatayi tasa shi farin ciki shine abunda take yi,
Ita kuwa burin ta kawai ta nema musu mafita tasan ta yadda zata shawo kan lamarin amma duk tunanin ta ta kasa gane ina ne bakin zaren,
Gashi komai k'ara ta'azzara yake sun jefa mata fitina.

Yana zaune suna tad'i tareda wani dattijo Udday ya k'araso wajen, zama yayi tareda gaida dattijon,
Ya amsa kafin ya tashi yabar wajen, cikin mamaki Udday ya kalli Aruuf yace, "wannan kuma waye?? Daga ina ka same shi? Ba kace baka da dangi ba??"

Aruuf yace, "haka ne Udday Abu na kawai shine dangi na, shi kuma wannan a cikin masarautar ku yake"

Girgiza kai Udday yayi yace, "a'a gaskiya wannan ba irin mutanen mu bane, ka lura sosai mana ba d'an masarautar nan bane sai dai idan an turo shi ne"

Cikin kad'uwa Aruuf yace, "an turo shi?? Kana nufin ya banbanta da mutanen ku??
Nifa a wannan masarautar nake ganin sa shine ma har muka zauna hira"

Cikin son kawar da zancen Udday yace, "to shikenan ina ganin kamar gane shi ne banyi ba,
Aruuf meyesa baza ka iya ganar da shugabar mu gaskiya ba?"

Yace, "akan me fa??"

Udday yace, "akan gaskiyar ka tana wahalar da kai kuma ni na sani tanada buk'atar temakon ka Ansaar kaji tausayin ta, rashin sani ne yasa take aikata abunda take aikatawa"

Jinjina kai yayi kafin yace, "to amma ita da bata son gani na? Kuma ku na kusa da ita kun kasa ganar da ita sai ni? "

Udday yace, "ai mu sai mu fad'a ta kasa ganewa kai kuma ta gane maka"

Girgiza kai yayi yace, "a'a tashi kaje kawai Udday dan Allah ka rabu dani"

Ya fad'a tareda had'e tafukan hannayen sa guri d'aya.

Jiki ba k'wari Udday ya tashi ya bashi guri.

Tsaki yayi zuciyar sa cike da takaici.

Da daddare yana cikin tafiya kamar yadda ya saba zagaye da shiga ko ina a cikin Masarautar a ko wane dare domin duba abunda yake faruwa, yau ma hakan ce ta faru.

Yana cikin tafiya yaji kukan yaro,
Da sauri ya fara dubawa domin gane inda yake,
Wata mata ya gani tana cin gudu wasu mutane su biyu suna binta hannun su rik'e da takobi sun shafe fuskar su da farar kala yadda baza'a iya gane su ba,
Tana ganin sa tayi sauri dawowa bayan sa tana kuka tace, "yaro na nice Hadima Urmi wannan yaron
End Ads