x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 8 - CORPER

  • 21001 words
  • 24000 words
  • Out of 46412 words

Category: Romance Story +18

Views 140

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
kowa,ta fita har bakin kofa nan ma shiru (kasancewa ranar kasuwa ce gari shiru kowa ya tafi cin kasuwa).
Dawo wa tayi cikin dakin cikin hausanta burkuttace wanda daga ji kasan kabila ce"ke Iya na(sunan da take kiran Fatima kenan),meke faruwa,yaushe kuka zo daga kebbin???"

"Na rantse da Allah kaka ko mutuwa zan yi ZAINAB da Kabir ba zasu sake zama gidan kowa ba,kafa na kafar su zuwa birnin Kebbi!"
Bana son shashanci,tambayar da nayi maki kenan?,ke faiza zo nan ki faɗa mun abinda ke faruwa nasan iya da zuciya ba zata kwantar da hankali tayi magana ba.

"Cikin kuka faiza ta warware ma kaka duk abinda suka gani da wanda zainab ta faɗa masu,dai dai lokacin na warware hijabi na da na rufe jikin Kabir dashi...

Sallati kaka ta saki tare da wasu maganganu da yare domin jikin Kabir ya tashi sosai ya shabe saboda ruwan sanyi dana wanke shi dashi ga hijab Dana kudundune jikin shi dashi na tsawon wani lokaci!
"Fuskar kaka dauke da hawaye take magana,yanzu ita rukayyah sakayya da zata mana kenan?,anji tausayin ta an bata amanar yara marayun Allah ta azabtar dasu,ga horon yunwa da daura talla!"
Shike nan Allah zai saka maku kuma tayi wa kanta,kaka ta figi Kabir a hanun na ko gale bata tsaya ɗauka ba.
"Nan ta bar mu da kukan zuci"
Kaka bata zame ko ina ba sai gwamawa gidan iyayen aunty rukayyah (Dama da mahaifinta da kaka uwa ɗaya uba ɗaya suke),koda ta isa suna zaune a harabar gidan su na shan iska gindin bishiyar mangoro ai kowa ta dangwara Kabir tayi a jikin uwar rukayyah tana huci,da harshen dakarci ta shiga surfo zagi da cin mutumci iri iri...
Sake baki suka yi suna sauraron ikon Allah domin har yanzu basu gane inda ta dosa ba sai da ɗan uwanta ya tsawata mata sanan ta natsu cikin ɓaci rai ta zayane masu komi tare da buhun Allah ya isa a kan rukkayah da addu'oin in shaa Allah ba zata taɓa ganin kwan ta a duniya ba har ta koma ga mahalicci ta!
Jikin su yayi sanyi sosai domin basu san rukkayah da wanan mugun hali ba,gaskiya ba don a baƙin da ba zai masu ƙarya suka ji ba da ba zasu taɓa yadda ba.
Duk da hakka maman rukkayah ta tashi da masifa ƙarya ake yiwa d'iya rta kuma addu'a kaka zai ƙare akan diyanta da jikokin ta!
Hayaniya ne ya kaure tsakanin kaka da mama nan take rayuka suka ɓaci da kyar baba ya tsawata masu kuma ya amshi kabir zai kai shi Hospital fafur kaka taki amincewa ta wuce dashi da kanta.
General hospital ta nufa dashi cikin hanzarin aka nufi emergency dashi saboda ya galabaita numfashi shi na sama yana ƙasa dole aka fara kona mai ƙarin ruwa kafin a fara treating wound nashi" allura kashe radadi aka fara yi sanan aka kwalde fatar jikin shi aka shafe ko ina da "DERMAZIL CREAM"Nan take ya samu bacci.
Lokacin kaka ta tuna bata zo da ko kuɗi ba dama babban likitan abokin ɗan ta ne shi yasa bai bata lokaci wurin ceto ran Kabir ba .
Bayan komi ya lafa ya kira ta office d'in shi yana kwantar mata da hankali kuma yana nuna mamakin shi a fili yadda haka ta faru kuma duk yaran da ke gidan a rasa wanda zai kawo yaro Hospital sai ita?
"Cikin faɗa ta kwashe komi ta ke faɗa mashi,ai kuwa ya kira number Usman (elder brother maman mu,Kuma ɗan kaka na uku),cikin harshen turanci ya sanar dashi komi tare da jadda da nashi yana don ganin shi yazo ya tafi da kaka gida kada ciwon ta ya tashi".

Lokacin da ya iso yaga halin da Kabir ke ciki kuka ne kawai ya rage bai yi ba saboda laifin sune suna ha rai da lafiya ɗan yar uwan su ya wulakanta!,tattara kaka yayi da kyar suka tafi gida saboda doctor ya basu assurance na nurses zasu kula da Kabir sosai.
Koda suka iso unguwar tun daga bayan hanya suka hango mutane cike da wuri ga motar yan sanda a gefe kowa na faɗin albarkacin bakin shi!,ashe bayan tafiyar su da yan sanda suka isa gidan aunty rukkayah ta Sanar dasu wai NI FATIMA na shigo har gidan ta na kona yaronta da niyar kisa,da Allah bai bani Sa'a ya mutu ba na rufe ta da duka...

Kuka ya kwace ma fatima,share hawaye farida tayi tana tapping bayan Fatima cikin tsigar rarashi"farida kamar Ni Fatima yar shekaru sha tara a lokacin take so yan sanda suka kama da laifin kisa???
Shine ta taso su gaba har gidan kaka a kama ni,ina ganin su na rufe kofa bugun duniya naki buɗe wa...,abunka da irin kofofin lokacin baya na ,zinc be baby wani karfe suka bale suna ja na ina turje wa,yan ƙanena suna rike dani suka kuka,ina kuka muka faɗa masu sharri aunty rukkayah ce wallahi ban san komi akan zargin da take mun ba hasali ma itace take neman salwantar da rayuwar yaran!!!
Ai kowa suka zuga su take tana faɗin basu san aikin su ba kamar ita matar babban mutum a garin zuru zata fadi ƙarya ko ta mun sharri kawai su tafi damu duka idan su faiza basu sake Ni ba...,ai kuwa nan aka fara kicaniyar kinkimar mu sai cizo da yakushi nake aika masu dashi nan take wani ɗan sanda mara imani ya buga mun kulki a kai jini ya fara fita jiri na dibana nan take na sulale na zube ƙasa.
Saboda tsabar rashin imani irin na aunty rukkayah Bata fasa basu order su kwashe mu ba a dai dai lokacin baba usman da kaka suka dawo mutanen angu wa suka fara tsegun ta masu...,a hanzarce ya shigo gidan tare da damkar wuyar aunty rukkayah bai tsaya wata wata ba yake janta tana turje wa har cikin motar yan sanda ya saka ta, already yan sandan sun biyo shi waje.
Identity card nashi ya fitar daga cikin mota "Air vice Marshal Usman zaki",suka gani a rubuce,ai kowa aka shiga sara masa domin sananne ne sosai a garin zuru da ke waye.
Lock her ,I will be there soon!
"Yes sir "
Jiniyar motar yan sanda ya karade wuri sai kallon ikon Allah yan anguwa keyi har aka bar wurin.
Cikin gida ya koma ya ɗauke Ni zuwa hospital saboda lokacin ban san inda nake bama har muka isa,nan aka yi dressing wound d'in nasha allurai nayi bacci.
Abun duniya duka ya ishi bana Usman saboda duk cikin family su mamana yafi kowa arziki da ɗauka ka sai dai kash bai dacen matar aure ba,shima kanshi bai jin daɗin ta bare wani nashi ya rabe su"uhmmmm",ranar ba kwanciyar hankali!
_aunty Sultan mace ce mai mugun rowa da gadara ko yaran ta biyu bata ki su kwana da yunwa ba idan har wani dan uwan shi yazo gidan ko masu aiki sun daura girki zata ce a sauke ranar babu mai cin komi har sai baƙin sun tafi.yanzu haka tana Lagos da yara shi ɗaya yake zuwa hutun shi_
Baba usman namiji ne wanda ya tsayu da ƙafafuwan shi,yana da son zumunci da yan uwan shi sai dai rashin mace ta gari,yanzu bashi da wani buri da ya wuce ya inganta rayuwar marayun nan amma ta yaya zai fara?
Kamar an tsigare shi ya nufi low-cost gidan Daddy,ai kuwa cikin Sa'a ya same shi...,mummy ke tambayar shi ko muna can gidan cuz tunda suka iso bata sake ganin mu ba.

"Suna wurin kaka",ya bata amsa kafin ya shiga palour wurin Daddy,bayan sun gama gaisuwan da jajanta ma juna bayan rabo ya fayyace mai duk abinda ya faru a yau ɗin!
Daddy ranshi ya matukar ɓaci da ya ji wai gidan rukkayah na ja faiza daga isowar mu har haka ta faru,dama shi a lokacin bai goyi bayan a ba rukkayah ɗiyan ɗan uwan shi rik'o ba babu yadda ya iya ne kawai.

Usman sannu da kokari domin kayi abinda ya kamata tunda ita rukkayah bata da hankali da tunani bata ɗauki zumunci a bakin komi ba ai zan sanar da mijinta komi nasan yau yana hanya daga Abuja zuwa weekend.

Uhmm Alhaji ba wanan bama, Ni gaskiya hankali bai kwanta da yaran nan su ci gaba da zama a state din nan baki ɗaya ba ma kayi hakuri zan tafi dasu Lagos zai fi kawai,idan yaso ita Fatima da faiza su ci gaba da zama wurin ka kada a lalata masu karatu.

Shike nan bazan ki ta taka ba kaima ubane a gare su kuma kana da cikakken iko akan su zan shigo anjima da mai daki na mu wuto dasu Fatima.
Sallama suka yi,daddy ya sanar da mummy abinda ya faru"kawai ta hau zarge zarge wai laifi nane uban wa yace in tafi gidan
Mutane daga zuwan mu?,ita bata ga laifin rukkayah ba kome ta faɗa a kai na nice naja.

zuwA dare abubuwa da dama sun faru farida;-mijin aunty rukkayah ya iso daga Abuja ya samu mummunar labari matar shi na tsare wurin jami'an tsaro,koda yaje an tafka muhawara sosai tsakanin shi da baba usman domin attafau ya nuna ba halin matar shi bane shi bai taɓa ganin tana maltreating nasu ba(saboda a gaban shi da mutane tana kul dasu sosai sai bayan idon mutane).

Baba usman kam ya kafe kai da fata ba za'a sake ta ba sai ta amshi laifin ta kuma an rubuta statement d'in gudun gaba koda a hanya ta gansu ko kallon banza ba zai hada ta dasu ba.
Ganin iya gaskiyar shi kenan ya sa tayi confensing crime nata,ai kuwa mijinta da iyayen ya sai Allah wadai suke da halin ta daga bisani aka bada ita suka nufi wurin kaka nan ta fashe da kuka tana neman gafara....

Lokacin kuwa daddy da mumy sun dauko Ni daga Hospital mun nufo gidan kaka,nan dai aka yafi juna amma fafur nace ban yafe mata ba duniya da lahira"duk da ina cikin maqiyan cin hali kai banda ya fashe an zagaye da bandage sai da mumy ta buge mun baki daya bayan hannu tana faɗa.

Wai don aunty rukkayah Bata da kunya alfarma take nema a bata zainab su koma gida!
Baba usman ya katse mata hanzari da cewa shi zai tafi dasu Lagos kowa ya huta.

"Kuka ta shiga yi tana magiya",Babu wanda yabi ta kanta haka mijinta ya ɗauke su suka nufi hospital duba kabir..

Nasiha mai ratsa zuciya kaka tayi magana sanan daddy ya kwashe mu da faiza muka wuce zainab na kukan rabuwa damu.

Tunda muka koma low-cost Daddy bai sake bari mun tafi gidan kowa ba,sai family house d'in su(baban mu), hospital sau biyu muka tafi duba kabir cikin ikon Allah ya samu sauki sosai ya murmure abun shi.


Cikin ikon Allah muka cinye hutun mu ana gobe zamu koma gidan kaka muka yini ta haɗa mana tsarabar ƙauye kala kala,lokacin take faɗa mana ta yanke shawarar baba usman zai tafi da ZAINAB Lagos a saka ta a makarantar kwana saboda matar shi bata da kirkiri,shi kuma Kabir zata kula dashi sosai.

Ban wani ji dadin haka da aka tsara ba cuz nasan halin aunty sultana Sarai tana iya hana baba usman saka zainab a boarding schl,tunda ko mu dai da daddy bai raga mu da komi ba muna cin kaniyar mu wurin mumy bare yar zainab.

Haka dai muka rabo cike da tsantsan kewar juna.

Uhmmmm,in takaice maki labari farida zainab ba karamar azaba tasha wurin aunty sultana ba tunda baba Usman ba mazauni bane yana kusan wattani uku zuwa shida baya Nigeria duba da yanayin aikin su,sauƙin zainab ɗaya aunty sultana Bata hana ta zuwA school da islamiyya cikin lokaci ba.

Hakuri dai kam zainab nada shi sosai domin ta fi mu hakuri nesa ba kusa ba,sai da muka haɗu karshen wata shekara lokacin na kamala secondary School abuna!

Lokacin da muka kebe zainab ta kwashe komi ta sanar damu,kuka sosai muka ci"nazari nayi naga dai a duniya duk inda zaka zauna idan ba gaban iyayen ka bane dole sai ka ga banbanci domin ba zaka taɓa samun 💯 kulawa irin wanda iyayen ka zasu baka ba,kuma ko ba komi gidan baba Usman yafi na aunty rukkayah tunda tana karatun ta babu rashin ci da muhallin kwarai sai rashin mutunci irin na aunty sultana.

Rarashin ta nayi cikin hikima na fahimtar da ita matakin Hakuri a zaman take wa na rayuwa wanda ya haɗa da:-
_Ydda da ƙaddara a duk yanayin da yazo maka,ka kasance mai hamdallah ga Allah ako wane yanayi ka samu kanka_

_Karantar mutanen da kake tare dasu ta hanyar sanin halayyar su,abinda suke so da wanda basa so wanan zai baka damar kyautata masu a saukake da taka tsantsan da duk wani abu da zai jawo matsala a zaman take War ku_

_Danne zuciya da tausasa kalamai yayin fushi zaka zauna da kowa lafiya_

_Dauke kai ga kyalekyalen duniya shi zai saka kowa ya amince maka kuma ya yarda da kai_

_A karshe riƙe Allah da neman zaɓin sa a duk abinda ya shige maka duhu ko ka saka a gaba_
"Idan muka riƙe wa yan nan matakan hakuri na zaman duniya tabbas nan gaba za muci riba yan ƙane na"

Lallai aunty ta yaya aka yi kika san wanan abubuawa?"cewar faiza".

Zama da mutane dabam dabam masu dabi'u dabam dabam da al'adu a makaranta shine ya karantar dani wanan babban darasi na rayuwa kuma zan so ku riƙe shi a duk inda kuke.

Zainab tace"in shaa Allah aunty farida ,WALLAHI bamu da kamar ki a duniya kin zame mana uwa da uba a lokacin da muke tsananin bukatar su.allah ya baki wanda zai riƙe ki da gaskiya auntyn mu.

Shiru Fatima tayi na ɗan lokaci tana nazarin wani abu...,daga bisani taci gaba.
Farida duk wani lalacewa,tambade wa,hargitsi,tabarbare War rayuwa ta ya samo a saline a lokacin Dana Kamala secondary School na KE zaune a gida bani wani aiki ko wurin zuwa sai gida.

Wata rana na tashi da matsananciyar ciwon mara da baya kamar ba zan rayu ba lokacin faiza na schol tana ss1,ai kuwa mummy ta kira daddy a waya a hanzarce ya dawo gida aka nufi federal medical center dani!

Kamar matatta aka nufi emergency dani,aka kira doctor on call SABIDA suka yajin aiki a lokacin sai da daddy ya saka baki sanan doctor ya amince zai zo kasancewar a staff Quarters yake zama cikin hospital d'in.

Yana zuwa yayi duk wani gwaje gwaje da scanning ya gano ina dauke functional ovarian cyst.

*BAYANIN SHI A GURGUJE*

_ovarian cyst:-wani kurji ne dake fitowa wa mace a saman inda maniyi ke bi ya shiga mahaifar mace(fallopian tube),haka zai ta girma yana kunsa ruwa Kamar maruru wanda idan ya dauki wani lokaci ruwan dake ciki zai koma jini daga nan ya koma yayi tauri lokacin ya kai(6cm-7cm) sai anyi wa mace surgery an cire shi idan ba haka yana haifar da matsaloli da dama ciki har da rashin zaman ciki a mahaifar mace,sanyin mara da mai tsanani wanda zai iya rikide wa zuwa cancer mahaifa(ovarian cancer)_

*ALAMOMIN SHI GA MATAN AURE DA YAN MATA*

_sun haɗa da:-kunburin mara(abdominal swelling)Wanda zaa yita tunanin cikin mace keda shi saboda girma da cikin zai ta yi_

_ciwon mara mai tsanani kafin ko lokacin al'ada(pelvic pain before or during menstrual cycle)_

_kumburin nono(breast tenderness)_

_jin zafi yayin saduwa(painful intercourse_


Bayan ya gaba binciken shi duka ina kwance a gado cikin dakin ya jona mun ƙarin ruwa har bacci ya tafi sani",gefe kuma daddy da mummy ne zaune suna kallon shi.
Rubuce rubuce ya gama sanan ya dago kai",sir kamar yadda sakamakon gwaji ya nuna tana dauke da functional ovarian cyst,Amma kada ku daga hankalin ku tunda functional ne bai wani Dade da fito mata ba in shaa Allah za muyi kokarin daura ta akan magunguna na kashe radadi da kuma kariya daga ci gaba da bunƙasa ciwon(antibiotics and analgesic)idan har ta tsare amfani dasu Ciwon zai shrinking da kan shi.

Shiru mummy tayi hankalin ta a tashe,daddy yayi magana"amma likita kana ganin ba zai ja mata wata matsala ba tunda budurwa ce bata taɓa aure ba fa,kuma menene musababbin wanna ciwo??"

Research ya nuna the cause is idiopathic (unknown),Amma wasu masana sun ƙara bunƙasa bincike akan harkar sun gano ba wani babban dalili ke kawo shi ba illah shekaru da kuma yawan sha'awa na mace(age and sexual urge),mace Mai yawan shekaru idan bata yi aure cikin lokacin da ya kamata ba da kuma yarinya mai karancin shekaru da yawan bukatar namiji.

Yanzu dai kada ku damu Alhaji naga ai bata wuce 19-20yrs ba za'a yi kokarin ganin an magance matsalar kafin ya wuce haka.

"Hannu ya mika mashi,mun gode sosai doctor nadeem Allah ya saka da alheri".

Murmushi yayi yana jin kunya yadda Alhaji ke masa godiya sosai akan aikin shi.

Na dauki lokaci a wurin kafin na farfaɗo garas dani da kafafuna muka tafi gida.

Tun daga wanan lokaci farida doctor nadeem ya zama kamar abokina kuma shine doctor na, cuz komi ya same Ni danganne da ciwon nan shi daddy ke kira a times har gida yana zuwa duba Ni.
Tun ina matuƙar jin kunyar shi har na saki jiki dashi ya bani number shi(dama daddy ya saya mun ƙaramar waya itel keypad )saboda idan wata matsala ta taso basa gida zan kira su,kuma dashi nake karance karancen littafan SOYAYYA"wata Maryam makwabciyar mu take tura mun".
Ai kuwa muka yi exchanging contact saboda idan wani abu ya shige mun duhu in Kira shi,but cikin ikon Allah ban taɓa kira na sake shi ba,ko wane lokaci number busy(the user is on another call),na danganta hakan da yanayin aikin shi domin likitan mata ne (gyniecology).

Duk da haka idan ya kamala yana kira na ina mai bayani n matsala ta.


Shakuwa Mai tsanani ya shiga tsakanin mu har ya kai idan an aike Ni kasuwa na kan biya hospital wurin shi mu gaisa haka.

_Doctor nadeema mutum ne mai yawan fara'a da son mutane,uwa uba kirki da tausayi_

Shine dalilin da yasa tamu tazo ɗaya,shakuwa ta makantar da idanu na har nake ganin doctor nadeem na matukar sona amma ya kasa sanar dani,idanu na suka rufe na afka kogin son doctor na har naji duk duniya babu wanda nake so da kauna kamar shi.


SANADIN FARUWAR CANZAWAR RAYUWATA:- Wata rana dana zaɓi na bayyana wa DOCTOR NADEEMA SIRRIN ZUCIYA TA!!!


[8/5, 6:48 AM] Hayat: *🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*CORPER*
_{Ɗan bautar mata}_
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

_~A Romantic Love Story~_

*BY*

End Ads