x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - CORPER

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 46412 words

Category: Romance Story +18

Views 145

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
Fulani kullum cikin yarantaka take kwana,ga kauyan ci shi yasa nake don kara aure_

"Uhmmmm!,Allah ya kyauta,amma ina ga ƙarin aure ba shi zai kawo masalaha a tsakanin ku ba idan har kuna zama lafiya tana yi maka biyayya gwara ka samu wace zata koya mata dukan abinda ake so cikin sauki sai ku zauna lafiya inaga zai fi,yanzu idan ka ƙara aure amarya ta hargitsa maka gida fa?".

Farida na yarda da tarbiyyar ki shi yasa nake son ki tare da burin ki zama uwar ya'ya na.

Nagode Alhaji ka bani lokaci kamar yadda na faɗa mu fahimci juna idan na tafi can garin mu wurin su mama za muyi tsayayya shawara da sauran yan uwana in sha Allah idan na dawo zan sanar da kai komi.

"Shike nan idan tafiya ta kusa ki sanar dashi ,ko tare zamu ne in gaishe da umman mu?

A'a kayi hakuri dasu yaya jamilu zamu.

Sallama suka yi tana nazarin maganganun shi.

Suna haɗuwa da Fatima a wurin aiki ta kwashi komi ta sanar da ita...
"Tsaki taja,ɗan iskan banza wallahi suna bani mamaki yadda suke blaming matan su na gida,yanzu haka matar shi babu irin kulawa da bata bashi amma yazo wurin ki yana yarfata domin ya kafa tashi gwamnatin",watan jin kunyar shi ta tsaya domin sai mun koya mashi hankali ta kwanta gidan sauki bana baban ihsan ya huta ke zaki yiwa kowa ragon layyah.

"Zaro idanu tayi!

Tabbas zaki yi da kudin Alhaji ina tabbatar maki idan muka fara tatsar shi wallahi shi da kanshi zai nemi hanyan guduwa...

Tafawa suka yi.


Ranar suna waya yaje sanar da ita wasu Kudi nashi da yake bin gwamnatin bashi akan kwangila da yayi na gina bohol da renovating wasu primary school sun fito kusan Naira miliyan ɗari kuma ya rasa abun yi da kuɗin.

Mamaki ya cika ta sosai watau Naira miliyan ɗari bashi da abun yi dasu ko?,tasan ta yadda zata bolo mashi Dama sallah ya rage saura sati biyu gashi da wuri suke tafiya zuwa wurin su umma SALLAH.

Kai tsaye tace daddy Dama kuwa ina cikin matsalar rashin kuɗi!

Rashin kuɗi ina da rai?,haba Farida ki faɗa ko nawa kike so zan baki su koda duka kuɗin nan kike da bukata wallahi sun zama naki,Ni fa akan don da nake maku zan iya komi ciki hadda rabuwa da kowa nawa....

Katse shi tayi"dubu ɗari biyar nake so kacal".

Kamar tana ganin shi ya zaro idanu dubu ɗari biyar?,me zaki yi dasu haka?

Wanan ba damuwar ka bace alhaji idan har zaka bani fine.

"Zufa har wanke mashi fuska tayi,ko duka kike so zan baki farry idan har zaki biya mun buƙata ta?

Wane irin buƙata alhaji?

Idan kin amince bayan kin kamala period mu kwana tare!

Wani dammmm gabanta ya bada!

Taso taki amincewa ta tuna da fatima,ai wanan ba matsala bace Alhaji ka bani zuwa weekend idan na Kamala period komi zai tafi yadda kake so







*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*CORPER*
_{Ɗan bautar mata}_
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

_~A Romantic Love Story~_

*BY*

*L££MA*

*DEDICATED TO MEELAT AND HUBBEEY*

*~Surayyahms DA meelat Musa Allah ya baki lafiya mai albarka,Allah Yasa kaffara ce amin~*

*All right reserved unauthorized copying, changing and translation of any part of this story in any form is prohibited.*


*🅿FOUR*

CI gaba tayi da trying number Fatima nertwork busy,haushi ya cika ta domin dai ta lura ba'a taba kiran Fatima a samu cikin lokaci kamar wata yar siyasa.

Dakin aunty salma ta shiga,tana ta faman gyara wodrob din ihsan...
"Sannu da aiki aunty?"

Yauwa ,ai na jiki shiru naso leko ki kuma nayi tunanin bacci kike yi.

Eh na ɗan kwanta ne,hannu ta saka suna shirya kayan suna taɓa yar hira.
"Kada in manta abban ihsan yace mu zamu fara tafiya zuru daga baya zai biyo mu saboda aiki ya masu yawa,din haka idan akwai wani shirye shirye da kike ki kamala da wuri."
Ba wani abu ai dama kayan da muka yi order daga Kaduna ne har yanzu ba'a Kamala ba,but nasan Koda muna can Fatima zata aiko mun dasu .

"Wai kuwa Fatima tana nan kuwa,kwana biyu bata shigo ba?"

Tana Nan aunty kin san zuwan nata na ganin dama ne shi yasa na ɗauke ƙafa daga zuwa gidan su kada aga kamar wani abun kake nema a wurin su ...
"Gaskiya ne hulɗa da yaran masu hali sai ana taka tsantsan"

Hira suka ci gaba da yi har suka kamala,Ni zan shiga wanka mijina ya kusa dawo wa.

"Masu miji manya,ai nice mijin aunty sai na fara gani kafin ya gani,suka tafa tare da sa dariya ta shige bathroom din dakin ta.

Ƙara gyara gadon tayi ta share mata dakin sanan ta nufi nata dakin, missed calls ta gani da dama ciki har da na fatima...

Number nata ta fara dialing....
"Ar fara ta affuwan."
Babu wani affuwan ke kenan kullum lokacin da mutum ke son magana dake ba'a samu ki...

Yi hakuri muna hanyar zuwa zuru ne dasu Daddy Wai mutane na yawan tambaya lafiya kwana biyu ba'a zo sani ba.....
Katse ta tayi"yanzu saboda banda muhimmanci a wurin ki shine za kiyi tafiya ban sani ba?

sorry tawan wallahi idan a son rai na ne a barni a gida in ci kare na babu babbaka amma ina nasan halin daddy!

Shike nan ya kuka isa?

Lafiya klau akwai labari kenan?

Sosai ma ke dai Alhaji shamsu ya bolo da sabon iskanci....
Sai ki bolo masa da sabon bura'uba!

Uhmm ke dai bari,ta kwashe komi ta sanar da ita.
"Sai yau na ƙara tabbatar da Farida baki da wayau,saboda da Allah cikin MILLION dari ki rasa nawa za kiyi requesting sai dubu ɗari biyar?"
Ina laifin MILLION biyu?
Keeee!,gidan uwar wa zan kai million biyu?

Gidan uwar ki,ga umma can zuru cikin tsohon gida,babu wadata masu,abinci ma sai ta jira yaya jamilu ya tura mata da kuɗi,ga hidimar karatun nafisa dake batun kamala secondary.
Sanin kanki ne yaya jamilu hidima ta masa yawa ya fara tara iyali da wanne zai ji?

Nanauyar ajiyar zuciya ta sauke,haka ne Fatima but dubu hamsin ma ya gagara Ni fitar wa kada a gane inaga MILLION biyu?
Baki da wayau wallahi,ai ba farat ɗaya za'a cire kuɗin ba,a hankali zaa hira amfani dasu,bare ke da kike mace ko yau Allah ya kawo maki miji aure za kiyi,uwar wa zai maku wasu hidimar tunda kina aiki ana expecting wasu abubuwan ke za kiyi.

Shike nan na fahimta,amma dai kinga ko dubu dari biyar din bashi da niyyar bayar wa cikin sauki....

Katse ta tayi,dole zai bada su babu boka ko mallami tsubbu,hikima da kissa ta ishe mu.
Yanzu text zan maki ko kina ITA saurara?

Faɗa mun kawai saboda kin san wani lokaci aunty na amfani da waya ta kada taga text ɗin.
"Nan take ta shiga zayyano mata zance tiryan tiryan har takai ayah."
Uhmmm Fatima baki ganin ana iya samun matsala?

Sai dai in ceke zaki bada matsala,but wanan abun is very easy.
Shike nan ki turo min audio d'in ta WhatsApp zan tura shi a wayar aunty Kawai zai fi.
"Good yanzu zan tura maki"
Ok Ina Kira ta katse wayar.

Zama tayi dabas tana tunani inda Fatima ta samo wannan irin hikima da salo na yaudarar samari.
Buɗe WhatsApp nata tayi chat nata shigowa har na Fatima ya shiru,ta buɗe ta saurara sosai tasha mamaki domin sak voice nata babu bambanci.
Repeatedly ta rinƙa saurara har ta gaji ta aje.
Wayar shi ta kira,ya katse ya kira ta.
"Tanko ya dade my sweetheart."
Tare da naka darling ya aikin?
Gashi muna fama yanzu haka ina ta wurin"ZINARI HOTEL"akwai wani plot da za'a sayar MILLION biyu da rabi shine zan saya in gina hostel saboda naga student na poly basu da isassun hostels....
Katse shi tayi domin bata son jin uwar surutun nan nashi doka idan ya fara babu comma ko fullstop.
Allah ya taimaka dama akan maganar mu ne tun safe period Dina bai dawo ba shine nayi wanka har nayi sallah,idan zai yiwu mu haɗu yau...

Cikin wata mahaukaciyar dariya yace"why not farry,wallahi kin gama mun komi a duniya tunda kika amince da buƙata ta komi zan iya maki a duniya".
Yanzu kinga 4:pm tayi idan mun yi sallah zan kama daki a Safar guest inn zuwa 8:00pm zan shigo na dauke ki.

Gaskiya Alhaji Safar yayi cikin gari da yawa ina laifin"MADONNA GUEST INN"wurin Badariya yafi rashin mutane,and zuwa 8pm zan zo har wurin in same ka,, saboda idan mutane suka ga ka ɗauke Ni mun fita za ayi ta surutun kasan mutane basu iya ganin abu.

Gaskiya ne,kin ga na rude ko?
Yadda kika ce haka za'a yi,idan na kama Dakin zan kira ki in faɗa maki room number.
Shike nan.
"Ok a wane account zan tura maki kuɗin?"
Xxxxxx0819 jaiz savings account number
Account name:FARIDA MAGAJI.
Good suka yi sallama.
Sallar la'asar ta gabatar ta jima sosai cikin sujjadar ƙarshe tana neman zaɓi Allah,daga karshe tayi azkar din ta data saba ta shafa addu'ointa.

Text ya shigo wayarta"500,000 HAS BEEN CREDITED INTO......
wani jin daɗi da saki a dakin sai da abban ihsan ya leko da aunty"LAFIYA dai ko?

Kunya ya kamata,lafiya lau yaya har ka dawo ya aiki?
Lafiya lau,ya naku?

Alhamdulillah,dariya aunty ta saka mata tare da jan hanun mijinta suka koma d'aki.
"Bayan sallah isha'i ta sheka wanka kamar gaske ta ɗauki kayan baccin ta kawai ta saka tare da daura zani sama tana yan shafe shafen ta,kiran shi ya shigo fafur taƙi daga wa sai daga baya."
Sorry Alhaji ina wurin wanka ne,ok dama rum No 2 na ɗauka idan kin iso kofar a buɗe take ki shigo kawai.
Ok dana gama shiri zan fito yanzu.

Tana gama shafe shafen ta ihsan ta shigo"aunty Farida mummy tace ki kunna mun kallo a wayar ki ko nata".

No,Ina amfani da wayar ne ,muje palour in kuna maki destiny junior ana Film mai daɗi.
"Da murtan ta suka nufi palour ta kunna sun ci Sa'a ana"SOFIA DA FIRST",sai da ta bari hankalin ihsan ya dauko tace Bara in shiga toilet Ina zuwa,ko amsawa bata yi saboda tsabar mayar da hankali akan tv.
Windows ta rufe da door sanan ta tura audio d'in a wayar aunty Salma data amso, ta gwada kunna wa ai kuwa sai ƙara sosai(irin katon keypad China phone d'in Nan ne mai mugun volume kamar mp)
"Yes ta furta a hankali"
Number Alhaji shamsu ta kira dama ta saita komi.
" Yana Daga wa ta danna audio din wanda ƙarar abun hawa zaka rinka ji kamar mutum na saman babur ko cikin adaidaita".
Handsfree ta saka nata wayar tare da manne shi da wayar aunty Salma"hello darling kana jina?
Eh ina ji amma ciki ciki har kin fito ne?
"Eh ina cikin adaidaita zuwa 2minute za mu isa wurin".
Allah kawo ku lafiya ina jira...
"Ji yayi kiiiiiiiiiiii kaaaaaaaaaa jagabbbbbb,sai Muryar ta tana faɗin innalillahi wa'inna ilaihi raji'un hasbunallahu wa'nimal wakil, wayyo Allah na shike nan na mutu(alamar da yaji yana nuna anyi wani gagarumin accident ne)".

Ta ƙara amfani da Muryar ta da audio ya kai ƙarshe tana faɗin wayyo Allah ƙafa na jini,kai na jini don Allah kada ku kira police gida ba'a san na fito har nan ba,karya nayi zan tafi bank kawai a barni in wuce na hakura!,kira ta katse wayar ta hanyar kashe ta gaba ɗaya...
" dama tana jiyo Muryar shi yana faɗin menene ke faruwa farry, accident kuka yi ko me ki sanar dani ta wurin ina, ka na ji ciwo sosai ne!"

Wata uwar shewa ta daka tana gode wa Allah plan din su yayi aiki successfully,kawia tayi deleting audio din a wayar aunty tare da bude door ta Koma palour wurin ihsan wace har tayi bacci, dauke ta tayi zuwa daki ta dawo palour tare da sauya channel ɗin zuwa"zeeworld",hankali kwance take kallon ta ,taso kwarai ta shafa wa Fatima labari amma bata don buɗe wayar a yau sai gobe da safe.

Ɓangaren Alhaji kuwa trying number Bata ya rinƙa yi switch off,hankali tashe ya baro GUEST INN din ya kama hanya amma babu yana dubawa ko Allah zai sa yaga ta wurin da suka yi accident d'in Amma shiru da yake dare ne,hankalin shi ya tashi matuƙa gashi yayi shaye shayen maganin ƙarin ƙarfi na maza wanda zai ɗauki lokaci bai yi ingali ba.
Cikin tashin hankali ya gaji da yawo ga marar shi ta kulle sai murdawa take,ga wayar farida bata shiga,yanke shawara yayi kawia ya nufi Kofar gidan su ko Allah zai sa ya dace idan ma Hospital aka tafi da ita dai dai sun dawo ya ganta,sai dai kash ya kai awa ɗaya zaune cikin mota ko gilmawar kare bai gani ba bare na mutum haka ya hakura ya koma ga uwar gidan shi wacce ya raina ya sauke sha'awar shi a kanta.

Washe garin ranar asabar suka tashi da sanitation a gidan,ko wane daki sai da suka canja mazaunin gado da mirror zuwa wodrob sanan aka canja curtains da bedsheets,palour ma aka juya furnitures d'in tare da goge komi sanan aunty Salma ta shiga kitchen, Farida Kuma ta kwashi kayan su na wanki ta zuba cikin midiun size washing machine nasu ta wanke tsaf ta shanya.
Bayan sun kamala zuwa 11:am dai dai ihsan ta dawo islamiyya suka shirya zasu yini gidan wata gwaggon su(ta wurin Uba),wani tunani ya fado mata ta shiga dakin aunty Salma ta ɗauko first aid kit nata cikin ikon Allah akwai plaster,bandage,,iodine,swab da gause.
*_Dama aunty Salma ta fara schol of nursing and midwifery har ta kai aji biyu ta samu matsala aka sallame ta,ta sake komawa bata dace ba kawai ta hakura tayi aure.shi yasa duk wasy minor treatment ta iya su_*
Sai data daidai ci aunty Salma na d'aki mijinta kawai ta diba iodine kaɗan cikin cotton ta dambara a goshin ta,ta azaba bandage sanan plaster,babban hijab ta saka da nikab kada aunty ta dago ta.
"Leka wa tayi ta masu sallama,aunty ta fara mata tsiya wai bata son su samu siriki shi yasa ta rufe fuska da nikab".
Dariya tayi suka fito tana riƙe da hanun ihsan ai kuwa ta hango motar anacin daga nesa da gidan su,ta ɗan fara ɗan geshi da kafarta har suka isa wurin motar duk da bai gane ta ba ta Daga nikab ɗin.

Cikin zafin nama ya buɗe motar ya fito fuskar shi dauke da tashin hankali ya fara magana"menene ya faru jiya farry?
Kayi hakuri kaga clinic zan koma wurin dressing wound d'in zan ari waya in kira ka saboda jiya an ɗauke waya ta a wurin da accident din ya faru.

Ki bari mu tafi tare mana...
A'a Alhaji kaga ba Ni kadai bace yanzu yaya zai fito tare da mu tafi,zan kira ka.

Shike nan ya ja motar shi.

Sai data tabbata ya bar layin nasu kawai ta samu adaidaita suka shiga sai alert estate din gwaggo JUMMAI.

A kofar gidan ta cire bandage ta yar saboda gudun surutun gwaggo suka shiga da sallama.

Lalle da mutanen GRA..
Cikin palour suka shiga sannu gwaggo ya gidan?
Matar da ba zata wuce shekaru arba'in ba ta amsa da lafiya lau ya kuke zkwana biyu ba'a ganin ki!

Uhmm aiki ya tasa mu gaba gwaggo,ina su Abdul?
Sun fita i think,yasu jamilu?
Lafiya lau suke gwaggo suna gaishe ku.
Wai ke kamar ba budurwa ba kullum ciki. Babban hijab yau kuma harda su nikab,a haka zaki samu mijin auren?
Kai gwaggo Ni korafi ne bana so.
Doke ni yar banza kawai wacce bata don gaskiya kin fi son zama karkashin matar ɗan uwan ki wacce ta mayar dake kamar jaka kina bauta mata.
Shiiiii,ta mata tana nuna ihsan!
Ina ruwa na ta kwasa ta faɗa mata mana duka na zata iya yi ko zagi na?
Yar banzar mace ta mallake mana ɗan Maraya kullum yana cikin hidimar ta dana yan uwan ta,ta hana shi kyautata wa kowa nashi!

Kai gwaggo jummai shi yasa da kwana biyu baki ganni ba saboda irin wanan kana nan maganganu,mata bata jiba bata gani ba a rinƙa ɗaukar alhakin ta.
Ba shakka hatta ke ta haɗa ta magance dole ba zaki taɓa ganin laifin ta ba.
Yanzu dai gwaggo mu bar maganar kawai yunwa nake ji...
Dama na sani ai ko girki bata yi ba bare ku samu na sakawa a bakin salati,ba ni ce da girki yau ba,amina CE kin santa da shiri rita yanzu tana iya kai har azuhur bata kamala ba,sai in Zaki dafa indomie.

Barshi kawai muna iya jira,bata in gaisa da ita (da yake kowa da part nashi amma gida ɗaya ne),da sallama ta isa part din aunty Amina suka gaisa cikin kulawa ta koma wurin gwaggo.

Wayarta dake cikin handbag ta ciro tare da kunna wa lokacin har 12:30pm tayi,ai kuwa yana kawo wa ta saka MTN line nata a Flight mood,Dama Bata bashi Airtel nata ba dashi ta kira shi...
"Yana Daga wa tace,Farida ce ka kira babu credit a wayar."
Tana katse wa kiran shi na biyo wa"da sallama ta amsa suka gaisa".
Farida don Allah ki yafe mun Ni na ja maki wanan accident d'in domin da ban fitar dake daga gida ba da hakan bata faru ba....
Katse shi tayi"no ai kowa ne ɗan Adam baya wuce ƙaddara shi,kawai dama Allah ya rubuta hakan sai ta faru kuma abun yazo da sauki domin ba wani rauni na ji ba ,shi mai adaidaita ne dai yadda karaya a ƙafa.
Ashhha wai a garin yaya hakan ta faru?

Wallahi kai dai bari,yana cikin tuki fa hankali kwance lokacin ina waya da kai sai wani ɗan achava ya gifta Mana Ashe da mota babban a bayan mu shike nan muka gangara rami!
Ikon Allah,lallai Allah ya tsagaita da ban san me zan ce da yayan ki ba.
Ahhhh kawai ba komi ai ƙaddara ce.
Zuwa anjima zan kawo maki sabon waya sai a yi welcome back na layin ki!
"Kai Alhaji hidimar tayi yawa da da ka barshi ma".
A'a bana son kina amfani da wayar mutane kada a raina ki.

Dariya ta saka tayi godiya.
Tana aje wa taga gwaggo jummai tsaye a kanta"ke da waye a wayar?
Uhmmm wani ne,an gama abincin ne?
Eh ki diba .
Bata damu da wani abinci ba ta kira zain ɗin Fatima ai kuwa karaf ta daga"ar fara ina kika shige ne,na shiga zullumi ko wani abun ne ya faru".
Ke dai mutumiyar harka ta yi kyau yanzu haka sabon waya zai saya mun!
Shewa ta saki lallai CORPER ya shiga hannu,ban labari!
Tiryan tiryan ta zayane mata zan ce har wayar da suka yi a yanzu.
Shege CORPER ya haɗu da gamon shi ai,yanzu idan ya kira layin anjima kada ki daga sai an ɗauki lokaci ko idan ya matsa ki canza murya ki nuna mai waya ta fita da abun ta!

Ai dasu ma ina tudun Wada wurin su umma.
Allah Sarki Fatima
End Ads