50k ba cikin kusan dubu ɗari biyar da yan kai saboda na sayar da zinari na,zobe ɗaya kawai ya rage a hannu na,bani da wata kadara data rage a bank ko gida sai motar nan gashi na kori duk wani CORPER da nake tare dashi ganin zan yi aure.
Tunani sosai na shiga yi yadda zan samo kuɗi na get together da zamu yi,ga sauran hidima sauki na ɗaya daga government house aka ɗauki nauyin walimar aure na.
Koda muka dawo gida mummy ta jani gefe,"ke lafiya number Dr Bata shiga kuma kin ce yau zasu kawo lefe shiru har yamma tayi,gashi an tara jama'a anyi girke girke?".
Shiru nayi tare da faɗa wa cikin tunani mai zurfi domin manyan mata masu fadi a ji a cikin garin mummy ta gayyato su zo tarbar lefe tunda tasan daga irin gidan da doctor ya fito.
Mummy Nima na Kira shi shiru ban samu ba,sai in zaa tada mutum ya tafi office d'in shi a duba ko gidan shi!
Uhmmm,Fatima zuciyata ta karaya da al'amarin Nadeem gaskiya,ace tunda aka fara hidimar nan bai leko ba,babu wani nashi daya zo ko ya kira waya gashi gobe daurin aure!,saboda Allah haka ake yi?
Sanyi sosai jikina yayi domin na fara dawo wa cikin hankali na, zuciya ta fara faɗa mun gaskiya(ba lallai bane kayi asiri ya kama mutum)!
Yanzu kije ki huta,zan kira daddyn ku a waya ko za'a samu mafita tun ba'a yi abun kunya ba.
Kuryar d'akin ta na shige tare da nade wa cikin bargo saboda wani irin zazzaɓi mai zafin gaske ya rufe ni,zuciyata ta fara raya mun doctor ya yaudare Ni ya fasa aure na,zuciyata ta fara raya mun aikin da akayi akan shi bai kama shi ba,asiri na zai tonu,doctor ba zai aure Ni ba!!!
Kuka na shiga rerawa tun inayi a hankali har na rinƙa buga kai na da gefen gado....,zainab ta shigo ta same Ni a haka itama ta faɗa kai na tare da fashe wa da kuka mai cin rai.
Aunty Fatima kiyi HAKURI haka Allah ya ƙaddara,dama can DOCTOR ba mijin ki bane,amma kanshi yayi wa bamu ba domin yaci baya ba gaba yaci ba, ya rasa wacce zai zaba ya bar ki sai Christian!, wacce bata sallah,bata san Allah ba!!!
Take kaina ya fara juyawa,wani irin jiri na diba na,"zainab ban gane inda maganar ki ta dosa ba???"
Allah sarki zainab a tunanin ta nasan abinda ke faru a cikin gida yanzu shi yasa nake kuka!
Aunty dama baki san abunda ya faru bane,kukan me kike yi??
Riƙe hanuwan zauna nayi,don Allah ZAINAB ki sanar dani abinda ke faruwa,Wallahi ban san komi ba amma zuciyata ta raya mun wani babban al'amari mara daɗi zai faru dani!!
Aunty kenan!,ai ya riga da ya faru banga amfanin boye maki gaskiya ba;doctor ya samu daddy a office yau tare da wata budurwa Lydia yana faɗa ma daddy Wai abaki hakuri da sauran yan uwa,saboda ya canza ra'ayi akan auren ki,ita budurwar nan da yazo da ita wai saboda shi ta musulunta tabar kowa nata saboda ya aure ta shine yayi jahadi tare da gwarin guiwar iyayen shi ya aure ta cikin ikon Allah ya samu karin girma zai bar garin Kebbi zai koma garin shi na haihuwa Jos da aiki!!!
Ban gama jin bayanin ZAINAB ba kawai na yanke jiki na fadi.....
Farida ban farfaɗo ba sai zuwa karfe 12:00am na dare a gadon Hospital Wanda hannu na ɗauke yake da ƙarin ruwa,mummy na gefe na da ZAINAB.
Ƙara runtse idanun na nayi hawaye na bin kumatu na masu matukar zafi,itama zainab kukan ta shiga taya ni tana rarashi na!
Mummy ta daka mata tsawata,"dallah can munafukar banza ai duk kece kika janyo wanan tashin hankali,sai da daddy yace kada a faɗa ma kowa wanan abun kunyar aci gaba da buki da safe kawai a ɗaura mata aure da abokin shi alhaji tanimu,amma da yake gulma na cin ki ban san yadda akayi kika ji wanan labari ba har kika faɗa mata.
Toni mummy ba gani nayi tana kuka a daki ba,shine kawai nayi tunani kora sani ne na faɗa mata,kuma ai koda daddy yake faɗa maki dasu kawo ina cikin dakin shi ya sani shirya drinks a babban freezer,"zainab tayi magana a shagwabe".
I said shut up nonsense!,bakin gadon ta dawo tare da ture ZAINAB gefe ta kawo hanu na ɗaya wanda babu ƙarin ruwa,cikin kwantar da murya ta fara;,,Fatima ke musulma ce ina so ki yadda da ƙaddara,dama can Allah ya rubuta DOCTOR nadeem ba mijin ki bane,saboda haka bamu ya wulakanta ba kanshi yayi wa kuma shi yaci baya,ya rasa wacce zai canza sai Christian wacce bata da tabbas!
Mun yanke shawara da daddyn ku akan za'a daura auren ki gobe da Alhaji tanimu wanda kin sanshi aminin sane kuma mutum ne mai tarin dukiya,gaskiya da amana.
Sai data karance Ni sosai sanan taci gaba;,matan shi baki da matsaya dasu,gidan su dabam naki dabam don haka ki kwantar da hankalin ki bana so ko kawayen ki su san halin da ake ciki sai bayan daurin aure yanzu haka check na million daya da rabi ya rubuta na kayan lefe da sadakin ki.
Tashi zaune nayi tare da kallon mummy Da kyau,,wallahi,tallahi ko sama da ƙasa zasu haɗe ba zan aure Daddy tanimu ba shike nan ke baki da wani buri a duniya sai kiyi kuɗi damu saboda bake kika haife mu ba,ai inda iyayen mu nada rai babu wanda zai mana haka,kuma ai kina da d'iya mace ki bashi bana!
Cike da mamaki na mummy ta sake baki domin bata yi zaton haka a gare Ni ba!
Watau Fatima Ni zaki cima fuska saboda inason rufa Mali asiri ko?....,kina dai son zamar dani jarin ki kamar yadda kika ma faiza ta koma abun tausayi a gidan miji!"shine amsar dana bata".
Musayar yawo muka shiga yi da mummy cikind daga murya har wata nurse ta SHIGO ta tsawata saboda muna damun sauran marasa lafiya kuma tace idan mummy ba zata iya jinya ba ta koma gida kada ta saka Ni a wani hali.
Daren ranar duka bamu runtsa ba,tun bayan sallar asuba mummy ta Kira driver a waya ya mayar da ita gida a cetar wa ta cire hannun ta a dukan abinda ya shafe Ni daga yau!
ZAINAB ce ta ci gaba da kwantar mun da hankali har doctor ya shigo ward round, faɗa sosai yayi saboda babu wani improvement ko break fast ban Yi ba Kuma magunguna da allurai yake so a mun na yau.
Babu mai waya a cikin mu,zainab na kokarin komawa gida tayi magana daddy,faiza,aunty Salma,inna rabi suka iso da breakfast,,Nan take aka zuba mun da kyar na iya shan team saboda zuciyata zugi take mun,bakina kamar madaci bana jin daɗin komi,bana son ganin kowa nafi kaunar mutuwa ta da wanan hali da nake ciki!
Sannu kowa ya shiga mun ana ƙara kwantar mun da hankali har na samu bacci.
Ashe mummy na komawa gida ta fashe da kuka a gaban kowa ta bada labarin fasa aure na da doctor yayi da kuma wai irin cin mutunci dana mata a Hospital daga taimako na da tayi niyyar yi,,daddy ya fito rai a ɓace ya wanka mata mari sabida ba haka suka yi da ita ba a jiya,itace ta bada shawara kada a faɗa ma kowa a nemi Alhaji tanimu tunda ya jima yana sona daddy bai bashi fuska ba,shine yanzu tazo tana tonon asiri a cikin mutane har kawaye na kowa yaji abinda ya faru,wasu na tausaya mun wasu kuma daɗi suka ji domin ganin yadda na samu ɗaukaka a dare ɗaya.
Abinda yasa daddy basu iso wurin aiki da wuri ba gidan Alhaji tanimu ya biya ya bashi check din shi kuma da ban hakuri ba za'a daura auren dashi ba saboda na nuna bana so,shi kuma ba zai tauye Ni ba,wayar shi yaba UNCLE Ansar a tura text ma duk contact na shi babu maganar daurin auren da za'a yi a gidan shi yau.
Yan buki duk sun watse sai yan uwa na jiki sosai suka rage,dama ita faiza tazo gaba ɗaya ne sai ta haihu already wayar haihuwar ta ya tsaya,haka nayita jinya mutane na tururuwa zuwa duba Ni,wasu gulma ke kawo su har nayi sati Daya cur.mumny bata sake leko Hospital ba Wai tana fushi!
ZAINAB ma an barta ta ƙara sati Daya a wuri na saboda hutu suke yi,cikin ikon Allah yan uwana biyu ke ɗebe mun kewa,amma fa idan na kebe nakan sha kuka mai isata,nayi nadama sosai mara amfani farida idan kika ganni nayi laushi sosai,daga ibada sai hira da yan uwana ko ina Bama zuwa har zainab ta koma Lagos.
Na cire duka layukan wayoyi na nayi flooshing nasu,yanzu bana d anumber ko wane CORPER ko kawa!
Haka mummy Bata shiga tsabgata kowa zaman kanshi yake,tayi harkar ta,nayi nawa idan kaga gidana da wani a gidan sai yaranta da faiza sister ta.
Wata rana Samuel yazo har gida ya aiko mai gadi a kira Ni kama a faɗa mun shine,hijab na saka na same shi a harabar gidan mu wanda rabo na ta fitowa wurin tun ranar da zainab zata koma muka rako ta wurin mota.
Bayan mun gaisa yake sanar dani wai yan fashi sun shiga gidan philo sun yashe komi yanzu haka tana Hospital sun sare ta a hannu da ƙafa data hana su key na mota na!
Tausayi ta bani sosai,nace idan ya tafi ya gaishe ta domin yanzu bana zuwa ko ina kuma na yanke alaƙa ta da kowa ce kawa musamman ita data kai ni ga halaka,kaya da aka ɗauke nawa da mota na yafe;kawai na shige gida abuna.
Sosai na tauye kaina,na koma tsohuwar karfi da yaji,bana kwalliya ko wani ado domin banga amfanin haka ba faiza ke tursasa Ni wani lokaci domin a cewar ta bata da wani buri daya wuce taga Allah ya kawo mun miji na gari nayi aure na bar gidan mummy!
Mijinta na kiran ta sosai suna waya kuma yan uwan shi na zuwa duba ta akai akai har nakuda ta taso mata muka nufi Hospital kwana ɗaya da yini ɗaya tayi tana abu daya kasancewar haihuwar farko ce,Allah ya taimaka ta haihu da dare aka samu Baby boy mai kyau dashi amma ɗan karami duk girman cikin ta!.
Awanni huɗu tayi a Federal medical center aka sallamo mu zuwa gida Wanda daddy ya saka an mata wani extra room and palour na. Zata zauna.
Ganin mummy na wani cika tana batse wa yasa ya kira kaka a waya a ɗauko ta itace zata kula da faiza tunda tana da saurin ƙarfin ta,kuma a ranar hajia Turai(mummyn Faisal) ta aiko da motan daukar kaya ɗaya da itace na wankan mai jego,gero buhu uku,shinkafa uku da saniya ɗaya na barka.
Mummy na ganin harkar arziki ta washe baki tare da sakin jiki ta shiga jama'a ana gudanar da komi da ita.
Kaka na isowa ta wanke yaro da uwar shi yasa aka ci gaba da kula dasu abubuwan arziki zai faruwa yake har uban yaro ya iso cike da zumudi.
Ana gobe suna aka kawo raguna manya biyu,set na kayan baby,faiza ma set aka mata na kayan fitar suna;mai girma minister ya Bata kyautar mota karamar mai kyau tukuici saboda Faisal ya mashi takara za'a rinƙa kiran yaron da Nawaz.
Sai da faiza ta nuna ɓaci ranta sanan naci kwalliya cikin kayan da daddyn yamun na fitar buki muka fito shar kamar yan biyu.
Anyi shagali sosai cikin kawaye na Habibah kawai tazo,itama ban gayace ta ba gulmar ta ya kawo ta domin tunda abun ya faru ta ɗauke ƙafa a gidan mu sai yau.
Ban wani nuna mata komi ba na saki jiki da ita akayi shagali kowa ya watse.
A kwana a tashi babu wuya wurin Ubangiji faiza tayi watanni biyu cur a gida wanda aka fara shirye shiryen komawar ta Abuja tare da mai rainon baby Nawaz,saboda Faisal na Tanzania.
Cikin yan rakiya har dani saboda ban taɓa zuwa ba.
Kwana biyu muka yi a Abuja gida kam barakallah komi yaji,shawarwari sosai na bata akan yadda zata kula da kanta da mijinta ba wai don ta haihu ta saki jiki dukan wani kulawa da tattalin ta ya koma kan baby kaɗai ba,yanzu ne zata ƙara tighting belt nata wurin ba Faisal kulawa na musamman fiye da lokacin farko saboda ɗan zuwa da yake yi gida lokcin data haihu na lura dashi mutum ne wayayya mai son a kula dashi,ita kuma faiza matsalar ta kunya da rashin mayar da hankali akan ABUBUWAN da yake so.
Koda muka dawo gida babu abinda ya canza a zamana da mummy kowa ta kanshi yake,na zauna nayi nazarin rayuwa sosai naga zaman haka ba zai fishe Ni ba,doctor ya manta da wata Fatima a rayuwar shi,nima ya kamata in manta da komi in fuskanci rayuwa domin akwai abubuwa da dama a gabada.
Kawai na yi ƙarfin hali na cire komi a zuciyata da taimakon Allah na canza layukan wayoyi na,bani da wani aiki daga ibada sai karance karancen littafai da neman ilimin zaman duniya a yanar gizo har result din mu ya fito wanda ban samu matsalar komi ba na amso statement of result na kawo ma daddy.
Farin ciki sosai yayi da sanya mun albarka lokcin ya fara fafutukar nema mun aiki ban sani ba,,cikin ikon Allah na samu aiki a birnin Kebbi local gv wanda tunda nayi reporting ban sake zuwa ba kuma babu wanda ya takura min sai na tafi.
Albashi na nafarko na raba ma yan uwa duka har na nesa na tura masu catin waya,mummy na saya mata wani dankareren lace Mai Kyau da tsada ai kuwa ta washe baki tana godiya.
Watanni uku da samun aiki ban taɓa zuwa ba lura da haka da head of department dina yayi yasa aka mun transfer zuwa wurin aikin ku farida,wanan shine takaitaccen tarihin rayuwata.
Hawaye Masu zafi Farida ta share,lallai fatima kin tafka babban kuskure a rayuwa,kuma Kinga jarabawar rayuwa sai fatan Allahu ya yafe maki Kuma ya tsare gaba.
Amma zan tambaye ki mana!
Murmushi Fatima tayi, faɗi duk abinda ke cikin zuciyar ki inada amsar tambayar ki aminiyata.
Gyara zama farida tayi;bayan duka abubuwan nan da suka faru samarin ki na baya sun dawo gare ki?,kin sake samun labarin doctor Nadeem?,ITA Kuma Philo ya ta kare da rayuwar ta?,sanan yaya akayi kika ci gaba da sauraren samari????
Dariya sosai Fatima tayi,dama nasan sai kin mun wanan tambaya;idan baki manta ba ai na faɗa maki cikin su babu wanda na taɓa bari yasan gidan da nake,illa appointment nake Basu muna haɗu wa wani joint ko restaurant haka and na cire duka layukan wayoyi na Kinga babu ta hanyar da zasu sake Ni!
Nadeem!,Nadeem!!, Nadeem!!!,,,Koda wasa ban sake samun labarin shi ba har yau saboda ban san kowa nashi ba,kuma ya koma Jos da aiki!
Philomina (NOKIA connecting people),poor her,yanke ƙafan ta ɗaya akayi wanda tasha jinya sosai har komi data tanada ya kare,samuel na ganin haka ya sanar da yan uwanta ya ƙara gaba domin duniya yanzu sai kana dashi za'a yi da kai,idan babu ka zama hoto!,yanzu haka wai yadda nau'i labari shagon SALOON wani tsohon saurayin ta ya buɗe mata a zuru amma ba maganar aure tunda ta gama lalata kanta a bariki irin su ba ko wane namiji ke iya auren ta ba.
Samari ko ince CORPER'S(yan bautar mata)kamar yadda nayi make yiwa mazan wanan zamani lakabi,bani ce na koma hulɗa dasu ba,farida sune suka kasa haɗe miyan su,suka kasa riƙe kwadayin su ko wane saurayi,yaro da tsoho a wanan zamani burin shi ya aikata zina da budurwa,bazawara har matan aure!
Wanan mummunar dabi'a ya zama ruwan dare,shine dalilin da yasa na ɗauki alwashin sai na zame masu karfen gada,zan koya masu hankali ta yadda basu tunani!,,farida na ɗauki alwashin kafin namiji na yaudare Ni,sai na yaudare shi,kafin namiji yaci amana ta sai naci amanar shi,kafin namiji Ya tona mun asiri sai na tona asirin shi a bainar duniya,kafin namiji ya ci mutunci na sai na cinye nashi mutuncin kaf Farida wanan dalili yasa na faɗa wanan rayuwa na amsar abun hanun namiji babu tausayi,ba gudu kuma ba jada baya har sai Allah ya kawo wanda zai soni da gaskiya kuma da niyyar aure na!
*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_
*All right reserved unauthorized copying, changing and translation of any part of this story in any form is prohibited.*
♥♥♫♪Happy Birthday to you ♪♫•*¨*•.¸¸♥¸¸.•*¨*•♫♪ Happy Birthday to you ♪♫•*¨*•.¸¸♥ ¸¸.•*¨*•♫♪ Happy Birthday !!!!! ♪♫•*¨*•.¸¸♥ ¸¸.•*¨*•♫♪ Happy Birthday to you! ♪♫•*¨*•.¸¸♥🎂🎂🎂🎉🎊🎄🎐🎁
*_HAPPY BIRTHDAY MUMMYN MUFEEDAH_*
*🅿 SIXTEEN*
Fatima na rasa wanan irin jaraba na mazan wanan zamani, musamman mazan aure burin su dai su aikata zinah,wani ma har mata uku zuwa huɗu ya aje a gida amma basu ishe shi ba,ko menene aibin matan su na gida?
Farida kenan,wani lokaci da laifin matan gida sai kiga mace bata san ta kula da hakkin aure ba,babu tsafta,iya kwalliya,hirar soyayya,girki,ladabi da biyayya!
Wani lokaci kuma babu abinda macen gida ke raga mijinta dashi amma idanun shi bai taɓa tsayawa wuri ɗaya,baya appreciating efforts na matan gida.
Uhmmmm,Allah yasa mufi karfin zukatan mu Amin!
Tadda sallar asuba yasa ko wacce ta mike suka shige toilet domin dauro alwala su gabatar da sallah,bayan sun idan ne suka samu bacci da basu yi ba a daren jiya.
Karfe goma na safe kiran mummy ya tashi Fatima daga dogon baccin da suke yi"hello mummy ya koka tashi?"
Ban sani ba Fatima,wai menene yasa bakya jin magana?,jiya baku leƙa wurin walima ba,yau gashi har an fara shirye shiryen daurin aure ba'a gan ku ba!
Mummy don Allah ki daina biye wa tsegumin mutane mana,daurin auren nan sai karfe biyu za'a yi ta daga nan a wuce wurin SWORD CROSSING CEREMONY....
Koma dai menene ya kamata Ku shiga cikin mutane ko wani aikin ne ku kama.
Shike nan mummy yanzu zamu fita,,,ok ki gaida mun da farida ta kashe.
Tsaki taja, Allah yasan bacci bai isheni ba,wallahi idan na isa sai na ci mutuncin ko wace munafukar mata dake kai gulmata wurin mummy,wanka ta faɗa.
Ta ɗauki lokaci mai tsayi kafun ta fito dai dai farida ta tashi,tana zaune gefen gado"er fara har kin tashi?"
Uhmmmm, Fatima ya gajiya?,,namu ne duka ki shirya yanzu muyi break fast sai mu isa gidan bukin mummy ta Kira ana jiran