x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 15 - CORPER

  • 42001 words
  • 45000 words
  • Out of 46412 words

Category: Romance Story +18

Views 135

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
mu.


Towel ta ɗaura ta faɗa toilet sharp Sharp tayi wanka ta fito suka shiga tsara kwalliya da kayan da suka sayo a kasuwa jiya,Fatima uwar iya make up ta kashe lokaci sosai ta watsa ma farida light make up,ITA ko ta shiga fuskar ta da heavy make up.

Text ya shigo wayar farida,kamar haka;-

_Barka da asuba gimbiya farry,ya ƙarfin jikin da fatan kin samu lafiya?,me kuke buƙata na break fast?_

Tsaki taja wanda ya dawo da hankalin Fatima wurin ta,lafiya dai?

Text ɗin ta nuna mata,murmushi ta saki tare da amsar wayar ta mashi reply.


Ba'a fi mintuna talatin ba kiran Alhaji CORPER ya shigo wayar farko da,,ta wani kashe murya cike da shagwaba"morning baby na,ok Ina zuwa".

Duguwar rigar material pitch wanda suka yi anko ta zura a gagauce,ta yafa ƙaramin Veil sky blue,Fatima dai na kallon ikon Allah.

Jamlock ta murɗa ya buɗe,ta wani toge jikin kofar tare da langwabe kai gefe ɗaya tana kashe mai idanu"ranka ya dade da girman kojerar ka".

Tare dake gimbiya,wanan irin kwalliya haka kamar mai zuwa gasar sarauniyar kyau?

Fari tayi da dara darar idanun ta,saboda kai akayi ko bai yi bane a canza wata?

Wane mutum,dole zan biya tukuici mai tsoka idan mun fita"yana magana yana wani shafa gefen fuskarta",kawar da zancen tayi...,har ka fita ne?

Ba dole ba gimbiya na bukatar abun kari dole a nemo ko a ina ne,ya miko manyan ledodi guda biyu.

Godiya muke ran goga na farida ya dade,,, ƙara washe shegen bakin nan yayi shi yasa nake mugun son ki saboda iya tsara kalamai masu ratsa zuciya,wallahi tallahi da ace dake na fara haɗuwa da bazai auri waccan guzumar bakauyar ta gida ba,wacce babu abinda ta iya sai ci daukar ciki da haihuwar yara mata duk shekara!!

Nan take gaban farida ya fadi,domin ta tsani namiji mai aibata matar shi ta gida"yanzu dai ka yi breakfast ko sai nazo nayi feeding naka,bayan an gama in wanke ka tas kamar sabon jariri"!

Wuhohoooo, daɗi kashe shi!
Kugunta ya rik'o da hanun shi na hagu yana kokarin haɗe jikin su wuri ɗaya wata dibara ta fado mata"na'am Fatima gani nan shigowa mana".

Saurin sakinta yayi,yanzu dai zan shirya naga har kun shirya karfe nawa zamu fita?

A shirye muke daka gama ka sanar damu kawai.


Juyawa yayi zai tafi nashi d'akin ya ɗan waigo suka haɗa ido,nan take ta kashe ido ɗaya tare da yin kiss ta hura mai ta shige d'aki...,mutuwar tsaye yayi a wurin kawai.



Tana shiga fatima ta fashe da wani irin dariyar mugunta.....,lallai farida ashe Juliet CE ke ban sani ba?,dole zan fara ɗaukar darasi wurin ki wannan irin kashe murya haka,ai sai Alhaji ya banka wa uwar gida saki goma bai san yayi ba!


Tafawa suka yi,bari kedai Fatima wallahi bana son mutumin nan, Allah ya sani wani irin haushi yake bani amma duk ya wani nace mun kamar tare aka haife mu,,wani tunani nayi kawai shi yasa na canja ra'ayi naga gwara na daina wulakanta shi tunda na lura wawa ne ko a cikin CORPER'S he's not qualify Amma ya naci sai yayi service!


Abinda nake ta so ki gane kenan farida,wallahi bakar magana,zagi ko cin mutunci ba zai taɓa sa namiji ya rabu da nacin sonki ba , musamman irin su wa yanda basu da wani buri da ya wuce su aikata zinah dake da kuma wanan bukata tasu ta biya wallahi zaki neme su ki rasa ne"gwara ki nuna mai kin fishi zama yar bariki kuma.kin fishi bukatar zinar a lokacin zai buɗe bakin aljihu shi da kyau yana maku barin nairaro kina adanawa har ranar da zaki zame shi daga jikin ki a hankali ba tare da wanan buƙata tashi ta biya ba.


Haka ne kam,suka janyo ledodi suka buɗe take away ne guda hudu,biyu na chips and a omlet,biyu na peppe soup din kaji ne,sai sandwich guda biyu da fresh milk gora biyu.

Ko wacce ta buɗe wanda zata iya ci suka fara karyawa a natse har suka kammala sanan suka haɗa sauran kayan su duka a bag ɗaya,sauran kayan ciye ciye kuma a babban leda ɗaya.


Fatima ta ƙara gyara masu make up d'in su sanan ta ɗaura ma farida dankali wanda ya zauna daram kamar an naɗa gwagwaro,itama ta ɗaura nata suka yafa mayafi a gefen kafada sai kamshi ke tashi.

Text ya masu yana cikin mota yana jiran su idan sun kammala....,suka fito cike da ƙasaita kamar wasu matan shugaban ƙasa!

A hanzarce ya fito ya buɗe booth ya saka kayan su tare da buɗe masu gidan baya suka kame ya ja motar sai da suka bar harabar hotel ɗin yayi karanci murya"gimbiya ina muka nufa?"

Sai da ta ɗan basar ta amsa a takaice,gidan buki!


Ko wace hankalin ta na kan waya suna chat har aka isa Quarters d'in dai dai kofar FLAT ɗin yayi parking a gurguje ya fito tare da buɗe masu mota,suka fito a yangance....,kayan za'a fito dasu ne?


Bar su kawai kuma kana iya zuwa ka dawo don ba yanzu zamu sake fita ba sai zuwa karfe biyu"ta faɗa cikin jan hankali.


Ko zamu koma can ne ki tayani bacci?,,,common kaga tun jiya baku sake leko wa ba dole zamu tsaya tare dasu har a daura aure.


Shike nan ki kula da kanki,nasan idan mun koma gida zamu deme ma juna kewa.


Sosai ma"ta bashi amsa",cikin mota ya koma yaja bayan sun ɗauki hand bag Kawai suka nufi steps na hawa flat d'in.


Babban palour gidan cike yake da yan uwa da abokan arziki sai ciye ciye da shaye shaye ake yi,,nan take Fatima ta shiga gaisawa da yan uwan su,tana gabatar da farida a matsayin aminiyar ta kuma tare suka zo.


Cikin sakin fuska aka gaisa daga nan suka shige Dakin yan mata wanda ko wace budurwa dake ji da kanta ta ɗauki wanka cikin shiga ta alfarma cikin ankon,kamshin su Fatima ya fara sanar da isowar su dakin sai kallo ya koma sama domin tun daga kan make up dake fuskar su,style na ankon su zuwa gwala-gwalai dake jikin su abun kallo ne,uwa uba wayoyin hanun su ga designer hand bag!


Kuskus ya fara tashi tsakanin yan mata ,ko wace ba tambayar yar uwar ta su wanene wa yan nan yan mata masu aji,daga ina suka fito?


Iklima cousin sister su Fatima ta fito kenan daga wanka tayi tsalle ta rungume Fatima"oyayo sister na sai yanzu wallahi nayi fushi ace tun jiya da kuka bar gidan nan ba'a sake ganin ku ba har wurin walima sai yan zu",,,sorry iklims kasuwa muka shiga basu samu fitowa da wuri vane.


Rik'o hanun farida Tayi,yi hakuri bakuwar mu ga wurin zama"ta kwashe tarkacen dake saman wani curshin ta zaunar da farida sama",bari na samu maku abun taɓa wa ko?


A'a mun gode sai da muka ya breakfast muka fito"cewar farida",,kai sister ko masa ai kwa ɗanɗana.


Wai dole ne tace bata ci kije ki shirya mana....,kefa teema matsalar ki kenan zafin rai!


Yan matan dakin dai ko wace idanu ta zuba masu sai santin haɗu War su take suna ji ina ma sune da wanan baiwar, wasu kuma hasada ke cin su saboda idan suka jera da wa yan nan yan mata dole tauraruwar su ta dakushe,, musamman ma Farida wace tafi Fatima kyau da tsari(ita Allah ya haɗa mata komi "kyaun fuska,surar jiki da dari duk da baka ce),Fatima kuma fara ce sosai,akwai boobs amma babu kyaun fuska.



Tunda suka gama hayaniya da iklima basu sake magana cikin dakin ba duka hankalin su na kan wayoyin su har aka fara kiraye kirayen sallah,palour Fatima ta janyo Farida suka aje hand bag din su inda gwaggo Hadiza ke zaune saboda tsaro,nan ta nuna ma Farida wurin da zata dauro alwala...,bayan ta gama itama ta dauro suka gabatar da sallah tare da kyara kwalliya fuskar su.


Suna cikin haka angwaye suka fara shigowa gida ya kaure da guda ana Masha Allah an ɗaura yau officer an zama babban mutum.


Tare yake da sujoji birjik cikin kaki suna Bara masa baya har cikin palour,yana sanya da babban riga na shadda wagambari ruwan ƙasa sai shek'i yake,ga sauran abokan shi sun rufa masa baya cikin farar shadda da bakar hula sai kamshi ke tashi!


Aje kayan kwalliya Fatima tayi tare da rungume dan uwan ta"congratulations my dear brother,may ALMIGHTY Allah bless your union"aka amsa da amin!


Tattara kayan Farida tayi ta kayar cikin jakar su aka shiga daukar hotuna awayoyi da camera Wanda kusan ko wane suna ciki hakan ya ƙara hasala yan matan dake wurin.



A gagauce aka kamala ɗaukar hotuna ango yace don Allah mummy ki shirya da wuri suna can suna jiran mu za'a fara ne,an tura motaci gidan amarya za'a wuce da ita can Barack ɗin,nima yanzu can zamu wuce mu shirya ,plz kuyi sauri saboda da zarar 2:30pm tayi za'a rufe gate sai na barrack din Wanda bai samu shigowa ba shike nan.


Gwaggo Hadiza ta rike baki TAUUUU!,ai dole mu hanzarta gamu nan tafi sai ku bar motocin da zasu tafi damu a fara kwashe wa yan nan yan matan kafin mu gama Kimtsa gidan.


Iklima ta kwala wa sauran yan matan kira"ku fito a fara kwasar mu motoci na waje",ruuuuuuu suka fito kamar ɗiyan awakai!


Ta kalli inda muke zaune,ko ba zaku bane?,,Fatima ta yatsina fuska,muna da driver yanzu zai iso ya tafi damu.


Ok zamu kira shi saboda bai san wuri ba kada a hana ku shiga.


Ran sauran yan matan ya matukar ɓaci da jin wai za'a bata masu lokaci saboda jiran mu har wata mai kaurin wuya a cikin su ta fara yada habaici!!


Ganin bamu tanka ba yasa suka fara fito zuwa cikin katuwar luxurious bus na barrack inda yan mata,yara da tsofaffi suka cika damm mu ake jira a wuce.


Text Farida ta tura wa CORPER Alhaji shamsu suna jiran shi....,ya mata reply ai tunda ya dawo Masallaci yake waje yana jira!


A yangance suke sauko wa daga steps din benen gidan har suka iso wurin motar ya fito da sauri ya buɗe masu gidan baya"ai kowa yan mata suka ƙara rude wa da irin matsayin mu!


Horn yayi wa soja dake jan Bus din,alamar yayi gaba...ya tadda motar muka bisu a baya har Barrack d'in.


Wurin kam ya kayatu sosai da sosai inda aka yi rumfar hudu(ɗaya yan uwan ango, ɗaya na amarya,ɗaya abokan ango da amarya, ɗaya kuma duk wani mai uniform Nan zai zauna),anyi indicating komi gwanin sha'awa,gefe ɗaya kuma abinci da abun sha ne kala kala saman dogon table!


Ba'a fi mintuna goma da shigowar mu ba aka fara gabatar da bukin inda ango da amarya suka shigo yana sanye da uniform nashi na air Force,amarya cikin white gown,sauran abokan aikin shi na take masu baya ana busa har wurin zaman su.


Bayan sun zauna aka gabatar da addu'a sai tarihin ango da amarya daga bakin manyan abokan su.



Paret aka gabatar kala kala daga bisani aka shirya gabatar da SWARD CROSSING Inda aka umurci kawayen amarya da abokan ango su fito a jeru a bayan su,masu uniform suka jera layi biyu ko wanne riƙe da takobi suka daga sama tare da harde su wuri ɗaya,ta ciki amarya da ango da sauran mabiya bayan su ke shiga suna tafiya har suka kai ƙarshe sanan suka sauke hannu aka tafa,daga nan aka yi jawabi dai tare da ba ango wanan takobi suka yanka cake dashi aka fara refreshments tare da ɗaukar hotona lokacin anyi sallah La'asar.


Tashi msuka yi ko wacce tayi sarving kanta idanu na kansu ko wanne namiji hankalin shi ya dauko har suka koma mazaunin su!

Bayan ciye ciye da shaye shaye aka buɗe fili duk mai bukatar taka rawa ya fito,,nan wuce ya kaure masu rawa nayi,masu zuba kuɗi nayi.

Sai a wurin Fatima taga daddyn su da sauran uncle's nasu,,a natse suka fito fili sai barin naira Yan ɗari biyu,biyu sababbi da CORPER ya basu ko wace bounch na dubu goma suka ta zuba kuɗin babu ji babu gani.....

Nan M.C ya shiga watsa kirari,yana koda Kyan su da haɗuwar su,burin ko wane namiji a wurin ya su damar Zamfara dasu ko number wYa ya amsa amma babu fuska.

Amarya dama mutuniyar Fatima ce ai kowa ta rik'o hanun ta dana angon ta suka shiga chashewa"Fatima gwanar rawa,an su abinda ake so",Farida kuɗi ta ci gaba da zuba masu fili ya watse aka barsu da amarya da ango sai barin kuɗi!

Shi kanshi CORPER Alhaji shamsu abun ya kayatar dashi sai imagining ranar auren shi da Farida yake domin yasan idan Allah ya mallaka nashi ita ya ga dace wa a duniya(wawa kawai).



5:00pm ango ya ɗauki amaryar shi suka bar wurin domin zai mayar da ita gida ayi shirin ɗaukar amarya zuwa kebbi,lokcin su Fatima ma suka amshi kayan rabo wurin aunty kubra suka ba CORPER ,ya amsa yana godiya suka dawo gida domin shirin komawa Kebbi.


6:20pm bayan kowa yayi Sallah,masu wanka da canja kaya sun yi akan ɗauki hanyar zuwa Kebbi da amarya!!!!



Karfe 9:00pm muka isa birnin Kebbi wanda muka aje Fatima a gida ban tsaya shiga ba saboda matar CORPER ta dame shi da kira wai taji shiru har yanzu bai iso bane,,yace ai tare muke sai ya sauke Ni a gida!

Da mamaki na kalle shi,kenan matar shi tasan da labari na!!!

_HALIMATU SADIYA MUHAMMAD_

*L££MA*📖🖊️



.



_HALIMATU SADIYA MUHAMMAD_

*L££MA*📖🖊️





*KUYI HAKURO DA WANAN DON ALLAH*



_HALIMATU SADIYA MUHAMMAD_

*L££MA*📖🖊️


~

_HALIMATUS SADIYA Muhammad_

~_l££MA~_


*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*CORPER*
_{Ɗan bautar mata}_
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

_~A Romantic Love Story~_

*BY*

*L££MA*

*DEDICATED TO MEELAT AND HUBBEEY*


*All right reserved unauthorized copying, changing and translation of any part of this story in any form is prohibited.*


*🅿 EIGHTEEN*




Sun ɗauki tsawon lokaci suna kallon kallon, Hafsah matar CORPER ta Fara ɗauke idon ta daga bisa ta furta"ina wuni can ƙasar leben ta".

Lafiya lau na amsa,ya gida ya yara?

Lafiya lau suke,,amma fa ban gane ku ba"na tambaya domin jita bakin ta".

Hafsah wacce ta zo cike da masifa da burin wulakanta Farida sai tayi sanyi domin ruwa ba sa'ar kwando bashi,kuma ko ido bai ci ba yasan kima!

Suna na Hafsah,nice matar Alhaji shamsu.

Allah Sarki ashe aunty CE da kanta ta kawo mun ziyara,sannu da zuwa barin kawo maki ruwa ko?,na mike ba tare da tsayawa jin ta bakin ta ba.

Maltina na gwangwani guda ɗaya,swam watar da Bobo na saka saman try da cup na nufo palour,sai kalle kalle take yi har na shigo bata sani ba!

Gaban ta na janyo ƙaramin table na ɗaura sama, Bismillah.

Mun gode ta furta tare da daura tagumi,,,,hannu na mika na ɗauki yar babyn da niyar mata wasa.

Yan mata yaya sunan ki?,sunan ta balkisu"mamar ta bada amsa".

Bobo na dauko na buɗe mata tare da saka tsinken a ciki,ai kuwa nan da nan ta zukee!


Karantar fuskar Hafsah nayi tsaf,a hasashe na bakin ta ɗauke yake da maganganu masu dama!

Shirun na katse domin Allah yasan fita nake son Yi,gashi ta jibge sai warin tsabi yarinya na karnin nono,ita bata fadi abunda ya kawo ta ba kuma bata wuce ba!


Aunty na baki sha ruwan ba,ko in zuba maki ne?

Nagode Farida,matsewa tare da cije wa tayi ta tattaro dukan jarumtar ta domin dai na mata kwarjini da yawa saboda koshi mijin nata idan ya furta wata kalma a gabana dana daga ido na kalle shi sai yasha jinin jikin shi.


Magana nazo muyi akan baban su,don Allah inaso ki fahimce ni.

Ina sauraren ki!


Akwai wata rana daya dawo gida cike da farin ciki wanda na dade ban ganshi cikin irinta ba,nake tambayar shi dalili?,budan bakin shi ke da wuya a gaban yara yace"Hafsah yau Allah ya cika mun buri na,na samu mace irin wacce nake burin aure a rayuwata,irin son da nake mata ban taɓa yiwa wata mace irin shi a duniya ba!

Duk da rai na ya matuƙar bace,cikin zolaya nace"har maman Baby",(matar shi da suka rabo).

Yace har ke Hafsah bana son ki kamar yadda nake son ta Kuma Nan bada jimawa ba auren ta zan yi!

Allah bada Sa'a kawai na furta,amma idan raina yayi dubu ya ɓaci!

Baby (babbar diyar shi mai shekaru sha shida),ta matso kusa dani"yanzu aunty kina ji kina gani baba na ci maki fuska har da wani addu'a kike bin shi dashi?".


Danne damuwa ta nayi,me kike so nayi baby?

Lallai gaishe ki aunty kina da zuciya mai kyau.


Farida tun daga ranar nan ban ƙara gane kan mijina ba,kullum tun da safe zai fice daga gida sai goma na dare ko sha ɗaya dai dai yara sun yi bacci,idan nayi magana yace yana wurin amaryar shi ne,sosai nake jin ciwon abun tun ina jiran dawowarsa har na bari kawai mu kwanta da yara.

Wata rana na kira shi ganin har sha ɗaya da rabi bai dawo ba,na tambaya lafiya kuwa?,,amsar da ya bani yafi surta mun kalmar yana son ki ciwo a rayuwa ta"ina wurin Farida amaryata,ki rufe gidan kawai wurinta zan kwana"!!!

Ranar nayi kuka har garin Allah ya waye,Farida babu irin tunanin da bai zo zuciyata ba har na yanke shawarar kila sihiri kika mashi ba'a banza zai rikice a kanki ba.

Tun daga ranar zaman lafiya ya kaurace a gida na,duk wata kulawa da nake ba mijina na aje sai cin mutunci.

_kalubale gare ku matan aure,wanan babban kuskure da yawan cin mata ke aikata shi ke tunzura mazajen su wurin aikata abinda basu ma yi niyya ba, musamman idan kin haɗu da miji mai barkwanci da yawan was"shi dai Alhaji shamsu wasa yake wa matar shi saboda koda ta kira shi a waya yana kofar gida,suna gama waya ya shigo ya rufe gidan bai bita kanta ba saboda yasan ranta a ɓace yake_


_A lokacin da mijin ki ya iya budar baki ya faɗa maki Yana son wata mace har fiye da yadda yake son ki ya kamata kiyi hakuri ki danne zuciyar ki(nasan ba ko wace mace zata iya ba),ki saki ranki cikin hikima da dubara har ya sanar dake dalilin da yasa yake sonta,irin kyautatawar da take mashi daga nan sai ki ɗauri damarar kyautata masa fiye da yadda ya faɗa tana masa wallahi duk son da yake mata dole ya rage,kema ya girmama ki fiye da misali,ya baki darajar ki na uwar gida koda amarya ta shigo dole ta
End Ads