Ba zan boye miki ba mijina babu irin kulawa da baya bamu ta fanin,abinci,sutura,kula da bukatu na dana yara!
Amma tunda na fara karta mashi rashin mutunci ya zabe hanun shi a kai na har yaran muka rasa gane kanshi har yanzu da nake baki labari,tsakani da Allah mijina adalin namiji ne a zaman mu bai taɓa tauye Ni ba,haka bamu taɓa samun matsala ba sai shigar ki rayuwar shi saboda haka nazo neman alfarma don girman Allah ki fita daga rayuwar mijina ko zai dawo dai dai mu samu kulawa kamar yadda muka sama.
Tunda ta fara bani wanan labari nake kallon ta cike da nazarin maganganun ta domin in gane gaskiyar abunda ya faru ta faɗa mun kota shirya ne.
Sai na gano wani abu, Hafsah gaskiya ta faɗa domin ɗan zaman da muka yi da Alhaji shamsu na san wasu daga cikin halayyar shi,gaskiya ta faɗa mutum ne mai kulawa kuma yana son a kula dashi wanda Hafsah ta gaza.
Na lura Hafsah yarinya ce karama ,bata da isasshen wayau da wayewar kai(saboda na girme ta).
kyakkyawar bafulatana amma rashin gyara da rashin kwanciyar hankali ya sa duk ta yamutse ta kudee kamar wacce tayi haihuwa shida!
Ba zan wani bata assurance zata samu yadda take so ta wuri na ba domin duk abinda mijinta ke mata laifin ta ne,kuma ba zan iya sakin jiki da amince mata a karo na farko da haɗuwar mu ba saboda ɗan adam bashi da tabbas.
Allah kaɗai yasan irin faɗi tashin da tayi a kai na bata samu Sa'a ba,shine ta ɓullo ta nan"ko waya nuna mata gidan mu ma oho".
Nannauyar ajiyar zuciya na sauke,aunty na kada ki damu in shaa Allah komi zai dai dai ta ki bani ɗan lokaci kin ji?.
Nagode amma don Allah kada ki faɗa mashi nazo wurin ki har mun yi magana,"a tsorace ta faɗa".
Indai nice baki da matsala.
Nagode Nagode Allah ya ƙara rufa asiri,Amin na amsa.
D'aki na koma na dauko sabulai guda shida(premier cool),na zuba a leda da Naira dubu ɗaya na mika mata"gashi ayiwa balkisu wanka dashi".
Sai data tsarko tare da kallon kanta da diyar ta sama da ƙasa sai lokacin ta tuna ko wanka basu yi ba bare wanki,"an gode"!
Hare bakin gate na raka su ina ɗauke da balkisu sanan na mika mata yarinyar,zan bar ku a nan Nagode a gaida gida(bana son fita kada tayi zargin ina son sanan hanyar da zata bi).
Waya ta ciro cikin ƙaramar purse ta miko mun,samun number ki!
Amsa nayi tare da kare ba wayar da ita kanta kallo,tecno L9+ CE ban kawo komi a raina ba kawai na rubuta mata number tayi dialing nasan ta tabbatar idan nawa na bataa....,tana jin ya shiga ta kalle Ni(alamar ina wayar).
Wayata na d'aki idan na shiga zan yi saving.
Koda na koma ciki abban ihsan na palour aunty na haɗa mai break fast,Ashe ya tashi ganin bakuwa a palour yasa bai fito ba.
Gaisawa muka yi na wuce d'aki,domin shi irin mutanen nan ne da babu ruwan su da abinda bi shafe su ba sai ka saka su cikin tsabgar ka suke shiga.
Gyara kwaliya ta nayi ina sauri in wuce aunty ta shigo da alama gulma ke cinta,"kee menene ƙaramar matar nan ta zo yi a gidan nan?".
Bata wani bata lokaci ba ta ba aunty salma labarin abinda ya kawo Hafsah gidan!
Uhmmmmm!,amma wanan anyie sakarar mace,kina matar aure ki kwaso jiki bada sanin mijin ki ba zuwa gidan budurwar da yake nema domin zubar ma kai da mutumci.
Katse ta tayi,koma menene Ita dai ta sani domin ko mijinta bai isheni kallo ba bare ita!
Ni na wuce gidan su Fatima rana nayi.
Aunty Salma Bata so haka ba domin taso jin ra'ayin Farida akan maganganu Hafsah matar CORPE,adawo lafiya.
Mintuna biyar suka kai Farida gidan su Fatima wanda yake cike da mutane yan ganin amarya kafin a kaita gidan mijinta da dare.
Gaisawa suka rinƙa yi da mutane har ta isa Dakin Fatima inda akayi wa amarya da yan rakiyar ta masauki!
Fatima zaune rashe rashe saman bed sai zuba surutu take akan dinner da aka gabatar jiya da dare wanda daga amarya da mutanen ta sai ango da abokan shi.
Salamar Farida ya katse ta aka shiga gagaisawa kafin ta gabatar mata da abun motsa baki.
Sai da suka kebe take ba Fatima labarin bakuwar ta"HAFSAH MATAR CORPER".
Dariya sosai Fatima ta kwasa har da kwantawa a ƙasa tana hawaye,daga bisani ta tsagaita"amma wanan anyi jahilar mace",a hakan take nema a bar mata miji?
Wai idan aka bar mata shi ina zata kai shi ita ɗaya?
Fatima idan kika tambaye ni,wa zan tambaya?
Naji daɗi yadda kika mata farida kuma koda wasa kada ki bata dama ta sake zuwa inda kike koda kina nan kawai a ce da ita bakya gidan,domin kasan akwai abinda zai biyo baya ko ba dade koba jima.
Allah kyauta,suka ci gaba da wani tattaunawar har zuwa wani lokaci Farida tayi sallama dasu,nan mummy ta cika ta da Abun buki ta kai wa su aunty.
Driver ya dawo da ita gida saboda Fatima hidima tayi masu yawa bata da damar fita rakiya.
Hafsah kar CORPER har ta isa gida tufka da warwara take domin bata ga ta zama ba mudin taci gaba da zuba ma mijin ta idanu wallahi wankin hula zai kai ta dare.
Don tsabar cin mutunci ya rasa wacce zai nema aure sai cikakkiyar yar Boko irin Farida!
Ya zama dole ta nema wa kanta mafita!!!
~BAZAN SAMI DAMAR TYPING GOBE BA~
_HALIMATU SADIYA MUHAMMAD_
*L££MA*📖🖊
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels Group
Hausa novels and fashion Group
Cool novel, makeup and kitchen1 Group
And
WOMEN24 TV Group
WHATSAPP NO:+2349030159301
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng