x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 7 - CORPER

  • 18001 words
  • 21000 words
  • Out of 46412 words

Category: Romance Story +18

Views 134

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
*L££MA*

*DEDICATED TO MEELAT AND HUBBEEY*

*_A MADA DIN BRILLIANT WRITER'S ASSOCIATION MUNA GAYATAR YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI ZUWA BUKIN AURE NA ƊAYA DAGA CIKIN MEMEBER NAMU"SADIYA MUHAMMAD BEJI"(AUTA BEJI MARUBUCI YAR"KAR KA MANTA DANI"),WANDA ZAA YI GOBE A NIGER STATE,MINNA OPPOSITE CHALLENGE INTERNATIONAL SCHOOL.ALLAH YA BADA IKON HALARTA AMIN_*


~MAMAN MU,MARYAM MUHAMMAD HASSAN, SURRAYAHMS,MEELAT MUSA,SIS OGANNIYA DA SAURAN YAN UWA MUSULMAI DAKE KWANCE GIDA DA ASIBITI BABU LAFIYA,ALLAH KA BASU LAFIYA YASA KAFFARA CE AMIN~

*All right reserved unauthorized copying, changing and translation of any part of this story in any form is prohibited.*


*🅿EIGHT*

A hasale ta shiga bugun kofar dakin Fatima kamar zata balle shi tana faɗin"bana son irin haka Fatima me yasa zaki mun haka,saboda na biyo ki shine zaki haɗa kai dashi ku wulakanta Ni Ko??".

"Yadda take magana cikin magiya Muryar nata cike da rauni yasa Alhaji shamsu jin matukar tausayin ta",kwantar da hankalin ki farida wasa Fatima ke yi wallahi ba zan taɓa aikata abinda baki so ba har sai zuciyar ki ta aminta dani,Ni masoyin ki ne na gaskiya bana burin cutar da rayuwar ki.

Yi tayi hankalin ta ya kwanta dai dai lokacin Fatima ta bude kofar tana kasar dariya hada riƙe ciki"ashe dama haka kike da tsoro farida?"

Ban sani ba,ta bata amsa tana kokarin shiga d'aki...

Fatima ta mayar da kofar ta rufe kafin ta isa wurin farida har ta faɗa toilet,ai kuwa ta ci gaba da dariya...,ai da kin fito mallama kin cire kayan ki Daura towel na rufe kofa ba biyo ki zai yi ba!

Banza tayi mata sai jin alamar saukar ruwa tayi,kenan har farida ta sakar wa kanta shower.

Bata wani ɗauki lokaci mai tsayi ba ta fito daure daure da veil nata fuskar nan murtuke!

"Gaba tawan ai kin san ba zan taɓa yin abinda zai cutar dake ba,wallahi tallafi bada wata manufa na aikata hakan ba,kawai don in nuna mashi kina son shi ne cuz na fuskanci mutumin yana son ki da gaskiya ba zai cutar dake ba kin ji besty na."
Tsaki taja tana dube dube inda zata ga bag d'in kayan su ta shirya zuwa walima.
Rik'o hanuwan ta tayi, believe me farida wallahi bana da niyar cutar dake,ina son ki har ga Allah ki yarda da dani zan maki bayanin komi kin ji?

Cikin sanyin murya ta amsa"shike nan Fatima wallahi ke ɗin ce yau duk kin caza mun ƙwaƙwalwa na rasa gane inda kuma dosa.

Wait lemme fresh up,zamu tattauna akan duk wani abu dana aikata yau,idan zaki amince ba lallai sai mun tafi walimar ba kawai dama nayi alkawarin baki tarihin rayuwata in shaa Allah zan yi anfani da wanan dama domin sanar dake koni wacece.

"Kina ganin rashin zuwar mu wurin walima ba zai zama matsala ba?"
Ko ɗaya zan yiwa mummy bayani.

Shike nan Bara na dan shirya kafin ki fito ..
Fatima na shiga toilet ITA kuma ta feshe jikinta da turaruka ta saka wata yar armless free gown ta faɗa saman bed d'in.
zuwA wani lokaci Fatima ta fito daure da towel tayi shafe shafen ta data saba ta saka ƙaramar riga itama sanan ta janyo sayayyar da suka yi duka a kasuwa ta hauro saman bed din.

Farida ki buɗe kunnuwan ki da kyau ki sauraren Ni kuma ki natsu ki fahimci dalili na nayin haka;set na gold dana saya da wasu zobe guda biyu wanda suka kama dubu ɗari huɗu da ashiri duka naki ne ..
Zaro idanu farida tayi!

Kada kiyi magana nasan zaki tambayi dalilin sayan su,kuma kina jin tsoro a gani a gidan ku,zan so ki aje tsoro" at your age yanzu kin isa ki ɗauki dawainiyar kan ki da iyayen ki saboda kuna aikin gwamnati,kin isa yi yiwa kanki abinda kike so koda ya kai na million ne babu wanda zai tuhume ki saboda ansan kina da hanyar samun kuɗi kuma kina iya juya su yadda kike so saboda haka maganar tsoro ko gudun surutan mutane ki aje shi gefe.

Ta Daga set na zinarin,ban sayi wanan saboda ki saka shi yanzu ba ko ki aje a gida ba,bank ɗin da kike operating zamu kai su ajiya koda zai kai shekaru ashirin ne babu abinda zai sake su har sai lokacin da kika buƙata,su wanan zobe guda biyu zaki saka su a hanun ki (70k kenan).duk wanda ya tambaye ki adashi kika kwasa kin rasa abun saya kika sayi zinari dasu zuwa gaba idan lalurar kuɗi ya taso maki ki sayar"dubi yatsuna",ta daga mata,ina fatan tunda muka haɗu kina lura dasu?,duka uku zinari ne da muka tafi Saudiya da daddy na sayar da guda biyu nawa kana na,na canza manya biyu na(40k each) da karami ɗaya na(30k) ,sanan ina da set biyu a bank manya wanda babu wanda ya saya mun a cikin ahli na duka kuɗin samari"CORPER'S"wanda basu bauta wa matan su na Sunnah sai matan waje.

Farida bana so ki sanar da kowa kina da jiyar zinari A bank,wallahi nasan nan gaba zai maki amfani matuƙa saboda halin rayuwa,baki da uba,umma bata da ƙarfi,yaya jamilu rufin asirin Allah ne kawai;misali auren ki ya tashi kina bukatar kayan more rayuwa a gyara maki gida dashi wanda baku da wanan ƙarfi lokacin duk wani tanadi naki zai yi amfani.
"Farida dai na riƙe da zobuna na zinari tana juya maganar Fatima a zuciyarta domin duk abinda ta faɗa gaskiya ne,itama tana sha'awar yadda taga Fatima na ado da kwaliya cia komi nata mai tsada ne,a nata wautar Fatima tayi mata zarra ƙarfin su ba ɗaya ba,bai kamata ta haɗa kanta da diyar commissioner ba!
"Hajiya ta bani hannu kin ji bana son dogon tunani idan kuma basu yi bane sai a mayar kawai a baki kudin ki".
Miƙa ganinta tayi,Fatima na isa ince basu yi ba wanan hidima da kike yi dani ai ko ciki ɗaya muka fito sai haka.Allah ya zaba mana mazaje na gari wanda zasu riƙe mu akan gaskiya da amana Amin.

Ɗas suka zauna a zara zarar yatsun ta suna shek'i,dama akwai azurfa da Fatima ta saya mata a Saudiya sai suka ƙara haska yatsun ta"murmushi mai kayatar wa ta saki"
Kin ga yadda kika haɗu kuwa Hajiya ta?,zinari a baki,zinari a hannu!

Suka saka dariya suna tafawa.

Sauran kayan data saya a "KWALLIYA COSMETICS"ta fitar duka,farida ba zancen cin fuska ba gaskiya kina bukatar kyara na Musamman dubi skin nayi don Allah kamar ba budurwa ba, especially yr face dark spot sun bata maki,kullum fuska fayau babu make up, suman kanki gashi da yawa amma babu gyara yadda ya kamata and lastly wodrob naki ma dole zamu canja nan gaba.
Fair and white gold nasan zai amshi jikin ki yana da kyau sosai nayi amfani dasu duka zan nuna maki yadda zaki yi amfani dasu,hand and feet lotion nasan kin san amfanin su,ga set na ANACONDAR HAIR KIT akwai relaxer, shampoo ,conditioner and hair cream.idan mun koma zamu tafi SALOON d'in da nake zuwa a maki gyaran kai na musamman,ga takalma nan dasu za muyi amfani.

Hawayen farin ciki ne ya wanke fuskan farida tana istigfari cikin zuciyarta domin zargin da tayi wa Fatima ba gaskiya bane,ashe saboda ita tayi wanan hidima baiwar Allah ciki Dubu ɗari da aka basu takalmin 7k kawai ta saya wa kanta.

Share mata hawaye ta shiga yi,common stop it,bana son ganin hawayen ki komi na maki nayi ne saboda Allah saboda soyayyar dake a tsakanin mu"plz no more tears".
Nodding tayi "ki yafe mun Fatima wallahi na zarge ki akan cin amanata...

Shiiiii!,ya isa haka nan komi ya wuce yanzu dai kiyi magana da shi mun gaji ba zamu fita ba sai Allah ya kai mu gobe,abinci ko nan ciki za muyi order.

Waya ta daga ta kira shi,ashe ma har ya fita abun shi.
Har kun shirya ne in dawo?
"A'a ba zamu fita ba a gajiye muke,take Your time".
Akwai wani abu da kuke buƙata ne?
Sai dai zuwa anjima yanzu a koshe muke.

Kallo Fatima take Binta dashi ganin yadda take yatsina fuska da take waya"oh farida idan baki son mutum ya shiga uku a duniya wanan yatsina haka?"
Uhmmm bari ke dai Fatima Allah ko Muryar bawan Allah nan bana son ji!

Yanzu dai barin kira mummy kafun wanan munafukan FAMILY namu su kira ta.

Number tayi dialing Yana ta ringing bata ɗaya ba,ta kira na anisa (younger sister ta)har ya kusa katsewa ta daga"hello aunty teemo ya skt?
LAFIYA,ina mummy?

Tana d'akin Daddy.
Ok idan ta fito kice ta kira ni cuz muna kasuwa da farida ba zan samu zuwa wurin walimar ba naga har lokaci yayi kuma bamu kamala abinda muke yi ba....

Gata nan ma ta fito"mummy ga aunty teemo a ways",hello Fatima bana son rainin wayau fa ina kuma shige auntie's naku sai kira suke tunda kika shiga gidan kuja fita ba'a sake ganin ku ba har sun wuce wurin walima!

Calm down mummy,Dama nasan sai anyi munafurci na,kawai gidan friend din farida muka tafi daga nan muka shiga kasuwa,kuma Ni bayan koma gidan nan ba ko wurin bacci babu mutane sun yi yawa zamu kwana wurin friend din farida...

Ya maku kyau dama duk abinda zaki ja mun zagi da cin mutumci a wurin dangin baban mu shi kike da burin yi Allah baki Sa'a.kut ta kashe wayar.

Tsaki taja,sai me a mutu har liman.
Keeee Fatima bana son Rashin kunya kawai ki tashi mu tafi wurin walima daga nan mu koma gidan...

Wallahi babu inda zamu domin babu wacce nake tsoro ko shakka a cikin su har mummyn.

Farida riƙe da baki tana mamakin tsaurin ido da rashin tsoro irin na Fatima.

Farida ki sauraren Ni da kyau zan baki labarin rayuwa ta domin ya zama darasi da iznah a gare ki,kuma nasan idan kika saurarar zaki gane manufata na yin duk wani abu da nake yi a yanzu.

*WACECE FATIMA?*
_ALHAJI MAHMUD SHARIF DA HAJIYA MARYAM MAHMUD SHARIF (DADDY DA MUMMY)BA SUNE IYAYEN FATIMA BA_
Cikin kaɗuwa da tashin hankali farida ta kalle ta!
Yes
Fatima A Ladan haifafiyar garin ZURU ce ƙaramar hukumar jahar kebbi,mahaifina teacher ne a (government day secondary School zuru),mahaifiyata asalin yar fakai,mahuta ce bata yi karatun boko ba.
Mu hudu iyayena suka haifa; Ni Fatima nice babba,faiza,zainab sai Kabir).mun taso cikin rufin asiri da kulawa inda nayi karatu na primary a cikin zuru daga nan na tafi government girls comprehensive secondary School aleru Ina jss 2 Allah ya yiwa mahaifiyar mu rasuwa wurin haihuwar kabir wanda ba ƙaramin tashin hankali muka shiga musamman ni da nake da wayau kuma nice babba saboda faiza da zainab primary schl suke a lokacin"mun ci kuka sosai daga baya na bar wa Allah komi aka tarkata Ni na koma makaranta,lokacin aka damk'a Kabir a hannun kanuwar maman mu ta shayar da shi.
A kwana a tashi har mama ta shekara da rasuwa baban mu bashi da niyyar ƙara aure kawai aka sa nashi idanu,duk wani kulawa da uwa zata ba yaranta yana ba su faiza har girki yake masu.
Cikin ikon Allah nonon gwaggo Asiya ya amshi kabir yayi kiba abun shi lokacin ya shekara da watani bakwai ta yaye shi,duk weekend sai baban mu ya kai su faiza family house d'in su mama su yi kwana biyu a dawo dasu har aka shekara biyu lokacin ina ss1 su faiza sun shiga secondary ciwon ajali ya taso wa baban mu,sosai yayi jinya har rai yayi halin sa.

Tun daga lokacin muka shiga maraici na gaskiya saboda kowa yasan ba wani abu baban mu ya mutu ya bari ba sai gidan da muke ciki wanda na gwamnati ne nan aka tara mu tsakanin dangin uwa dana uba za'a raba domin a tallafi rayuwar mu;Ni da faiza aka damk'a rik'on mu hanun Alhaji Mahmud wanda shine elder brother na baban mu,lokacin yana aiki da"ministry for agriculture and rural development birnin kebbi",zainab da Kabir aka bar su nan zuru wurin aunty rukkayah(wacce ta shekara goma da aure amma Allah bai bata haihuwa ba kuma mijinta hamshaqin attajiri ne a cikin zuru),sai dai kash bata da hali,muguwa ce ta buga wa a jarida.

Haka taro ya watse muka rabu muna kuka aka wuto damu kebbi lokacin daddy yaran shi biyu(Abdul Rahman da Anisa) a lokacin yana zama a legislative Quarters ne,da yake mun saba da matar shi bamu wani sha wahalar zama da ita ba hutu na ya ƙare na koma schol,faiza kuma aka nema mata transfer taci gaba da zuwa"government day secondary School gesse,jss2".
Zaman mu a birnin Kebbi sai godiyar ALLAH domin babu daɗi babu kuma wahala,saboda gaskiya muna ci muna koshi,ana mana sutura na sawa cuz Daddy baya bambanta mu da yaran shi duk wani abu da zai saya masu na more rayuwa yana mana,babban matsalar mu mummy Maryam domin mace ce mai son kanta da yaran ta,tana son hutu da murki shi yasa duk wani aikin wahala na gidan Ni da faiza ke yi tun daga wanke wanke,shara da gyaran gida,girki,wankin kayan ta dana yaran ta har guga.
Tun bamu iyaka komi ba muna kwaba wa tana zagin mu da duka haruka zage damtse,idan nazo hutu nice ke duk wani aikin gidan saboda bazan juri ganin faiza na wahala ba,idan na koma schl wahalar ya dawo kanta shi dai daddy ba Mai yawan hayaniya bane,baya hana ta duk abinda take so har aka samu hutun karshen shekara muka tafi zuru cike da zumu ɗin zamu ga yan kan nen mu"ai kuwa ana isowa bamu ko shiga gida ba sai GRA gidan aunty rukkayah...

Farida har in koma ga mahalicci na ba zan manta da abinda na gani a gidan aunty rukkayah ba"wani irin kuka mai rikitarwa ta saki"
Rungume ta tayi tana rarashinta...

Farida tunda muka buɗe gate d'in gidan nan nake jiyo kukan kabir yaro ɗan shekara hudu! , Koda muka shiga ciki ya jawo tukunyar miya dake saman electric cooker duk ta bare Mai a jiki saboda azaba sai tsala kuka yake yana birgima!!
Babu shiri na rarume shi nayi wurin pampo dashi tare da sakar mai ruwan sanyi"ban sani ba ashe ƙara mai azaba nake yi" ,sai kuma muke nisa faiza ina faɗin ina ZAINAB ɗin???
Na nufi dakin aunty rukayyah ko ina rufe sai sanyin AC je tashi tana sharar baccin ta son ranta.
Ban san lokacin dana jefa wa faiza Kabir ta riƙe ba na shiga dukan aunty rukayyah ta ko ina ba ina faɗin"muguwa azalluma tashi yau Allah Ya tona asirin ki kuma yaga mugun nufin ki shi yasa bai baki haihuwa ba!!!

Da mamaki ta tashi tana kallo na irin har kin yi kwarin wuyar da zaki shigo har d'aki na ki mun rashin mutunci!

Wayarta ta daga ta kira wasu mutane cikin harshen turanci da alama jami'in tsaro ne.
Ina a tsaye kikam ko gezau sai zaginta nake yi ina wurgi da kayan Dakin ta..,kuka da Kabir ya sake kwalawa ya fargar dani na sungume shi nayi hanyar waje nan kuma ci karo da ZAINAB ta shigo gidan kamata almajira da yagagun kaya duk tayi baƙi kanta ɗauke da babban kula Yellow da dukan alamu daga wurin talla take.
Duka kuka muke faiza ta yi wurgi da kulan dake saman kan ZAINAB nan gorunan zobo suka zubo ƙasa muka nufi gate Amma fafur Mai gadi ya hana mu fita wai umurnin hajia ne.

Muna tsaye tsamo tsamo muna kallon ikon Allah ZAINAB ta shiga jan majina"shike nan aunty faiza yau kin ja mun wahala a duniya na rantse yau nasan a store zan kwana cikin azaba ga zobo basu ƙare ba yanzu kin zubar mata dashi"!

Cikin tsawa nace da ZAINAB wai zobon wacece?

Na mumy rukayyah ne kullum Ni zan haɗa kuma in tafi talla ko schl bana samun zuwa Allah,tun 4:30am take tashi na daga bacci in gyara gidan nan kaf in wanki da wanke wanke sanan in haɗa zobo ko break fast d'in ta Bata bamu,Kabir yayi ta kuka saboda yunwa sai an gama ci za muci,haka zan bar shi yana kuka in tafi talla sai yamma zan dawo yadda na bashi babu wanka babu wanki haka zan dawo in same shi cikin fitsari da kashi wani lokaci ta koro shi bakin gate yayi kuka ya gaji har yayi bacci babu mai tausayin mu!

Zuciya ta kai mun ko ina"don uban ki shine kima zauna baki faɗa ma kowa ba ko ki dauke shi ku gudu???
Aunty Fatima wallahi har wuka ta samun a wuya wai idan na faɗa ma kowa sai ta kashe mu ko ta kashe Kabir wai tace nice na kashe shi,kuma a gaban mutane tana kula damu sosai saboda ko mijinta bai san abinda take yi ba tunda yanzu a Abuja yake aiki sai weekend take zuwa.

Saba Kabir nayi a bayana,na riƙe hanun faiza da kyau ta hanun dama na,gefen hagu na riƙe ZAINAB da kyau muka riga a guje tare da hankale mai gadi muka samu nasarar barin gidan ai kuwa muna shiga kwana sai jiniyar motar yan sanda muka ji ta nufa to gidan!





*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊

_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_


🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*CORPER*
_{Ɗan bautar mata}_
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸

_~A Romantic Love Story~_

*BY*

*L££MA*

*DEDICATED TO MEELAT AND HUBBEEY*


*All right reserved unauthorized copying, changing and translation of any part of this story in any form is prohibited.*

*SURRAYAHMS INA TAYA KI MURNA KAMALLA LITTAFIN KI"AJALIN SO"ALLAH YA BADA CIKAKKIYAR LADAN FADAKARWA.MUNA JIRAN SABO...*

*JAMILA MUSA"MEELAT" INA TAYA KI MURNA FARA SABON LITTAFIN DA DUMBIN MASOYA SUKA DADE SUNA JIRA MAI TAKEN"KWARATA"*

*MARYAM MUHAMMAD HASSAN"MEEMA"ƊAUKE DA HAƊAƊEN LABARI MAI TAKEN"MAI JIDDA"MASOYA MASU SHA'AWAR NISHA ƊAN TUWA DA KAYATATTUN LITTAFAN MU SAI KU GARZAYA SHAFUKAN MU NA SADA ZUMUN TA DOMIN SAMUN WA YAN NAN SABBIN LITTAFAI{KWARATA &MAI JIDDA}*

~_Masoyya littafai na a duk inda kuke ina mika sakon gaisuwa da fatan alheri musamman a gare ku:-_~
~*Naja'atu kazaure*~
~*Ummu adnan*~
~*Mummyn ummah*~
~*Ummu Sultan*~
~*Queen Esher*~
~*Khadija nijar*~
~*Maryam zuru*~
~Da sauran wa yanda ban ambaci suna yen su ba Ina godiya mara adadi~

*🅿NINE*

*CI GABAN LABARIN FATIMA*
Muna fitowa daga gidan muka yi saɓa Ni da motar yan sanda kasan cewa gidan ta a bayan police station na GRA yake,gudu muke kwasa wa riƙe da hanun juna kamar wan yanda aka koro kowa ya haɗu damu sai kauce mana yake yi har muka isa tsohuwar tasha inda gidan iyayen maman mu yake.

A gigice kuma a galabaice muka faɗa dakin kaka achimie (uwar maman mu),sai haki muke duk mun fita hayacin mu...
Tashi tayi a firgice ta leka tsakar gidan wayam babu
End Ads