Nagode da kulawa Allah ya bar zumunci.
Amin farida sai na jiki anjima.
Yini suka yi a gidan gwaggo jummai har yaranta maza uku suka dawo dana bata da mace sai yamma baban ɗan ta ya dawo dasu gida a motar ta.
Zuwa dare Alhaji shamsu ya kira kusan sau nawa ba'a daga ba,daga baya ta daga tare da canja murya"wanene ke samun mutane don ALLAH?
Yi hakuri ina son magana da farida ne.
Tana gida na fita da wayata ka kira anjima.
Ashe kiran da yake mata yaji wace irin waya take so bata Daga ba kawai ya saya mata"INFINIX HOT7 PRO".
zuwA 30minut haka ta masa flashing ya Kira Wai Ashe tun lokacin yana kofar gidan su ya kawo wayar.
Ta fito tana ɗan gashi suka gaisa,babban ledar"SHAA'BAN SUPERMARKET"ya mika mata tayi godiya tare da shige wa gida.
Koda ta duba,dangin kayan fiye fiye da shaye shaye ne kala kala sai kwalin waya.
Ai kuwa ta jawo aunty Salma Dakin ta nan ta sake baki tana kallon ikon Allah tare da yaba wa.
"Yanzu aunty idan baban ihsan ya gani fa?"
Ke don ALLAH da shegen tsoron tsiya ba zai gane ba.
Shike nan yanzu ga tsohuwar tawa idan na kwashe Abinda ke ciki zan baki ciki gaba da amfani da ita.
Sai data tana kara kan murna domin rabonta da babban waya tun ihsan na ƙarama duk wayar da ya saya mata sai ihsan ta lalata shine ya gaji ya haɗa ta da keypad.
Koda ta haɗa wayar da charge full yadda sabon layi na MTN Wanda AKAYI welcome back,Kare shi tayi kawai ta zuba layukan ta ciki nan da nan tayi copying duk wasu important Abu dake ciki ta aje wa aunty Salma tsohon nata tecno k7.
Da safe ta mika mata ai kuwa abban ihsan yayi ta faɗa ina ta samo wayar dubu sittin?
Karya aunty Salma ta shirya mashi sanan ya hakura.
Haka rayuwa ke tafiya kullum da karyan da Fatima zata haɗa mata ta samu ta amshi wani abu a hanun shi har lokacin tafiyar su zuru sallah yayi nan ma wata hidima yayi domin turmin atamfa manya biyu,manyan arabian performs kusan kala hudu da tarkacen sabulai ya haɗa a kai wa umma banda kuɗi dubu hamsin na kashe wa daya bata.
Ana gobe zasu wuce yazo suyi sallama babu yadda bai yi ba ya rabi jikin ta amma keme me taki amincewa.
"Ranshi ya ɓaci ya shiga masifa,ita kenan kullum da excuse iri iri shi da ya fara gajiya gwara kawai ta sanar dashi matsayin shi idan bata son shi ne ya sani amma ba zai zauna ya zuba mata idanu yana mata hidima tana kauce wa ba dole ayi ɗaya kota bashi hadin kai ko a san nayi!
A zuciyar ta bude motar ta fita zuwa gida domin zuciyarta ta ɓaci sosai ta tsakiya namiji mai nuna wa mace maitar shi a fili don haka duk abinda zai faru ya faru.
Mamaki ta bashi yadda ta iya barin shi yana magana ko hakuri bata bashi ba"kwafa yayi wallahi sai na yi maganin ki zaki san ni ba irin sakarkarun maxan nan bane da ake raina wa hankali.
*~DON ALLAH KU TAYA MU DA ADDU'A MAMAN MU BA LAFIYA SERIOUSLY,MUNA ROKON ALLAH YA TASHI ƘAFAƊAN TA,YA BATA LAFIYA MAI AMFANI~*👏🏻👏🏻
~Sweety SMASHER may Almighty Allah Grant you lafiya mai amfani acikin gaba da suburbudo mana"WANI AL'AMARIN..~👏🏻
*All right reserved unauthorized copying, changing and translation of any part of this story in any form is prohibited.*
*🅿FIVE*
Tunda safe abban ihsan ya kai su tasha, kuɗin mutum uku ya biya masu yadda zasu ji daɗin zama agidan baya ai kuwa ba'a ɗauki lokaci mai tsayi ba motar su ta tashi zuwa zuru...
"Cikin mota babu abinda take sai tunanin rayuwa,irin zaman da take yi da Alhaji shamsu,ita dai tasan bata taɓa jin son shi ba'a zuciyarta,kwata kwata halaye da ɗabi'un shi basu mata ba anya kuwa wankin hula ba zai kai ta dare ba?"
Duba da yadda Fatima ke zuga ta sai amsan kuɗin shi take yi babu wanda ya sani a gida,yanzu idan yace ta biya shi daga ina zata soma?,,thank God bata taɓa kuɗin ba dubu ɗari biyar suna nan cif,hamsin ɗin Farko ne ta kacal cala suka yi kayan sallah set biyu masu kyau da tsada daga kaduna ,a cewar Fatima bai kamata big girl da ita kowa yasan tana aikin gomnati ga salary mai tsoka amma ba'a ganin tana ɗaura manyan kaya.
"Koda ta waiga gefen aunty tayi bacci abunta kasan cewa a daren jiya tasha soyayya da mijinta ,yau kuma da wuri suka tashi.
Ihsan ce keta kalle kalle tana zuba surutai irin nasu na yara"....
Awannin uku ta kawo su"KOKO BESSE LG",Nan aka ɗan tsaya saboda masu jin yunwa ko wani lalura suyi kafun aci gaba da tafiya.
Ke ba zaki fita ba?"cewar aunty salma".
Girgiza kai kawai tayi!
Aunty Salma ta kama hanun ihsan suka nufi public toilet ta biya suka shiga domin rage marar ta,suna dawo wa ta saya mata nutrie milk da biscuit suka dawo cikin mota.
Da yake sun yi breakfast ihsan Kawai taci abunta.
Masu bread keta zagaye su,farida ta fidda 1k aka basu manya na ɗari uku,uku guda uku"aunty Salma dai na kallon ta har suka ci gaba da tafiya.
Kowa shiru har suka wuce marafa,mahuta,dabai sai gasu a City gare"WELCOME TO ZURU".
_Gari mai dumbin tarihi wanda ake yiwa lakabi da"A COMMUNITY WHERE SOLDIERING IS A FAMILY PRIDE",saboda kusan ko wane zuri'a yankin suna da ma'aikacin kaki(army).Akwai yalwar arziki duba da yadda mazaunan garin suka mayar da NOMA toshen arzikin su(there mainly occupation is farming and and going to army),wurin neman ilimi ma ba'a bar su a baya ba domin suna da babban collajin noma"COLLAGE OF AGRIC DA
SAHAM COLLAGE OF HEALTH TECHNOLOGY"Wanda aka buɗe bada jimawa ba.zuru na ɗaya daga cikin local government na Kebbi da ke dauke da dimbin tarihi a Nigeria, sun tara manyan sojoji irin su;BRIGADIER MOHAMMED SANI SAMI Sarkin zuru mai ci a yanzu wanda ya taɓa yin gomnan BAUCHI STATE daga january 1984 zuwa August 1985 durin military regime of MAJOR GENERAL MUHAMMAD BUHARI.Ga(rtd)MAJOR GEN.MOHAMMED MAGORO Wanda yayi senata a 2011,former chief of army staff(rtd)Lt Gen.Ishaya Bamaiyi,late major Gen.Tanko Ayuba,(rtd)colonel samaila yombe Dabai.Shi Yasa ake alakanta ma'anar zuru da"A LAND WHERE LION LIVED".
"Keeee farida Wai tunanin me kike yi haka har an tsaya baki sani ba?"
Na'am aunty ba komi Amma tafiyar tayi sauri ko?
Ban sani ba ta amsa a hasale domin labarin farida ya fara bata haushi.
Achaba suka samu wanda zai kai su tudun Wada saboda garin akwai ƙarancin adaidaita sahu.Har kofar gida kuwa aka aje su da kayan su ai kuwa nafisa ta fito a guje ta rungume ihsan tana iso...
"Dallah mallama Jaye Kamar wata mahaukaciya wai mutum ya girma amma har yanzu yana abu kamar jariri!"
Kai aunty farida nayi missing ɗin kine...
Tsaki taja tare da dibar kayan da suka iso dasu tana shiga ɗan madaidaicin gidan su mai dakuna biyu da palour sai toilet haɗe da bathroom a cikin gidan, kitchen ma haka.
"Aunty Salma dariyar su kawai take Yi domin tasan yan drama ne.
Umma na zaune palour tana saurarar FM radio taji sallamar su...,maraba da mutanen birnin kebbi kun sha hanya.
Fuskarta dauke da fara'a ta amsa"wallahi kuwa umma ya muka same ku?
Lafiya lau ya dawainiya da farida?
Kai alhamdulillah umma.
Nafisa dauko masu abincin mana kina tsaye a kan mutane sai washe baki ki ke kamar gonar auduga.
Sallama farida tayi da sauran kayan su niki jiki ta kai dakin umma sanan suka gaisa da kyau.
Ganyen rama ne aka soya da man kaɗai wanda yaji daddawa na aihinin kalwa da fresh attarugu da tattasai sai kamshin albasa yake yi,gefe ɗaya kuma tuwon ainihin farar shinkafa ce da miyar zogala wanda yaji gyada da naman ƙaramin dabba,gefe ɗaya kuma kunun zakin dawa ne da dankali yayi sanyi sosai cikin jug.
Ihsan Sarkin son ganye ai kuwa Bata bita kan miyar ba ta farma ganyen da ci..
Bayan sun kamala ne nafisa ta kwashe kayan tare da gyara wuri suka koma gindin bishiyar magoro dake cikin gidan suna shan iska kasan cewa an ɗauke wutar nepa.
Umma ce ta tsira wa farida idanu na ɗan lokaci"yanzu Salman ba za kuyi ma wanan yarinya faɗa ta fitar da mijin aure ba saboda Allah duk warin ta a nan sun yi aure daga masu yara biyu sai uku!"
Cikin girmama wa Salman ta amsa"umma komi lokaci ne addu'ar ku kawai muke nema Allah ya zaba mata mafi alheri.
Haka kike faɗi ko wane lokaci kuma goya mata baya tana iya shegen iri iri idan wanan ya fito bayan kwana biyu ta canja,kusan sau uku kenan tana kawo miji sai magana tayi nisa tace ba mijin aure bane!
"Umma a ƙara hakuri dai duk wanda suka zo suka tafi dama can ba rabon ta bane domin babu mai auren mijin wani ko matar wani."
Na gaji da jin wanan bayani salma,akalla shekarun farida sun kai 23 zuwa 24yrs,lokacin da take karatun kun hana ta tsayar da miji tun tana da sha'awar ta ana sonta,yanzu shekaru biyu kenan da kammalawa amma babu tsayayyen mijin aure!,wai baki san mace duk kwanan duniya rage kyau da tsari take yi ba?,wallahi Salma banda babban tashin hankali a gaba na da ya wuce farida,kwara ita nafisa yanzu zata kamala secondary ko ITA din idan ta samu miji aurar da ita zan yi.
Shiru kawai Salma tayi domin umma ta fi su gaskiya...
Bambamin faɗa tace gaba dayi tana ƙari har aka kira sallah suka watse.
Koda aka ciro kayan tsarabar da Alhaji shamsu ya bata a matsayin na umma,da kyar ta amsa tana daure fuska domin bata sanar da umma wani ya bayar a bata ba.
Ai kuwa tun daga ranar umma bata sakar wa farida fuska gani take da gangan taki tsayar da hankalin ta wuri ɗaya.
Abun duniya duk ya isheta,ga Alhaji shamsu ya dame ta da waya yana son sanin matsayin shi idan ba haka ba dole ta biya shi duk abinda ya bata,ita kuma Fatima sun tafi aikin aikin Hajj da daddy su ba'a samun ta.
Tare da aunty Salma suka zaga dangi cikin garin zuru da kewaye duk inda suka shiga maganar kenan"FARIDA TA TSAYA RUWAN IDO",da suka isa gidan iyayen aunty Salma Nan ta kule kanta a toilet Tasha kuka mai isar ta Wanda aunty Salma tana hankalce da ita.
Bayan sun dawo an shiga kwanciya
_Dama dakin yaya jamilu na samar taka nan suke sauka shida matar shi idan sun zo da yake babban daki ne,umma kuma na ciki da palour._
Tunda suka zo tare da farida suke kwana kafin ya iso ta koma dakin umma.
"Farida tashi magana za muyi na fahimta",babu musu ta tashi zaune domin bacci ya gagare idanun ta.
Farida idanu ki rumtse idanun ki,ki taushe kunen ki daga ji da ganin abinda mutane ke faɗa akan ki,nasan kin kai munzalin aure,mace kike baliga Mai lafiya kuma kina ci kina koshi dole kiji sha'awar ɗa namiji.Aure,mutuwa da haihuwa lokaci ne babu wanda ya isa yace ya shirya masu domin zuwa suke lokaci ɗaya,duk surutun da za'a yi a kanki idan lokaci bai yi ba auren nan ba zai yi kanshi ba dole sai kin daure da addu'a, ɗaura niyya da koma ba wani daga cikin masu neman ki dama,wanan kaɗai zai nuna wa duniya kin saka abun a gaban ki,musamman umma wacce ke cikin halin damuwa kuma ban ga laifin ta ba domin baba ya rasu ya barta da ku babu wanda ya taimaka mata da komi na dawainiyar ku,ci,sha,sutura da ilimi sai ɗan uwan ku da taimakon Allah kika samu ingantacciyar rayuwa,saboda haka ya zama dole ki ɗauki damarar faranta zuciyar umma.
"Shawara,mai zai hana kiba Alhaji shamsi dama yazo yaga yayan ku,idan Allah yasa dashi za'a yi shike nan,idan kuma ba alheri bane sai kofa Allah ya kawo wani nan gaba".
Nanauyar ajiyar zuciya ta sauke,dama aunty ya matsa mun akan haka nace ya bari mu tafi gida zan yi shawara abinda aka yanke zan sanar dashi.Amma wani hanzarin ba gudu ba aunty Salma wallahi bana son shi ko kaɗan,baya cikin irin mazan da nake so gashi tsoho ne sosai da....
"Faridaaaaaaa!,wanan ba matsala bane a hankali idan ku ka fahimci juna zaki so shi,maganar baya cikin tsarin wanda kike so a aje ta gefe domin ba lallai bane a rayuwa ka samu abinda kake so musamman akan mijin aure mutum baya taɓa samun 100%,wallahi gwara ki aure elderly man da yaro wanda bai san ciwon kan shi ba bare yasan ciwon ki saboda haka"A WORD IS ENOUGH FOR THE WISE..."
Nagode aunty Salma zan yi istihara akan lamarin shi.
"Better". addu'a bacci suka shafa ko wanne ya kwanta cike da tunani iri iri a zuciyar shi har bacci ya kwashe su.
Shawara ta yanke data cire layinta na MTN har su koma kebbi hakan ne kawai zai bata cikakkiyar natsuwa ta samu daman fuskantar abunda ke gabanta,saboda ba kowa ne yasan layin AIRTEL nata ba.
Ana gobe bukin Sallah ta yiwa ihsan da nafisa kitso,saboda ita da aunty Salma saloon zasu a gyara masu gashi bayan kwana biyu suyi kitso.
"Aiki sosai suka sha na gyaran kaji da zasu yi abinci ranar sallah sai tafasasshen tumatur na biya ga cake da za suyi na raba ma mutane'.
A ranar da dare abban ihsan ya iso ai kuwa da maganar farida umma ta tarbe shi sosai ta nuna mashi ɓaci ranta,sai hakuri yake bata.
Washe garin sallah da safe suka dafa white rice da stew,sai salad cream da suka haɗa, pepper chicken da zobo drink na abokan abban ihsan da zai shigo dasu idan sun dawo masallaci.
Suna kammalawa suka sheka wanka ko wacce ta sha kwalliya anata hotuna da wayar farida har aka dawo Masallaci suka yi serving abincin ma baƙin abban ihsan sanan suka nufi saloon Nan kusa da gida kafin a gama yanka su yi aikin naman layya.
A ranar dai kayan ciki kawai suka soya har zuwa da safe suyi aikin nama saboda aunty Salma zata tafi yini gidan iyayen ta wanda haka suka saba.
"Haka dai aka yi bukin Sallah aka kamala wanda farida ba wani daɗin shi ta ji ba saboda yadda umma ta canza mata kwata kwata,ranar da zasu dawo saboda irin faɗa data sha a wurin umma hadda kuka taci".
Cikin mota sai faɗa abban ihsan yake ya bata sati ɗaya ta fitar da koma wanene idan ba haka ba zai mugun saɓa mata!
*~Ba zan iya bayyana farin ciki na ba akan kulawa da dumbin masoyya suka nuna mun,MAMA kam na jin jiki but ALHAMDULILLAH saboda CIWO ke shiga lokaci ɗaya LAFIYA kuwa a hankali yake samuwa.JAZAKUMULLAHU KHAIRAN for the prayer,love,care and encouragement~*
*All right reserved unauthorized copying, changing and translation of any part of this story in any form is prohibited.*
*🅿SIX*
Komi ya kwace ma farida babu inda zata raɓa taji dama dama saboda su Fatima basu dawo ba har lokacin shine dalilin da yasa ta ƙi buɗe layin ta na MTN.
Ɓangaren Alhaji shamsu kuwa ya shiga damuwa sosai yana ganin banza zata sha shi tunda farida ta wawuri kuɗi mai tsoka baya samun ta a waya,ya bincika wurin aikin su an sanar dashi bata yi resuming ba,sai saka da warwara yake akan ta yadda zai bolu wa lamarin ta.
"Aunty Salma kaɗai ke bata kwarin guiwa da shawar wari,abban ihsan kuwa gaisawa kawai ke shiga tsakanin su".
Kwana uku da faruwa haka jirgin su fatima ya sauka a Sokoto state daga nan basu wani tsaya ba suka kamo hanyar birnin kebbi da yamma ai kuwa gidan su cike da jama'a Yan jiran tsaraba...
Sai da k'ura ta lafa sanan ta ɗauko ƙaramar wayarta data bari a gida ciki layinta na MTN yake,number farida ta fara kira..
Lokacin ta gama shan faɗa abban ihsan kenan ta koma d'aki tana sharar hawaye taga kiran Fatima"cike da zumudi ta daga".
Mutuniyar yaushe a gari?
Wallahi yau da yamma nan duk na ƙagara in ji Muryar ki.
Hajia Fatima kenan kun dawo lafiya?
Lafiya klau hajia farida"suka sa dariya"
Allah yasa anyi ibada karbabbiya.
Amin don darajar annabir rahama (S.A.W)
"Ɗan jimmmm farida tayi saboda tana son faɗin matsalar ta kuma tana ganin bai dace ta daga mata hankali daga dawo War ta ba"
Naji kin yi shiru?
Kuka ta fashe dashi,akwai damuwa fatima ina cikin tsaka mai wuya!
Subhanallah farida menene yayi zafi haka?
Cikin kuka ta kwashe komi ta sanar da ita,nan take idanun Fatima suka ciki da ruwa sosai domin matsalar rashin tsayayyen mijin aure na ɗaya daga cikin dalilin da ya saka ta matsa wa daddyn su aka tafi Hajjin bana da ita saboda duk gidan babu yaron da aka taɓa biyawa itace ta farko.
Ki kwantar da hankalin ki farida wallahi nayi mana addu'a sosai in shaa Allah cikin shekarar nan ko wace zata bar gaban iyayen ta,gobe zan samu lokaci in shigo...
Haba ai Ni ya kamata in shigo kawai ki dubi hanya na zan shigo da safe.
Allah ya tashe mu lafiya,suka yi sallama.
Da safen bayan ta kamala ayukan da ta saba ta shirya tsaf cikin ƙaramar ABC wax dunkin doguwar riga fitted play,Bata Yi amfani da dankali ba kawai tayi rolling mayafi ta sallami aunty Salma ta wuce.
Bakin gate ɗan achaba ya aje ta,norking gate ɗin tayi security ya leko ta ƙaramin window,yana ganin itace ya washe baki tare da buɗe mata suka gaisa.
_kana shigowa makeken farfajiyar gidan makale yake da interlock,gefe guda rumfar aje motoci ne a ɗaya gefen garden ne babba wanda ya kasu kashi biyu gefe ɗaya kayan lambu, ɗaya gefen kana nan dabobi ne gwanin sha'awa._
Steps ta haura wanda zai sada ta da babban palourn gida....,ai kuwa tana sallama mutane ne makil maza da mata,manya da yara yan zuwa Barka da dawowa"haka ta ratsa su har ta isa palourn mumyn su nan ma manyan matan yan siyasa ne"
Gaisuwa ta kwasa"mumy na mata tsiya sai yau taga damar leko su tunda Fatima ta dawo",,murmushi kawai ta saki,daga nan ta nufi dakin Fatima wanda ya gaji da haduwa domin ko toilet d'in ta abun kallo ne"har lokacin Fatima bata tashi daga bacci ba"
Curtains ta