kanshi zai nemi hanyar gudu wa lokacin kin ci shi har ƙashi.
"Uhmm Fatima kina ganin a zamanin nan akwai namiji da zai yadda ya sake Mali kuɗi ba tare da nemi wani abu a tare dake ba?
Sanin kanki ne samarin yanzu cikin 💯% dake zuwa wurin budurwa only 10%ke zuwa da niyyar aure,sauran duk yaudara ce da lalata ke kawo su.
"Ni zan baki wanna labari farida domin na fiki waye wa da hulda da manyan mutane,nasan a zama na dake kina mun kallon wata babban ar duniya wace idanun ta ya buɗe da kuɗi,ta saba da harka da maza.
Wallahi ko ɗaya ba haka bane hasali ma inada babban dalilin da yasa na tsunduma kai na a cikin irin wanan rayuwar,insha Allah zan samu lokaci in baki labari.
"Nannauyar ajiyar zuciya Farisa ta sauke,"gaskiya Fatima na daɗe ina zargin abubuwa da dama akan rayuwar ki,yadda kika san manyan mutane,kina abinda kike so,ga kuɗi ba matsalar ki bane....
Haka ne Farida saboda kwata kwata ba muyi wattani biyu cikakke da sanin juna ba,shi yasa baki san komi game da personal life Dina ba.
" Duk da mahaifina babba ne a garin nan kuma mai arziki ne soyayya hakan bai hana Ni son abun hanun maza ba wanda yana da nasaba da wani buri nawa na dabam da nake son cimma akan maza.
" a hankali Zan warware maki komi Wanda nasan Zaki fahimce Ni Kuma ki goya mun baya akan kuduri na".
Riko hanun ta tayi,shike nan zan jira har lokacin da kika Ni niyya ki sanar dani,ta ci gaba da aikin Fatima,ita kuma Fatima na chat har lokacin tashi yayi suka nufi Masallaci gefen mata suka gabatar da sallah.
Suna fitowa wata Range rubber spot fara ce Parker a gefe tana jiran su,ai kuwa suna isa wurin motar wani dattijo ya fito jiki na rawa"ranki ya daɗe Aminiyar mu ya aiki?
Cikin jin kunya farida tace alhamdulillah Alhaji,ita kam uwar gaya sai shan Kamshi take ya buɗe masu gidan baya suka shige ya ja mota.
Wasu maza dake zaune bakin ma'aikata suka ce lallai yaran nan na cikin lokacin su,Mallam sale ko ka gane wanda yazo daukan su?
Na gane shi mana babban dan kasuwa ne,kwana kin nan ya buɗe wani gidan shakatawa a hanyar bypass babba wanda duk garin nan babu irin shi.
Tsohon banza yanzu haka yayi jika dasu fa amma dubi yadda yake rawar ƙafa yara ƙanana sun mayar dashi driver. "mtswwwww suka ci gaba da tattaunawa akan alhajin.....
Sai da aka yau titin sosai ya tsaita front mirror dai dai fuskar fatima"Madam Barka da rana?
"A ciki ta amsa Barka dai.
Farida mamakin duniya ya cika mata zuciya domin tunda akayi posting Fatima a department din su Allah ya haɗa jinin su kasan cewa su biyu ne yan mata,sauran daga matan aure sai maxan aure da samari,kullum kwanan duniya samari kala kala ke kawo Fatima wurin aiki babban abun mamaki wanda ya kawo ta ba shi zai zo daukar ta ba kusan watan ta na biyu kenan a ma'aikatar nasu.
"A kullum da mamakin Fatima take kwana ko a ina take samo irin wanan manyan mutane masu kuɗi kuma tana wulakanta su,gata dai ba kyau ba sai farin fata ɗaya gyara ta amma akwai farin jini da iya sarrafa maza da bakin ta.
Duniyar tunani farida ta shiga ta yadda itama zata zage damtse ta yi amfani da daman ta a matsayin ta na budurwa a fantama da ita.
_masu karatu ku biyo NI a cikin wanan labari mai ɗauke da sabon salo domin jin yadda zata kaya tsakanin wa yan nan yan mata biyu da samarin zamani" shin sune da riba ko samrin??_
*All right reserved unauthorized copying, changing and translation of any part of this story in any form is prohibited.*
*🅿TWO*
Gida suka fara aje Farida tayi godiya,suka wuce abun su domin Fatima ba gida zata ba.
A palour ta samu aunty salma suna homework da ihsan.
"Barka da gida aunty?"
Barka dai farida, ya aikin?
Alhamdulillah har yanzu baban ihsan bai dawo ba?
"Eh wallahi kin san yanzu over time suke yi a wurin aiki sai 4:0pm".
Allah ya taimaka,"tayi jugum kamar mai nazari....
"Hawaye dake bin fuskar ta ya dauki hankalin aunty salma ta have hanunta zuwa bedroom.
Farida menene damuwar ki?,,da quruciyar ki zaki sama kanki wani ciwon?
Kuka ta fashe dashi,aunty Ina cikin matsakaici tashin hankali da damuwa!
Share mata hawaye tayi,Farida ke amana ce a wurin mu ba zan so ganin ki cikin ɓaci rai ba,ki sanar damu damuwar ki!
Aunty shike nan aure ya buwaye Ni?,ki duba tunda na kamala karatu duk wani namiji da zai zo wurina bada niyar aure yake zuwa ba sai yaudara da lalata!
"Kullum kwanan duba fa ƙara shekaru nike,kyawu na yana raguwa....
Shiiiiii!"ta katse ta,bana son Jin wanan maganar kwata kwata shekarun ki nawa farida?
"24years"
Shine kike damun kanki?,ki gode wa Allah U luk younger than your age ma,ga Yan mata nan birjik wanda suka yi shekarun ki biyo shiru babu mai so bare ya taya,amma ke kina samun masu zuwa wurin ki amma kina ɗaga hankalin ki!
Aunty dole zan daga hankali na musamman idan na tuna da mafarkin da nayi kwana ki akan abban mu,yana kuka yana roƙon gafara,yana sanar dani irin azabtar da shi da akeyi a kabari musamman lokacin al'adata saboda rashin aure da ban yi ba.
Jikinta sanyi yayi sosai domin sai da tayi tambaya akan mafarkin nan da Farida tayi aka nuna mata yana iya zama gaskiya domin Allah kan nuna ma bawa ishara a mafarki wanda hakan na iya kasancewa gaskiya musamman akan mamaci.
"Farida ki cire wanan magana a zuciyar ki,mafarki ne kawai ba komi ba,zan so kici gaba da rike mutuncin kan ki,kada ki yadda kwadayi da don abun duniya ya rufe maku idanu ki aikata sab'on Allah,rabon ka baya wuce ka haka aure lokaci ne kuma nufi ne na Allah.
Ajiyar zuciya ta sauke,shike nan aunty Nagode kuma zan kula.
"Zan so kiba wanan Alhajin dama idan Allah yasa kun fahimci juna shike nan,kuma mu ci gaba da addu'a.
"Gaskiya ita kam alhajin nan bata jin komi azuciyarta game dashi,gashi ma kazami,bakauye irin"MONEY MISS ROAD"d'in Nan ne.
Yanzu dai kici abinci ki huta zan duba aikin da ihsan ke yi.
Bathroom ta shiga ta sakar wa kanta ruwa kafin daga bisani ta nemi abinda zata ci.
Zama tayi cikin dakin abubuwa da dama na mata yawo a zuciya sai tunanin rayuwar ta...
_Iyayen su yan asalin jahar Kebbi ne,karamar hukumar zuru,su uku aka haifa"yaya jamilu, farida sai auta nafisa".sun taso cikin rufin asirin Allah har yaya jamilu ya kamala degree nashi ya samu aiki a cikin birnin kebbi Allah ya buɗe mai hanya na arziki yayi aure ya mallaki gidan kan shi da abun hawa.ta kamala secondary School da watanni shida Allah yayi wa mahaifin su rasuwa dai dai yaya jamilu ya sama mata admission a"FEDERAL POLYTECHNIC BIRNIN KEBBI"zaman ta ya dawo kachokan wurin shi saboda matsala da auntyn salma keda shi a mahaifar ta duk ta su ciki sai ya lalace har aka samu na ihsan ya tsaya,yanzu haka ta kamala"NCE nata a fannin COMPUTER SCIENCE"Allah yasa ta samu aiki.Shekarun ta shida kenan a birnin Kebbi sai lokacin sallah suke zuwa zuri'a ko karshen shekara,umma ita ɗaya ce da aura nafisa wacce ke ss3 a yanzu._
RINGING din wayarta ya dawo da ita daga duniyar tunani da ta shiga....
"Salamu ALAIKUM ta furta"
Waalaiku musalam ranki ya daɗe,ya aiki?
"Alhamdulillah ta amsa.
Dama in shaida maki zan shigo anjima akan maganar mu...
"Shiru tayi na dan lokaci,ok sai ka zo,suka yi sallama.
Fatima ta shiga nema a waya domin Allah yasan ba son shi take yi ba,anya zata iya bashi dama kuwa?
"Har ya Kari ringing Bata ɗaga ba."
Tsaki taja ta nemi wuri ta kwanta domin tasan halin Fatima idan tana harkokin ta bata kula waya.
Ba'a fi mintuna sha biyar ba alamar shigowar sako taji a wayar ta.
Koda ta duba na Fatima da Alhaji ne.
Na Fatima ta fara bude wa
_"Hey babe I will get back to you when I'm done_.
Alhaji kuwa VTU ya mata na 5k MTN recharge card.
Cike da mamaki take rike da wayan domin Ita dai duk iya samarin ta da tayi babu wanda ya taɓa turo mata koda 2k credit ne bare har 5k.
Kiran Fatima ya shigo"ar fara ina kika shige ne?
Wallahi mun biya"BLUE MART NE "naci abinci yanzu ya aje ni"HAƊA KATA SALOON".
Ok Dama akan maganar Alhaji shamsu ne,wallahi ya matsa wa rayuwata yanzu haka VTU na 5k ya mun kuma wai zai zo anjima....
"Dariya tayi sosai,wanan ko a cikin CORPERS,babba ne domin yasan yadda zai cika mace da kuɗi ya saye zuciyarta zama ɗaya,nasan idan yazo anjima definitely zai nemi wani abu a wurin ki yanzu zan maki text duk abinda ke ciki shi zaki aikata.
*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_
*All right reserved unauthorized copying, changing and translation of any part of this story in any form is prohibited.*
*🅿THREE*
Bayan sallah isha'i ta shek'a wanka cikin simple lace Riga da skirt Wanda ya amshi jikinta sosai,tayi light make up tare da yane kanta da veil Mai kauri wanda ya sauko har bayan ta.shirya kanta tsaf tayi kamar yadda Fatima ta rubutu mata a text ɗin.
"Da sallama ta shiga d'akin aunty salma wacce ke shirye tsaf cikin English wears da alama d'akin mijin ta zata.
"Barka dai aunty?"
Yauwa farry sai ina?
Nan bakin gate aunty"tana magana idonta na kan ihsan dake shan bacci ta hankali kwance.
"A dawo lafiya kuma ki kula da kanki "
In shaa Allah ta fice.
Tana fita bakin gate din wata sabuwar matrix fara fol ta gani ɗan nesa da gidan,horn ya mata wanda hakan ya sa ta gane shine.
A yangan ce ta ke takawa ko ina na jikin ta na kadawa har ta isa ya buɗe Mata front door ta shiga.
"Yayi relax idanun shi kyam a kanta,ranki ya daɗe....
Fari tayi da idanu"tare da naka,ta furta cikin wata irin kasalaliyar murya".
Ya gida,ya aiki?
"Alhamdulillah.
Watau Allah ya jarabce Ni da sonki sosai,bana iya zama ba tare da jin Muryar ki ba ko ganin ki,ina so ki bani dama i promise u that ba Zaki Yi regretting ba.
"Hanunta ta saka cikin nashi tana murzawa a hankali,murya can ƙasa"kada ka damu alhaji Ni ɗin taka ce, Allah ya mana jagora.
Washhe baki ya shiga yi"Amin Amin my farry,yanzu me Zaki CI ne?
"Naci abinci ai"
No,ya kamata mu fita wanan albishir da kuma bane ya zama dole na kyautata maki.
Shiru tayi na ɗan lokaci tana kara gode wa Allah da ya haɗa ta da Fatima da yanzu ya zata kasance.
Murmushi ta saki,mu tafi ko?
Gyara zaman shi yayi tare da ba motar wuta suka nufi hanyar"AZBIR ARENA",suna Parker wa ya buɗe mata kofa.amma fafur taki fitowa wanda ba haka yaso ba.
Da ya matsa tace duk abinda ya dauko tana so.
"Zaman minti kusan goma goma tayi a motar kafin ya dawo da ledodi niki niki ya aje a back sit.
Farry baby,kaji ne da su shawarma sai drinks idan ba suyi ba a sauyo wasu?
A'a sun yi kawai Nagode.
"Dariyar mugunta ya saki ya hau titin da kyau.
Zan cen zuci ta shiga yi"lallai maza basu da kirki yanzu duk wanan uwar siyaya da yayi ina zan kai su?",menene ma dalilin shi na yin hakan?.
Bai zame ko ina ba sai gare din"KAKALE GROWN GUEST INN",kirjin ta sai dukan tara tara take yi domin bata taɓa expecting irin haka daga wurin shi ba tunda yace da maganar aure yazo!.
Parking yayi a gefe"ranki ya dade mu shiga ko?
Taso ta Musa sai ta tuna da maganar Fatima,kawai ta fito hankali kwance kamar dama ta saba irin wanan harka.
Key ya amsa wurin receptionist suka haura sama inda dakin yake,ya buɗe suka shige.
"Well furnished single room madaidaici ne,ya Kuna light da zama bakin gado yana washe bakin nan nashi mai doyi (lol).
A hankali ta isa bakin gadon ta zauna saman laps nashi,ganinta ɗaya sagale a wuyan shi,ɗaya kuma tana shafa face nashi.
Nan take Alhaji shamsu ya fara fita haya cin shi(da yake bagidaje ne bai san me ake kira making love before sex ba),ya fara kiciniyar cire rigar shi da alama yana so ta daga ya cire wanda a fara harka.
"Easy Baby,am all yours let's enjoy ourselves first !
Wani daɗi ya ƙara kashe shi"ke ɗin ce baki da dama kina son kashe Ni da salon ki".
Har ga Allah ba halin ta bane kuma bata saba sake ma namiji jiki ba,but she have to do this domin ya aminta da ita ta kwashe kuɗin banza.
Ai kuwa karaf ya sagale hanun shi cikin rigar ta yana neman tabo boobs nata,sai dai kash rigar ta matse ta sosai hannu bai shiga dole sai ya buɗe zip Wanda cikin dibara taki bashi daman haka,kawai sai ya fara damkar su haka nan ta saman riga sai zafi suke mata.
Shafa dukkanin ilahirin jikin shi ta shiga yi tana wasanni dashi har ya fita daga hayacin shi yana kokarin tura hanu cikin skirt nata ya ji abu cikin pant nata kamar pad, Kara tura hannu yayi domin tabbatar wa.
"A kasance ya furta,Baby dama kina period be?"
Cikin jin nauyi tayi nodding (kamar da gaske).
"Kwana nawa kike yi?".
10days"ta furta a raunana.
Can ƙasan makoshi ya furta"oh No!,yaso yaci gaba da jagola ta kawai ta nuna mai yayi hakuri har wani lokaci.
A hanzarce ya fada toilet ya tsaftace jikin shi ya fito dai dai ta gyara zaman mayafin ta saman kai ya riko hanun ta yana kokarin kissing nata tana kawar da kai har ya gaji ya hakura suka fita.
Sai da ya tabbatar sun hau titin sosai ya tambaya Wane account tafi anfani dashi?,ta sanar dashi nan take ya nemi ta faɗa mashi details d'in ya Mata transfer.
Bata wani mayar da hankali ta duba ba kawai tayi godiya dai dai sun iso gidan ta jidi kayan ta suka yi sallama.
Tana shiga suka haɗe da aunty Salma a palour tana jiran shigowar ta"lafiya dai kika dade hankalinsa ya tashi?
Cikin inda inda tace ai gidan su Fatima muka tafi daga nan ya mun take away.
Nanauyar ajiyar zuciya ta sauke,ok ki aje su a fredge har gobe kinga dare yayi.
Suka yi sai da safe ta shiga d'aki ta wanda dama ita da ihsan suke kwana,koda ta duba kayan kaji gashin injin manya guda biyu,shawara guda shida sai babban goran farm pride yoghurt,chi exotic da babban rubber vanilla ice cream.
Cikin fredge ɗin ta aje kamar yadda aunty ta faɗa,ta watsa ruwa tare da gabatar da shafa'atu da wutri tayi addu'a ta kwanta sai ta duba wayarta"alart na 50k ta gani daga Alhaji shamsu wanda bayan salary Bata da yake 35k,babu wanda ya taɓa bata kyautar 20k a dunkule.
" juyi take amma bacci yaƙi daukar idanun ta sai tunani take yadda zata yi anfani da kudin nan ba tare da sanin aunty Salma ba domin idan har aunty Salma ta sani sai ta zarge ta"
Fatima kawai ta fado mata a zuciya,tana ƙara gode wa Allah kuma tana gode mata da irin shawarwarin da ta bata a yau ɗin.
"Tana mamakin yadda Fatima ta san wanan plan kuma har ta gane alhaji shamsu zai nemi wani abu a wurin ta,yanzu kenan ba don Fatima ba da shike nan afka mata zai yi?,idan kuma ta hana shi yana iya zama sanadin rabuwar su wanda bata sun haka a yanzu,tana son yin amfani da hikimar ta kamar yadda Fatima ta bata shawara ta fito gari da dukiyar shi cikin ruwan sanyi ba tare da ya samu nasara a kanta ba.
Da safe bayan ta kamala komi da ta saba ta shirya ihsan itama ta shirya ta nufi wurin aiki domin ta manta kwata kwata da maganar kayan da Alhaji ya saya mata a juya Wanda aunty Salma na sane,Bata Yi magana bane saboda mijinta na gida idan har ya gani zai faɗa.
Kamar yadda ta saba suka fita da ihsan bayan sun yi breakfast ta aje ta a schl sanan ta wuce wurin aiki.
"Yau ma kamar kullum sai da taci rabin aiki sanan Fatima ta iso".
Ai kuwa ta shafa mata labarin abinda ya waka na a tsakanin ta dashi a jiyan da alart da ta gani na 50k.....
Cike da jin daɗi tace koke fa?,yanzu ba gashi nan cikin sauki kin samo 50k a banza ba tare da ya samu abinda yake so ba,wallahi wanan kamar yadda na faɗa maki babban CORPER ne bashi da wayau bare ilimi saboda haka zamu dai dai dashi,nasan ba zai fasa bijiro maki da buƙatar shi,in shaa Allah Nima ba zan faɗa nema mana mafita cuz nayi dealing da wanda suka fi kuɗi da naci amma sun gaji sun shafa mun lafiya.
"Murmushin jin daɗi farida tayi,yanzu dai yaya za'a yi da kudin nan?"
Ki aje su kawai farida kuma bana so aunty salma ta San da kudin zuwa gaba zan faɗa maki yadda za kuyi dasu.
Hira suka ci gaba da yi taɓa kara wayar mata da kai har aka tashi yau CORPER da yazo sukar su saurayi ne first class son kowa kin wanda ya rasa amma sai shan kanshi Fatima ke yi har suka aje farida a gida.
Bayan tayi sallah ta kimtsa ne aunty je mata maganar kayan ta duba sun yi yawa ita bata don hidima irin haka da yawa.
Shiru kawai tayi domin bata da bakin magana,nan sai suka ɗauki kaza ɗaya da shawara uku suka yi warning a mini ovean suka baje a palour suna ci kafin baban ihsan ya dawo.
A ranar ya kira ta a waya kusan sau goma yana kara jaddada mata yadda yake ji da ita nan take tambayar shi asalin shi da kuma iyalin shi.
Dariya yayi sosai.....
_asali na bahaushen burin Kebbi ne mata na biyu amma na rabu da ɗaya saboda rashin mutuncin ta,yanzu mata ta ɗaya yarantaka biyu da ta wadda ta fita guda yara na uku._
Amma menene yasa kake son kara aure?
_uhmmm,mata ta na yanzu Yarinya ce sosai wacce ba zata wuce 20yrs ba,MARAINIYA ce kuma bata wani yi karatun boko ba,kinga tana da ƙarancin waye War kai da ilimi,rashin iya girki na zamani,kula da gida da mai gida,bata iya dauke mun buƙata ta saboda kunya tasu ta