da hawaye adaidai lokacin ATA ya shigo d'akin sakamakon kiransa da mami tayi bai qarasa inda suke ba ya samu waje ya tsaya ya jingina bayansa da bango d'akin ya rungume hannuwansa duka a qirjinsa yana kallon nana hauwa'u dake zubar da hawaye yayinda aunty shahida ta mike daga mazauninta tana faman rarrashinta tana goge mata hawaye ."
Ahankali hisham ya turo kofar dakin ya shigo ya tsaya yana jin wani iri a gabadaya ilahirin ajikinsa kafafuwansa sukai masa nauyi ya kalli inda ATA yake tsaye rabonshi da ganinsa yau tsawon kwana uku kenan ,numfashi ya sauke yana qoqarin danne abinda yaji yana taso masa kafin ahankali aunty shahida ta qaraso inda yake ta riko hannunsa ta zaunar dashi kusa da nana hauwa'u agaban mami ."
"hisham ga amanar nana hauwa'u nan na danqata a hannunka ba dan ina tunanin zaka cutar daita yasa na damka maka amanarta ba sai dan yanayin rayuwa da kuma yadda aurenku ya kasance, aure ne da babu wanda yayi tsamanin faruwarsa amman dake haka allah ya qaddara babu tsimi babu dabara sai ya kasance ,kema nana hauwa'u ga amanar hisham d'ana na damka miki, kisan mahimanci amana ko ban gaya miki ba aure amana ce atsakanin ma'aurata kuma duk wanda yaci amanar dan'uwansa allah bazai barshi ba."
" na tabbatar d'ana hisham bashi da matsala idan naga wata matsala daga gurin ne zaki kuma ki kuka da kanki dan bazan ta'ba d'aga miki kafa ba ko baki uzuri ba dan haka ki kiyaye "aunty shahida dake durkushe kusa dasu tace "hisham ga amanar auta nan allah ya tayaka riko "aunty khadija da zabiba ma dai abinda suka fad'a kenan "shi dai ya shiga ukunsa yanzu mumynsa ta gama damka masa amanarta kafin ya fito tana jadda masa ko rama taga nana hauwa'u tayi sai ya hadu da mummunar fushinta ,yanzu kuma ga mami dasu aunty shahida shi ya suke son yayi da rayuwarsa ?" shifa baya jin zai iya rike wata amana amman babu yadda ya iya muryarsa a sanyaye yace "in sha allahu mami zan kiyaye allah ya qara girma ya qara lafiya" Ameen Ameen hisham allah yayi maku albarka ."
Banda kuka babu abinda nana hauwa'u Ke faman yi wanda hakan Ke sake d'aga hankalin ata kwata kwata irin wannan rayuwar bata burgeshi zaa akai mutun gidan miji amman yana kuka irin haka kamar zaa kai shi kabari ,a tunaninsa wannan zalinci ne sam bai kamata a had'a irin wannan auren ba gara idan nmj ke so komai na zuwa da sauki canza rayuwar mace ba abu bane mai wahala ga d'a nmj amamn canza raayin nmj abune mai bala'i wahala ahankali yaga an mikar da nana hauwa'u tsaye shima hisham ya mike suka jero."
Kamar ance nana hauwa'u ta d'aga kanta idanunta ya sauka akanshi tsaye cike da sanyin jiki ta soma tahowa zuwa inda yake tsaye yana ganin haka ya kau da kanshi gefe yana sauke numfashi har suka qaraso inda yake bai waigo ba ,nana hauwa'u ta kasa wucesa kowa yayi mata fatan alkhairi tare da damka amanarta a hannun hisham amman banda shi tasan halinsa shirunsa yana nufin abubuwa dayawa a gareta dan haka ahankali ta dawo ta duka agabansa tana masa sallama sautin kukanta na tashi."
jikinsa yayi sanyi gayayyun idanunshi ya ware akanta still tana durkushe tana kuka yayinda tafin hannunta ke kife a saman kafarsa wani abu ya had'iye mai d'aci daya tsaya masa a makoshi bai ta'ba sanin cewar yana qaunar qaramar kanwarsa ba sai da aka samu wannan canjin ,babu yadda zai yi daita né domin itace da kanta ta amince, da tursasata akayi sai dai ayi bala'i da zaayi amman bazai yarda ba ,kukanta ya dinga ta'ba zuciyarsa bai san lokacin da ya kira sunanta ba "nana hauwa'u!"
Kanta ta d'ago wanda ke cike da ruwan hawaye ta zubawa yayanta tattausan murmushi ya sakar mata kafin ya mika mata hannunsa alamar ta kama ta mike tsaye ,da wani irin sauri ta kama hannunsa tana ganin kamar a mafarki yake mata murmushi "ina mafarkine ko kuwa ? tayi maganar a fili tana kuka " menene auta ?murmushinka yaya wannan shine karo na farko danaga irin wannan murmushin akan fuskarka" ya qarasa mikar daita tsaye ya kwantar daita akafad'arsa yana shafa bayanta " kiyi hakuri kukan ya isa haka auta "lafewa tayi sosai ajikinsa Kmr wata baby "yaya ka yafe min ban bi umarninka ba "karki damu dani ki kula da kanki ".
shi kuwa hisham zuba masu ido yayi yana jin wani zallar 'bacin rai na ratsashi "ki daina kuka auta idan kinga da matsala ki kirani babu wani uzuri da zanwa hisham shima kuma yasan halina bazai yi any thing nonsense ba "wani irin kallo hisham din yayi masa kamar yace masa "me zai yi idan aka samu matsalar sai ya duba idanun mutane dake wajen mami bazata ji dadi ba hka sauran yanuwata da suke da kima a idanunshi ,sannna idan ya fad'a haka mumynsa bazata d'aga masa kafa ba idan taji labari ."
ATA ya kamo hannunta ya saka acikin na hisham ya damke waje d'aya "ga amanar auta please ka kular min daita fiyye da yadda zaka kula da kanka" shiru hisham yayi masa yaki cewa komai, Jiki babu kwari suka fice daga d'akin, aunty shahida da aunty Khadeeyja da zabiba na biye dasu suna qarasowa parlour'n hisham ya zare hannunsa cikin nata yayi gaba shiru tayi kawai tana duban bayansa kawayen hajiya zulfa'u mutun uku da suka tsaya suka mike tsaye maryam ta qaraso ta rungume nana hauwa'u tana cewa "shikenan sister zaki tafi ki barni" ta qarasa mgnr tana fashewa da kuka "ai baku rabu ba mrym tunda duk mazajenku 'yan gidan nan ne ,kusan kullum suna nan inji cewar hjy nurriya."
Da kyar aka 'bam'bare maryam ajikin nana hauwa'u hjy sumayya ta riko hannunta suka fito zuwa haraban gidan ta bud'e mata bayan mota ta shiga ta zauna ta rufe murfin ,yayinda hisham ke qoqarin qarasawa wajen abokansa hjy summaya ta kwalla masa kira ya dawo ya tsaya gabanta "shiga"mumy kuje kawai daita zan biyoku "aa hisham ba'a yin haka shiga kawai sai wani daga cikin abokanka yajaku "kai !"ya furta a fili sannan ya shiga ya zauna ko kallon inda take bai yi ba ."
Su biyu ne zaune abayan motar sai salim a mazaunin direba hawaye yaki tsayawa a idanun nana hauwa'u,wani sabon kuka ne ya kufce mata sanda suka fito daga estate dinsu suka hau titi ,gefe tayi da kanta tana damke hannuwanta cikin juna "salim kasan wani abu ?salim dake tuki yace "aa sai ka fada "wai ATA ke bani amana" salim naji haka ya manna ipod a kunnensa ya cigaba da tuki "aikin banza sai kace shi ya iya rike amanar' yar wasu da yake son shi a rike masa amanar kanwa, mutun sai shegen son kan tsiya sai kazo kasani dole na rike maka amana."
kunnuwan nana hauwa'u ya jiyo mata maganarsa acan kasan makoshi kamar ta juyo inda yake sai kuma ta fasa ta cigaba da kallon titi ya sake motsa bakinsa kmar zai yi magan sai kuma yayi shiru ya ciro wayarsa dake ringing yanayin yadda ya amsa ta fahimci yaya amar ne "kaga amar dan allah ku barni da damuwata kowa amana amana !! wai me kuke nufi dani ne ?" me yasa bakuje kuncewa ATA ya rike amanar maryma ba sai ni zaku dameni da wata amana saboda kun rainani ?"dan girman allah ku barni na huta naji da damuwata no no!! bazan fa gane ba wayar salim ce ta d'auki qara ya danna iPod din dake makale da kunneshi yana cewa "okay mumy an gama har ya gama wayar musayar magana hisham yake akarshe dai ya kashe yana furta aikin banza kawai ."
Tafiyar mintuna ta kawosu ikeja gra atare suka qaraso gbdynsu har abokan ango sanda salim yayi parking a haraban gidan hajiya sumayya tayi parking a haraban gidan, hisham ne ya fara fitowa yayi gaba ,jiki a matukar sanyaye nana hauwa'u ta fito hjy sumayya ta qarasa da sauri ta riko hannunta cikin nata suka biyo hisham abaya cikin natsuwa har zuwa bakin kofar shiga parlour'n hajiya zulfa'u tana zaune cikin kawayenta ."
wata kawarta marry wacce ta kasance yoroba ta mike da sauri hannunta rike da cup wanda Ke cike da ruwa ta tsaida nana hauwa'u abakin kofar shigowa ta zuba mata ruwan akafafunta tana cewa "barkanki da shigowa gidan d'ana yadda kika shigo cikin koshin lafiya haka zaki qare rayuwarki cikin koshin lafiya ,gidan nan bazai miki zafi ajiki ba ,gidan nan zai zame miki tamkar ruwan sanyi ne yadda muka ga wannan ranar allah ya nuna mana sabuwar shekara munzo suna haka akarshe ta rungumeta ajikinta ."
ta shigo daita parlour'n kai tsaye marry gaban hajiya zulfa'u ta nufa da nana hauwa'u ta duka a gabanta hjy zulfa'u ta kai hannunta ta d'agota ta zaunar daita a gefenta kamar yadda hisham ke zaune abokansa gbdy suka shigo nasiha tayi masu mai ratsa jiki abokan ango na jiran abasu amarya su wuce daita gidanta mumy tace su wuce sai tayi sati anan gabadaya sukai mata sallama suka kama gabansu ahankali ta riko hannun nana hauwa'u ta nufi dakin dake kusa da nata suna shiga ta zaunar daita a bakin gado tare da cewa" ina zuwa ."!bata jima ba ta dawo hannunta rike da cup ta mika mata "ki shanye!" babu mutsu ta karba wani abu ta gani kamar zuba ta kafa kanta ta shanye tana yatsina fuska "akwai d'aci né ?"ba sosai ba "!ta bata amsa da hakan "okay bari akawo miki abinci nasan da wahala idan kinci wani abu ta juya ta fita ."
Ahankali ATA ya juya zai bar d'akin mami aunty shahida da aunty khadija suka dawo d'akin "yauwa a she ma ya nan mu koma magana zamuyi da kai "bai ce masu uffan ba ya koma ya tsaya tare da tura duka hannuwansa acikin aljihun wondonsa ,aunty khadija da aunty shahida suka zuba masa ido suna tunanin ta inda zasu fara masa magana ahankali ya lumshe tsumammun idanunshi na second biyu sannan ya budesu fes akansu tare da tsura masu ido alamun yana sauraronsu " .
"adam !"
aunty shahida ta kira sunansa bai amsa ba illa tsura mata idanunshi da yayi "me yasa ka zabi ka 'bata rayuwarka akan auren nan ?giya fa adam meye hadinka da shan giya saboda allah ? kai babu wanda ya isa da kai kana ganin mahaifiyarmu zata zaba maka abinda zai zame maka matsala né arayuwarka?mami kullum só take taga cigabanmu amman kai da yake mara mutunci né kullum qoqarin kake ka 'ba.""dan allah malama ya isa haka nasan da wannan nasan tana son cigabanmu amman me zanyi da wuce hkn?yayi shiru yana fesar da iska zata zauna yace "meye next dan ina son naje na huta ya katseta ta hanyar fad'ar haka numfashi ta sauke kawai batayi mamakin abinda ya fad'a ba dan tasan halinsa zai iya ma fadar abinda yafi haka ."
Aunty khadija tace "dan allah adam karka qara shan gi..."nifa bazan daina shan giya ba kawai ku barni da rayuwata tunda ni kad'ai damuwarta ta shafa abarni da damuwata kawai ,fuskarsa a daure ya cigaba da magana "wai me yasa kuke manta wani bazai iya ji da ciwon wani ba ?"wannan ciwona ne ni kad'ai abarni kawai naji da ciwona yana gama fadar haka ya juya a fusace ya bar d'akin yana fesar da numfashi."mami ta girgiza kai Kawai cike da taikaci take masa addua.
A parlour'n mami na biyu suka kusan cin karo da maryam da sauri taja baya gabanta yayi wani irin mummunar faduwa sannan ta d'ago ta saci kallonsa adaidai lokacin daya d'ago idanunshi suka tsarke cikin nata wani irin yanayi ta tsinci kanta ciki wanda babu tantama na tsoro da qaunar da take masa ne , wani irin mugun kallo yayi mata mai firgitarwa sannan yaja tsaki yana furta" nonsense"! a fili ya wuceta jiki a sanyaye tabi bayansa da kallo "ya rabbi me zanwa wannan bawa naka ya soni ?rashin qaunarsa gareni yana damuna ya allah ka nuna min hanyar da zanbi ya soni ."
Kai tsaye samansa ya hau ranar yau din ata jinsa yake dabam ,jinsa yake kamar an sauyashi daga adam din daya san kanshi zuwa wani adam din dabam ,wani irin bakinciki ke ratsa shi wanda ga duk wanda yasan shi yasan aininhin zahirin fuskarshi zai ga alamun komai ya qara sauyawa agaresa, domin sauyawar yafi na da muni fuskar nan tashi sam babu rahma attare daita ta dawo tamkr ta kumurcin macijin ."
Har karfe bakwai sauran wasu mintuna nana hauwa'u na zaune a bakin gado ta zabga tagumi sosai tayi shiru tayi zurfi cikin tunani jefa jefa tana zubar da ruwan hawaye da kallon kular abincin daaka kawo mata da ko bud'esa batayi ba ,tun baaje koina ba ta fara kewar gida wani irin ta dinga ji a ilahirin ajikinta tasan adaidai wannan lokacin da take cikin kad'aici da auren soyayya tayi da dole tasan mijinta yana kusa daita yana rarrashinta bazai barta ta kasance ita kad'ai ba ,amman da yake bai sonta ya bawa banza ajiyarta yayi zamansa a parlour'n ."karfe bakwai da minti goma ta mike tsaye ta shiga bathroom din dake manne da d'akin ta dauro alwala ta fito ta gabatar da sallar magrib tayi adduointa ta sake komawa ta zauan kamar yadda take a d'azu tana cigaba da zubar da hawaye ."
hajiya zulfa'u ta turo kofar dakin ta shigo bakinta dauke da sallama yyinda hannunta ke rike da wani cup ba irin na d'azu ba,nana hauwa'u tayi saurin goge hawayenta ta bud'e baki da kyar ta amsa mata sallamar da tayi "har yanzu kina nan a zaune diyata ?"ki rage kayan jikinki mana ki sha iska."nana hauwa'u tayi murmushi kawai d'an bata da wannan kwarin gwiwar bare ta samu karfin zuciyarta aikata haka , burinta a yanzu bai wuce taga yaya hisham ya saki fuskarsa kamar yadda yake mata ada kafin ta zama mata agaresa ba ."
tana buqatar sakin fuskarsa ko kadan ne daga garesa ,ahankali ta zare mayafin jikinta ta ajiye cike da jin kunyar hjy zulfa'u,cup din hannunta ta miko mata tana cewa "ungo ki shaye "a natse tasanya hannuta ta karba cike da girmamawa ta kafa kai ta shanye tana yatsina fuska dan kamar irin na d'azu ne kawai kalarsu ne ba iri daya ba ta mika mata cup tana cewa "na gode mumy allah ya qara girma "dan ko bata fad'a mata ba ta fahimci irin maganin da take bata "karki qara yi min godiya dan na baki abu ni fa mahaifiya ce agareki ,ki saki jikinki dani kinji ki cin abinci dana sa akawo miki ?tayi shiru tana tunanin amsar da zata bata kafin tayi mgn har hjy zulfa'u ta qarasa ta bud'e kula abincin yana nan Kmr yadda aka kawo mata "ya baki ci abinci ba ?ki cire komai aranki kice abinci kinji "nana hauwa ta gyad'a mata kai alamun taji " idan kinyi wanka ga kaya can ki canza "tana gm fad'ar hk ta juya ta fice daga dakin ."
Wani abinci hjy zulfa'u tasa aka sake kawo mata wace ta kawo abinci na fita ta dawo dakin wanda kafin ta fita a dakin sai data lallabata dan dole ta fara cin abinci bata wani ci daywa ba ta mike ta shiga bathroom tayi wanka da alwala ta fito ta sauya kaya tayi sallah ishai byn ta idar ta kwanta a gefen gado tana kukan , ita kanta kukan ya isheta haka amman da zarar ta tuna yanayin yaya hisham sai kukan ya sake dawo mata ."
hisham daya shigo dakin yaja tsaki karo na farko da yaji ya tsani kukan da take duk da yasanta tun tashinta yasan yadda mami take ji daita ya santa da saurin kuka but ba irin haka ba ,tasan bata són shi me yasa ta amince aka daura masu aure ?dan yasan itama raahin sonahi né yake sata kuka, lalle ko akwai aiki dan wannan na cikin dalilin da zai sa yaji ya qara tsanarta shi kuka idan bana nuzla bane ai aikin banza né a wajensa ,nuzla itace macen da zai iya jurar komai nata tasoshi ko karta só shi he does care wannan alqawarinsa ne ko a wani hali take zai jure matukar akanta ne saboda yana matukar sonta bai zauna ba ya juya ya fice daga dakin daman mumynsa ce ta tursasa masa shigowa ."
******
Da misalin karfe goma na dare ranar lahadi maryama na zaune a d'akinta akan kujerar roba tana zane domin yanzu yana cikin abinda ya fara rage mata damuwa da ta zame mata jiki ,yusif kuwa tuni ta fidda shi aranta da dawowarsa da rashinsa duk daya ne a wajenta ,shi kuwa baba gali tun sanda yayi mata maganar sauyi akan yusif taji duk duniya babu wanda ta tsana kamar shi hatta gaisuwar da take shiga bangaresa ta gaishesa ta daina zuwa ,ko ganinsa tayi a waje gaisuwar sama sama take masa tunda ta rigada ta tabbatarwa kanta baya qaunarta ,ta kuma tabbatarwa kanta baba gali makiyinta ne da keda fuska biyu har ma gara aunty salma dashi ita daman can bata ta'ba nuna tana qaunarsu ba, amman shi baba gali wani lokaci yana nuna yana sonsu ,akan ya'yansa ne ma wani lokaci suke fuskantar tsana shi kuma wannan daman ta ajiyesa a matsayin uban wani da ya'yan wani akwai bambamci ."
Ta numfasa sannan ta dakata da abinda take tare da tura bakin pencil a bakinta tana tunani "life goes on maryama karki qara yarda ko amincewa wani d'a nmj arayuwarki da sunan soyayya, ba lalle sai da aure zaki yi rayuwa ba ,ko da aure ko babu zaki rayu dan haka ki natsu ki qara kwantar da hankalinki ki qare bautar kasa ki samu aiki mai kyau wanda zaki kula da kaninki da mahaifiyarki ki ajiye wani batu na aure dan muddin aunty salma aunty hassana baba gali da sauran yanuwan mahaifinki na raye bazasu bari kiyi aure ba "na karbi qaddarata allah ka bani ikon cin jarabawa sanyayyen numfashi ta sauke ta cigaba da abinda take."
Washegari ya kama monday tun da asuba ta tashi tayi sallah bata koma ba ta shiga