ki fara shirin aurensa nan da kwanaki goma ." cikin firgici da tashin hankali ta shiga d'aga kafafunta zuwa inda yake zaune "me yasa yaya ?" dan Allah kayi hakuri karka min haka wallahi ni bana son shi a matukar tsawace yace "nace karki sake fad'ar wata magana anan , karki sake kula kowa acikin masu sonki shima wanda kike so ki kashe soyayyarsa acikin zuciyarki ki so wanda yake sonki .."
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 20
jikinta na wani irin rawa ta k'araso ta durkushe a gabansa har bata san sanda ta d'aura hannuwanta duka bisa cinyoyinsa tana kallon cikin kwayar idanunsa da suka rikid'e suka canza kala a wulakance ya zame jikinsa yana mai kawar da fuskarsa gefen hisham dake zaune tmkr mutun mutumi yana kallonsu cike da matsanancin tashin hankali ,shi kuwa mr ata alamun baya son kallon fuskarta ne yasa shi maida idanunshi kan hisham ".
"dan allah dan Allah !! yaya adam kayi hakuri ta kai hanuta tana qoqarin juyo da fuskarsa gareta domin su fuskanci juna , zuciyarta na wani irin bugawa da karfin gaske take kallonsa haka ma hisham zuciyarsa ce take ta bugawa fiyye da kaida ya soma jin wani sauyi na daban a gabadaya ilahirin jikinsa wanda ke gauraye da tsantsar tashin hankali, shi kuwa mr ata mamakinta yasa gbdy ya qasa magana duk da maganar yake son yi .
Kwayar idanunta suka cicciko da ruwan hawaye muryarta a sarke tace "dan Allah yaya kayi hakuri karka bari wannan auren ya kasance domin zuciyata bazata iya d'aukar wannan nauyin ba, wata razananniyar tsawa ya buga mata wanda ya kamata ace ta tsorata ta dawo da hankalinta jikinta amman ina sai ma sake narkewa tayi a wajen zuciyarta babu tsoron komai acikinta , muryarsa a kausashe yace " tashi ki bar nan ki kuma fara shirinki kamar yadda na fad'a miki oya leave ."
"dan Allah ka saurareni yaya "ya girgiza mata kai yana cewa " I don't want to listing anything from you just leave now "dan allah yaya adam kayi hakuri ka saurareni akwai maganar da idan na fad'a maka nasan zaka fahimceni "ata dan Allah ka barta ta fad'i abinda ke zuciyarta Hisham yayi maganar yana qarewa jikin nuzla dake rawa tmkr mazari da kallo , yadda take cikin tashin hankali haka shima ya tsinci kanshi cikin tashin hankali mai tsanani har yana jin ma kamar ya cire mata nata damuwar ya qarawa kanshi "
Hisham yayi tsuru tsuru yana jira yaji abinda zata fad'a ,yayinda mr ata bai ce uffan ba ya yunkura ya mike tsaye ya kwashi wayoyinsa ya fara taka kafafunsa da kyar zai bar wajen kasancewar bai son yawon magiya bare irin nata dake hargitsa kwakwaluwa nuzla tayi saurin shan gabansa tana fad'in "yaya karka wuce ka bar zuciyata cikin maseefa tayi maganar cike da tausayawa ,bai yi mata magana ba ya cigaba da tafiya yana mata gargadi da hannunsa alamun ta shiga hankalinta , bata daddara ba ta sake shan gabansa dan gbdy zuciyarta ta rigada ta bushe babu abinda take qoqarin aikatawa face ta bayyana masa ciwon dake cikin zuciyarta ."
Ya tsaya kawai yana mata wani mugun kallo
yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa muryarta cike da rauni da buqatar atausaya mata ta fara magana "bazan iya jure ciwon rabuwa da wanda nake só na auri wanda kake só ba ta karasa mgnr tana rungumeshi ajikita tana kuka a matukar zuciye ya fixgeta daga jikinsa yana sake furzar da iske "are you out of your sense ?ni sa'anki ne da kike shiga gabana? " ko ina wasa dake ne da ina magana kina magana ? ya fad'a yana kawar da fuskarsa akanta domin dai zuciyarsa ta fara tausaya mata tausayawar da bata da wani amfani dan bazai ta'ba iya mata taimakon da take nema daga garesa ba ."
Hisham ya rasa meke faruwa atsakaninsu babu abinda zuciyarsa bata kissa masa ba a zaune da yake tmkr an dasashi irin kallon da take ata da rungumar da tayi masa ya fara gasgata zuciyarsa akan abinda bai niyyar yarda dashi ba yaso ya mike ya qarasa zuwa inda suke tsaye yasan ko akan me take masa magiya har da runguma amman hakan nan yaji gara ya cigaba da zama a inda yake zai fiyye masa alkhairi kuma bugu da qari yayi imani ata bazai ta'ba aikata komai ba face abinda yasan zai zamewa rayuwarsa farinciki he really trust him mutun ne shi mai kyakkyawar zuciya akanshi ."
Hawaye na gangaro mata bisa kuncinta yayinda magana ya fara fitowa daga bakinta "ina qaunar ka yaya ? bai yi mamakin jin fitowar hakan daga bakinta ba domin ya rigada ya gama karantata tsab "na sani sai akayi yaya ?ya fad'a yana kallonta yana jin kamar ya soma yar yarfa mata maruka ta dawo haiyacinta "dan Allah yaya karka ce min a'a ! a kowani hali zan kasance tare da kai " ta maimaita hkn a fili yafi sau goma tana mai kai hannu ta shafa kasumbar dake kwance a fuskarsa ji yayi kamar ta shafa masa garwashin wuta ,shi fa duk duniya babu macen da yake jin zata ta'ba shi yaji wani abu ajikinsa sai princess ita ma din yanzu ya soma gogeta a zuciyarsa da rayuwarsa ."cikin fita haiyacinta
ta riko fuskarsa sosai ta sanya kwayar idanunta dake tsiyaya ruwan hawaye acikin nasa " ban san hka soyayyarka tayi tasiri acikin zuciyata ba sai dana qasa amsar soyayyar kowa ."
"Ban san tasirin soyayyarka ta kai mizanin da zan iya rasa rayuwata ba sai da naji zaka min nisa , yaya kaine duniyata ruhina yana tare da kai ako da yaushe , nayi yunkurin bayyana maka soyayyata a tun lokacin da mubina Ke mutuwar sonka amman na gaza aikata hakan ina ganin cewar zan iya cire soyayyarka na cigaba da rayuwata amman still na qasa domin kuwa every each second nake jin sonka na qaruwa a cikin zuciyata , ina ta qoqarin sheida maka halin da zuciyata take ciki kwatsam kuma sai ga batun aurenka da marsi bance ka bar marsi ba amman dan allah ka had'amu ka auremu " rokonki bai kar'bu ba bare wata alfarmar ya kamata ku koyi yadda ake iya control din zuciya "ka taimakeni ban san ya zanyi ba " kar allah yasa ki sani ya fad'a yana jan tsaki ."
kuka take sosai tana kallonsa tmkr ranar ta fara ganinsa shi kuwa haushi ne ya turnikesa a wajen zuciyarsa banda tuttukin bakinciki babu abinda yake , a ganinsa ma ta balain rainashi
shi zata kalla tace tana so alhalin ga hisham dake mutuwar sonta? "kayi hakuri dan girman Allah nasan zakayi tunanin komai akaina wallahi haka ne , dan na rigada na haukace akanka bazan iya jurar abinda nake ji akanka ba sannan bazan iya amsar soyayyar yaya hisham ba ,dan kona auresa gangar jikina ya aura zuciyata da komai nawa yana gareka da kawai zan iya rayuwa ..."
Ta riko hannunsa hawaye na zuba daga idanunta ta soma tafiya dashi taku d'aya biyu yayi ya tsaya cak , itama ta tsaya suna fuskantar hisham naunaye ajiyar zuciya ta sauke tana goge hawayen dake tsiyaya ,ahankali ata ya zare hannunsa dake cikin nata ya yarfar sannna ya zura cikin aljihun wondonsa yana jan tsaki "ya hisham! ta kira sunansa a kid'eme "banyi niyyar fito da sirrin dake zuciyata ba amamn ya zama dole na fad'a maka tunda na fad'awa yaya adam babu komai acikin zuciyata sai..." karki kuskura kiyi wannan ganganci dan kome zaki yi tawa zuciyar bazata amince ba "to kuwa gara ka ksheni da hannunka na huta dan nima bazan iya auren yaya hisham ba , yana sona ni kuma kai nake so.."you're very stupid Kiyi maza ki danna madannin gogewa ki gogeni arayuwarki da zuciyarki dan ni mallakin mafarkina ce " yana gama fad'ar haka ya juya ya haye sama yana taka step yana magana " hisham ka manta da shirmen wannan yarinyar ka soma naka shirin domin wannan auren ko zata mutu sai anyisa useless girl kawai ga inda ake sonku aka damu daku amman ku dinga kai kanku inda bazaa ta'ba sonku ba nonsense "
Hisham ya runtse idanuwanshi "kenan hasashensa ya tabbata , zarginsa ya zama gasky kenan akan ata yake shan wulakanci da tsana da wahala a wajenta ? ,"ya kalleta cike da tausayawa yace "daman ata Kike so ?jikinta yayi mugu mugun sanyi ta rasa me zata cewa hisham illa ta runtse idanunta gam tana jin zafi da ciwo mara iyaka a zuciyarta ,ta durkushe qasa tana kuka tana nemawar kanta mafuta dan dole tasan abun yi kafin a had'ata aure da hisham shima ya durkushe gabanta ya dago ha'barta ya sanya kwayar idanunshi cikin nata , tai saurin buge masa hannu tana kallonsa cike da tsantsar tsana "ka kyaleni ni wallahi bana sonka tunda burinka kenan na soka , dan girman allah ka rabu dani ka manta dani, ka manta da maganar ka ta'ba sona arayuwarka , ka mantani ta qarasa fad'ar haka tana fidda huci mai zafi ."
"Dan allah kiyi hakuri nasan irin ciwo da zafin da Kike ji acikin zuciyarki ciwo ne kwatankwacin wanda nake ji acikin zuciyata nasan zafin ciwo da radadin kana son wani baya sonka ,wallahi na tausaya miki amman me yasa nuzla ?"me yasa sai ata zuciyarki zata kamu da so byn ni ina qaunarki ya kai hannunsa yana share mata hawaye"ata bashi da wannan lokacin wahalar da kanki da zuciyarki kawai zakiyi babu wannan tausayin a zuciyarsa a karshe ya rungumeta ajikinsa tsam yana shafa bayanta ahankali ahankali babu yadda ta iya dole ta kasance rungume ajikinsa domin tana bukatar wanda zai rarrasheta kuka take sosai tana rungume ajikinsa "ki daina kuka nuzla dan zuciyata bazata iya ganin hawayenki da damuwarki ina matukar sonki da zaki bani dama da sannu zaki daina son ata ki soni ya fad'a yana qara rungumeta gam ajikinsa ahankali ya mike tsaye tare daita ya nufi kofar fita tun kafin mutane su shigo su fahimci halin da suke ciki ."
Washegarin da misalin karfe tara na dare ata ya shiga d'akin mami sanye cikin fararen kayan bacci wondo da riga , hannunsa rike da black cup dinsa dake dauke da ruwan coffee ,yayinda dayan hannunsa Ke cikin aljihun wondonsa ya samu mami tsaye a gaban wordrobe dinta tana qoqarin rufewa tana ganinsa ta sakar masa murmushi tana cewa "Masha allah adamcy nan ya karfin jikin ?alhamd sweetheart ya qoqari dani ?kwana nawa ya saura ai Allah Allah nike Kayi tafiyar nan ka dawo mu sha biki ranar bani da dama zan aurar da d'a daya tilo ya girgiza kai kawai yana ajiye cup din hannunsa akan bedside dinta ya tsura mata tsumammun idanunshi yana kallonta tmkr wani maraya "yaakayi adamcy nan duk sanda kayi haka akwai abinda kake son fad'a "haka ne sweetheart kin fi kowa sanin halina alfarma nazo nema ."
"Alfarmar kuma ?mami ta maimaita abinda ya fad'a
"Eh ina neman wata alfamar a wajenki sweetheart "ina sauroronka Allah yasa zan iya ,ya marairaice murya sosai kafin ya soma mgn "dan darajan Allah sweetheart ki qara min lokacin auren nan wallahi wallahi wallahi !!! kinji na rantse miki zan auri yarinyar nan zabinki , wasu yan kwanakin kawai zaki qara min har naje na dawo dan zan dauki lokaci a france daga nan ma zan wuce hollond yi wasu abubuwa masu mahimanci a yanzu na samu sauyin lokaci amman kuma idan kina ganin zaa iya yin komai ko bana nan fine na amince a daura auren ayi komai amman da zaa bari na dawo sai nafi farinciki kasancewar ina son a hada auren dana hisham da nuzla yadda take kallonsa ya fahimci kamar bata yarda dashi ba "na rantse fa duk wanda aka rantse wa bai yarda ba shi din bana allah bane nayi miki wannan alqawarin sweetheart zan aureta ".
"naji amman har zuwa wani lokaci ni wallahi zaka sani jin kunya auren sauran kwanaki ace an daga "karki damu sweetheart idan akwai damuwa kawai ayi ko bana nan amman na fi son ina nan ,sai kace wata tsiyar zaka kulla ko kana ?ya dan ciza gefen lips dinsa "bansani ba ko zan iya kulla wani abu a auren da bana só ?kaji dashi tunani tayi karta je a daura yaki dawowa ya bar yar mutane da nauyi akanta gara kawai ta qara masa lokaci idan ya dawo sai ayi"Kwanaki nawa zan qara maka ?uhm ko Kmr wata biyu haka yayi "what ! kai adamcy ban yarda da kai ba ,wallahi ki yarda dani sweetheart bazan baki kunya ba, ba kuma zan saba alkwari ba I promise you ,ka cika alqawari adamcy ,karki damu sweetheart na ranse fa ,shikenan na yarda da kai ta fad'a kafin su fad'a hirar duniya a nan yake bata labarin nuzla murmshi mami tayi tana cewa "adamcy nah mai farinjini ."
Zaune mr ata yake agaban hajiya zulaiheart sanye cikin suit wondo da riga bakake jikinsa na fitar da wani kamshi na daga hankali fuskar nan nashi dake kwance da kasumba tayi fresh tayi kyau tana fitar da wani haske na dabam mai daukar hankali abun ka ga fari mutun sallama ya shigo mata dan sauran awa daya jirgnsa ya daga zuwa kasar france "Allah kiyayya ya tsare min kai , ka kular min da kanka sosai banda wasa da abinci aci abinci akan lokaci kamar yadda doctor ya fada "in sha allahu zan kiyaye sweetheart. Allah ya qara girma,ya qara miki lafiya da nisan kwana mai amfani kema ki kular min da kanki "Ameen summa ameen nayi maka wannan alkwarin Allah yayi muku albarka gabadaya ku "inji mami ,sannan taja musu addu'a suka shafa tana shafa masa na hannunta a fuskarshi ."a tare suka mike suka fito inda tawagarsa Ke jiransa a haraban gidan shi kadai ne zaune a bayan motarsa limozin sai driver a mazauninshi, hawaye ya tsiyayowa mami sanda motocinsa suke qoqarin barin gidan sai take jin kamar kar ya tafi amman kamar yau ne zai dawo gareta wannan karan mami ta kasa daurewa sai da tayi qwalla, gefe tayi da kanta tana dauke hawayenta ."
*****
Yau tsawon kwana uku kenan mlm yahuza yana zariyar zuwa gidansu maryama amman kamar kullum bai samu ganinta ba yau ma daga massalaci ya wuto kofar gidansu yana neman yaron da zai aika cikin gidansu ko cikakken minti goma bai yi da tsayuwa ba, sai ga yaya sadam ya fito daga cikin gidan , nan ya mika masa hannu suka gaisa "ina fatan dai lafiya kwana biyu nan kake zuwa gidan nan ?"Lafiya lau wajen maryama nake zuwa sai dai duk zuwan da nake yi bana samun ganinta ,shine dan naci kake ta zuwa ?to ya zanyi sadam tunda zuciyata ta kamu da matsanancin sonta duk da bani da tabbacin ko tana sona amman nasan tana son fitowa inda nake habib ke hanata fitowa yanzu dai taimaka min ka fito min daita dan nasan muddin habib na cikin gidan bazai barta ta fito ba ,murmushi sadam yayi yana cewa "kai habib hukuma ne wannan yaron bari ina zuwa !ya juya ya koma cikin gidan ya shiga side dinsu maryama ."
a parlour ya iskesu gabadaya suna hirar duniya ya zauna yana fuskantar maryama suka gaisa da aunty sannan maryama ta gaishesa haka ma habib ya amsa masu da "lafiya lau cikin sakin fuska ,ya gida da aiki sadam ?Alhamdulillah aunty mun godewa Allah yace yana duban maryama "ga malamin ku yahuza can a kofar gida yana jiranki yau tsawon kwana uku kenan ina ganinsa ashe wai saboda ke yake zuwa amman bakya fitowa."wata irin kunya ta kama maryama ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da zara zaran yatsun hannunta".
"ai ga d'an albarka dake hanata fita nan , ko shi zai aureta bansani ba ?yaro qarami dashi sai aikin nuna isa da iko ita kuma shegen son dan'uwa tana biye masa aunty ta qarashe maganar tana zabgawa habib harara ,habib bai ce komai ba ya tashi ya shige ciki dan matsawar yana zaune a falon bazai iya barin maryama ta fita zuwa koina ba km hakan zai sa yaya sadam yaji babu dadi "ai yahuza mutumin kirki ne kuma ga dukkanin alamun da gaske yake aunty tace "allah yasa shi wai habib dan matsalar daake ta samu akan masu zuwa suna tafiya né yake jin haushi "nima na fahimci haka amman in sha allahu komai yazo karshe dan nasan yahuza bazai mata haka ba nima gsky na yaba da hankalinsa maza tashi kije maryama karki dade maryama bata ji dadi ba ganin habib ya tashi ya barsu km tasan duk akan mgnr fita ne ,amman babu yadda ta iya yaya sadam da aunty suna da karfin iko arayuwarta ta mike ta fita ta bar aunty da yaya sadam suna magana bata san abinda ya cigaba da wakana atsakaninsu ba ."
acikin duhu ta sheida murmushinsa ganin hasken hakoransa ta dan saki ranta da kawar da damuwar fuskarta barkanki da fitowa gimbiya maryama "numfashi ta fesar "kai ya kamata a yiwa barka da zuwa da kuma sannu da qoqarin zuwan da kayita yi baka samun ganina da km qoqarin da kayi da iyayena last week na gode sosai " ya dan kyaleta "iyayenmu dai na gyara miki ." maganarsa ta dan mata dadi wannan yasa ta dan sakin fuskarta kad'an "ya kamata mu samu waje mu zauna ko can ne ya dan nuna mata wani dakali dake makoftansu ."
tare suka qarasa amman shi yaki zama ya tsura mata ido ya kamata ace kece kika fara zama sannan ni tayi shiru dan tuni ta gane manufarsa ta dan kallesa da idanunta cikin