********
"Adam zaune a makaken office dinsa dake cikin kasar hollond zagaye da makeken table wanda ke d'auke da file files dabam dabam sai qaramin frem din hoton mahaifiyarsa da mahaifinsa , sanye yake cikin riga fara sol da wondo baki sai yar saman suit dake sanye a saman farar rigar . ya d'auki wayarsa dake qara tun mintuna ashirin da suka gaba har zuwa lokacin daya d'auka yana dubawa miss call's ne rututu bama zai iya kirgawa ba , wasu yasan number's wasu kuma bai sani ba .
ya sauke numfashi sannan ya fara da kiran MB kasancewar shine wanda ya kirasa karshe MB ya d'auka yana cewa " hello friend ykk ? Lafiya alhamdulillah okay ai Ina ganin zan shigo cikin satin nan dan sweetheart ta matsa lallai nazo ayi mgnr aurena da wannan yarinya gashi ni wallahi har yanzu bana Jin son yarinyar Ina jin qinta sosai abinda ke Kona min rai yadda sweetheart ta nace akan lallai sai anyi auren nan kusa .
"kasan har cewa tayi bata yafe ba muddin ban aureta ba ."Kai gskiya Ina ganin ya kamata kayi wani Abu tunda kaji abinda tace maganar MB ta doki kunnensa ",amman ni aganina da an bari zuwa wani lokaci sai ayi auren tunda ba neman kai akayi dani ba " waya fada maka ?ai kuwa muna neman kai da kai mun gaji da ganinka haka dan haka karka fara cewar ba yanzu ba domin kuwa zaka samu matsala da mami kawai kabi umarni ka tunkari yarinyar da kanka."nace mata me MB ? yayi masa tambayar yana ciza lips dinsa na kasa , shiru shima MB yayi yana sauke numfashi "ya kake wata mgn haka ?ya sake tambayarsa a kufule "darajan da tsinuwar mami shine abun lura
shiru ATA yayi can yace "Anya kuwa zan iya MB gara kawai a d'aura auren zai fiyye min sauki akan na tunkareta da batu na soyayya dan har abada bazan iya ba ."
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
Book one
Last free page
*AYSHA A BAGUDO*
AREWABOOKS
AYSHAABAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 10
"ai Kuma shine babban matsalar abokina domin yarinyar itama ta kafe akan bata sonka amman nasan da zaka mata magana da kanka zata iya amincewa kayi k'okarin ka shawo kanta da kanka dan Allah ,ka kwantar da kai ka shawo kanta yarinya nan yar'uwarka ce jininka ce sannan ita din mace ce ,mace Kuma 'yar rarra..."
"ban son iskanci MB ya katseshi a matukar tsawace yana furzar da huci mai zafi daga bakinsa " sbd me zaka fad'a min hk ?" how dare you talk to me like that ? “
shiru mb yayi yana mamakin yadda abokin nashi ke saurin daukar zafi akan abinda bai kai ya kawo ba "to me ma ya fad'a da zai dauki zafi haka ?mr ATA ya mike zumbur daga Kan kujerar da yake zaune tare da tura kujerar baya tamkar ita tayi masa laifi ya soke hannunsa daya cikin aljihun wondonsa "Ita din makiyata ce ita din ba jini bace karka sake fad'a min cewar yaruwata ce ko jinina ce Ka dinga sanin irin maganar da zaka fad'a min taya da girmana da mutuncina zakace na tunkareta common mace daita yarinyar da umarni kawai zan bata kuma dan dolenta tabi ,ta Inda yake shiga bata nan yake fita ba "
Shikenan kayi hakuri abun ne yazo hk amman dai ka k'okarta ka....."dan Allah malam ka maida hankalinka jikinka sai wani qoqarin son saka min magana abaki kake wannan ai mgnr banza ce "ka tsaya ka saueareni mana nifa hankalina yana jikina kai dai.... "dan Allah malam kayi min shiru babu wani saurararka da zanyi a yanzu ".yana gama fad'ar hk yay disconnecting din Kiran yana huci ..."
"Nonsense girl kawai ai bata Isa ba ,bata ma kai wannan matsayin ba shi da mata ke bi suna kuka suna rokonsa ko gaisawa su dingayi bai kaskantar da kanshi ya amince ba bare har ya ajiye girmansa matsayinsa komai nashi yace yana son mace macen ma irinta ko cikakken minti biyar bai yi da katse kiran ba kiran hjy zulaiheart ya shigo sai da gabansa yayi wani irin mummu nar fad'uwa kusan yanzu duk sanda zai ga kiranta sai hankalinsa ya tashi saboda yasan Kiran baya wuce akan wannan banzar yarinyar bane ."
ilai kuwa yana d'auka da maganar ta fara "Adamcy kana son ganin 'bacin raina yayi saurin girgiza mata Kai kmr yana gabanta "wallahi zan cire hannuna acikin lamarinka idan haka kake so "kiyi hakuri sweetheart inshallahu zanyi yadda kike so "kullum abinda kake fad'a kenan ka kasa aiwatarwa dan hk ka shirya shigowa nigeria dan cikin satin nan maryam zata dawo Kuma tana dawowa zaayi mgnr aurenku da baba babba har ta gama maganarta bai sake cewa qala ba ganin tayi shiru shima yayi shiru yaki cewa komai duk da yaso komai yaya ya bata hakuri amman zafin da zuciyarsa keyi ta hanashi aiwatar da hakan har kusan minti goma tana jin yadda numfashinsa Ke sauka da karfi kamar wanda yayi gudun tsare da kyar ya iya fezgo magana "sweetheart akwai abubuwan da nake son na kammala bazan samu damar dawowa nan kusa ba zaku iya yin .."
"No babu wani uzuri da zanyi maka kayi duk abinda zakayi ka gama ka shigo cikin satin nan shiru ya sake yi yana sauraronta tana gama fad'ar haka ta katse Kiran bayan wayar ta katse ya bita da kallo zuciyarsa na rawa ."ajiye wayar yayi akan makeken table din dake office din ya buga wani uban tagumi wanda dagani na takaici ne."
ya sake had'e fuskar nan tashi sosai wani irin bakinciki yake ji acikin zuciyarsa, ji yayi kamar zuciyarsa zata kama da wuta yana matukar jin bakinciki abinda mahaifiyarsa take bukatar yayi ,shi da yake adduar komai ya watse a manta komai amman ita kullum burinta bai wuce taga faruwar wannan auren ba .
banda 'bacin rai mai Kona zuciya babu abinda yake ji mikewa yayi ya shiga zariya a office din yana zagaya koina yana zurfafa tunaninsa kafin ya soma magana shi kadai "ya zanyi ?me zanyi ?taya zan soma rayuwa da yarinyar da kake qoqarin amincewa aurenta ? sosai kwakwaluwarsa ta shiga tunani neman mafuta dan dole yasan abun yi kafin mahaifiyarsa tayi masa wannan auren mr ATA ranar kwana yayi yana tunani ."
******
Bayan kwana biyu maryam ta dawo daga Abuja murna gurin nana hauwa'u hjy zulaiheart da sauran 'yammatan gidan babu magana dan sunyi matukar kewarta sosai hira ce ta yaushe gamo ta barke a tsakaninsu sai yamma suka bar gidan haka ma washegari suka cika gidan har da rukkaya makociyarsu anan grã gidansu yake asalinsu nufawa né suna cikin hira rukkaya ta Kalli maryam sannan ta Kalli diyana da nuzla tace "nafi kowa Jin dadin dawowar marsi bari na baku labari nayi wa marsi saurayi kyakkyawa ajin farko ."
maryam ta kalleta tana kwa'be fuska cike
da takaicin Jin maganarta yayinda itama rukkaya
ta kalleta tana sakar mata murmushin jin dadi .
Sai dai a matukar wulakance maryam ta
cigaba da kallonta kamar ta rufeta da dukan
mutuwa sannan ta fara magana cikin fushi da 'bacin rai "bangane kinyi min saurayi ba ance Miki bani da saurayi ne ko ya ? ke da duk fuskarki ta dame da bille kota Ina an watsa miki shi ba'a ce anyi miki saurayi ba sai ni da fuskata take lafiya lau babu zane ko daya ,Kalli bakinki duk a warwatse kamar lefen sakarya shine zakice kinyi min saurayi , karki qara min irin haka wallahi banaso ai kinfini bukatar saurayi ."
Gabad'aya suka kwashe da dariya rukayya kuwa tsayawa tayi tana kallon maryam da mamaki nana hauwa'u kam har da zubewa kasa tare da rike ciki dan dry ."Ina ganin dai baki san aljanu sun shigi marsi ba ko ? ai babu damar ayi mata maganar maza sai hankalinta ya tashi ." nifa ba haka bane Ina da zabi acikin zuciyata Ina da ra'ayin irin mijin da nake son aure ba kowani shasha ba amman dai na barwa zuciya irin mijin da nake so Ke mai bille sai ki rike saurayin dan kinfini bukata ."
rukayya ta Kalli nuzla nuzla ta kalleta sannan a matukar fusace rukayya tace "karki qara cewa fuskata anyi min bille "to karya ne ba'a yi miki ba ? "idan bakya so nace miki hk nima ki barni da batun wani saurayi can tun da bance miki nayi ina son ba wadan da nake dasu ma sun Isheni bana neman qari sun dade a d'akin suna hira akarshe duk suka watse suka kama gabansu."
******
Karfe shabiyu daidai jirgin Mr ATA ya sauka a lagos a haraban gidansu tun kafin jirgin ya k'arasa sauka security's dinsa ke zagaye da gurin har sanda ya sauka , a hankali ya mike yana gyara zaman rigarsa Sannan ya fara takowa daga matattakalar bene yana taku da kyar cikin tafiyarsa nan nashi na Koda yaushe wato tafiya cike da alfarma da izza yana d'aga kafafunsa yana shakar iska da kyar tare da hura hanci escort dinsa already sun fito suna nan tsaye suna jiransa duk Inda ka duba acikin haraban gida masu aiki ne ke Kai kawo suna aiwatar da aikinsu."
yana qarasa saukowa escort dinsa da security's sukayi masa caaaa har zuwa Inda yake tsaye Inda ya fara taku suna biye dashi har zuwa bakin kofar shiga cikin parlour'n mahaifiyarsa na d'aya , yana isowa gurin yaja ya tsaya d'aya daga cikinsu mai suna muzammil ya bud'e masa kofar ya shiga yabi bayansa shi kad'ai rike da bakar jaka ATA bai tsaya akoina ba sai a babban falon mahaifiyarsa ya shiga ya zauna ya kame akan d'aya daga cikin kujerun falon ya d'aura hannunsa d'aya akan gwiwarsa yana d'an jijigawa yaronsa muzammil ya rankwafo ya ajiye masa jakarsa ya bashi izinin tafiya ya juya da sauri ..."
A hankali mami tayi sallama cikin had'ad'd'en falon a zaune ta samesa akan kujera ya lumshe lumtsatsun idanuwanshi ,da kyar ya bude baki ya amsa sallamarta batare daya bud'e idanunshi ko matsowa ba har sanda ta zauna akan kujerar dake kallonsa tana jin sanyi da farinciki mara misaltuwa da ganin kamilallen danta mai nagarta da haiba illarsa dai rashin ajiye iyali da miskilanci da zafin rai duk wannan farinciki daga ciki take jinsa dan bata bayyana shi ba .
a hankali ya bud'e lumtsatsun idanunshi ya mike ya k'araso gabanta ya rusuna har kasa "mun sameku lafiya sweetheart? Wani sanyin dadi Ya ratsata ta kai hannunta kanshi "alhamdulillah ka sauka lafiya ya aiki Ya fama da jama'a ? ta fad'a fuskarta babu yabo babu fallasa "alhamdulillah sweetheart yayi magana yana matukar tausayin Kansa dan yasan tunda ya zo ya dinga cin karo da matsaloli kenan dole sai yayi hakuri dan magana daya ce za'a yita ana mai maitawa ,."
A natse ya mike ya koma mazauninsa ya zauna
yana neman layin M.B da sauran friend's dinsa kafin kace me hjy zulaiheart tasa an cika masa gabansa da kayan itatuwa dabam dabam sai dai babu wanda ya d'auka yaci illa amsa waya da yake ta bangare damba dabam , nana hauwa'u ta shigo ta gaishesa cike da ladabi "yayanmu Ina yini ka dawo lafiya .?"
"Lafiya auta ykk ya fad'a atakaice" lfiya ta bashi amsa da haka sannan ta mike ta koma ciki dan yadda fuskarsa take a murtuke nan komai zai iya faruwa , haka rashida da muna yaran baba qarami sun shigo gaishesa a mutunce , babu yabo babu fallasa ya amsa haka akayita shigowa yi masa sannu da zuwa sai dai ya amsa atakaice ba tare daya bi ta kansu ba maryam ce kawai bata shigo kawo gaisuwa ba har sanda MB ya k'araso sai daya yi sallama a bakin kofar falon aka bashi izini shigowa sannan ya shiga .
ATA bai motsa daga Inda yake ba har MB ya shigo ya zauna cike da tausayin abokinsa dan kallo d'aya zaka masa kasan baya tare da walwala da farinciki har wata siririyar rama yayi "ATA..!" ya kira sunansa anatse ATA bai amsa ba illa zuba masa kwayar idanunshi da yayi yana sauraronsa "yana ga duk ka rame ? shiru yayi bai ce uhm ba bare uhm uhm sai dai ga dukkanin alamun hankalinsa na kanshi "dan Allah ka kwantar da hankalinka komai na duniya mai wucewa ne idan kabi komai a sannu da sannu komai zai zama normal ."
wani huci numfashi ya saki yana sake tsaida idanunshi da gbdy suke cikin damuwa akan mb
sai da yayiwa MB kallon wasu mintuna sannan ya furzar da abinda ya tsaya masa a makoshi mai mugun daci cikin son danne duk wata damuwarsa yace "na rasa yadda zan cire wannan damuwar MB "kallonsa MB yayi yayinda ATA ya Maida idanunshi ya lumshe "Ina zanganta ?ya furta a saman labbansa cikin tsananin damuwa "wa kenan ..?Idanunsa dake lumshe ya d'an bud'esu da kamar bazai yi magana ba sai Kuma ya furta ", princess.."
murmushi MB yayi "ka iya fad'ar sunan nan tamkar kai ka fara tsarashi a duniya "zaka ganta inshallahu Ina maka adduar ta zamo mutun ce ba aljana ba , sai abu na gaba ka fara da abinda mami take so "bana jin zan iya MB zan dai ta bin sweetheart a hankali har sanda zan samo yarinyar ko kuma na samo wata dabam amman wannan guntuwar yarinyar bazata zamo mata a gareni ba sun dade suna tautaunawa kafin daga baya sukayi sallama duk Kuma maganar da suke akunne mami sukayita ,
dan haka ta shaka sosai tun a lokacin ta fara shirya abinda zata masa ."
Tunda masu aikin gidan suka san ATA ya sauka kowan nensu ya shiga hankalinsa hatta shigowarsu part din hjy zulaiheart ya taikaita sannan komai cikin sauri suke yi kasancewar sun san shi dan Oya oya ne duk da ba abincinsu yake ci ba sai na mahaifiyarsa kuma bata zauna ba har washegari tana kan yi masa hidimar abincin da zai ci tare da abokansa Amar, shawul, shamsu MB sun baje a falonsa sai kwasar abinci suke Amar yace "friend duk fa matar da ka aura muddin bata iya girki irin na mami ba zaku samu matsala daita ",Sosai kuwa dan ni dai Ina ganin zan kawo fedy gurin mami a sake bata class na mussaman dan wanan girki yayi inji cewar MB " suka sa dariya banda ATA dake rike da waya yana duba mahimmam bayanai masu shigowa .
Sai daya rage mahimmam abubuwansa sannan
ahankali ya motsa lip's dinsa "gaskiya ne Ina son macen da ta iya girki kuma qala dabam dabam shiyasa kuka ga Ina dojewa auren yarinyar nan dan nasan babu abinda ta iya sai salo da rike waya da shiga social media ,ni Kuma ta Inda za'a samu matsala dani kenan dan bazan yarda da rashin kamun Kai ba.
gbdy suka gyda Kai batare da sunce komai ba sai can shawul yace "ai idan princess dinka ka aura ko bata iya girki ba zaka zauna daita haka har karshen rayuwarka ATA ya sauke numfashi kawai batare da yace uffan ba "kayi shiru ko ba haka bane ? Inji cewar MB "ka'ajiye wannan magana bama zata zo a haka ba am very sure ta iya komai ." Shawul yayi sigili yace " mai kmr mrym me zaiyi da wannan princess din taka ya watsa masa wani mugun kallo "ra'ayina kenan princess bana son mace irin wannan yarinyar da ake kokarin lika min yayi mgnr yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa.
"Wai Kai wayace maka ana auren mace mara kiba a yanzu Kai gaka ba jiki ba , Kai Kashi ita kashi kuzo Kuna haihuwar kasusuwa Kai da zaka samu mai nama irin Marym chubi daita komai zamzam inji cewar Amar gbdynsu babu Wanda bai dara ba MB kam har da fadowa yayi kasa daga kan kujera dan dariya "ko jini zamu dinga haifa ba kasusuwa ba. nafi sonta akan wannan mai siffar aljanu guntuwa gata nan dai fari ne kawai ya taimaki rayuwarta.
nana hauwa'u da mryam dake tsaye a bakin kofar falon hannu nana hauwa'u rike da tiren silver mai d'auke da gasashen kifi anyi raping dinsa ita kuma mryam na rike da tire na harish suka Kalli juna dan sunji abinda suke tautaunawa daga ciki , naunayen ajiyar zuciya nana ta sauke tace "mu shiga sister ta fad'a tana rike tiren hannun maryam dake k'okarin subucewa qirjinta na dokawa tace "a'a sister ke dai ki shiga ke kad'ai bari na tsaya anan har ki fito banason na shiga Ina jin tsoron kar ya disgani agaban abokansa ta k'arasa maganar tare da d'aura tire dake hannunata akan tiren hannun nana hauwa .
suna tsaka da hira suka jiyo sallama a bakin kofar falon MB ya bada izinin shigowa tare da komawa mazauninsa ta shiga a natse ta gaishesu cike da ladabi sai dai kallo d'aya zaka mata kasan ranta a 'bace yake ta tsani taji yayanta yace bai son mrym ko aibantata bare yau a gaban abokansa ."
Amar ya washe baki yana dubanta kana ya soma mata wasa kasance warsu abokan wasa "a'a gasu cubi hauwa fa ,farar mace alkyalbar mata Ina ganin nida madam zamu lalla'bo muzo ki sammana man da kike shafawa kullum ke da maryam kmr bakwa fita rana, gaku na nan dau kmr yanzu kuka sauko daga sama."
tayi masa banza tana jan tsaki a ranta "Ina kika baro mrym dan nasan ke daita 5&6 ne? ta sake sharesa tana kokarin ajiye tiren hannunta wayarta dake rike a hannunta tayi kasa zata fadi madadin ta bar wayar sai tayi k'okarin rikota Aiko tiren gbdy suka sullube a hannunta sukayi kasa tiren kifi ya kife nan take mai ya fara malala gabanta ya buga da karfi nan take jikinta ya kama rawa ta d'ago da sauri ta Kalli Inda ATA yake