An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page1
......." Katanfarin company ne da tsayawa fadar iyakarsa bata lokacin ne domin mutun bai Isa ya fadi adadin girmansa ba , hatta shi Karan kanshi mamallakin company bazai ce ga iya adadin girmansa ba adalilin kullum sake siyan wasu bangaren yake yana hadewa da company .
"mutane kimanin million biyu da wani abu ne ke aiki a karkashin wannan maikatar daake sarrafa karafuna sanye da kayan aiki ."
mamallakin wannan company ya mallaki companies masu yawa sai dai akwai guda daya wanda ya kasance hadin gwiwa ne tun mahaifinsa na raye suke kula dashi tare da ya'yan 'yanuwa ."haka ma bayan babu ran mahaifinsa bai wuftar da al'amarin wannan company ba ya cigaba da kula dashi saboda yana matukar qaunar company a cikin zuciyarsa dan ba qaramin wahala mahaifinsa ya sha akansa ba kafin ya samu daukaka da kar'buwa a duniya gabadaya ba ."
A.G.C"wato Abdullahi group's company,company ne daya amsa sunansa, company né da suke da duk wani nau'in kayan sakawa ajiki ,kama daga na sarakuna ,manya attajirai ,shuwagabanin na duniya , kayanmu na gargajiya har ma dana turawa wato suit da kowani irin design's na tsarkoki ,daga ko wacce kasa ka bukaci kayansu zaka samu cikin sauki sannan kuma suna zana duk irin design's din kaya da tsarkokin da kake so har ma da zanen kanfanunnuka ,zanen hotuna kai duk wani nau'in na zane suna da kwararun masu zanawa wuyarta ka zaba desing's zasu yi maka ."
daya daga cikin maaikatan gurin ya dago yana kallon shugaban da aka d'aurawa halakin kula da ma'aikatar karafuna wanda isowarsa kenan "barka yallabai "barka dai malam mashkur fatan komai dai yana tafiya kamar yadda aka tsara ? dan sam bana son a samu wata matsala sannan bana son a samu sa'banin akan karafen can ka tabbatar an cigaba da samun irin wadan can, sannan wadan can kayan Ina son akawo su da wuri dan mai gida zai .... "bai kai ga karasa maganarsa ba sautin qarar jet din mai gidansa ya katseshi hakan yasa a hankali manager malik ya d'aga idanunshi dake manne da bakin glass zuwa sararin samaniyya cikin sauri yace "shikenan kaje ka cigaba da kula da duk masu aiki ga mai gida nan ya iso ."
ADAM TARIQ ABDULLAH kenan, shugaban kafanunnunka ATA companies ...... matashin dan kasuwan da yafi kowani dan kasuwan bahaushe kudi a Duniya kallo daya zaka masa ka fahimci matakin shekarunsa, bazaka kirashi da yaro ba haka zalika bazaka kirashi da dattijo ba shi din matashi ne me kimanin shekaru talatin da bakwai a duniya fuskar shi babu yabo babu fallasa kasancewar haka yanayinsa yake, kullum haka zaka ganshi fuskar nan tashi a hade tamkar hadari sai dai na wannan lokacin ya zarta na sauran lokutan baya wanda hakan ya faru ne akan abinda ke dawainiyya da rayuwarsa."
.Adam Tariq abdullahi wanda ake kira da (mr ATA) a duk fadin duniya kyakkyawa ne ajin farko mai tsantsar kamala da kamewa tattare da haiba sai dai sam bai da faraa komai cikin zafin rai da zuciya yake aiwatar wa , " rayuwarsa rayuwa ce dake da bambamci data sauran mutane , shi din mutun ne miskili mara saukin Kai dan idan kayi Kuskuren shiga track dinsa zaka gane baka da wayo dan ya iya duk wani nau'i na tozarci da rashin mutunci tare da disga mutun sabanin mahaifinsa da mahaifiyarsa da sauran yanuwnasa da suka kasance masu tsanani saukin kai tausayin mutane tare da tallafawa bayi mabukata ,fari ne sol dan babu digo tabo ko daya ajikinsa hatta bakin kwayar idanunshi gauraye yake da fari ,dogo ne sosai mai matsakaicin jiki , da kyakkyawar fuska da idanuwa , fatar jikinsa na ya'yan masu kudi sai sheiki yake daga samansa har kasansa babu makusa sannan babu alamun babu a tattare dashi yana da matakin karatu na Phd akan kasuwanci kuma har lokacin yana kan karatu bai ajiye ba ,shine ya tattara gabadaya kyawun mahaifiyarsa hajiya zulaiheart da mahaifinsa marigayi barrister Kuma shararen dan kasuwa Alhaji Tariq Abdullah ."
"duk wani ma'aikacin dake aiki agurin tsayawa yayi cak ya kasa cigaba da aikinsa kamar yadda aka umarcesa saboda kwadayin ganin wannan kyakkyawar fuska har sanda jirginsa mai saukar ungulu ya sauka idanunsu na kanshi , sai da jirgin yayi kamar minti biyu da tsayawa sannan a hankali kofar jirgin ya bude Inda ya matso a hankali shi bai fito daga cikin jirgin ba haka zalika shi bai zauna sosai ba yana kada kafarsa daya cikin nuna Isa da izzar shi din wani ne .a zahirin ake iya ganin gangar jikinsa wanda hakan yasa kayan dake sanye dashi suka bayyana, Suit ne wando da riga ruwan madara yayinda yar cikinsa ya sakance baki kafafunsa sanye da black shoe's haka idanunshi na manne da farin glass yana qarewa haraban gurin kallo tare da kallon ma'aikatan dake aiki ."
a natse ya fito hannunsa daya na cikin aljihun wandonsa yana taku daya bayan daya cikin Isa da izza yayinda escort dinsa ke gefen hagu da damansa kowannensu sanye da suit iri daya da makaman tsaronsa wato bindigu ."daya daga cikin escort dinsa na rike da wata karamar brief case kalar suit din jikin Mr ATA ." manager malik ya karaso da sauri cike da ladabi ya tsaya a gabansa "ranka shi dade mr ATA barka da zuwa? shiru ne ya biyo baya na kamar second biyar sannan a hankali ya motsa labbansa da kyar "barka m . malik ya kokari ?." alhamdulillah sir " m.malik ya fada yana mika masa hannu Mr ATA ya mika masa dayan hannunsa dake waje yayinda har lokacin dayan hannunsa ke cikin aljihun wandonsa " gaskiya naji dadin yadda na iske kamfani kowa na kan aiki Wanda nasan duk cikin kokarinka ne dan ga dukkanin alamun aiki na tafiya yadda ya kamata ya karasa maganar yana zare hannunsa cikin na malik ya tsotsa bayan keyarsa sannan ya cigaba da magana yana tafiya a natse "kana yin yadda ya dace daman ba daidai bane tsuntsu ya cinye tsaba batare da yayi aiki ba "ai yallabai dole ayi aiki yadda ya kamata dan kai din na dabam ne sannan bakayi abinda tsuntsun zai cinye tsaba batare da yayi mata aiki ba "ka ajiye wannan maganar na gama daita yanzu, ma cigaba daga baya " m.malik ya gyada masa Kai alamun yaji cike da ladabi yace "sir mu karasa zuwa office mana ? runtse idanunshi yayi kawai batare da yayi kokarin aikata hakan ba ."
bayan kamar mintuna talatin ya numfasa "Petir da sinadarin gas tsawon shekara bakwai kenan nayi Ina nema a wani yakin a cikin apapa ban samu ba sai gashi kwatsam na sameshi bayan na kashe billiyoyin kudade , sai dai ka taki sa'a dan Kai na zaba a matsayin wanda zai kular min da gurin ..."
duk wannan maganar da yake har lokacin bai zauna ba tafiya yake ahankali a haraban ma'aikatar "Kai amman gaskiya naji matukar dadi ranka shi dade sai dai da za'a barni anan na cigaba da kula da bangaren karafai zai fi min , dan ba lallai ka samu Wanda zai kular maka da gurin nan yadda ya kamata ba ."
"karka damu m. malik already y ma nazo da wanda zai cigaba da kulawa da nan din ,adaidai karshen wannan maganar tasa ya samu guri ya zauna akan wata hadaddiyar kujera mai runfa zagaye da kujeru na alfarma dama Kuma duk sanda bai ra'ayin shiga office dinsa ba idan yazo anan yake zama ya d'aura hannunsa daya akan table , Shima m. malik ya samu guri ya zauna yana fuskantar me gidansa da sauraronsa "na zabeka ne saboda baka da wasa akan aikinka gashi kana da rikon amana da mazantakan kula da komai fatana ka cigaba a yadda na sanka ."
Ya Kai hannunsa na hagu bangaren hagunsa , nan take escort dinsa me rike da brief case ya daura brief case din hannunsa akan table ya bude ya ciro wasu manyan freme mai dauke da zane day day har guda goma Kuma duk abu daya ne zane acikinsu .
Mr ATA ya dauka ya tsurawa zanen lumtsamtsun Idanunsa masu fitar da zaiban haske tsabar hasken dake cikinsu, second biyar ya dauka yana kallon zanen sannan ya numfasa ya ajiye akan tablet din gabansa yana cigaba da kallo "ko ka samota m. malik ? ko samun labarin wanda ya santa ? "Ina har yanzu dai tukun nan yallabai amman Ina iyakar kokarina kuma zan cigaba wai shin wa...."babu ruwanka da wannan hurumin m.malik dan ....." qarar daya daga cikin wayoyinsa ne ya katse shi yayi shiru batare daya ci gaba da magana ba yana jiran a miko masa wayar escort din dake rike da wayoyinsa ne ya miko masa "my sweetheart " .ya fada tare da rusunawa mr ATA .
da sauri mr ATA ya amshi wayar a hannunsa ya manna a kunnenshi ya mike tsaye cikin tsananin tashin hankali da girmamawa ya fara tafiya yana magana a natse "inna lillahi dan girman Allah sweetheart ki qara hakuri dani , ki Kara bani lokaci zan yi qokari ,okay I know nasan kin yi hakuri dani amman Ina da tabbacin wata rana zakiyi farinciki sosai, ina kan neman matar da zan aura ni dai ki tayani da addua murmushin gefen baki ne ya bayyana akan fuskarsa adalilin uzurin da tayi masa nan take ya samun natsuwar zuciya ya cigaba da abinda yake ."
*******
LAGOS
Da misalin karfe biyar na yammacin ranar laraba "Yammata ne su hud'u zaune a cikin wata hadaddiyar mota kirar land cruiser prador ,mutun biyu zaune a gidan bayan ,yayinda biyu ke zaune a gaba akan titi masha dake surelere , humaira dake kusa da mubina ta Ciro wayarta iPhone 12 Pro max acikin jakarta ta soma d'aukarsu snap tana ta'ba kafad'ar mubina dake driving dan ta shigo cikinsu ,mubina tayi murmushi ta dan shigar da fuskarta tare da d'aga yatsunta biyu kana ta maida hankalinta kan tuki ."
tafiyar mintuna ce ta kawosu Apapa gra suka tsaya a gaban wani makeken get da aka rubuta ABDULLAHI ESTATE tare da yin hon ,daya daga cikin masu gadin estate din ya leko adaidai lokacin da mubina tayi kasa da glass din motar ganin yaran estate din ne ya koma da sauri ya bude .mubina ta danna hancin motarta ta shiga Katafaren estate din nansu mai d'auke da gidaje fiye da ashirin sama da kasa sai dai acikin gidajen akwai guda daya wanda ya bambamta dana saura wato gidan hjy zulaiheart ."
yanayin gidanta ya bambamta dana saura ne sakamakon marigayin mijinta yafi sauran yanuwansa tarin dukiya kuma ko bayan mutuwarsa yaranta sun cigaba da qawata mata gidanta kullum cikin gyara yake da canza kayan ado na zamani , 'yan aiki ma sun bambamta dana saura ,yan aiki guda goma sha biyar ne ke zariyar kula da kowoni bangare na gidanta ,sannan kowannensu sanye da fararen kaya masu ratsin baki .
babu mutun ko daya na cikin ahlin estate din dake tsaye akan kafafunsa domin yin aiki sai dai dan aiwatar da ibada , kowa acikin gidan dan gata ne hatta bakin dake zuwa gidan jin kansu suke tamkar ya'yan wasu saboda mutuntaka na mutanen gida, tsarin gidan hjy zulaiheart kuwa kace a gidan turawa ne kowani bangare shirye yaki da kayan alatun na more rayuwar duniya ,haka ma kofar da zata shigar da mutun bangaren hjy zulaiheart tsare yake da securities guda biyu masu duba jikin mutane koda zaa shigo da wani abun cutarwa .
mubina ta dauki hanyar inda aka tanada domin paka motocin bangaren gidan hjy zulai nan take sauran yanuwanta kuma kawayenta suka hada baki gurin cewa "ya haka kuma ?"Sai data dan marairace fuska sannan tace "dan allah mun dan shiga muga su marsi kwana biyu bamuga juna ba daga nan ma sai mu tsaya muyi sallar magrib da ishai sai kowace ta kama gabanta dake duk suna shiri da juna yasa babu wacce tayi mata mutsu har tayi parking tare suka firfito daga cikin