ya furta yana miƙewa ya bar Falon, da kallo ta bisa tana girgiza kai"Anya Yayah Naja'atu zan iya bayar da auren Maheer ga Bobbi?"
"Coz of what da ba zaki iya bayar da Maheer g Bobbi ba? bayan magana ta ƙare saura fa 5 days aurensu ya ɗauru ,ita Maheer ɗin ba mace bace da ba zata iya sace zuciyarsa ta hanyoyi daban_daban ba?"
dogon Numfashi Mammi taja tana furta "duk abinda kika lissafa zata iya mana, sai dai ina ƙara tsoron wulaƙancin Bobbi da kuma kishiyar ta don kin san talakawa da baƙin hali,yanzu haka baki san abinda take shiryawa ba, dole fa mu tashi tsaye Yaya Naja'atu ina tsoron kishiya ta kassara man yarinya"
dariya ta fashe da ita tana furta "su ɗin talakawa wane power garesu? da zata iya dukkan abinda kika lissafa, ai tun da ta shigo gidan na wllhy harta iyayenta ta rabu dasu dan ko nan da can ba zan barta taje, ba sannan sai na mayar da ita jakar gidan nan"
*MUNEEBBA*
duƙe take cikin rana, ga Uban wankin dake gabanta, tana cizga sai faman miƙewa take tana sharce zufa, ga Aunty Meera dake zaune bisa kujera cikin inuwa tana korawa da lemu hannunta riƙe da wayar wuta, jin bayanta ya riƙe ya saka Muneebba ɗagowa tana yarfe hannunta tare da sharce zufa tana sauke wahalallen numfashi
"Ke!!!! uban mi ya kaiki ɗagowa ba cewa nayi ba dukkan wankin dake gabanki sai kin wanke sannan ki ɗago"
hawaye ta share tana furta "yi haƙuri bayana ne ya riƙe shi yasa na ɗago"
Taɓe baki Aunty Meera tayi tana furta "Bayan naki ya ƙille idan y tashi ba damuwata bace"
ba tare data ƙara cewa uffan ba ta mayar da hankalinta kan wankin ga cikinta dake ta faman uban ƙugin yunwa don Aunty Meera tace ba zata ci Abinci ba sai ta idar da wankin dake gabanta, tabbas ta san da ace a gidan Nazeer take da tana can suna gudanar da tsabtacciyar soyayya, sai dai ƙaddararta data juye a bisa yacce ta santa, tazo mata a bai _bai tare da sanyata cikin halin rayuwar da batai tsammani ba, tabbas wannan auren sai dai ta kirasa da auren Bauta domin bautar ce ta kawota,
cikinta taji yana juya mata da wani kalar tuƙar Amai ga gaɓoɓin jikinta ji take kamar an mata shegen duka,jiki ba ƙwari ta ci gaba da wankin, har ƙarfinta ya ƙare sannan ta ida,
miƙewa tayi tana tafiya kamar zata faɗi saboda jirin dake son yada ita, wajen Baba Sa'a ta nufa tana zama, cikin yanayin tausayi Muneebba ta kalli Baba Sa'a tana faɗin "Baba Sa'a dan Allah Abincin zaki bani nafci yunwa nake ji"
"Ayya ƴar nan Abinci kuwa tuni ya ƙare sai dai ki haƙuri a girka wani, idan kuma ba zaki iya ba kije wajen Hajiya ta sam miki"
Jiki a mace ta miƙe dan babu yadda ta iya dole taje, kamar wacce ƙwai ya fashe mawa haka ta nufi part ɗin Mommi a hankali ta tura ƙofar Falon bakinta ɗauke da sallama
daga Mammi har Mommi shiru su kayi suna jifanta da ƙasƙantaccen kallo wanda ya saka ta kauda kanta gefe guda tana haɗiye abinda ya tsaya mata a maƙoshi, durƙusawa tayi tana sadda kanta ƙasa tare da furta "Hajiya kamar yadda Allah ya temakeki ki taimakeni wllh yunwa nake ji idan ban ci ba ji nake kamar zan mutu dan Allah ki bani Abinci naci" ta ƙarashe zancen tare da saukar wasu hawaye
kallon takaici Mommi ta bita dashi tana furta "A gidan uwarki zan baki Abinci ai wallahi wahala ce kin ɗaura aure da ita kenan shegiya jakar banza matsiyaciyar talaka, ƴar gidan talakawa marar Asali da galihu, har yanzu baki fara ganin komai ba na yankin azaba, wallahi sai kinyi da na sanin shigowarki gidan nan"
sosai mu nanan kalmomin da Mommi ta jefeta dashi suka tsayar mata a rai tare da ɗago idanunwanta tana duban Mommi dasu wacce ke ƙara jifanta da kallon tsana, "Fice man a Falo ko nayi miki shegen dukan da ba za'a iya ganeki ba shegiya mai kama da Mayun daji"
jiki a mace ta miƙe tana fita daga Falon,zuciyarta na mata wani kalar suya da zafi, ta ina zata fice ta bar wannan baƙin gida wan da y zame mata baƙin kurkuku, da ƙyar ta idasa fita daga Part ɗin tana nufar Garden ta nemi inuwa tana zama,Idanunwanta ta ɗaga tana kallon sama hawayen tausayin kanta na zubo mata da kuma tunanin Mamma da Yah Kahabir,
zamewa tayi daga zaune tana kwanciya tare da dafe cikinta wanda take jin tamkar babu komai a cikinsa, ga jikinta dake ta faman Kyarmar masassara,
Jin ƙarar tafiya na tunkaro inda take ya sakata tashi da ƙyar tana bin inda take jin sautin tafiyar da kallo, Tafiya yake cikin ɗan sassarfa jikinsa sanye Da Kayan Pajames Kafaɗar sa rataye da School bag
miƙewa tayi jikinta na rawar sanyi da karkarwa ta tunkaro ABEED tana zubewa a gabansa ",Ƴal laɓai dan Allah kai taimakeni da Abincin da zan ci yunwa nake ji" ta ƙarashe zancen da ƙyar sbd galabaitar da tayi
ɗago da fuskarsa yai yana kallonta tabbas dai wannan Ma'aikaciyar gidan ce "Amma taya kika zauna da yunwa baki ci Abinci ba, naga dai gidan ko ina wadace yake da Abinci" ya faɗa yana ƙarewa Muneebba kallo
"Naje ko ina sun ce babu ya ƙare sai an girka wani" ta faɗa tana kallonsa
Jim yayi sannan yace "ok bani minti biyu" da to ta amsa tana komawa inuwar ta zauna
bai fi minti biyun ba sai gashi ya fito da Flat ɗin Abinci da ruwa, waje ya samu ya zauna da murmushi ɗauke a fuskarsa ya miƙa mata, hannunta har ɓari da kyarma yake wajen amsar Abincin, buɗewa tayi taga Shinkafa ce da miya sai Salat da zaƙo_zaƙon nama a ciki, spoon ɗin ta fidda tana gyara zama tare da bismillah ta fara cin Abincin ba ƙaƙƙautawa hannu baka hannu ƙwarya, tun da ta fara cin Abinci yake kallonta da mamaki, don duk uban Abincin dake shaƙe a Flat ɗin sai da ta cinyesa tas, sannan tabi da ruwan sanyi,wani ni'ima taji na saukar mata, ɗago da idonta tayi tana furta "Nagode"
"Don't mind but You New house mad? ya tambayeta da ƴar dariya
Itama cike da jin kunya da kuma tausayin kanta ta ɗaga masa kai tana miƙewa
************************************
*YOLA*
*FATTU*
cikin ta shin hankali ta shiga bukkar da niyyar Jawo JODDi su bar rigar don tana jin tsoron Abinda zai biyo baya
kwance ta samesa ya ɗaga kansa sama idanunwansa a buɗe "JODDi zo muje" ta furta tana ƙara leƙawa
bai fahimci abin da take faɗa ba illa bin ta da ido da yake, kamar Fattu ta kurma ihu haka take ji sbd ta shin hankali
Jin hayaniya na tunkaro inda suke ya sakata leƙawa tana kallon dandazon Mutanen da suka nufo inda suke ko wane da makamai a hannunsu.........
[5/21, 8:13 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*
*BOOK 1*
*By: RIAMCOOL*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*
*P.31&32*
______________Ganin Mutanen na ƙara tunkarosu ya saka jikinta kyarma don tabbas ta riga da tasan kashe mata Joddinta za ayi,ita kuma sai ta karɓi hukunci tsatstsaura idan har Ja'e bai mutu ba
da gudu ta tunkari JODDi hawaye na bin fuskarta hannunsa ta kama tana son miƙar dashi "JODDI miƙe mu tafi za su ƙaraso" ta furta tana son ta dashi
haɗe rai yayi yana ture hannunta tare da turata gefe guda yana kallonta, bata bi takan wannan ba ta ƙara tun karosa tana fashewa da kuka,ganin yadda suka shigo haiƙam da mugayen makamai a hannunsu, gabansa ta tsaya tana karesa tare da girgiza musu kai tana furta "ku ƙyalesa don Allah wallahi bai san komai ba, nice na dace da hukuncin ba shi b......"
bata idasa ba Baffalo ya ɗaga hannu ya wanketa da mari yana furta "Fattu kin cuceni Allah ya isa tsakanina dake, dama ashe yawon iskanci kike zuwa daga yau na fidda ki a jerin Ƴaƴana ki fidda ran cewar ke Ƴata ce, na barwa duniya ke Fattu, wallahi nayi da nasanin haifarki kin jawo man abin faɗa a gari" ya ƙarashe yana juyawa cikin ɓacin rai
Fattu kam dukkan wani aiki da ƙwalwarta keyi cak ta tsaya kalmar Allah ya isar da Mahaifinta yai mata na dawo mata da kuma furta ya barwa Duniya ita, "waye zata faɗa mawa ya yarda da cewar ita ba fasiƙa bace sannan abin da suke zato ba haka yake ba" ta faɗa wasu zafafan hawaye na bin kuncinta juyawa tayi da nufin ƙara kare Joddinta amma sai taga wayam babu shi, sai dai hayaniyar dake dakwai, da gudu ta fita tana nufar wajen cincirandon Matasan dake gewaye da JODDi, turesu tayi ta wuce, hannu ta ɗora a kai tana kurma ihu tare da son nufar in da Joddinta yake a kwance cikin jini malale gashi ko motsi ba yayi, riƙeta kam wani Hassanu Abokin Ja'e yai yana ƙara wanka mata mari, tare da fizgarta yana tafiya da ita duk cikin mutanen babu wanda yai yunƙurin da Katar dashi, kowa Allah wadai yake da Fattu,
cikin rashin Imani da tausayi Hassanu ya fizge zanin Fattu da kuma rigarta yai mata zigidir cikin Al'umma, Kuka riris take tana niyyar kare jikinta amma babu hali sbd mugun riƙon da akai mata, a haka suka dinga tafiya har aka isa fadar mai gari da ita, wan da nan ma mutane ne cike da ita daga Mata har maza, JODDi suka fara ɗaurewa a iccen bedi wanda jinin har yanzu bai daina zuba ba
Fattu ma ɗaureta sukai wacce ta kasa ɗaga kanta ta kalli kowa, idanunwanta basu daina zubar da hawaye ba,
Kowa na wajen tsit yai ana sauraren hukuncin da mai gari zai yanke, shiru mai gari yai yana kallon Ja'e wan da aka samu jinin ya tsaya domin harya farfaɗo,gyaran Murya mai gari yai ya fara magana "To kamar dai yadda kuka sani dukkan wani na cikin garin nan muka kama sa da aikata zina za muyi masa horo mai tsanani sannan mu koresa daga nahiyar garimmu, don haka hukuncin Fattu da za muyi mata ai mata bulala ɗari sannan idan an gama ina da buƙatar a kaita ɗakin duhu na cikin gidana,tayi tsawon wata biyu a ciki, kafin ta bar garin, sannan shi wannan akan kisan daya so aikatawa duk da ba mai hankali bane shima hukuncin kisa ya hau kansa ina da buƙatar a halin yanzu ku zazzaga masa fetur ku ƙonesa, Sannan kai Baban Fattu na janye Auren Fattu da Ja'e don haka kai ne zaka bayar da tarar Shanaye Goma"
kan Baffalo a duƙe ya amsa da to kamar ya fashe da kuka a cikin ransa yana jin kamar ya shaƙe Fattu ta mutu, ji yake dama Fattun ce ta mutu ba wai ace ya bada shanayensa ba,
kowa na wajen yai na'am da zancen mai gari Fattu kuwa kuka take kamar ranta zai fita tana son kuncewa daga ɗaurin da aka yi mata domin ceton Joddinta ,duk da tsawar da bafaden mai gari ke mata bata dai na kici_kicin kuncewa ba,sharɓeɓiyar dorinar dake hannunsa ya ɗauka yana zuba mata a jiki wacce ta sakata shiɗewa wata azaba na ziyartarta, nan take farar fatar jikinta ta fara fashewa har jini na zuba,bata ida dawowa hayyacinta ba ya ƙara zuba mata wata wacce ta saka Numfashinta tsayawa cak jikinta na ƙara malalar da jini, dukkan wani mai tausayi da imani yaga halin da Fattu take sai ya tausaya mata,ba tare da tausayawa ba yai mata bulala ɗari cif lkc babu alamar rai a tare da ita,jikina duk ya ɓaci da jini kamar an yanka dabba kunceta sukai ana samun zani tare da lulluɓa mata a jikinta don an tabbatar data riga ta mutu
JODDi ma da zasu zazzaga masa Fetur liman ya hana sai dai dukan da sukai masa wanda ba zaka taɓa ganesa ba, dan lkcn ko numfashi babu a tare dashi, Umarni mai Gari ya bayar aka fita da gawarwakin su Fattu daga cikin garin
********************************
*MAMMA*
Zaune take waje guda tayi zugum duk abin duniya ya isheta tun ranar da Muneebba ta bar gidan hankalinta ya kasa kwanciya,ga miyagun mafarkan da take yi akan Muneebba, Mamma Ladiyo dake kallon Mamma tun da ta lula duniyar tunani tace "Wai Shatu ba zaki cire damuwa a ranki ba? Muneebba fa na cikin kwanciyar hankali dan fa baki ga yadda Uwar mijin ke nan da nan da ita,mu kammu mun ga karamci a gidan nan".
wata doguwar Ajiyar zuciya Mamma ta saki tana faɗin "Wallahi Mamma Ladiyo kwanan nan miyagun mafarkai nake akan Muneebba shi ya saka hankalina ƙin kwanciya"
Wani kallo Mamma Ladiyo ta bita dashi mai cike da tarin ma'anoni tana furta "Ayya ba abinda zai sameta sai Alkhairi Shatu ki kwantar da hankalinki A'ishah"
ɗaga mata kai Mamma tayi ba tare da zuciyarta ta nutsu ba akan zantukan Mamma Ladiyo,
Misalin ƙarfe 3 na dare Mamma Ladiyo ta miƙe tana leƙa fuskar Mamma wacce bacci ya ɗauke ta zanin jikinta ta kunce tana ɗauko ƙullin baƙar leda ta kunce tana barɗawa Mamma bisa jikinta tayi minti biyar tsaye a kanta tana wasu surutai kafin ta miƙe ta shiga ɗakin, Akwatin kayanta ta jawo tana buɗawa ta fito da wani madubi wan da yake lulluɓe da jan ƙyalle mai ratsin baƙi,yaye ƙyallen tayi tana buɗesa nan take wani baƙin duhu ya ƙara mamaye ɗakin baka jin motsin komai sai wani gurnani dake tashi zubewa tayi ƙasan madubin tare da kai goshinta ƙasa tana sujjada, tayi tsawon mituna a haka kafin ta ɗago tana duban madubin, wani kalar duhu ne ya mamaye madubin baka ganin komai a cikinsa, buɗe bakinta tayi ta fara wasu surutai masu wuyar ganewa da wata murya mai kama data yara aka fara faɗin "kurwa zanci ki bani kurwa naci ko ki bani na riƙe na dinga lasarta kwaɗayin kurwa nake"
ɗago da kanta Ladiyo tayi tana duban madubin tare da bugawa yarinyar dake cikin madubin tsawa tana faɗin "Julaisa kina bani aiki wallahi a gidan wa zan samo maki kurwa a cikin daren nan?"
dariyar mugunta Yarinyar ta fashe dashi tana faɗin "kin riga da kin san sharaɗin dana gindaya maki a duk lokacin dana nemi kurwa kika hana ni taki zan kama taki kuma dama irin taki nake kwaɗayi daga gani zata yi maiƙo da mai wai har kin ja kwaɗayina ya tas.....?"
bata idasa Mamma Ladiyo ta buga mata tsawa tana faɗin "Julaisa Aniyarki ta biki kika ƙara irin waɗannan baƙaƙen maganganun wallahi sai nayi maki mugun hukunci mai tsauri kin san yanzu dai ke baiwa tace baki da ikon a kaina har sai na karya maki sharaɗi don haka idan kurwa kike nema yanzu yanzu zani baki ita"
dariya yarinyar ta sake fashewa da ita tare da ƙwalalowa Mamma Ladiyo manyan idanunta tana fito da harshenta, miƙewa Mamma Ladiyo tayi tana fita daga ɗakin, kai tsaye inda Mamma ke kwance ta nufa,nan take wani abu mai kamar fara ya fara yawo a sama, damƙesa tayi tana murmushi ta shiga ɗakin, madubin ta kalla tare da miƙawa Yarinyar cikinsa farar, amsa Yarinyar tayi tana kallonsa sannan ta yatsina fuska tana kallon Mamma Ladiyo "wannan tayi ƙadas da yawa babu maiƙo daga gani ma ba zata ciyu ba sai dai na dinga lasarta,sannan jinin Mutumin can da nake sha yanzu babu yai nesa da iyalin nashi"
"na baki abinda kike so ban san wani dogon tsogwami ki ɓace man da gani" Mamma Ladiyo ta furta
dariya yarinyar ta sake fashewa da ita tana faɗin "ban so kika samo man kurwa ba naso ace taki ce na lashe dan kullum haɗiyar yawu nake, ɓacin rana kawai nake jira tazo naga kurwarki a hannuna"
Jan ƙyallen Mamma Ladiyo ta saka tana rufe madubin sannan ta ajiyesa cikin kayanta tana fitowa waje ta samu ta kwanta tana sakin wani sheɗanin murmushi tare da kallon Mamma
********************************
Tun da Muneebba taci Abinci ta miƙe ta nufi side ɗin ƴan aiki don a can ne aka mayar da ita, ko da taje waje ta samu tana kwanciya don jin masassarar ta ƙara rufeta ga kanta da bai daina ciwo ba, Indo ce ta shigo taga halin da MUNEEBBA take cikin tausayawa tai mata sannu sannan ta taimaka mata ta miƙe ta rakata wajen Doctor ɗin su tai mata Allura da bata maganin
Bayan kwana biyu
sosai gidan ya kacame da hidindimu kasancewar bikin Maheer daya matso anata hidima amma babu ango hakan ya sakasu dakatawa da wasu Event waɗanda suka shirya kuka sosai Maheer taci ganin irin halin da take ciki da kuma mijin da zata aura wanda bai ma san tana yi ba
zaune take fatar nan tata sai glowing take tayi sumul sai ɗaukar ido take saboda tsabar gyaran da tasha, kayan dake gabanta ta tisa tana kallo zuciyarta cunkushe da damuwa tayi nisa cikin tunani taji an dafa kafaɗarta wanda ya sakata juyowa tana duban Maheer wacce ta kafeta da ido murmushi ta ƙaƙalo tana dubanta "wai Maheer ba dai zaki cire damuwa a ranki ba kullum cikin tunani kike"
murmushin takaici ta saki wanda wasu zafafan hawaye na biyo kuncinta "ba zaki gane ba Iftihar" ta faɗa tana miƙewa........
Love Yhu All my Habibties, thanks for your comments, much love and ƙauna lodi_lodi🤩💖💖💖💖
[5/21, 8:17 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*
*Book 1*
*By Riamcool*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*
*P.33&34*
koda Maheer ta miƙe iya Toilet ta faɗa tayo wanka fitowa tayi jikinta sanye da towel, wajen bakin Bed ta samu tana zama tare da kallon Iftihar wacce ke haɗa mata kayayyakinta tsab cikin Akwati "Iftie ina zaki tafi dasu ne? Maheer ta tambaya
Kallonta tayi tana furta "Maheer gidammu zamuje dake kamar baki san yau ne Mother's day ba, ki wuf ki shirya mu tafi dan yau hada Yaya Asad nasan zai zo"
Murmushi tayi tana miƙewa tare da shafa Lotion masu daɗin ƙamshi, sannan ta ɗan yi Kwalliya sama_sama, wani dakakken leshi blue mai ratsin pink sabo ta ɗauka ta saka, ba ƙaramin kyawu tayi ba, tsam haɗaɗɗiyar doguwar rigar tai mata, zama tai ta kashe ɗauri mai masifar kyau sannan ta ɗauki Haɗaɗdiyar sarƙar Gold da awarwaro ta saka, mayafin leshin ta ɗauka tana azawa a kai,ga haɗaɗɗun Flowers na ƙunshi da akai mata wanda zai tabbatar maka da cewar Amaryar ce, wani ƙayataccen murmushi ta saki tana ƙara bin jikinta da Mayun