x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 12 - BAYAN WUYA free pages complete

  • 33001 words
  • 36000 words
  • Out of 37650 words

Category: Tale Stories

Views 165

27 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
yake yiwa bakin nata wanda kai kasan ba a cikin hayyacinsa ya ke yinsa ba, ihun neman ceto Muneebba ke son yi amma babu hali ko damar yinsa, cire bakinsa yayi yana cire mata Hijab ɗin Tata da riga wanda ba ƙaramar kokowa suka sha ba harya samu galabar cire mata kayan jikinta, kuka take da ihu amma babu mai jinta, saboda muryanta daya dishe............






*Tabɗi jam,Koya zata kaya tsakanin Bobbi da kuma Muneebba? Mu haɗu a next Page, Habibties, ina matuƙar godiya ga ƙoƙarin comments ɗinku, much love All*


*Riamcool ce*
[5/21, 8:18 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*

*Book 1*

*By: RIAMCOOL*


*MIKIYA WRITTER'S ASSOCIATION*



*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*


*P.39&40*


Kamar wani tsohon mahaukacin Zaki haka yake sarrafata, da ƙyar ya samu ya cire kayan jikinsa, duk yadda taso ƙwatar kanta ta kasa har sai da ya cimma burinsa a kanta wani kalar Azababbiyar ƙara ta saki lokacin da ya ratsata ya wuce, tun tana kuka harta sadaƙas da tabbas mutuwa za tayi, ya daɗe a kanta yana aiki kafin ya saki ƙara tare da ƙanƙameta kamar zai ida tsagata gida biyu, lamo yai a jikinta yana sauke ajiyar zuciya, da ƙyar ya sauka daga jikinta yana samun gefe ya kwanta nan take wani wahalallen bacci ya ɗauke sa, kuka Muneebba keyi sosai tana ƙara jin tsanar Bobbi a ranta, ji take duk duniya bayan Mahaifinta babu wanda ta tsana sama dashi, Anya shi cikakken mai imani ne? ta tabbatar dashi ɗin mugun mutum ne marar tsoron Allah mai aikata saɓo da ɗaukar zunubi a wajen Ubangiji, shin Ƴam mata nawa ya aikata ma haka, nawa ya zalunta tare da sakasu kuka? ba tare da yasan ita ɗin matar sa bace ya kusanceta, da ace ba Matar sa bace da yau ya zubar mata da mutuncin data daɗe tana riƙewa, ta faɗa a zuciyarta wasu zafafan hawaye na bin kuncinta





Sosai jikinta yai tsami hakan ya sakata ƙoƙartawa tana miƙewa tare zaune da ƙwalla uwar ƙara jin azabar data ziyarceta, cije leɓe tayi tana ida miƙewa kamar ta fasa ihu haka take ji, cikin dakiya da dauriya ta shiga bedroom nashi dan ta gasa jikinta, koda ta shiga Toilet ruwa masu zafi ta haɗa a Sit bath ɗin zama tai ta fara gasa kanta dauriya kawai take, tayi gashi tayi ya kai sau ukku kafin ta samu taji ta ɗan fara dawowa, dai_dai, wankan tsarki tayi tare da ɗora Arwalla kasancewar Ishsha'i ta wuce fitowa tayi a hankali kamar wata mai koyon tafiya, rigarta ta mayar da Hijab ɗin sai niƙab, har lokacin hawaye basu daina zuba ba a fuskarta, key ɗin ta ɗauka tana fita daga Falon,jawo kofar tayi tana saka key ɗin ta kulle, a tsorace tabar side ɗin tana fita ta ƙofar da tasan baza a ganta ba, taci Sa'a harta shiga side ɗin ta bata ga kowa ba,A Falon ta zube tana mayar da numfashi, Sallar da ƙyar ta idar da ita tana kwanciya wani Zazzafan zazzaɓi na rufeta, da ƙyar ta samu baccin wahala ya ɗauke ta



Maheer ce tsaye tana kai da komowa ji take kamar ta fasa ihu dan tun bayan dawowar Bobbi ta nufi part ɗin shi sai dai tayi bugun duniya bai buɗe ba, haka zalika ta saka key ɗin bai buɗe ba, Alamun akwai key a jikin ƙofar hakan ya sakata dawowa kamar ta fasa ihu, tana fatan Allah ya hana Bobbi Shan lemon, bakin bed ta samu tana zama, ta daɗe a zaune kafin ta samu ta kwanta, bacci ɓarawo ne ta samu ya ɗauke ta





A hankali Bobbi ke ware lumsassun idanuwansa yana furta sunayen Allah, ga kansa dake mugun sara masa ida tashi yai zaune yana duban jikinsa da mamaki da kuma tashin hankali ganinsa tik babu kaya ga jini duk ya ɓata wajen daya ke zaune "Innnalilahi wa'inna ilaihirraji'un" ya furta da matsanancin tashin hankali, Abin da ya aikata ne ya fara dawo masa a brain wan da a lokacin da yake aikatawa sam hankalinsa bai jikinsa gani yake tamkar a mafarki, dafe kansa yai yana nanata sunaye Allah tare da dafe kanshi dake barazanar tarwatse masa, shine yau da aikata Zina,wace mace ce ya aikatawa haka, da wane ido
yarinyar daya aikatawa hakan zata kallesa da wane bakin zai iya bata haƙuri, mai ya saka mata suke shiga rayuwarsa su tarwatsa masa farinciki a koda yaushe, waye ya aikata masa wannan ɗanyen aiki??????????????? Dan ya san tabbas lemon daya sha ne ya saka sa a babban haɗari, shin wai ma mi ya kawo yarinyar a ɗakinsa? tabbas da wata manufar aka aikata masa hakan, waɗannan tunanukan su suka addabi zuciyarsa, da ƙyar ya miƙe ya faɗa Toilet yai wanka, salla ya fara yi kafin ya fara karatun Alqur'ani ko zai ji sauƙin abinda ke zuciyarsa, ya ɗanjj sauƙi hakan ya sakasa miƙewa ya fito Falon da kanshi ya gyara Falon duk inda jinin yake y gyarasa tas

A Daren ranar ko rintsawa bai samu yayi ba,


Washe gari ya daɗe kafin ya fito, kai tsaye Part ɗin Mom ya fara shiga, bai sameta a Falo ba hakan ya sakasa tunkarar bedroom ɗin ta, zaune take tana damna waya, ciki ciki yai sallama, gaisar da ita yai tana amsawa a hankali tare da dubansa, cikin fara'a "Mom tambayarki zanyi"


hankalinta ta tattara ta mayar dashi kan Bobbi "Ina saurarenka son"

"Shin kin aika man wata a jiya ne ta kai man abinci"


"Eh" Mom ta furta, da ɗan gabanta na faɗuwa, "shin wacece ita wacce kika aika man?"


"Son na mance wacce na aika maka a jiya, dan ba tantancesu nake ba kasan yawan ƴan aikin gidan nan ba a ganesu"

"Ko wacce ke man gyaran ɗaki ce kika aika man?"


da sauri Mom ta girgiza kanta "ba ita bace ita wannan ma ai ta tafi garinsu dubo gida ina tunanin gobe ko jibi ma zata dawo,amma mi ya sa kake man waɗannan tambayoyin?"


"Saboda ina son na gargaɗeta ne ta daina shigar man a Falo koda an aiketa" ya furta yana miƙewa tare da ya mutsa fuska kamar da gaske, Ajiyar zuciya Mommi ta saki jin ba abinda zuciyarta ke zato bane, amma taya harya gane tana masa gyaran ɗaki? tana tsoron kada Bobbi ya dinga ganin Muneebba harya faɗa sonta, hakan kuwa ma ba zata taɓa faruwa ba dole ne tama ko wace hanya ta hana Muneebba sake haɗuwa da Bobbi,


Koda ya fita kasa sukuni yai, dan yau ko Office bai je ba,


Muneebba kuwa tun da ta tashi take jin jikinta na mata tsami ga hakan ya sakata ƙara gasa jikinta, da ƙyar ta samu kingin Maganin zazzaɓi tasha, tana kwanciya dan har rana ta fito bata fita ba, kwance take taji an ɗaka mata duka wanda ya sakata saurin miƙewa tana kallon AUNTY Samhat wacce ke Binta da matsiyacin kallo "ke Uban mi ya hanaki fitowa yau?" Samhat ta faɗa


murya a cunkushe ta furta "ban lafiya" taɓe baki Aunty Samhat tayi tana furta "babu ruwana da ciwo ki fito ki gyara man ɗaki na sannan kiyi man haɗaɗɗun delicious, zanyi baƙi yau"


"Wallahi bazan iya ba"ta furta da muryan tausayi, ji kake tasss ta wanketa da Mari tana furta "harni zaki faɗa wa baki da lafiya wallahi tashi muje sai kinyi abinda na sakaki Shegiya ƴar matsiyata"


Hawaye na bin fuskarta haka ta miƙe tabi Samhat jiri na ɗibanta, dukkan Abinda ta sakata sai da tayi, fitowa tayi tana layi kamar zata faɗi da sauri Maheer ta riƙe ta tana furta "lafiya Muneebba?"

"Aunty ban lafiya ki taimakeni" ta faɗa tana hawaye, da sauri Maheer ta taɓa jikinta tana faɗin "subhanallahi Muneebba ba lafiya kuma kike aiki kuma baki sha magani ba, wai me kike son mayar da kanki ne kin san nasan komai ke ɗin matar Yah BObbi ce, shin aure kika zo ko bauta, wallahi Muneebba idan baki tashi ba sai kun zama shara abar watsawa, ki ƙwaci ƴancin ki da kanki mana"


tunda take maganar Muneebba ta shiga shock jin cewar tasan ita ɗin matar Bobbi ce, "da gaske kin san ni Matar Bobbi ce?"


kallonta Maheer tayi "eh Muneebba nasan ke ɗin matar Bobbi ce kada kiji komai a ranki ki ɗaukeni tamkar yayarki nima haka na ɗauke ki a matsayin ƙanwata,ba kishiya na ɗauke ki ba abokiyar zama na ɗauke ki" ta faɗa da Murmushi

ajiyar zuciya Muneebba ta saki tana yaba kyakkyawar zuciya irin ta Maheer, "na gode Sosai Aunty" ta furta, Maheer da kanta ta bata magani sannan ta tisata taci Abinci a yinin ranar wajenta ta yini tana kula da ita,


Kwanaki na tafiya makwanni na shuɗewa, kullum a wajen Bobbi bashi da kwanciyar hankalin abinda ya aikata, yayi bincike bai ganota,ba ga babban tashin hankalin da yake ciki shine fara aikin dake gabansa yaƙara abokan hamayyarsa, a wajen Muneebba kuwa ta warke tuni sai dai har yanzu ciwo da ɗacin da take ji bai bar zuciyarta ba,ga wani kalar bacci da cin Abinci da take yawan yi ta rasa gane ko minene a tunaninta cutar bacci ce ta kamata, sosai ta sake cikowa ko ina nata ɓul ɓul, Tsaye take a kichen ita da Indo suna faman girki, hannunta toshe da hancinta saboda ƙamshin manjan da take ji, cikinta taji ya hautsina hakan ya sakata fita da gudu tana zagayawa ta baya nan ta fara sheƙa Amai kamar Ƴan cikinta zasu fito saboda Amai, wani wahalallen numfashi ta sauke lokacin data gama, kichen ɗin ta koma da niyyar ci gaba da aikin kallonta Indo tayi tana furta "sannu ashe baki láfiya? kin ga ki barni na ƙarasa jeki kisha magani ki kwanta" ɗaga mata kai kawai tayi tana fita daga kichen ɗin domin ji take tabbas ta tsaya tana shaƙar ƙamshin manjan tsab zata ƙara wani Aman,shigewa tai side ɗin ta tare da kulle ƙofar Falon saboda mugun baccin dake fizgarta kwanciya tayi nan take bacci mai nauyi ya ɗauke ta tun tun Azahar take abu guda sai wajen shidda na yamma ta farka da wata masifaffiyar yunwa, wanka da salloli ta fara yi kafin ta samu ta fita Abinci ta samu ta zubo wanda sai mutum biyar yaci sa, tun da take cin abinci Indo ta ƙura mata ido da mamaki ganin ta cinye Abincin tas "Wai nikam Muneebba lafiyarki? Naga kwanan nan duk kin canza Abincin Mutum biyar kike cinyewa zama ɗaya, ga bacci kamar kasa, ko dai wata cutar ce ta sameku?"


Cikin ɗan tsorata da furucin Indo Muneebba ta zaro ido tana furta "kuma fa nima Abin nan na bani tsoro Indo ga kasala da nake ji ko dai wata cutar ce zata kamani?"



"A gaskiya Kije kiga Doctor Dan ba láfiya kike ba" Indo ta faɗa

Da to ta amsa kawai jikinta a sanyaye tare da Alwashin zuwa ganin likita, haka kwanaki sukai ta tafiya Muneebba bata je ba gashi abin nata sai gaba yake, tun Mom bata lura ba harta fara lura da yanayinta bata kawo komai a ranta ba sai dai ma ƙara Azzarawa Muneebba da tayi


Zaune take ita da Indo a gaban Doctor ɗin tana kora mata jawabi, shiru likitar tayi yayin da Muneebba ta gama kora mata jawabi, test ɗin fitsari da gwaje-gwaje ta turata tayi, koda tayo kawo mata tayi ƴan rubuce_rubuce tayi tana bata result tare da furta "congratulations, kina da juna biyu na tsawon 1 Month"


Cikin razana da firgita ta yada result ɗin tana furta "what Doctor Anya kinyi bincike dai_dai kuwa kada ki furta man haka mana Doctor kice Abinda kunnuwana suka jiye man ba gaskiya bane" ta faɗa da son gazgatawa

cikin mamaki Doctor tace "tabbas tana da juna biyu,abinda kunnuwanku suka ji shine, miye na tada hankalinku kuda za kuyi murna da godiya ga Ubangiji"


girgiza kai kawai Indo tayi tana jan hannun Muneebba suka fice a Office ɗin, tafiya suke babu wanda ya tankawa wani, har side ɗin ta Indo da kanta ta rakata har side ɗin ta, shiru tayi wasu zafafan hawaye na bin kuncinta, tabbas ya zama dole ta nemo Bobbi ko dan ta fitar da kanta


"Miye na damuwa Muneebba gdy ga Ubangiji za kiyi tunda cikin ya kasance ɗan sunna, na san da cewar tabbas cikin jikinki na Mijinki ne tunda kina da aure na san ke ce Matar Asad BObbi ce" Indo ta furta


Da mamaki Muneebba ta kalleta tana faɗin "amma taya kika san nice Matar Bobbi?"


"Tun ranar da kika sako kafarki gidan nan nasan kin mance ni lokacin dana zo kawo maki Abinci na ganki,a lokacin dana ga kin dawo cikin House maid ba ƙaramin mamaki nayi ba, ki ƙara haƙuri kawai d ƙaddararki Muneebba"

Wani wahalallen numfashi ta sauke tana furta "tuni na amshi ƙaddarata tun ranar da igiyar Auren Bobbi ta hau kaina nasan na buɗe shafin kundin ƙaddarata"

cikin tausaya mata da ƙara kwantar mata da hankali Indo ta dinga furta mata kalamai masu kwantar da hankali,a haka Muneebba ta share kwanaki kullum cikin neman Bobbi take a gidan amma babu shi a yadda taji wajen Maheer yayi tafiya kuma zai ɗauki lokaci bai dawo ba hakan na nufin Dole sai cikinta ya fara fitowa sannan zai dawo, taya zata fitar da kanta a wajen mutane waye zai yarda cewar cikin jikinta na Bobbi ne, wane mataki Mom zata ɗauka yayin data gano tana da ciki????? Waɗannan tambayoyin su take yawan nanata wa a koda yaushe, ga wani sabon Al'amarin na Zaidu dake tayar mata da hankali a kullum sai ya haɗa mata tarko tana tsallake sa, ita yanzu ma tsoro sosai abin ke bata

ranar wata Asabar tana zaune a garden wajen furanni tana shaƙar ƙamshinsu dan a yanzu kullum sai tazo shaƙar ƙamshin furanni, tsaye taga mutum hakan ya sakata ɗagowa tana dubansa gabanta na faɗuwa sosai, tare da neman tsarin Ubangiji ya kareta da mugun sharrin Zaidu, cikin murmushin mugunta ya dubeta yana furta "kin ƙi bani kanki ta ruwan sanyi to muddin yanzun baki bani kanki ta ruwan sanyi ba zaki ga abinda zan aikata maki wanda fita ma sai ta gagareki mutuncin da kike riƙewa sai na zubar dashi a wajen kowa, na baki kwana biyu ki kawo kanki idan ba haka ba zaki yi da nasani"


da mamaki take kallonsa tana maimaita sunayen Ubangiji ta furta "in Sha Allah Allah ba zai taɓa baka nasara akan cutar danj ba, tabbas dana ci amanar aure gara komai za kayi kayi nasan Ubangiji ma ba zai baka nasara ba, ka sani zalunci baya nasara akan gaskiya, kai wane kalar mutum ne?"

da kallo ya bita yana girgiza kansa sannan ya wuce, waɗannan kalmomin sune suka dinga bawa Muneebba tsoro a koda yaushe ta tuna su,



Zaune take cikin wani kogon baƙin dutse tana surutan da ita kanta bata ganewa saboda tsoro, wata kalar dariya taji an fashe da ita wajen na girgiza da kururuwa cikin ihu da ƙara ji aka furta "to la'ananniya taɓaɓɓiya me kike so wace buƙata kike da ita yanzu yanzu ba tare da kin bar wajen ba zata biya"

cikin ɗan tsoro ta furta "Ya la'anannen baƙin sheɗani Marƙudus ina da buƙatar yarinyata ta mallake zuciyar Mijinta ta samu soyayya da kulawar sa sannan da baƙar mallaka, sannan ina so a san yacce za'ayi da Kishiyarta"



wata sheɗaniyar dariya aka saki ana furta "Buƙatar ki kafin ki kai ta biya sannan ita kishiyar faɗa Mani hauka ko mutuwa kike so tayi"


cikin ruɗewa ta furta "baƙin hauka nake son tayi ta haukace ya sheɗani ka haukatar man da ita ko mi kake so zan baka"


dariya ya fashe da ita "yace an gama kalli gabas ki nanata kalmomin da kika furta yanzu"

Kallon gabas Mammi tayi tana nanata wa tare da rufe idonta "buɗe idon" taji an furta buɗe wa tayi tana kallon ƙaton madubin da Muneebba a cikinsa, tana bacci

Da murya me tsoratarwa ya furta ga jinin da kika kawo can ki ɗakko sannan wancan baƙin zanin mahaukaciyar dake zaune ki yanko sa ki kawo a wajen gunkin can, duk yadda yace tayi haka tayi, wata baƙar ɗiyar roba ta sakawa zanin mahaukaciyar tare da bin ko ina ta ƙulla mata baƙin ƙyalle da kuma jan ƙayalle, "zagayata sau ukku kina nanata kalmomin da kikayi"

Zagayata tayi har sau ukku tana furta kalmomin, kamar wata mai rai haka ɗiyar robar ta miƙe tana wata girgiza haka Muneebba dake kwance itama ta fara wata jijjiga sai da ɗiyar robar ta tsaya sannan itama ta tsaya, tana buɗe idanunta tare da dafe kanta dake mata wata irin juyawa


"Hhhhhhhhhhhh aiki ya biya kije ki nemo baƙin mahaukaci kiyi zina dashi, sannan nan da kwana biyu ki kawo man jinin da nake buƙata"



Amsawa tayi da to tana fita da baya_baya harta fice daga kogon, tsayawa tayi ƙyama tana fito da wani baƙin zobe tare da murzasa tana rufe idonta, buɗe idon tayi ta ganta a bedroom ɗin ta, ƙarƙashin gadonta ta nufa tana jawo wani ɗan ƙaramin akwati ta buɗe wata ƴar siririyar kwalba ta fiddo tana buɗe ta nan take baƙin hayaƙi ya fara fitowa


**************************


tun da Muneebba ta tashi take jin kanta na wani irin juya mata wani abubuwa na daban na shigarta gashi. ta kasa faɗin sunan Allah,da ƙarfin gaske aka turo ƙofar Falon ta wanda Indo ce da kallo Muneebba ta bita tana furta "Indo láfiya naga hankalinki duk a tashe"


itama Indon kallonta take tana faɗin "Muneebba miye ma bai faru ba,yanzu naga wani sabon tashin hankali wajen Nazifa Muneebba wallahi Vedionki na gani dake da wani kuna aikata Alfasha kuma tabbas fuskarki ce, yanzu Vedio ya bazu ko ina, kizo ki gani"


"Ke Indo kin san kuwa abinda kike faɗa Ni ɗin ce nake aikata fasiƙanci da wani sannan harda Vedio na kuma fuskata ki dai bincika mai kama da nice" Muneebba ta faɗa a ruɗe, tana tuna kalmomin Zaidu


Indo ce tace "wallahi Muneebba ke ce na gani tabbas fuskarki ce kece ba wani ba, ki fito ki gasgata da ido ki"



"Innnalilahi wa'inna ilaihirraji'un, Indo waye zai fitar dani daga baƙin sharrin nan ga cikin dake jikina babu wanda ya san dashi Mijina shi kanshi bai san dashi ba ki faɗa man waye zai yarda dani, waye shedata????" ta faɗa tana fashewa da wani sabon kukan


"Muneebba Allah ne shedarki, indai baki aikata ki taso muje kiga nayi"

Tashi tayi kamar zata faɗi da ta fito
End Ads