data fara isarsa sai da ya ɗan ƙara zagaya Company sannan ya futo, buɗe masa Motar akai ya shige sannan kingin suka shiga kai tsaye Guest house ɗinsa suka nufa don yana buƙatar hutu
*********
*Yola*
*FATTU*
wata kalar busa sarewa ce ke tashi a cikin jeji wacce Fattu keyi a duk lokacin data fito kiwon Shanu data fara busa jejin zaiyi tsit tsuntsaye za suna dinga safkowa tana watsa musu tsaba suna ci tana ƙara busawa, wani juyi take ƙara yi tana rugawa da gudu ta hau wani ƙaton dutse dariya tayi tana ƙara kai sarewar a bakinta ta fara busata cikin ƙwarewa da iyawa, wani sautin na daban mai ratsa dukkan gaɓukkan mai sauraro Fattu keyi jejin ne ya ƙara yin shiru yi take harta fara gajiya
ganin babu alamunsa yasa Fattu raurau da ido ta buɗe baki tana faɗin "JODDI!!!JODDi!!! JODDI!!!" da ƙarfi take kiran sunansa namma shiru babu alamunsa sarewar ta ƙara kaiwa bakinta ta fara busan da tasan indai yana kusa to tabbas zaizo wata kalar busa yanayinta mai taken ban tausayi take yi
Wata kalar feɗuwa aka yi wacce ya sata sauka daga saman dutsen tana bin hanyar da feɗuwar ke fitowa tasan tabbas shine wata kalar busa tayi wanda zaka rantse da usur akayita amma da baki tayi shi nufar hanyar tayi tana ƙara yin wata shi kuma yana feɗuwa da wani kalar sauti,
yana ganinta ya nufota da gudu itama da gudun ta nufesa tana kallon yadda yake dafe cikinsa kamo Hannunsa tayi da Yaren fulatanci take faɗin "JODDI ina ka tafi? yau kayi nisa" dukda tasan bazai maido mata amsa ba kuma ba zai fahimci abinda take nufi ba tunda ba hankali ne dashi ba,mamadin ya bata amsa saima haɗe rai da yayi yana nuna mata cikinsa, murmushi ta saki tana jawo hannunsa suka nufo inda ta ajiye masa ƙwaryar furar data damo masa tasha kindirmon Nono zaunar dashi tayi ta ɗauki ludayin ta dinga ɗebowa tana bashi a baki har sai da ya ƙoshi sannan ta ƙyalesa miƙewa yayi da nufin komawa inda ya fito, dama tasan daya sha zai tafi saboda shi kullum take zuwa nan kiwon Shanu wanda ta rasa baya ga tausayinsa me take ji da kanta ta rakasa bukkar data kafa masa tun farkon ganinta dashi sai da ya shiga sannan ta dawo tana kaɗa Shanunta suka sha ruwa sannan ta kaɗasu suka bi hanyar gida kasancewar Magriba data doso sai dai tana tunkarar gidan gabanta ya fara faɗuwa don tasan yau Innaro da Baffalo sai sunyi farfesun Namanta tunda ta ibarwa Innaro fura a ɓoye kuma Saro ta ganta tasan zata faɗa "Ya Allah" ta furta tana nufar garken shanun dasu sannan ta nufi bukkarsu da nufin ta saɗaɗa ta shiga sai dai jin saukar Sanda a ƙwabrin ƙafarta ya sata durƙushewa Baffalo ne ke kallonta cikin Yaren fulatanci yace "ke Fattu yaushe kika koyi sata? furan Innaro irgagga da zata tafi kasuwa ta siyar ita kika ɗiba to yau sai na miki ligib ƴar jakar uba" yana gama faɗin hakan ya ɗaga sandarsa ya dinga sauke mata tun tana ihu a hankali har yakai ga tana yi da ƙarfi sai da ta daku sannan ya ƙyaleta
Bukkarta ta shiga tana share hawaye tana ji Innaro da ƴarta Saro suna yada mata habaici ta shige, murmushi ta saki tunawa da JODDi wanda akansa ne akai mata wannan duka ji tayi ma dukkan haushin dukan ya fice, sandarta ta ajiye tana nufar rafi don tayi wanka
*Wacece Fattu*
FATTU dai ƴa ce ga Mlm Isah Baffalo wanda matansa biyu Innaro da mairo Mahaifiyar Fattu wacce tun tana shan Nono Mamanta ta rasu wanda ta taso cikin uƙubar Innaro tun tana ƙarama take ɗaukar Sarewar Baffalo wanda sana'arsa ce busa Sarewa , hakan yasa itama ta gada, zuwa kiwon Shanun da take ta haɗu da wani mahaukaci cikin jeji wanda ta saka masa sunan JODDI busa Sarewar da take yasa kullum yake zuwa wajenta ita kuma ta tausaya masa tana kawo masa Abinci duk lkcn da zata fito kiwo,
tana gama wankan ta shiga jeji ta hau bishiya don can take kwana
*KANO*
Zaune take bisa bed ɗinta fararen idonta sanye da farin gilashi ta kafe Photon dake jikin Laptop ɗin da ido tana sakin Murmushi tea ta kurɓa tana ƙara zooming ɗin Photon "Yah Bobbi" ta furta a hankali tana lumshe manyan idanunta "Maheer Maheer Maheer" taji Mami na ƙwala mata kira rufe loptop ɗin tayi tana ajiye tana fitowa a hankali take bin step ɗin benen kamar bata son taka ƙasa, ida sakkowa tayi ta nufi Mami tana faɗawa jikinta "Mammi gani" shafa kanta Mammi tayi tace "ki shirya gobe zaki je gidan Mommy, ayi dayi danni na fara gajiya ƙara kije ya dinga ganinki kusa kafin ayi muku baiko, har ya saba dake sannan wannan muskilancin naki da aji ki ajiye shi ki dinga shishige masa ta hakan ne zaki samu shiga gurinsa" tashi tayi daga jikin Mammi tana kallon Mammi tace "Mammi gsky ba zan iya shishige masa ba kinsan Yah Bobbi da diz gi da muskilancin kawai dai zan je gidan" ta faɗa tana miƙewa, da kallo Mammi ta bita har ta haye.....
Ba kwa man share fa😞 Habibties ku daure ku dinga man share dan Allah
[5/21, 8:10 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*
BOOK 1
*BY MARIAM SANI RIAMCOOL*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*P.15&16*
__________koda ta shiga haɗa kayanta taci gaba da yi saida ta haɗasu tsaf cikin Akwati sannan ta faɗa Toilet tayi wanka saida tai nafilfilu da karatun qur'ani sannan ta kwanta
Washe gari tana tashi ta faɗa kichen ta haɗa musu break fast a gurguje ta faɗa Toilet tayo wanka haɗaɗɗun Lotion ta shafa sannan ta ɗauki wani Blue ɗin material mai ratsin baƙi ɗinki A shape wanda tasan zai karɓi jikinta, ba wata kwalliya tayi ba amma tayi kyau sosai fuskar nan tata ɗauke da yalwataccen murmushi, parking ɗin dogon gashinta tayi ta ɗauki mayafin Material ɗin ta yana a kanta, ta aza farin gilashin ido wanda yake ƙara fito da ainahin kyanta duban kanta tayi a Mirror tana sakin wani ƙayataccen murmushi Hand back ɗinta da wayarta ta ɗauka ta fito
Koda ta fito zaune ta iske Mammi da Daddynta suna break "Morning Mom nd Dad" ta faɗa tana manna musu sumba " da murmushi suka amsa mata ɗaya daga cikin kujerun Dinnig taja tana zama Chips nd plantain kawai taci ta miƙe kallon Mammi tayi tace mata zata wuce "Ok ki gaisheta ki kula da abinda ya kaiki" Mammi ta faɗa tana duban ƴar tata, da to ta amsa tana ficewa da kanta tai Driving koda taje bata wani sha wahalan shiga ba kasancewar an santa parking Space ta nufa ta ajiye motar sannan ta wuce kai tsaye ta wuce sama kasancewar ma'aikatan gidan sun santa ko wane miƙo mata gaisuwa suke, da fara duka take amsa musu, a hankali ta tura ƙofan Falon ta shiga, zaune ta iske mazan gidan JUNAID AFIF ARYAN ZAMEER ABEED HAROON sai IFTIHAR dake gefen ARYAN ana caftar da ita, ganin basu lura da ita ba ya sata gyaran murya tana Sallama, da gudu IFTIHAR ta taso tana rungumeta tana faɗin "Oyoyo Matar BIg bro" dariya tayi tana faɗin "lallai IFTIHAR kina da aiki a gabanki fa ta ina shi Yah Bobbi yasan dama ni" dukan kafaɗarta tayi tana faɗin "lallai kuwa Aunty Maheer kina nufin Mom bata faɗawa Mammi amincewar Yah Bobbi ba?"
Kallonsu Zameer yayi yana taɓe baki yace "ke IFTIHAR kiji tsoron Allah yaushe shi Yah Bobbi harya amince kina gani fa saboda auren ya ƙauracewa gidan nan sannan akan auren fa yaiwa Mom hijira wanda har iyanzu bai shiga shirgin Mom a yanzu" dariya ARYAN yayi yana miƙewa yace "kudai ake ji inaga Aljana ta auresa har iyanzu shi yasa"
wani kalar dum Maheer taji zuciyarta tayi jin zancen Zameer wato saboda itama ya bar ya bar gida a dalilinta ya bar shiga shirgin Mom, "tabbas ya zama dole ne nabi shawarar Mammi ta haka ne kaɗai zan iya samun Yah Bobbi tunda YAH DEEN ya kubce mini wannan bazan barshi ya kuncemin a karo na biyu ba" ta faɗa a zuciyarta
dafata Iftihar tayi tace "tunanin me kikeyi ne?" "Nothing" ta faɗa tana ɗaga kafaɗa tunda Zameer yai maganar JUNAID ya karanci yanayin Maheer dariya yayo yanawa HAROON da ABEED signal da ido dariya sukai HAROON na faɗin "cabɗijam lallai kam da sauran ruwa a kaba, akwai fa wasan game a gidanmu"
Maheer da bata fahimci abinda suke nufi ba ta haura sama ɗakin Iftihar ta ajiye akwatin sannan ta zame gilashin idonta tana share hawayen da suka samu damar gangarowa a kuncinta share hawayen tayi, ta fito koda ta fito ta samu Aunty Samha da Aunty Meera waɗanda suna kan ibadar tasu wato danna waya da gudu ta isa wajensu tana rungumesu da murna sosai suka rungumeta suna mata ƙorafin rashi zuwa da ba tayi kwana biyu,Mom ta tambaya aka faɗa mata bata nan tana gun aiki ita da Samha da Seemah
********************
*ASAD BOBBI*
Kwance yake a baki Swimming pool ya lumshe idonsa ya ɗauki kusan 10 minute buɗe idanuwan nasa yayi waɗanda sukai masa jajir saboda ƙunci da takaicin da yake ciki, wanda duk da hakan bai hana ainahin kyawun nasa fita ba da sirrin kyawun idanunsa, ba wai yana takaicin rasa dukiyarsa da yai ba, sai don takaicin abinda akai masa meya tare musu? Wanda suke son karyasa kafin su ɗauki rayuwarsa kamar yadda suka ɗauki ta ɗan uwansa Deen wanda har gobe yake cikin raɗaɗi da zafin zuciya na rashin ɗan uwansa wanda suka zauna ciki guda wanda daƙiƙu kaɗan ne a tsakaninsu, ko bacci bai taɓa rabasu ba amma yau azzalumai sunyi nasarar rabasa da wanda yafi ƙauna a rayuwarsa, yasan target ɗinsu na gaba a kansa ne sai dai ina bazai taɓa basu wata dama ba wacce zasu samu ɓaraka a gurinsu, rintse idanunsa ya ƙara yi tunowa da auren Maheer wanda ya ida dagular da zuciyarsa amma zai bi komai a sannu ya warware, miƙewa yayi tare da fara tafiya cikin taƙama da kuzari, tafiya irin ta ƙarfafan masu ji da kansu da cikakkiyar izza,kai tsaye wani ƙofan ya shiga sai gashi ya faɗa a bedroom, bathroom ya faɗa yai wanka ya fito ƙugunsa ɗaure da towel mirɗaɗɗiyar ƙiran tashi duk a waje ga skin ɗinsa se sheƙi take kai tsaye shiryawa yai cikin wasu arnayen ƙananan kaya masu masifar kyau yai parking ɗin gashin kansa tare da ɗauresa kyau bana kaɗan ba Bobbi yayi dukkan wata mace ta gansa sai tayi suman wucin gadi kafin ta dawo hayyacinta, wayoyinsa da keys nasa ya ɗauka har zai fita sai kuma ya juyo a hankali ya tako har zuwa inda wani makeken photo yake wanda sak kamannisa ne keda na jikin Photon sai dai shi wannan Photon anyi sa da fara'a ne, ɗaukar Photon yai yana shafawa "DEEN" ya faɗa a hankali rungume Photon yai yana sakin ajiyar zuciya "bazan kyalesu ba DEEN zan ɗaukar maka fansar ranka" ya faɗa da fitar da wani huci mai zafi ya ɗau kusan daƙiƙu kafin ya ɗauke photon daga ƙirjinsa, ganin zai makara a meeting ɗinsu wanda aka shirya na manyan ƴan kasuwa harma dana waje yasa shi fita a gurguje Securities na take masa baya
Manyan jigagan Motoci na Alfarma suka shiga baƙaƙe wuluk dasu guda biyar ta tsakiyar ya shiga Driver naja suka nufi wajen Meeting ɗin ga baki ɗaya kowa ya hallara a wajen shine kawai babu kowa na wajen zuciyarsa cike take da takaicin Bobbi ganin ɓata musu lokacin da yayi wanda kuma koda yazo idan banda Hy daya furta bai sake faɗin komai ba, Zaidu dake gefen Mas'ud ne cikin takaici yace "BObbi wane kalar wulaƙanci ne haka zaka ɓata mana lokaci kuma fa kasan a kanka za'ai wannan Meeting ɗin"ya faɗa da ɓacin rai
"Ohh kuma fa so kuyi abinda ya kawo mu kuna ƙara ɓata man lokaci muddin lokacin dana ibarwa kaina ya ƙare zan tafiyata fa 15 minute gareku" ya faɗa kamar baya son maganar yana ɗagewa Zaidu gira tare da kashesa da wani Munafukin murmushi
Nan da nan kowa ya fara masifa kan rainin wayon Bobbi, cikin masifa Alhaji Habu ya dubesa yana faɗin "ASAD AHMAD BOBBI na kiraka da manyan baƙi kaji kuma ka ƙara ji ba wani abu bane yasa mu zaman meeting ɗinnan sai don kashe mana companies da kake bamu kaɗai ba har ƴan waje kana neman kashe nasu companies to bari kaji kamar yadda muke saka farashin kayammu da kuma yadda muke sarrafa su kaima haka zakai, bata yuwa kazo ka tarwatsa mana companies na tsawon shekaru"
kallonshi yake da rinannu idanunsa waɗanda suka sauya kala ya zuwa na ɓacin rai "shawara kake bani ko umarni?" Bobbi ya faɗa yana ƙare mashi kallon rainin wayo dariyar takaici Alhaji Habu yai yana faɗin "duk yadda ka ɗauka Bobbi, amma ba shawara bace umarnimmu ne yadda kowa yake kaima haka zakai"
Kallon agogon hannunsa yai yana faɗin "Time up, lokacinku ya ƙare yana gama faɗar hakan ya miƙe ya fice
Kowa da kallo sake da baki ya bisa suna ƙara jinjina rainin wayonsa da kuma taurin kai irin na ɗan uwansa Deen kowa da takaicin abin ya bar wajen tareda alwashin baƙin ƙudiri akan Bobbi
Tunda Bobbi ya fita kai tsaye Company B.D Wanda gobara ta kama yaje, Company duka an fara gyarasa an canza masa wani sabon design mai jan hankali Murmushi ya saki yana lumshe idonsa ya buɗe
jin kiran waya yasa sa ɗaukar wayar yana dubawa Dad ya gani shiru yai na wasu ƴan daƙiƙu "Asad ni kake so na fara gaisar da kai koya?" Dad ya faɗa
shafa dogon gashin kansa yai yana faɗi "No Dad, Afterning Dad" murmushi kawai yai yana ƙara mamakin halin yaron nasa "ok kaje Meeting ɗinne?" "eh" ya furta "ba kadai nuna musu rashin ɗa'ar daka saba ba ko?" "Saidai kar a kuma Dad" dariya kawai Dad yai ya kashe wayar daman yasan Asad ne dai_dai dasu ɗin
********************
MUNEEBBA
ranar haka ta kwanta sukuku ta tashi ba walwala Abinci ma don kar Mamma ta shiga cikin damuwa yasa taci, tunda Hajiyar Nazeer tazo tasan ta riga data rasashi kenan inama zata iya fitar da son Nazeer da tuni ta fitar dashi
kwance take tayi luf abin duniya dukya isheta jin wayarta na ring ya sata miƙa hannu ta ɗauke ta saman katifa, sunan wanda ta gani ne ya sata miƙewa tana sauke ajiyar zuciya a hankali tai picking call ɗin da sallama ɗauke a bakinta,
wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya Nazeer ya saki "Hayatee" ya kirata da wata kalar sassanyar murya wacce ta sata lumshe idanunta tana buɗewa, "mi ya hana kai picking call ɗina?" yaji saukar tambayarta
babu abinda ya ɓoye mata ya faɗa mata dukkan abinda ya faru, murmushin takaici tayi tana share hawaye, tare da barin zancen ta jawo musu wata firar sun jima kamar koda yaushe suna wayar kafin suyi sallama da juna
dukkan abinda Muneebba keyi Mamma na saurarenta girgiza kai tayi kawai "Muneebba" Mamma ta Kira sunanta da na'am ta amsa tana zama kusa da Mamma wacce Mamma ta tsira mata ido kamar tana ganinta dafa kafaɗarta tayi tace "Muneebba tabbas ni uwa ce kuma ina jin zafin dukkan abinda ake miki, yadda banyi rayuwar farinciki bana so kema ki taso cikin rayuwar ƙunci, domin duk yadda Mijinki ke sonki indai uwarsa bata sonki to babu kwanciyar hankali da zaman lafiya a rayuwar auratayya, kiyi istihara idan da Alkhairi Allahu zai tabbatar, amma ki rage wannan makahon son da kike yiwa Nazeer"
Jiki a mace ta amsa da "Insha Allah Mamma" murmushi kawai Mamma tayi
Bayan kwana biyu babu wata matsala da Hajiyar Nazeer ta sake shigowa da ita mu'amala suke da Muneebba tamkar su lashe junansu saboda so ga lokacin bikinsu saketa matsowa
tafe take ita da Hafsat a hanyar dawowarsu islamiyya tunda tazo bakin senter gidansu ta hanko Motar data saba gani wacce duk lokacin dawowarta islamiyya sai taga Motar, abinda ke ɗaure mata kai bai wuci yadda dattijon dake bayan Motar koda yaushe yake sakar mata Murmushi, kauda kanta tayi daga kallonsa tana jin zuciyarta na wani kalar harbawa saboda kamannin da take gani tattare dashi zuciyarta ce ta fara ayyana mata wani abun daban da sauri ta girgiza kai tana faɗin "kai ina ba haka bane ba dai shi bane" ta faɗa da sake kallon wajen da Babban Mutumin yake wanda kallo guda zakai masa kasan ya jiƙu da Naira, sai dai ganin mutumin na aman jini yana dafe saitin zuciyarsa yasa Muneebba zaro ido tana taɓa Hafsat tace "kinga kuwa abinda na gani?"
da tausayi tace "wallahi na gani Muneebba mutumin gwanin ban tausayi kullum fa sai yazo yana wa almajirai da talakawan Anguwar nan sadaka yanzun nan fa wajen ya ƙetaro naga ya duƙe yana Aman jinin nan" Hafsat ta faɗa kamar tai kuka
Jijjiga kai Muneebba tayi da tausayi tana faɗin Allah ya kyauta, a haka har kowacce ta wuce gidansu koda taje kayan islamiyya ta cire ta nufi bayi tai wanka da Arwalla ta fito, bayan sun idar da sallan Ishsha ne ta zauna tana kallon Khabir tana tariyo kamannin mutumin data gani
"wai lafiya ne kike kallona haka Muneebba?" Khabir ya faɗa yana kallonta, sauke tagumin tayi tace wallahi Ya Khabir wani mutum mai kama dakai sak na gani dandai shi ba fari bane, amma yadda kuke kama ta ɓaci, kuma fa kullum yana Anguwar nan yana sadaka, wallahi baka gansa ba gwanin ban tausayi ɗazun da zai ƙetaro sashen da muke fa ya kama aman jini baka gani ba"
wani dumm_dumm Mamma taji gabanta ya faɗin jin zancen ƴar tata ta tabbatar dashi ɗinne amma ba zata bari yaran nata susan da shine Mahaifinsu ba, "Ayya Allah shi kyauta kin san shi kama babu inda ba'a samun mai kama da kai, ga kaf danginku babu mai kama da Khabir da sai nace wani jinin naku ne" Mamma ta faɗa tana gyara ɗaurin ɗan kwalinta
Ajiyar zuciya Muneebba ta sauke jin zarginta bai tabbata gsky ba, ƙwanya Khabir ya sakar mata yana faɗin "kila dai idanunki gizo suke miki"