x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - BAYAN WUYA free pages complete

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 37650 words

Category: Tale Stories

Views 158

27 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
da ita yai kwaɗayin zama da ita,ya bata ilimin da bata samu ba, wanda kullum cike yake da mafarkin son kasancewa a tare da ita sai dai kash Mama Ladiyo ta riga tai mai katanga da dukkan wani cikar burinshi akan Shatu, ya shiga cikin damuwa sosai harya kai ga ko walwala ba yayi





ɓangaren Shatu ma haka yake kullum cikin kuka take wanda ta ida lalacewa tai baƙi ta ƙara rama, amma a haka Mama Ladiyo babu tausai ta saka Sati guda da bikin Shafu da Idi ɗan Jimmai, hankalin Shatu ba ƙaramin sake tashi yayi ba, tana ji tana gani aka ɗaura mata aure da Idirisa wanda taci kuka ta tabbatar data riga ta rasa gatanta iyayenta, haka aka kaita gidan Idi wanda shima ya ƙara zame mata baƙin kurkuku wanda kullum cikin cin dukan Idirisa take ga cin zalinta da yake dan ko kwanciyar aure sai dai ace fyaɗe yake mata wanda ta ƙara lalacewa sosai ga shaye'_shaye da yake wanda har giya yake sha idan ya shawo haka zai zo ya malaya mata Amai a yace kuma dole sai ta shanye sa,idan taƙi yai mata ɗan banzan duka da taji wahala haka ta gudu ta koma gidan Mama Ladiyo ta faɗa mata komai, amma sai Mama Ladiyo tace mata tayi haƙuri ta komawa nan ai shine zaman auren haka Mama Ladiyo da kanta ta tisa Shatu ta maida ita gidan Idirisa, Abinci kanshi Idirisa bai damu daya bata ba, ganin yunwa zata kasheta yasa ta dinga bin makwabta tana amso wankau tana masu ,wasu tai masu wanke_wanke shine zata samu ɗan Abinci, randa kuma babu ta kwana da yunwa, ta samu ciki ya kai biyu amma fyaɗe Idirsa shike zubar da cikin..........






By Riamcool Star of the Squad

08109554986,only call
[5/21, 8:09 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*

*Book 1*

*By Mariam sani Riamcool*


*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*



Bismillahirrahmanirrahim


*P.11&12*



__________✍️Wahala ba kad'an take sha ba ta shirya guduwa sau ba adadi amma sanin bata da inda zata yasa ta haƙura a haka har suka cimma shekaru biyu da aure tana cikin uk'uba duk ta ƙara lalacewa idan ka ganta ba zaka taɓa cewa Yarinyar mace bace kuma wacce bata tab'a haihuwa ba,haka zalika dukda ni san da Muhammad yai mata zuciyarta bata taɓa mancewa dashi ba koda da second guda ne



kullum cikin kuka take da fatan mutuwa, wata ranar Alhamis tana zaune lokacin Idirisa yayo shaye_shayensa yazo yai mata mugun duka sannan ya had'a mata da saki ukku cir,ba ƙaramin farinciki tayi ba na rabuwa da k'addararren auren, sai dai tunawa da Mamma Ladiyo yasa murna tata komawa ciki dan tasan ta koma za'a dasa aya daga inda aka tsaya don muguntar Mamma Ladiyo ba zata canza zani ba, koda taje ta faɗa mata abinda ya faru, ga mamakinta sai taga tayi murmushi tana lallashinta abin sosai ya d'aure mata kai sai dai tasan wannan murmushin na Mamma Ladiyo ba Alkhairi bane gareta, hakan yasa taci gaba da neman tsari gareta, wani abinda ya ƙara d'aure mata kai bai wuci yadda take bata Abinci akai akai ba, don tun tana tsoron kar tasa mata guba abinci harta dayaye take ci, amma bata saki jiki ba, wani k'arin abinda ya d'aure mata kai harta yarda Mamma Ladiyo tuba tayi shine kukan da take fashewa ta nemi gafararta, wani mugun dad'i Shatu taji ganin cewar Marik'iyar tata ta dawo daga daga rakiyar shed'an wata kalar tarairaya take sha don harta kammala Idda amma Mamma Ladiyo bata d'ora mata talla don Mamma Ladiyo kud'i tayi sosai wanda ta rasa ta inda take samunsa ga fitar daren da takeyi kullum hakan yasa ta dasa mata ayar tambaya da bincikenta a b'oye amma bata gano komai ba






tunda A'ishatu ta gama idda take zuwa inda take tallan goro a da wai ko zata ga Muhammad amma shuru kakeji tayi kuka don tasan ta riga da ta rasashi





Zaune take fatar nan tata data yamushe a baya yanzu tayi luwai saboda cimar da take samu wajen Mamma Ladiyo hakan yasa ta ƙara fitowa shar da ita fatar nan tata ta buzaye kamar ka latsa jini ya fito, sanye take da wata Atamfa ja mai ratsin yellow riga da zani wacce Mamma Ladiyo ta d'inka mata, fitowar Mamma Ladiyo da shirinta na Alfarma yasa ta maida hankalinta wajen Murmushi Mamma Ladiyo tai mata tana shafa kumatunta tana kallonta da ƴan jajayen idanunta kamar na Mayu harshe ta fiddo sai dai tunawa da wani abin yasa tai control d'in kanta tace "am ki zauna zanje wani bikin d'an k'awata kila na dawo yau ko kuma gobe" ta faɗa tana ficewa da sauri don jin idan ta tsaya ba zata iya dakatar da kanta daga umarnin zuciyarta ba



da kallo kawai A'isha tabita zuciyarta na harbawa da sauri tana faɗin Allah yasa kar zarginta ya tabbata don ta tsorata da yadda idanunta sukai ja da tana kallonta hawaye ta share tana zama, sosai ta lula cikin tunani har yaro ya shigo yana sallama bata ji ba sai da yai mata ukku sannan firgigit ta dawo tana tambayarshi me za'a bashi



"Ance ana sallama da A'ishatu" da mamaki take kallon yaron don tunda take babu wanda ya tab'a cewa yana sallama da ita idan ba Muhammad ba kuma tasan shi ya riga da yai mata nisa


"Kaje kace ba nan gidan bane" ta faɗa tana shigewa d'aki ba da daɗewa ba saiga yaron ya dawo yace "wai ance nan ne ki fito ki ganshi"


Ƙaramin tsaki taja tana dauko mayafi ta yafa ta fita sai dai ganin dalleliyar motar dake wajen ya sata zaro ido don tasan anyi b'atan kai ba dai wajenta ba juyawa yayi da nufin komawa taji an rik'e mayafinta k'amshin da taji da bugawar zuciyarta ya tabbatar mata da ko waye a hanzarce ta juyo tana kallonshi yadda ya kafeta da ido yana sakar mata da wani lallausan murmushi ita kuwa k'a waro masa manyan idanunta take don tabbatar da shi d'inne hawayen da take riƙewa ne suka samu damar sauka a kuncinta a hankali yasa hannu yana dauke mata su, "haba Aysher ki daina kukan nan haka nan kinsan fa a halin yanzu ke babba ce da da rabo da kin ajiye babba kamata" ya faɗa da sigar zolaya



ba shiri tai dariya tana k'ara kallonsa tana matsa yatsun hannunta wanda yasha ƙunshin ja, "Ina ka shiga?" ita ce tambayar da taji ta fito a bakinta wani murmushi mai ciwo yayi yana share zancen da jawo mata wata fira, itama ganin bai bata amsa ba yasa ta share, a wannan karon ma ya ƙara mata maganar aure wanda zuciyarta taji ta tsinke don tana gudun Mamma Ladiyo ta ƙara yi mata auren dole wanda ba zata jura ba k'ara ta gudu tabar gidan da ta rasa Muhammad a karo na biyu




ha sukai sallama jikinta a mace yake tana cikin zullumi, kwanciya tayi tana sak'e_sak'e a ranta bacci ya fara d'aukanta taji ana lashe mata fuska wanda firgigit ta buɗe idonta tana kallon baƙar magen da ke tsaye tak'i matsawa ta kafeta da idanunta juyayi tana fito da jan harshenta tana tand'e bakinta, Addu'a take son yi amma ta kasa da ƙyar ta samu taja wata Addu'a wacce yasa magen ja da baya tana mata Murmushi sannan ta jijjiga kai ta haura katanga,wata kalar zufa ce ta dinga tsatsafo mata cikin tsoro ta samu tayo Arwalla tayi salloli tare da Azkhar har bacci ya ƙara kwasheta







da safe Mamma Ladiyo ta dawo ganin jikin A'ishatu na kyarma alamun zazzaɓi ya sata tunkararta tana tambayar ta abinda ya sameta cikin tashin hankali, magani ta bata tasha ta gasa mata jikin




haka ta kwana biyu sannan ta warware ga Muhimman bai dawo ba,zaune take tana matsa hannunta bakinta na motsi alamar son ta yiwa Mamma Ladiyo magana, lura da hakan yasa Mamma Ladiyo fad'in "faɗi maganarki mana ƴata naga har yanzun kamar baki ida sakin jiki dani ba"


murmushi kawai tai mata cikin shakku ta faɗa mata yadda sukai da Muhammad, a mamakinta murmushi tayi nan take ta amince ta kuma nunawa Shatu jin daɗinta





sai da akai sati Sannan Muhammad ya dawo wajen Shatu ba ɓata lkc ta faɗa masa amincewar Mamma Ladiyo wanda yai murna kamar ya taka rawa haka yake ji, ba ɓata lokaci ya turo magabatansa aka tsaida ranaku wanda iya Sati aka saka, sati na zagayowa aka ɗaura auren A'ishatu da Muhammad wanda faɗa maku irin farincikin da masoyan suka shiga ɓata baki ne, wani satin na zuwa ta tare a katafaren gidanta wanda Part biyu ne nata saina Mansura sosai suke zuba soyayya wacce a gaban kowa basa jin kunyar nunawa junansu ita



haka sosai dangin Muhammad suke nuna mata harma da Abokiyar zaman ta Mansura wacce ta riƙeta da Amana, da kanshi Muhammad ya samo mata mai koyamata karatun Addini dana zamani, a haka har suka kwashe tsawon shekaru biyu A'isatu na samun ciki yana ɓarewa, wanda anyi na Asibiti dana gida amma babu sauyi, don duk lokacin data samu ciki haka zatai mafarkin magen nan wacce ta taɓa gani tana zaƙulo ɗan cikinta tana cinsa, da tashi cikin jikinta ke zubewa






da ƙyar aka samu cikin ikon Allah ciki ya tsaya a jikinta harta haifi Kyakkyawan yaronta mai kamar ubansa wato Khabir wanda duk wata kulawa tashi tana hannun Mansura, haka Habib shima yake kula dashi tamkar wanda suka fito ciki guda





sai da yai 7 years sannan A'isha ta samu wani cikin inda ta haifi ƴarta mace sak ita ta biyo, ranar suna yarinya taci suna Muneebba, wanda Muhammad yayi bajinta yai hidima tamkar bai san ciwon kuɗi ba, don tun ranar da Muneebba tazo duniya yake jin sonta daban a cikin yaransa, bayan kwanaki kaɗan itama Mansura ta haifi ƴan biyunta Mata waɗanda suka ci suna Hanifah da Sharifah, haka rayuwa ta gangara har Muneebba ta cika 3 year






misalin ƙarfe biyun dare gudu yake sosai harya ƙaraso Part ɗin A'ishatu yana zuwa ya saɓi Muneebba yana tashin Mamma, (wato A'ishatu) a firgice ta miƙe zatai magana ya rufe mata baki ya tado Khabir, a galabaice ya buɗe get ɗin gidan yana Aman jini haka yaja hannunsu suka dinga gudu har suka isa wani wajen Motar da yai parking shiga sukai ya fizgesu Ita dai A'ishatu ta kasa magana illa binshi da ido da take dan ta kasa gane me ke faruwa, ga bakinta yai mata nauyi ta kasa furta kalma koda guda ce wanda take ji tamkar an datse mata baki ne, tun dare suke tafiya sai gab da Asuba suka shigo garin Kano wanda ya saukesu a wata tshohuwar unguwa ya bata maƙuddan kuɗaɗen, ganin da gaske tafiya zaiyi ba mafarki take ba ya sata riƙo rigarsa ta baya wasu hawaye na bin kuncinta, shima kallonsu yake yana hawaye "ba nida zaɓi ne Aysher illa hakan, shine zai baku damar tsira da rayuwarku tabbas rayukanku na cikin haɗari, ba don ina so zan nesanta kaina daga gareku ba, saduwar Alkhairi" yana gama faɗin hakan ya janye hannunta yana shiga Motar ya wuce





durƙushewa wajen tayi ta fashe da kuka, da ƙyar ta rarrashi kanta har, tayi shiru.
kasancewar unguwar da jama'a yasa ta nemi temakon Jama'a ganin hada yara yasa wani Alhaji Mamman temakonta ta zauna a gidansa har saida ya samo musu gida da kansa, wanda ɗan zamanta a gidan tasha tsangwamar Maman Nazeer wato Matar Mamman wanda ko ɗanta yazo wajen Muneebba da zummar yi masa wasa zata dinga masa faɗa wani sa'in harda duka amma bai daddara haka washe gari zai ƙara zowa gun Muneebba da Khabir





Bayan sun dawo gidan sosai abubuwan suka rincaɓewa A'ishah Abinci kanshi na neman gagararsu sai wanda yaga Allah zai taimakesu a hakan ta saka ƴaƴanta makaranta, wanda tun dawowarsu taji mutane na faɗin wai wani yazo ya faɗawa mai unguwa a tada ita don ƴar bariki ce ƴaƴanta ma duka a hanyar bariki ta samesu, nan danan unguwar ta ɗauka wanda taci kuka sosai ta kuma daɗe kunnuwanta dana ƴaƴanta, sosai rayuwa ta ƙara juyewa Mamma a ciki kuwa harda makantarta wacce ta wayi gari kawai ta ganta taje anyi maganin amma duk a banza, ganin bata da isasshen kuɗi yasa ta haƙura,



dukda warning ɗinda Maman Nazeer taiwa Nazeer ɗin bai hanasa silalawo yazo gurin Muneebba da kawo mata kayan wasa dukkan wani abu ya samu Muneebba yake kawo mawa harta fara mallakar hankalinta wata kalar shaƙuwa ce ta shiga tsakaninsu da Muneebba, harta fara mallakar hankalinta ta wayi gari da soyayyarsa wanda bata san lkcn data shiga ba, a lkcn Khabir ya fara aiki wani gareji ciki ne suke samun nacin Abinci da ƴan buƙatunsu




tun da Muneebba ta wayi gari ta, ta shi da tsanar Mahaifinta wanda a ganinta da gangan ya barsu dan jawo musu rayuwar tozarci, wanda ta Alƙawartawa kanta koda taga mahaifinta ba zata ɗaukesa a matsayin Uba ba, duk lkcn da taga Mamma na kuka takan ƙara tsantar kanta da jin tsanar Mahaifinta, a haka ta taso da tsanar Mahaifinta har kawowar yanzun wanda babu mahaluƙin da take gani cikakken mara tausayi irin Mahaifinta.......



(tabɗi rigiji gabji, a kafta wasa farin girki ba'a fara wasan ba)



Love U all my Habibties a daure a dinga Share🥰plz Ina godiya ga masu ƙoƙarin Comments



Dawowa labari



Mu haɗu a next Page
[5/21, 8:10 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*

*Book 1*

*By Mariam sani Riamcool*




*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*


Bismillahirrahmanirrahim


*P.13&14*


*DAWOWA LBR*



_______Tun da ta shiga ɗakin take faman rizgar kuka wanda tana ƙara jin zuciyarta na hauhawa da farashin tsanar Mahaifinta, jin gyaran muryan Mamma yasa ta ɗago da fuskarta wacce tai jawur saboda kuka share hawayen tayi tana kama Mamma ta zauna faɗa Mamma ta soma yi mata kamar zata ari baki, wani kukan ta sake fashewa dashi, banza Mamma tai mata har tayi mai isarta




koda Khabir ya dawo yai lallashin duniya amma taƙi sakin jiki taci koda Abinci ne gani take a Silar rashin mahaifinta zata rasa Nazeer wanda ba zata iya juran hakan ba, waya ta ɗauka tana danna masa kira wanda tayi yafi a ƙirga amma bai maido ba, zuciyarta ce ta sake tsinkewa tex ta tura mishi nan ma babu reply shiru,





Kwance yake yana juyi bisa makeken gadonsa yana ganin kiran Muneebba na shigowa a wayarsa amma ya gaza ɗauka saboda Hajiya data kasa ta tsare wayar ma hannunta take, kallonsa Hajiya tayi tana taɓe baki tace "wai ni Nazeer na rasa me ka gani a jikin yarinyar nan duk kyau da izzarka amma ace ga ita ka liƙe ita ɗimma ƴar zina marar asali da galihu ga ƴaƴan Manya masu asali da dukiya suna binka amma kaƙi kulasu to bari kaji wallahi indai kaga kayi auren nan bana numfashi, amma aure kasa niyya ban hanaka ba" tana kaiwa nan ta miƙe ta fice



da kallo kawai ya bita yana jin wasu siraran hawaye na biyo kuncinsa ko kaɗan baya son kalmar rabuwa ta gifta tsakaninsa da Muneebba da zai iya rabuwa da Muneebba da tun yana ɗan ƙanƙani zai rabu da ita ko dan dukan da yake sha a gurin Mahaifiyarsa amma ina bazai iya ba sonta ya riga da yai masa mugun kamu wanda ya zamto guba a jikinsa, ɗauke hawayen yayi da yatsan hannunsa yana miƙewa ya shiga Toilet Alwalla yayi yai nafila yana fawwalawa Ubangiji lamurransa bacci a ranar sai dai ɓarawo ya ɗaukesa



A ɓangaren Muneebba ma hakan ta kasance



*ASAD BOBBI*

Jerin gwano motoci ƙirar Marcedes Benz farare sol ke tsula gudu a titin wanda ganin irin gudun da suke ne zai tabbatar da ba lafiya ba, hakimce yake a bayan Motar ya lumshe kyawawan idanunsa yana yamutsa sumar kansa gani yake kamar motocin basa gudu buɗe lumsassun idanunsa yayi yana kallon wani gefe daban wanda a zahiri ba can yake kallo ba ya tafi wata duniya ta daban jin tsayuwar Motar yasa hankalinsa ya dawo a gangar jikinsa, a hankali yakai dubansa ga wajen yadda mutane sukai cincirindon da ƴan jaridu kallon Company yake yadda gobarar ta ƙonesa ƙurumis ga kayayyakin da suka ƙone suma ana fito dasu rufe idonsa yai yana ƙara buɗesu, duk fitowa na cikin Motar sukai Sai Motar da yake ciki ce ba buɗe ba, tun tsayuwar Motocin mutane da ƴan jaridu suka zuba ido da son ganin wanda ke ciki har akai 5 Minute, a hankali aka buɗe Motar yana zuro da Kyakkyawar ƙafarsa wacce take cikin takalmi Cover shues masu azababben kyau saida yai wasu ƴan mimtuna sannan ya zuro da gudar ƙafar tasa yana ida fitowa, kowa na wajen kallonsa yake yadda ya wani haɗe rai kwarjini da haiba sun taru a jikinsa, uwa uba Izza da jin kai wanda a jininsa suke, a hankali yake takowa ƴan Jarida nayo masa caaaa ko wane na wullo masa tambaya, wani ɗan Jaridan ne yasha gabansa yana ƙara gyara farin gilashi idonsa "me zaka iya faɗa mana game da ƙonewar Company ka, shin da gaske abokan hamayyarka sune sukai ta'addin ƙonewarsa, sannan..." bai idasa ba saboda wani kallo da Bobbi ya jefeshi dashi wanda yasa shi haɗiye kingin tambayoyinsa yana bashi hanya



Kallon ɗan Jaridan yayi yana sakar masa wani killer smile wanda shi kaɗai yasan ma'anarsa, kai tsaiye ya shiga Company da securities ɗinsa kallon Company yake ganin yadda har iyanzu bai daina hayaƙi ba, cije lips ɗinsa na ƙasa yayi sannan ya sake sakin wani shu'umin murmushi "Zaidu" ya furta a hankali




Ma'aikan Company ne suka taru suna miƙo gaisuwa babu wanda ya amsa mawa kallonsu yake ɗaya bayan ɗaya yana nazartarsu, wanda kowa cikinsa ya ɗuri ruwa uwa uba Manager Company, bai ce uffan ba har manager ya miƙe yana magana tare da saddar da kansa yace "Oga ka gafarce mu wallahi dukkammu ba musan yadda akai gobaran ta tashi ba"



shiru ya ƙara yi na wasu daƙiƙu dan sun fidda ran da zai basu amsa "Ok ban tambayeku ba'asin yadda akai gobaran ta kama ba, bana buƙatar jin wani ƙarin zance daga gareku haka Allah ya riga ya tsara mana" suka ji saukan muryanshi wanda yake yi kamar baya son buɗe bakin nasa don shi magana wahala take masa




yana gama faɗa ya miƙe yana fitowa wani ƙaramin tsaki yaja ganin yadda mutane ke kallonsa kamar ba Mutum ba ga hayaniyarsu
End Ads