Yah Bobbi ko da ace yana da Mata 3 ne ni zan zauna a ta 4, saboda ƙaunar da nake masa dukda bai san dani ba, Mammi na kasa samun zuciyar Yah Bobbi"
"Daughter zaki samu zuciyar BOBBI, zan samar miki da ita tabbas zan mallaka miki zuciyar BOBBI ko da ace zan rasa rayuwata ta wannan hanyar, sannan ko da ace DEEN na raye tabbas zaki zauna dasu su biyun zaki mallaki zuciyarsu"
wata doguwar Ajiyar zuciya Maheer ta saki tana du ban Mammi da mamaki "Mammi me kike nufi"
"ba zaki gane abinda nake nufi ba Maheer"
Numfashi Maheer ta ja, tana tashi daga cinyar Mammi, hawayen dake ambaliyar a kuncinta, ta saka hannun ta share, tare da miƙewa ta nufi ɗakinta dan jin tsohon mikin daya daɗe mata a zuciya na tashi, wato Soyayyar DEEN wanda ba tasan shi da BObbi waye tafi ƙauna ba, jiki a mace ta faɗa bedroom ɗin ta tare da faɗawa bisa makeken Bed ɗinta ta fashe da kukan tausayin kanta,zuciyarta na azabtar da ita da soyayyar mutum biyu, sai da taji kamar kanta zai tsage gida biyu sannan tai shiru tana mayar da numfashi,bacci ɓarawo na ɗaukar ta
**********************
*ASAD BOBBI*
Ƙit ƙit ƙit sautin ƙarar agogon ɗakin ke badawa a daidai ƙarfe 2:00Am na dare a dai_dai lokacin ne kuma wayarsa ta fara ƙara Alamar Alarm ne ya buga,
A hankali ya fara ware manyan idanunsa tare da motsa bakinsa A hankali yana karanto Addu'a, kamar an tsikaresa yai wuf yana miƙewa da azama, Bathroom ya faɗa ya fito, wasu kaya da ke gefe baƙaƙe wuluk ya ɗauka yana sakawa sannan ya ɗauki baƙin ƙyalle yana rufe fuskarsa, komai na jikinsa sai da ya rufe da baƙin ƙyalle, wayoyinsa ya kashe yana ajiyesu a gefe ya fice
wani Coridor yabi yana tafiya har ya isa ɗan ɗakin,mabuɗi ya saka yana buɗewa tare da haska Tocilan ɗin hannunsa, du bansa ya maida gefe yana kallon Mutumen dake kwance shi ma da kalar shigarsa, cikin tafiyarsa ta Jaruman maza ya tunkarosa, duƙawa yai yana yaye baƙin ƙyallen daya rufe fuskarsa ya kware, ƙare masa kallo yai yana sakin wani Miskilin Murmushi, tare da zare ID card ɗin da ke gaban rigar mutumin da kuma phone ɗin sa, da azama ya fito yana rufe ɗakin tare da bi ta ƙofar baya, wanda babu wanda zai taɓa cewa akwai wata ƙofa a tanan, ɗan gudu gudu yake haɗawa, harya fice bakin layin gidan nasa, wayar y kunna yana turawa Number dake cikin Sim ɗin message,
kamar jira ake sai ga wata mota baƙa wuluk, dai dai wajensa ta tsaya ana buɗe masa murfi, da Azama ya faɗa cikin motar, rufe marfin Motar aka yi mutumen dake gefensa yana saka masa baƙin ƙyalle ya rufe masa Idanu, da ƙarfin gaske suka figi mota suna sharara Uban gudu kamar zasu tashi sama,sunyi tafiya ba ta wasa ba sannan suka isa mugun ƙungurmin jejejin wanda ba zaka taɓa tsammanin mutum zai kawo kansa a gurin ba
Fitowa sukai suna tsayawa bakin gidan tare shigewa a ciki,taresu wasu ƙazdawan Mutane sukai tare cewa su nuna ID card nash, nunawa sukai sannan suka shige, wata ƴar hanya suka bi wacce ta sadasu da wani ɗan ƙaramin Holl, da bismillah ya ɗaga ƙafafunsa yana shiga, kujera ya ja ya zauna suma haka mutanen da suka tafo a tare, Mutane nen wajen ya kalla a ƙalla sun kai 12 a wajen taune lips ɗinsa na ƙasa yai yana bin kowa da ido
Miƙewa wani mutum yai yana zagayasu tare da ƙirga su, sannan ya dawo ya zauna, tare da gyaran murya ya fara magana da muryan mugaye masu ji da ta'addanci "As you know, every beginning of the year we have this meeting bcos muna son ƙara ƙwatarwa wannan ƙungiya tamu ƴanci, sannan muna kawar da duk wanda ya shige mana gaba,a wannan shekarar muna buƙatar akwatin wasiƙar sirrikan Company A.A.B limited don shine ya shige mana gaba yanzu ya hana masana'antummu ci gaba, shi ne ya saka aka fara zaƙulu gurɓatattun Company mu, da wasiƙar ce kaɗai za mu iya cin galaba a kansu, wannan shi ne Step one wanda idan yai za muje a Step 2, ina son a fitar da gwarzon Namiji wanda zai iya satar Akwatin wasiƙar a ƙasar Italian"
wajen tsit yai kowa na Imagine cikin dakiya da murmushi Bobbi ya miƙe yana sauya muryarsa ya zuwa ta gwarazan maza da tantirai "Can I choose someone who can do this job for you?"
da kallo mutumin ya bisa yana miƙewa ya daki kafaɗarsa "Yes you can as long as we have a mailbox"
Murmushi ya saki yana furta "ok Sir" fitowa yai yana zagayasu, kafin ya ƙure ƙazdin Mutumin dake zaune a wajen wanda tabbas ya ganesa kuma ya sansa gun a jajircewa wajen ta'addanci da cin galaba yana son a kara a wasan shi ya sa zai zaɓesa, hannu ya saka yana nuna sa "Of course wannan zai iya, in har yai nashin nasara nine zan karɓi hukuncinsa ina da sure akan zai mana abinda muke so"
Shiru shugaban yai yana furta " rashin nasara fa yana dai_dai da fitar numfashinka, muddin muka faɗi a matakin farkon nan za kayi ban kwana da rayuwarka, ka san mu kammu abin sai ya shafemu a wajen manyan Shuwagabannin ƙungiyar nan"
"Yes na Amince" ya faɗa yana zama tare da danna zoben hannunsa yana binsu da ido,
kowa bashi dama akayi akan su faɗi ra'ayoyin su akan zaɓen wanda zai saci mailbox din, wasu suce bai yi ba wasu suce yayi, waɗanda suka fi raja'a shine zaben da akayi yayi shi yasa aka bar wanda Bobbi y zaɓa
**************
*YOLA*
Fattu
cikin tsoro da razana Fattu ke bin Ja'e da su Sa'adu da kallo, girgiza kai tayi hawaye na biyo kuncinta, wani wawan mari Ja'e ya kwalfa mata, yana ƙara sauke mata wani a kunci, "Fattu dama ke ƴar iska ce? Wato iskancin naki ya fi ƙarfin ki bi na gari sai dai ki jawo mana baren kwarto ki kawo mana,to wallahi yayi ta rayuwarsa zan rabasa da duniyar, sannan nayi abinda nake son yi dake a yanzu kafin aurena dake, zan yaga miki rigar mutunci Fattu" ya faɗa yana kai hannunsa jikinta yana kince zanin jikinta
durƙushewa tayi a wajen tana fashewa da wani kalar marayan kuka mai ban tausayi tare da girgiza masa kai..........
[5/21, 8:13 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*
*Book 1*
*By: RIAMCOOL*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*P.27&28*
_____________Durƙushewa tayi a wajen tana sakin wani marayan kuka tare da ƙanƙame jikinta tana girgizawa Ja'e kai bakinta na karkarwa
"Wallahi ban taɓa abinda kake zato ba, haka zalika ban taɓa kusantar zina ba, ina ƙyamatar zina ina ƙyamatar mai yin ta, kamar yadda Ja'e kai ma nake ƙyamatarka na tsani halayyarka ta zinar" ta faɗa tana zubar da hawayen takaici
wani wawan mari ya sake kwalfa mata wanda ya saka bakinta fashewa yana tsartuwar jini, dogon gashin kanta yaja da ƙarfi yana ɗagota kafin ya fashe da wata muguwar dariya yana bin manyan Boobs ɗin ta da kallon haɗama,fuskarsa ya kai dai_dai sai tinsu yana gogawa, wanda nan take wani matsanancin ɓacin rai ya ziyarci Fattu, turesa take da iya ƙarfinta tana ihu, tare da kiran JODDi wanda tunda Ja'e ya riƙe Fattu ya ke dubansa da rinannun idanunsa bakinsa na karkarwa tare da jikinsa kamar mazari
rigar jikinta yake ƙoƙarin zarewa wanda ya riƙeta da iya ƙarfinsa yana son cimma burinsa, kamar mai nazari haka JODDi ya lula yana kallon dutsen dake gabansa, hannun ya saka yana ɗaga ƙaton dutsen da iya ƙarfinsa yana saukewa Ja'e a kai, wata muguwar ƙara Ja'e ya saki yana dafe sai tin gefen kansa wanda ya fashe yana tsartuwar jini, cikin dakiya da tafiyar ƙarfafan maza ya tako ya zuwa gun Ja'e yana ƙara shaƙosa da iya ƙarfinsa, ya ƙara kai masa wani wawan duka a gefen wuyansa wanda ya saka sa tafiya luuuu yana faɗuwa idanunsa na rufewa wanda numfashinsa ya tsaya cak
cikin razana Sa'adu yaja da baya yana
yada makaminsa,yana barin wajen da gudu cikin tashin hankali, jikin Fattu na karkarwa ta miƙe tana ja da baya tare da ɗora hannu a ka, kallonta JODDi yai yana ɗaukar zaninta ya miƙa mata tare da kauda kansa gefe yana shigewa bukkar
Zanin ta ɗora tana duƙewa wajen ta fashewa da kukan tashin hankali,domin tabbas ta san akwai babban Abin da zai biyo baya muddin Ja'e ya mutu, yan zun ta san da cewar rayuwar Joddinta na akan haɗari, amma taya zatai ta cecesa daga wannan ƙangin daya jefa kansa a ciki ta ina zata ja sa su gudu domin tsira da rayukansu waɗanda suke daf da gangara
*************************
MUNEEBBA
Kiran sallar Asuba ne ya tasheta daga barcin wahalar daya kwasheta mai cike da mugayen mafarkai masu firgitarwa
bakinta ɗauke da Addu'a ta miƙe tana ƙara buɗe idanunta waɗan da su kayi mata nauyi ta kasa buɗesu saboda kumburin da su kayi
kamar wacce aka yiwa shegen duka haka ta miƙe ko ina na mata ciwo Toilet ta faɗa tana wanka da ɗauro Arwalla tare da kabbara salla, bayan ta idar ta hau rera karatun Alqur'ani wanda ya fara sanyaya mata zuciya, ta daɗe tana karatu kafin ta ɗaga hannayenta sama tana kaiwa Ubangiji kukanta,bata tashi daga kan sallayar ba sai da rana ta fara fitowa sannan ta fito Falo tana kwanciya nan take wani sabon baccin ya sake kwasheta
ruwan sanyin da taji an zuba mata ya sakata tashi a razane tana furta sunan Ubangiji, bata ida dawowa ba taji an kwasheta da mari tare da ƙara mata wani,hannunta dafe da kunci ta ɗago tana kallon Mommi wacce take Binta da kallon wulaƙanci "ke har kin samu wajen zama ki kwanta ki huta ko? to ki sani wallahi tun yanzu zaki fara karɓar hukuncinki, na aurar man Yaro da ki kayi, ke da rayuwar jin daɗi a gidannan har abada, ki sani Auren bauta ne ya kawoki gidan nan domin bauta ce zaki ci gaba da yi mana tun daga yau"
tun da Mommi ke maganar Muneebba ta mayar da kanta ƙasa hawaye na mata ambaliya a kunci "Ya Allah wannan wace kalar ƙaddarariyar jarabawa ce ka jarabceni da ita a lokaci guda? baya ga wacce nake ciki"ta tambayi kanta
"Maza tashi ki sauya kayan jikinki ya zuwa na hause mad kizo ki shige cikin ƴan aiki domin tun daga yau zaki fara aiki,yau ko mai kece za kiyi, sannan tun daga yanzu ina son duk wanda zai zo ki nuna masa cewar ke ƴar aiki ce, har Mijin naki karki nuna masa cewar kece matarsa zan san yanda zanyi"
kamar wata taɓaɓɓiya haka Muneebba ke bin Mommi da ido da mamaki, wanda marin da ta sake ɗauketa dashi ne ya sakata dawowa hayyacinta, da yatsa Mommi ta nuna ta tana furta "ke ki bini a sannu wallahi ba'a min da wasa ki aiwatar da abinda na umarceki ga kaya nan na baki nan da 5 Minute ki canja ki fito" ta faɗa tana juyawa
kamar jira Muneebba take ta fita ta fashe da kukan da sai yanzu ta samu ya fito, wace kalar baƙar rayuwa ce ke shirin tunkarota? baya ga ƙaddarar rabuwarta da Nazeer,ga kuma wata na shirin ɓullo mata ta ɓoye kanta a gurin Mijinta, hawayen ta share tana cire kayan jikinta ta mayar dana house mad wanda riga da skert ne blue color, hular ta ɗauka tana saka ma kanta, kamar wacce ƙwai ya fashewa haka ta fito tana tafiya a hankali
tsayawa tayi ta rasa ta hanyar da zata bi taje Part ɗin Mommi, bubbuga bayanta da taji anyi ya sakata juyowa tana kallon Indo wacce take sakar mata Murmushi wacce daga gani ba zata wuce sa'arta ba, "Sannu ko Hajiya ce tace nazo naje dake mu fara aiki" Indo ta faɗa da ƴar fara'a
murmushin yaƙe Muneebba ta ƙaƙalo tana ɗaga mata kai ba tare da tace ƙala ba, duk inda Indo tayi nan Muneebba ke Binta, wani Coridor ta jata in da zata kaita waje shugabarsu ta bata aiki, tafiya suke har suka isa Side ɗin ƴan aiki waɗanda kowa aikin gabansa yake, ɗakin dake daga gefe Indo ta shiga da ita da sallama ɗauke a bakunansu, amsa musu ƴar dattijuwar dake zaune tayi
cikin mutuntawa Muneebba ta sake gai sar da ita "Ok kece wacce Hajiya tace sabuwar ƴar aiki za a kawo na baki aiki?"
"Eh" ta furta tana wasa da yatsun hannunta, "ok Indo je ki gwada mata Falon Hajiya da ɗakunansu in da ita ce zatana dinga kula da gyaransu, sai fannin girkin da zaku ɗin ga shiga kichen a tare" Baba Sa'a ta faɗa
*Asad BObbi*
bai baro wajen ba sai ƙarfe 4 na dare wan da sai da aka rufe masa idanunsa da baƙin ƙyalle sannan aka mai do sa in da aka ajiyesa
ta ƙofar baya daya fito ta nan yabi ya koma yana shiga ya cire vaƙar shigar da yai yana shigewa ciki, haɗaɗɗen Falonsa ya nufa yana zama kan ɗaya daga cikin kujerun zobe dake hannunsa ya kalla yana murzasa, nan take ya kawo wata jar danger, murmushi ya saki yana miƙewa.ya faɗa bedroom tare da dauko Laptop ɗin sa, zama yai yana kunnata kafin ya fara sarrafata cikin gwanancewa
hannun ya saka yana zare zoben hannunsa tare da ɓalle dutsen sama ya fito da ƴar wata na ura, Flash ya ɗauko yana sakawa a ciki, sannan ya saka cikin computer, Vedio da ta naɗa ya Kunno yana kallonsa a tsanake, tun daga shigarsa motar har ya zuwa isarsu jejin da akayi Meeting ɗin
Ƙara kallon vedio yake tare da kallon hanyar da suka bi, wacce babu wanda zai yi tsammanin akwai wata hallitar ɗan Adam da zata iya ratsawa cikin ta cikin jejin,Ajiyar zuciya ya saki yana lumshe manyan idanuwansa "shin ta ina zai fara tarbar wannan gagarumin aikin dake tunkarosa?" ...........
*Assalamulaikum Habibties kuyi haƙuri bi sa ga tsayawata da Rubutun Bayan wuya kwana biyu, I'm Appreciate da kulawa*
*Bismillahirrahmanirrahim*
*P.29&30*
_______________Miƙewa yai yana faɗawa Bathroom yai wanka tare da ɗoro Arwalla kasancewar Asubah tayi, jikinsa ɗaure da towel y fito ɗayan towel ɗin kuma yana goge gashin kansa, Jallabiya ya zura yana ɗaure dogon gashin kansa ya fita Masallaci
Ko da ya dawo a gajiya ya kwanta yana rufe idon sa wani bacci mai mai nauyi na ɗibarsa
Bashi y farka ba sai wajen sha biyu na rana ya buɗe idanuwansa, bakinsa ɗauke da addu'a y tashi yana janye dogon gashin kansa wanda y rufe masa fuska, cikin jarumta da kuzari Bobbi y miƙe yana shiga Bathroom wanka ya sake yi ya fito, cikin tafiyarsa ta ƙasaita ya ƙaraso , haɗaɗɗu Lotion ɗin sa masu ƙamshi ya shafa, kasancewarsa ba ma'abocin saka manyan kaya ba ya saka sa ɗauko ƙananan kaya ƴan ubansu masu matuƙar haɗuwa da tsada brown color, sai rigar cikin da take fara
, agogon Diamond ya ɗora a tsintsiyar hannunsa wacce ta zauna tsam a Kyakkyawan hannun nasa, kama dogon gashin kansa yai yana ɗaurewa wanda yake vaƙiƙƙirin sai ƙyalli yake, turaruka masu tsada da ƙamshi y feshe jikinsa dasu, sosai y zuba uban kyau dan tabbas duk wata ƴa mace mai jini a jiki ta gansa dole wani abu y ɗarsu a ranta, kyakkyawan Ba indiye sak Bobbi ya fito, fuska a haɗe ya ɗauki wayarsa yana nufo inda Photon DEEN yake, murmushi ya saki wanda fararen hakoransa suka bayyana yana shafa photon kamar yacce ya saba duk lkcn fitarsa da kuma dawowarsa, a faffaɗen ƙirjinsa yaiwa Photon masauki yana rungumesa tsam a jikinsa tare da sauke Ajiyar zuciya "DEEN ta ina zan fara ɗaukar maka fansa ne?," Ya tambayi kansa
ya jima a haka kafin ya sauke Photon a ƙirjinsa yana ƙarewa Photon kallo wanda DEEN ɗin ke dariya, lumshe idanuwansa yai yana ƙara buɗesu ya mannawa Photon sumba ya fice
koda ya fita escord nashi na nan a baki ƙofar ɗakinsa, fararen motoci farare sol aka shirya masa ƙirar Bugati masu matuƙar kyawu da birgewa, cikin ta biyu aka buɗe masa yana shiga y hakimce a baya tare da ɗora ƙafa ɗaya bisa ɗaya yana lumshe idanuwansa wanda wannan ya zame masa Al'ada,ba tare daya kalli Driver ba y bashi Address ɗin inda zasu nufa, cikin tsari da tsaruwa motocin suka bar harabar gidan nasa suna nufar gidan Dad, a hankali Motocin suke tafiya gwanin burgewa da tsari don tun da suka hau Titi duk wan da yaga tabbas y san wani babba ne zai wuce, hakan ya saka ana kaucewa a basu hanya
ba tare da ɓata lokaci ba suka isa gidan tun daga wucewarsu get ɗin farko Bobbi ya tsinci kanshi cikin wani kalar ɓacin ran daya rasa na miye, Addu'a yaci gaba da yi harya samu zuciyarsa ta lafa da ɗacin da tai, jin ƙara buɗe murfin motar y saka sakasa dawowa tunanin daya tafi, yayi five minute kafin ya fito, A hankali yake tafiyarsa mai cike da Izza da tsantsar jarumta, ƙofar Falon ya buɗe bakinsa ɗauke da sallama wacce ba ta fito ba,
Mommi da Mammi da suke zaune suna ƙara tsara yadda bikin Maheer da Bobbi zai kasance, ganin Bobbi ya saka Mommi miƙewa tana tunkarosa rungumesa tayi tana sakin kuka "Asad ina ka shiga? ka barni cikin zullumin halin da kake ciki akan auren da akayi ma" ta ƙarashe da kuka hada sheshsheƙa, hannunsa ya saka yana ɗago da fuskarta ya share mata hawayen tare da sakar mata Murmushi, yana furta "Ba abin da ya faru dani,Ayuka ne su kai man yawa,ki kwantar da hankalinki Mommi"
da to ta amsa tana kamo hannunsa tana zaunar dashi murya a dashe ya gaisae da Mammin Maheer,kallonsa Mommi tayi tana kiran sunansa "Asad" da na'am y amsa yana mai da dukkan wata nutsuwa tasa a gunta
"Asad me ka ɗauki wannan auren na Maheer?" Mommi ta tambaya, cikin ko in kula y furta "Auren haɗi"
wani ɗaci da zafi ne y ziyarci zuciyar Mammi akan furtawar da yai auren haɗi, wato ƴarta ce kaɗai ke hauka, ƴarta ce kaɗai ta makance a soyayyar Bobbi,ba tare data kallesa ba ta furta "Bobbi auren haɗi fa kace ?"