Allah dani da kai mutu ka raba" murmushi yai yana mata sallama dan zuwa yai wanka, "ok bye take care" ya furta tare da kashe mata ido
Murmushi tai tana rufe fuskarta da tafin hannunta, da ƙyar ya kashe wayar shima dan Abokansa na masa tsiya ne kar lkc ya ƙure ango ya makara
Ajiyar zuciya ta saki yau jinta take cikin maɗaukakin farincikin da bazai musaltu ba, miƙewa tai Hafsat na ɗaukar su Photo wanda sunyi kyau sosai
Ƙarfe 2:30 wajen ɗaurin auren damƙam yake da mutane da manyan jiga_jigan motoci na alfarma wanda kowa sai da yai mamakin ganin manyan Mutane da suka zo ɗaurin auren
Zaune yake a bayan mota mai baƙin glass Wanda babu wanda ke ganisa fuskarsa sanye da farin gilashi janye gilashi yai yana share hawaye, ya gaji da wannan bakar rayuwar da yake ciki wanda dashi da iyalinsa sai dai kallo daga nesa Anya zai iya kuwa? ace ana ɗaura auren Ƴarsa guda wacce take mafi soyuwa a rayuwarsa amma ba zaije ba, kamar ba babban mutum ba haka ya fashe da kuka mai ban tausayi, Manyan Motocin da suka Kunno Kai su suka saka sa tsayawa da kukansa yana kallonsu, fitowa na cikin Motar yai tareda Securities murmushi ya saki ganin Ahmed A Sadis ya hallara
tunda Motocin suka hallara gaba ɗayan Mutanen wajen hankalinsu ya dawo wajen ganin shahararren ɗan kasuwa mai ji da kuɗi, murmushi yai ya samu waje ya zauna, nan ya bayyana musu shi ɗan uwan Mamma ne yana so a bashi waliccin babu ɓata lokaci za'a fara gudanar da ɗaurin aure
cikin hamzari Nazeer ya miƙe jikinsa har ɓari yake jijiyoyin kansa sunyi ruɗu_ruɗu "bana buƙatar auren nan bana so na fasa auren kada a ɗaura man aure da Muneebba wallahi bana so na fasa" ya faɗa da ƙarfi kamar zuciyarsa zata fito
tsit wajen yai kowa na kallonsa da mamaki yanda yake kuka riris tareda sheshsheƙa, da gudu Alhaji Mamman yazo yana faɗin "Nazeer kana cikin hankalinka kuwa? idan baka cikin hankalinka ka dawo, ko wani abun Muneebba ta aikata?"
"Wallahi bana sonta kawai na fasa dan Allah a janye auren nan kowa ya tafi" Nazeer ya faɗa, babu yadda ba'ai da Nazeer ba amma yaƙi hakan yasa Mutane fara haramar tafiya, sai dai ɗan shelar da yai magana ne akan kowa ya dawo za'a ɗaura aure yasa su dawowa ana zama, Nan take Dad ya fiddo 500k yana bada sadaki bai tsaya wani dogon tunani ba, Sbd ɓacin rai, mutane saiji sukai ana faɗin an ɗaura Auren Muneebba Muhammad tareda Asad Ahmad Bobbi akan sadaki 500k lakadan ba bashi,
Nan take wajen ya kaure da hayaniya ganin abinda Dad yai tare da mamakin babban millionaire Asad BObbi da Muneebba ta aura nan take yanke ƴan faɗi ba'a tambaya ba suka fara watsawa a media, ana gama ɗaurawa Dad ya miƙe da nufin zuwa gidan su Muneebba dafashin da yaji anyi ya sashi juyawa yana kallon Abbie wanda ya dora kansa a kafaɗa yana kuka riris tareda Habib shima wanda kukan yake, ɗago da Abbie Dad yai shima hawayen nason taruwar sai dai yai ƙoƙarin shanyesu yana ƙaƙalo murmushin dole, "haba Muhammad miye na kuka kamar ƙaramin yaro kaga yadda mutane hankalinsu ya fara dawowa wajenmmu, kayi shiru mana"
"Dad wallahi dole Abbie damu kammu muyi kuka baka san halin da muke tsintar kammu ba har yanzu kasan kuwa ita kanta halin da Ummi ta shiga dalilin haka fa har yanzu Ummi ko magana ba tai, ita Mamma makanta Ita Ummi rashin magana, shi Abbie Aman jini, shin Dad ka faɗa mana wanna ba abin ai kuka bane?" Habib ya faɗa tareda share hawayensa
"bani da abinda zance maka Yah Ahmad haƙiƙa ji nake a yau ka maye mani gurbin yayyena banda abinda zance maka na fitar da ƴata kunya dakai, bani da bakin gode maka" Abbie ya faɗa tare da share hawayensa
Murmushi Dad yai yana dafa kafaɗarsa tareda ɗago haɓarsa yana share masa hawayen yace "Muhammad ba batun gdy a tsakanimmu nima ai ƴata ce bata da wani banbanci tsakaninta dasu Iftihar kamar yadda suke ƴaƴa itama haka take a wajena, kayi haƙuri komai mai wucewa ne"
A can gidan kuwa gidan ya kacame da guɗa ana faɗin an ɗaura aure, Muneebba dake ɗaki wani irin farinciki ya kamata tana tashi ta rungume Hafsat tace "Alhmdllh yau burina ya cika na zama matar Nazeer Hafsah ko yanzu na koma ga mahaliccina nayi farinciki" ta faɗa tana dariya, dariya itama Hafsat ta saki tana tsokanarta tare da kingin Abokansu,
Khabir ne ya shigo jiki a sanyaye jiki ba ƙwari "bada Nazeer aka ɗaura ba Mamma wallahi bada Nazeer bane" Khabir ya faɗa yana fashewa da kuka tareda rungume Mamma kamar wani ƙaramin yaro, Salati Mamma Ladiyo ta saki da ƙarfi yadda kowa zai iya jiyowa har maƙota tace "Nazeer kana nufin bada Nazeer aka ɗaura auren Muneebba ba, to waye mijin??? Innnalilahi wa'inna ilaihirraji'un A'ishah kuna ganin jarabta" Mamma Ladiyo ta ƙarasa zancen sa fashewa da kukan Munafurci wanda kowa zaiyi zaton daga zuciyarta yake fitowa
MUNEEBBA dake ɗaki tana dariya jin zancen da Mamma Ladiyo tai ya sata fitowa ɗakin da gudu tana kallon Yah Kahabir da Mamma wanda suke hawaye, kallon Mamma Ladiyo Khabir yai yana faɗin "Mamma Ladiyo Nazeer cewa yai ya fasa baya son Muneebba wallahi da kansa ya furta ya fasa" wani irin zillo zuciyar Muneebba tai tareda harbawa baki na karkarwa da jikinta tace "Yah Khabir wallahi ba gsky ka faɗa ba, ka gyara kalamanka Nazeer bai taɓa ƙina ni nasan da Nazeer aka ɗaura man aure kada ka ƙara danganta igiyar aurena tare da wani Yah Kahabir Nazeer ya riga daya zama nawa" ta faɗa tare da durƙuahewa wajen tana sakin wani marayan kuka tareda fatan Allah yasa ba dai dai kunnuwanta suka ji mata ba,
"Ai kam Muneebba sai haƙuri yanzu Rabilu kefa ce man bada Nazeer aka ɗaura ba da wani Asad BObbi ne wanda duniya tasan dashi, kuji ikon Allah" Rabi maƙociyarsu data yafo zani ta faɗa
basu ankara ba sai jin faɗuwar Muneebba sukai ta zube ba numfashi a tare da ita, idanunta sun wani ƙaƙƙafe, "Innnalilahi wa'inna ilaihirraji'un Muneebba ki tashi dan Allah, mukaita asibiti" Hafsah ta faɗa tana kuka, Mamma ma kukan take ita da Khabir wanda ya ɗauki Muneebba da gudu ya nufi ƙofar fita da ita, karo suka ci da Dad Wanda yake yunƙurin shigowa hankali a tashe shima ya amshi Muneebba yana nufar motar da ita Sbd tashin hankali da ƙyar Mamma tasa Hijab ita da Hafsat suna shiga Motar tareda Khabir Dad kuma na wata motar wani gudu suke shararawa har suka isa Private hospital Wanda aka karɓeta da gaggawa ganin halin da take ciki
kuka Mamma keyi riris Hafsat na bata baki, taƙi tai shiru, dukansu zaune suke sunyi jugum_jugum, Abbie dake daga gefe can yana kallonsu hawaye na bin kuncinsa, dashi da Habib wanda babu halin zuwa wajensu su duka, kallonta yake zuciyarsa na masa zafin yadda take zubar da hawaye, " wannan ma na gani Aysher ban san iya kukan rashina da kikai ba, dole nazo wajenki koda kuwa a yau ɗin nan zan fitar da numfashin ƙarshe ba zan juri ganin hawayenki ba Aysher na kasa jurewa" ya faɗa da ƙoƙarin tunkaro inda take, Habib ne ya jawosa yana girgiza masa kai hawaye na zuba yace "Abbie na roƙeka kada kaje zamu iya rasaka kasan kuwa iya jinin da kake zubarwa wajen yunƙurin zuwa garesu? Abbie kada ka ƙara cilla mu a wata matsalar ka barmu da iya wacce muke ciki ba dammu ba sai dan Mamma da kuma Ummi da suke buƙatar ka samo musu mafita" ya faɗa tareda riƙe ƙafar Abbie yana kuka shima, hawaye Abbie ya share yana dawowa ya ɗago Habib yana kallo yace "naji Habib ba zanje ba amma zanyi nesa da ƙasar nan ko dan ku da iyayenku, zan bar ƙasar gaba ɗaya na nisanci kaina daga Iyalina tunda hakan shine mafitata" ya faɗa yana barin wajen da sauri, da kallo Habib ya bisa yana share hawaye shima yabi bayansa
dukkan wata zirga_zirga Dad ne ya dinga yinsa wannan ne ya tabbatarwa Mamma lallai zasu iya kular mata da ƴarta, hakan yasa hankalinta ɗan kwanciya suna jiran tsammani don Doctor ya Kira Khabir da Dad, ganin sun fito fuskarsu da ƴar walwala yasa Hafsat sauke ajiyar zuciya, kallon Mamma Dad yai da tausaya a fakaice yana share hawaye yace
"Alhamdulillahi tunda an samu nasar daidaita Numfashinta, dama shine yake barazanar ɗaukewa yanzun anyi nasarar daidaita sa, bacci take yanzu sai tsawon 3 hours ta farka, sai dai na sake baku haƙuri akan abinda ya faru tunda lallai wannan auren sai dai muce nufin Allah ne wanda ba muyi zato da tsammani ba haka zalika shine mijin da Ubangiji ya rubuta zata aura tun dirowarta a doron duniya, ita ƙaddara zanen zabo ce, kuyi haƙuri da kalar rayuwar da kuka tsinci kanku insha Allah komai mai wucewa ne Bayan wuya sai daɗi" ya faɗa da Murmushi
hawaye Mamma ta sake sharewa tana faɗin "bawan Allah ni bani da abinda zan gode maka dan ka fitar da ƴata kunya dani kaina da ka rufa mana asiri lallai na yadda da cewa komai a rubuce yake bawa bai isa ya sauya zanen ƙaddararsa ba, haka Allah ya tsarawa Muneebba bama da tsimi da dubara, Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi yasa kuma Abokin rayuwa ne" Mamma ta faɗa cikin dauriya
Murmushi Dad yai yana ƙara jinjinawa Mamma akan tawakalli da yarda da ƙaddara, take away yai musu da yi musu sallama akan gobe zashi dawo, ɗakin da take kwance suka shiga,kwance take fuskar nan tayi fari fat hancinga sanye da oxygen hawaye Hafsat ta share tana duƙawa a wajen ta kama hannunta tana riƙewa gam, Alwalla Mamma tai tana salla la'asar da Magriba wanda tashin hankali bai barta tayi ba sai da daddare Khabir shima ya tafi zuciyarsa cunkushe da damuwa
Misalin ƙarfe 3:30Am a hankali take ware manyan idanunta harta waresu duka akan farin silin ɗin Idanunta na zubar da hawaye wanda ta tabbatar da lallai ba Nazeer bane Mijin nata wani ne daban aka ɗaura mata igiyar aurensa a kanta, "Ya halayyarsa take, wane kalar mutum ne, wanene shi, wace sabuwar rayuwar ƙaddara zata gudanar, shin mai kyau ko akasin hakan?????" Waɗannan tambayoyi sune ta ɗinda maimaitawa kanta tana hawaye
Gidan Mom sosai ya kacame da hayaniyar Mom tun la'asar take abu guda wanda ganin auren Bobbi na yawo a media ga kuma fuskar Dad wanda ke murmushi wannan ya tabbatar mata da lallai auren Bobbi ɗinne su kansu su Zameer abin ya ɗaure musu kai,uwa uba Maheer wacce take kuka taƙi magana sai dai bin kowa da ido, wannan ne ya ƙara tada hankalin Mom ta dinga kiran Dad da Bobbi ba ji ba gani.......
Wayyo akwai fa cakwakiya, ina uban gayyar yake ma🥺ku dai yi haƙuri yau ba'a taɓo ɓangaren Fattu ba da kuma Bobbi
[5/21, 8:12 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*
Book 1
*By Riamcool*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*P.21&22*
___________Tayi kiran iya kira babu wanda ya ɗaga a cikinsu daga baya ma Bobbi kashe wayoyinsa yai dan lokaci shi kanshi yana buƙatar keɓewa Dad kuwa lokacin yana Asibiti wajen Muneebba sai daga baya yaga kiran kai tsaye gidan ya nufa
da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga fuskarsa a haɗe tamau babu alamun wasa ko rahama kallon ƙasa da sama Mom tai masa cikin ɓacin rai ta miƙe "mi kayi haka? wannan wane kalar tozarci da cin mutuncin kaja mana kasan kuwa abinda ka aikata?" ta ƙarashe zancen da huci
"Yes nasan abinda na aikata dan na isa ne shi yasa na aikata aure na yiwa yarona kuma ita ce wacce na zaɓa masa abokiyar rayuwa ta har abada babu wanda ya isa ya hanasa zama da ita" ya faɗa yana haura up stairs
binshi tai da azama tana faɗin "wallahi ba zai zauna da wata shegiyar ƴa ba in ba Maheer ba Maheer ce zaɓina kuma ita zai aura wannan kuwa ranar da tazo gidan a ranar zata barshi dan sai ya mata saki ukku cir, wanna wane kalar rayuwa ne ka saka ƴar mutane a damuwa gashi tunda Maheer taji auren nan ko Abinci bata ci ba ƙarshe ma kulle kanta tayi a ɗaki to wallahi tallahi indai ni na haifi Bobbi sai na saka ya saki ƴar matsiyatan can kuma zanyi bincike"
kallonta yai yana kauda kansa gefe guda Sbd ɓacin rai "idan bake kika haifesa ba fa?" yai mata tambayar yana kafeta da ido, itama kallonsa tai tana sakar masa wani Miskilin Murmushi daga bisani kuma ta jijjiga masa kai tana barin wajen da sauri, da kallo ya bita har shiɗa, haurawa sama yai yana shigewa bedroom ɗinsa zama bisa bed yai yana dafe kansa dake masa ciwo
Mom kuwa tana shiɗa dasu ABEED ta fara cin karo suma sunyi jugum_jugum kallonsu kawai tai ta wuce, duk lkcn data gansu ranta yana sosuwa sbd ta tsani Mahaifiyarsu ganinsu kansa tuna mata yake da Mahaifiyarsu, ita ce mafarin tarwatsa mata farinciki ita ce sarauniyar Ahmad ita ce magadiyar wannan gida Sbd haifafar ƴaƴa Mazan da tayi taya zata ma bari su kansu ƴaƴan nata suyi farinciki wasan na nan zuwa kansu
*Asad BObbi*
A hankali yake saukowa daga Step ɗin haɗaɗɗen benen wanda ƙarafen benen kanshi na zallar azurfa ne cikin gadararriyar tafiyarsa ta ƙarfafan maza yake saukowa harya ƙarasa saukowa a haɗaɗɗen Falon wanda yaji Furnitures Set Ukku haɗaɗɗu, dukkansu zubinsu na kalar gidan sarakai ne ga wani lallausan Cafet dake malaye a tsakiyar Falon zama yai ɗaya daga cikin kujerun yana ɗaukar wayarsa ya kunna, Missed call ɗin Mom ya gani yafi hamsin ɗaga giransa guda yai yana taune lips ɗinsa na ƙasa
Data ya kunna yana ƙara shiga Instagram wanda anan ne Vedio yafi yawo kallon vedio yake yana ƙara maidosa baya ya tabbatar da lallai shi ɗinne aka ɗaurawa aure ba wani ba "Mace" ya furta yana ƙara tauna lips ɗinsa, babu halittar da yafi tsana a duniya sama da mace, mace ita ce maƙasudin cin galaba a kansu mace ita ce maƙasudin shigarsa ƙuncin rayuwa wacce bai san ranar fitarsa ba, Mace ɗaya ce yake so a faɗin duniya ita ce Mahaifiyarsa, shi abinda ya ɗauki Mace ita ce makira maƙaryaciya maci amana, kuma shi ɗinne ake son yayi rayuwa da mace har biyu "ta ina zan iya? ina bazan iya ba na tsani mata kuma bazan zauna dasu ba dole ko wace ta kama gabanta" ya faɗa a hankali tare da lumshe idonsa tuno da DEEN ɗinsa mace ce ta haɗa makircin kashe masa Deen shiko ta Ina zai iya mancewa da mace, ganin tunani zai masa yawa ya sashi tashi yana shiga wani Coridor wanda zai sadasa da wani haɗaɗɗen Bedroom wanda bai cika wani karikitai da yawa ba makeken Bed ne guda ɗaya kawai sai Wardrope da mirror bethroom ya faɗa yayo wanka ya fito iya boxes ya kwanta dashi yana jan blancked ko 5 Minute bai yi ba bacci ya ɗauke sa
*MUNEEBBA*
tunda ta farka take faman zubar da hawaye tana motsi da bakinta Mamma dake Lazimi jin motsi ya sata juyowa tana lalube harta lalabo Hafsat dake kwance "Hafsat duba man Muneebba ce ta farka" ta faɗa tana ƙara lalabo gadon da Muneebba ke kwance, kallon inda Muneebba ke kwance Hafsat tayi tana murmushi da hawaye tace "eh Mamma ita ce"
da gudu Hafsat ta fita tana kirawo wani Doctor Oxygen ɗin ya cire mata, hannuta Mamma ta kamo tana jin shesheƙar kukanta "Muneebba" Mamma ta Kira sunanta cikin dakiya "na'am Mamma"
"MUNEEBBA ke ɗin musulma ce kinsan ƙaddara kinsan jarabta, ina son ki ɗauki dangana da haƙuri ki ɗorawa rayuwarki Muneebba duniya ba dukkan abinda kake so kake samu ba, zata iya yuwa abinda kake so ba Alkhairinka bane wanda baka so shine Alkairi, dukkan musulmi ana son ya zamto mai haƙuri kinsan kuwa shi kanshi haƙuri yana da ladarsa, sannan ki zamto mai yadda da ƙaddara da dangana, indai ni Mahaifiyarki ce Muneebba kuma ni na haifeki ina so ki cire Nazeer a ranki kisan cewa da igiyar aure a kanki Tunanin wani ɗa Namiji bai kamaceki ba dukda nima kaina na ɗanɗana gubar da kika lasa Muneebba sai dai har abada bana so kiyi rayuwar dani nayi, ina so kiyi rayuwar farinciki Muneebba, Muneebba dan Allah ki cire damuwar nan a ranki"
tunda take maganar Muneebba ke kuka "Mamma kece kika haifeni Mamma nai maki Alƙwarin zan cire Nazeer a raina dukda shi so baya taɓa ciruwa sai dai ya ragu amma ni zanyi ƙoƙarin ciresa zan koyi son wanda igiyarsa take a kaina,sai dai ban san wace rayuwar zan gudanar ba a sabon littatafin kundin rayuwata, wane shafin sabuwar ƙaddarar zan buɗe? wannan ne ban sani ba Mamma, kuma ko ke nasan kina wannan tunanin" ta faɗa da sakin murmushin takaici mai ciwo
"Muneebba kada kice haka ki yiwa kanki kyakkyawan yaƙinin jin daɗi a gidan Mijinki insha Allah wahalarku ce ta yanke saƙa" Hafsat ta faɗa tana shafa kan Muneebba, kallonta Muneebba tai tana faɗin "Hafsah akwai kingin rina a kaba" ta faɗa tana lumshe ido, yanzu ne take jin tabbas akwai wata gagarumar ƙaddararriyar rayuwa da zata gudanar, tabbas jikinta ya faɗa mata zata buɗe shafin kundin ƙaddararta ne sai dai ita yanzu komai ya sameta zata godewa Mahaliccinta dan haka yake son ganinta
shiru dukkansu sukai har ɗan bacci ya ɗauke su, har sunso makara sallar Asuba,babu laifi jikin Muneebba da sauƙi, koda suka gama sallah sunyi Azhar da karatun Alqur'ani, a haka har gari yai haske rana ta fito
zaune suke suna ɗan fira jefi_jefi wanda Muneebba ta ɗan saki jikinta, sallamar Mamma Ladiyo da maƙotan su Muneebba ya saka su maida hankalinsu a kansu, da azama Mamma Ladiyo ta ƙaraso tana kama hannun Muneebba "sannu ƴar nan kinji Allah yasa hakan ne mafi Alkhairi kinji kuna ganin Jarabta" ta faɗa da share hawaye
dukkansu sunyiwa Mamma ya mai jiki sannan Rabi maƙociyarsu wacce gulma ta kawota