wasa ta banka masa tana turo baki tace "ni wallahi mai kama dakai na gani"
dariya kawai yai ya miƙe yana shigewa ɗakinsa ganin itama haka yasa suka kwanta
************************
*FATTU*
tafe take tana kora Shanunta tare da rera waƙarsu ta Fulani a haka harta isa jejin, jin kukan tsuntsaye yasa ta fara busa sarewar tata tana watsa musu tsaba, wani fili ta samu taja tana tsalle wanda ya sata tuntuɓe da wani girkakken dutse ta faɗi ƙasa kanta ya bugu da wani ƙaton dutse dake gabanta, nan take kanta ya fashe jini na tsartuwa wata ƙara ta ƙwalla wacce tasa dajin amsa kuwwa
A mamadin yaji busa sarewar da yake jira sai jin ƙararta yai wacce tai amsa kuwwa cikin Dodon kunnuwansa, miƙewa yai da zummarsa yana keta itatuwan wajen yana nufo inda take yashe jini na tsartuwa jini kuwa duk ya jiƙa mata farar rigarta ta Fulani, cike da jarumta ya tunkaro inda take yana yatsina fuska da ƙara ɗaureta tamau alamun hakan ya zame masa Al'ada, tunani ya tafi can kuma saiya gyaɗa kai yana yage tsummar rigarsa wacce take fes kamar bata mahaukaci ba, duƙawa yai yana tallafo da kanta ya zuwa azasa bisa cinyarsa tsumman daya yaga ya ɗauka yana ɗaure mata goshin tamau dashi jinin ya daina zuba, ganin bata numfashi ya sashi ɗaukarta kacokan ya azata a kafaɗarsa, yanayin tafiyarsa zai tabbatar maka da cewa gwarzon jarumi ne, da cikakkiyar gadara da Izza wani bakin rafi ya ajiyeta yana ibo ruwan da tafin hannunsa yana shafa mata a fuska kamar wani mai cikakken hankali.......
[5/21, 8:11 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*
BOOK 1
*BY MARIAM SANI RIAMCOOL*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*P.17&18*
_________Ɗago da fuskarta yai yana azata a cinyarsa bakinsa yakai dai_dai saitin nata yana hura mata iska, a hankali ta dinga ware manyan idanunta tana buɗewa harta waresu duka, yawo ta dinga yi da idonta tana murzawa tana ƙara rufewa don ta tabbatar da cewar mafarki take ganinta bisa cinyar wani murɗaɗden Mutum, ganin ba mafarki bane ya sata ƙwalla ƙara tana miƙewa da azama, da sauri ya ɗago da fuskar tasa yana kallonta wanda itama shi take kallo da mamaki, nunasa tai da yatsa tai da gurɓatacciyar hausarta take faɗin "Hoɗijam JODDI dama ke ƴar iska ne ashe ban sani ba, ashe ke ba mahaukaciya na ba? kike fakewa da hauka, kina shanye man fura wacce kullum sai naci dukan Innaro a kanki, to kwarankwatsa ko ludayi guda kin gama sha man" ta faɗa tana share hawaye ganin ashe Joddinta ɗan iska ne
bai fahimci abinda take nufi ba ya miƙe tsaye jikin nan nasa a murɗe ko ina yana tunkaro Fattu wacce take kuka riris ɗago idonta tai tana rufewa da tafin hannu "JODDi karki ƙarasho a gurina bana shonki yanzu Alqur'an tunda baki da kunya dukda kina mahaukashiya, ki juya baya na rufe idona"
ƙara tunkarota yake yana nuna mata cikinsa dake murmurɗe, buɗe ido tai ta ƙara arba dashi a hakan, kuka ta fashe dashi tunawa daya taɓa ta kuma ta tabbatar yanzu tanada ciki tunda taji Innarsu Fatse tace duk Namijin daya taɓa mace ciki take shi yasa ko Baffa zata miƙawa abu bata bari hannunta ya shafi nasa, "Honi Fattu JODDi kin shusheni aradu kin mani ciki, Aradu yunwa ta kasheki yau ko ludayin fura bazan baki ba" ta faɗa tana juyawa da gudu tabar wajen
da kallo kawai yake binta dan baya fahimtar abinda take faɗa kai tsaye shima ya biyo bayanta bata lura da biyonta da yayi ba, saida taje gurin Shanunta, ganin jini ya sata tunawa da ashe tayi tuntuɓe taɓa goshin tayi taji an ɗauresa, "Ohh Allah Sarki JODDi ashe temakona yai ba ɗan iskan bane, nifa nasan Joddina" ta faɗa tana juyowa kallonshi tai inda ya kwanta yai lamo alamar yunwa yake ji, tausayi ya bata, da kanta ta ɗauki kingin tsummar rigar daya yaga tana yafa masa a jiki, ƙwaryar furar ta jawo ta fara basa, sannan ta jawo kwanon tuwo tana bashi sai da yaci ya ƙoshi ta basa ruwa yasha, yana gamawa ya miƙe yana tafiya itama bin bayansa take har suka isa bukkar tasa, kingin furar ta ajiye masa tana ɗauko wata riga ta basa ta nuna masa ya saka, babu musu ya saka murmushi tayi ta fito daga bukkar tana leƙe_leƙe tana tsoron ace wani ya ganta dukda ƙungurmin daji ne ba masu shigosa sai maharba
Ajiyar zuciya ta sauke ganin ba kowa ta fito harga Allah tana tsoron ranar da wani zai gansa don tasan ɗanyen hukunci za'a masa kafin su koresa dukda yana mahaukaci ba zasu ji tausayinsa ba,
saida Magriba tayi sannan ya kaɗa shanayenta suka nufi hanyar gida, saida ta fara ɗaure shanayen a garke sannan ta shiga ciki, da sallama ta shiga tana wurwura sandarta
babu wanda ya amsa sallamar tsakanin Innaro da kuma Saro, kowa da uwar harara yake binta, saboda ba ƙaramin haushinta suke ji ba,
bata kula kowa ba ta shige bukkarta tana ɗaura zaninta ta nufi rafi wanka da can zata tsaya sai kuma taji yau tana son zuwa dandali, da azama ta dawo tana shiryawa ta caɓa uwar kwalliyarsu ta Fulani, kai tsaye dandali ta wuce, an cika da ƴam mata da samari anata kaɗe_kaɗe da bushe_bushe, cikin wasa ita babu abinda yafi burgeta irin busa, usur tayi wanda yasa aka tsaya ana ihu da sowar ganin Fattu dan kowa son busa sarewarta yake, murmushi tayi tana dawowa tsakiyar filin inda makaɗan suke, sarewar ta ɗauka ta fara busata cikin gwanancewa da fitar da wani sauti wanda yasa ƴam matan wajen da samari shiga wani shauƙi da daban, dukkan wani saurayi da budurwa sai sunzo sun mata liƙi, wani ɗan fulanin saurayi ya fito Filin yana zuba mata liƙi tare da aika mata da wani kallo yana murmushi, alamun ya bayyana mata soyayyarsa, kowa na wajen tsit yai har ita Fattun data da kata da busar tana kallonsa da mamaki ganin baya tsoron rayuwarsa tasan tasa ta ƙare, zaro ido waje tai ganin abinda ya faru Ja'e ne ya murɗe wuyan Haruna yai masa yankan rago
faɗuwa yai wajen yana shure_shure harya daina jawo Fattu Ja'e yai yana kwalfa mata mari yana huci, cikin fulatanci yace "Fattu sau nawa zance miki ki daina zuwa dandali kina busa kin kuwa san irin kishinki da nake???? a kanki zan iya ɗaukar duka rayukan ƴan garin nan kin sani"
Kallonshi tai tana zubar da hawaye zuciyarta na mata zafi "kishi kace Ja'e ? Kishinka ko jahilci da dabbanci tunda harka iya ɗaukar rai, wallahi Ja'e koda rayuwata zaka ɗauka bazan taɓa sonka ba zan dai bi zaɓin Mahaifina amma ba wai don ina sonka ba koda na aureka gangar jikina ce a wajen ka amma ruhina da zuciyata suna wajen wanda zuciyata ta aminta" ta faɗa tana duƙewa wajen tare da sakin wani gunjin kuka
da mamaki Ja'e yake dubanta duk garinnan babu wanda ya taɓa gaya masa magana irin Fattu cije leɓensa baƙi yai yana kallon mutanen wajen, murmushin gefen baƙi yai yana damƙo gashin kan Fattu wuƙa ya zaro yana aza mata ita a wuya yace "idan na kasheki fa? kinga zuciyarki da ruhinki ba zasu tafi wani waje ba, muddin na tabbatar da hakan zan aika ki inda ba'a dawowa" yana gama faɗa ya soke wuƙar yana barin wajen
Saro dake ganin dukkan abinda ya faru ta saki murmushin gefen baki tana faɗin "kaɗan kika gani Fattu" tana gama faɗa ta juwa tana barin wajen kowa watsawa yai sai Fatse ce data tausayawa Fattu tana miƙar da ita ta rarrasheta kuɗin ta tattara ta bata, kai tsaye ta juya ta nufi inda take kwana, harta hau bishiyar sai kuma taji tana buƙatar zuwa inda yake itama ta kwana acan, dirowa tai akan bishiyar ta nufi jejin tana tafiya ko alamar tsoro babu a tattare da ita, haka taita tafiya harta ƙarasa gurin, tsit dajin yake, zaune yake waje guda ya lumshe idonsa farin wata ya haske wajen lafewa tai a baki bishiya tana leƙensa kamar wata biranya haka ta ɗare bishiyar tana kallonshi, har bacci ya ɗauke ta
*KANO*
zaune suke a Dinnig kowa ya hallara harda Mazan gidan duka Bobbi ne kaɗai ke babu da Zaidu, su kaɗai ake jira kallon Iftihar Mom tai tace "jeki kira man yayan naku" zaro ido Iftihar tai tace "Mom kinfa san halinsa" dariya Maheer tai tace "Mom ni bari na kirasa" ta faɗa a siyasance tana miƙewa, kallonta JUNAID da Aryan sukai suna dariya ƙasa_ƙasa "Maheer zauna na kirasa kinsan shifa ba'a masa gwaninta koni nasan kafin na fito saina sha koda maruka biyar ne jihadi zanyi kawai" Zameer ya faɗa yana miƙewa dariya AFIF yai yace "tabɗi ai gidan nan aiki ya samemu yanzu zamu zuƙe yunwa ta kamamu tunda Yah Bobbi ya dawo cin abincin ma sai an mana gadara"
loma ABEED ya buga yana kallonsu yace "kudai kuka sani sai ku zauna yunwa tai maku illa kafin ya fito, ina dalili na zauna yunwa tai mani ƴaƴa a ciki na haifesu ta ina" ya faɗa yana ƙara kai spoon ɗin Indomie a bakinsa
Kaidai ake ji, kai har yanzu kaƙi girma kullum baka da aiki sai cin taliyar yara" Aunty Meera ta faɗi tana dariya, dariya HAROON yai yana faɗin "yo Ina girman Aunty Meera? tunda nifa har yanzu banga taɓarya ba" nifa ina tunanin ABEED mata maza ne wallahi shi ko ɗan ciwon maran nan da samarin gidannan keyi da wankan asuba ban taɓa ganin yayi ba"
dariya duka suka saki "zanfa ci ubanka HAROON kuda baku jin kunyar ɓaro zance" Mom ta faɗa tana dariya, shafa sajensa yai yace "Mom kinsan bakimmu ba shida tsarki idan kin gammu ki dinga barin wajen, harararsa Samha tai tace "kudai ake ji ai"
ɗaure da towel Zameer ya samu Bobbi yana shiryawa, wani yawu Zameer ya haɗiye yana sadda kansa ƙasa kamar na Allah baki ya buɗe zaiyi magana Bobbi ya dakatar dashi yana keto paper da biro yana rubutu ya miƙa masa, amsa yai yana ƙara mamakin halayen Bobbi wato ko su ƴam gidan nasu ma ba zai buɗe baki yai musu magana ba, juyawa yai yana gunguni ba tare daya bari Bobbi ya gansa ba,
Paper ya miƙawa Mom yace "bai yi magana ba ga Paper kiga abinda yasa wai baya buƙatar cin komai, kuji man bala'i ita kanta Muryar tasa rowar jinta yake man"
tsaki Zaidu dake baya yai yana zama tareda jawo warmer yana zuba farfesun ƴan cikin tareda haɗa kakkauran Tea babu wanda yaiwa magana ya zauna kallonsu Aryan yai yana buga musu tsawa "wai ku ubanwa kuka raina kamar ni na zauna ina matsayin yayanku amma babu mai gaisar dani amma da Munafukin can ne da tuni jiki na ɓari kun gaisar dashi yana muku wulaƙanci"
Bread Junaid ya tura a baki tare da kurɓan tea yanawa Zaidu kallon rainin wayo "kai wa ka gaisar a cikin su Mom da Aunty Meera?" ya faɗa yana hararan Zaidu
fatali Zaidu yai da kular farfesun yana miƙewa a zuciye ya bar wajen da kallo suka bisa Zameer yana ɗora hannu bisa kai yace "wayyo ni Zaidu ko baƙin mugu kular farfesun ya zubar shifa nake haɗiyarwa yawu tun ɗazu, wacece ta yisa?" Zameer ya tambaya
"Indo mana" Suhaima ta bashi amsa miƙewa yai yana tafiya da gadara kamar bashi ba, dan dukkan ƴan gidan haka suke a gida da barkwanci da an fita kuma su zama masu gadara da Izza wanda wannan a jininsu suke
Yana zuwa ya sameta tana gyaran kichen jikin nan nata fes gata ƴar kyakkyawa dukda tana baƙa amma baƙinta mai kyau ne harɗe hannuwansa yai a ƙirji yana haɗe fuska tamau "Ke" ya kira sunan juyowa tai a hanzarce tana sharce zufar da tai yatsina fuska yai yana kallonta a wulaƙance yace "maza kiyi wanka sannan ki ƙara dafa man Peppersoup ɗin da kika yi a ɗazun, sannan kisa detol ki ƙara wanke ƙazamin hannunki kafin ki girka man na baki 10 minute" yana gama faɗa ya juya, hawaye ta share a fakaice idan banda ma ƙaddara mi zai kawota aiki
kamar yadda yace haka ta tafi ta wanke hannu sannan ta shiga tai wanka ɗaukar warmer ɗin tai tana nufar ɗakinsa nocking tai come in aka furta a hankali ta tura ta shiga bakinta ɗauke da sallama
bai amsa ba shida HAROON saima maida hankalinsu da sukai a game suna dariya tsaye tai tana jiran yai magana "ajiye ki fice daga cewa ki wanka sai ki wani caɓa kwalliya ajiye ware bana son kallonki" ya faɗa yana ɗaure fuskarsa
Maheer koda suka gama dinner up stairs ta haye tana haurawa ɗakinta wanda Mom ta ware mata, gado ta faɗa tana fashewa da kuka mai ciwo anya kuwa zata iya samun Bobbi ta ruwan sanyi mutumin da zata iya rantsuwa ta maya bai san fuskarta ba amma shi zuciyarta ke kawo mata, ya zama dole tabi dukkan wata hanya dan ganin mallakar zuciya Bobbi, share hawaye tai tana ɗaukar phone ɗin ta Mammi ta dokawa kira tana ɗauka ta fashe mata da kuka "Mammi bamu haɗu ba har yanzu,bashi ma zama gidan yanzu"
"Calm down Daughter ki ƙara haƙuri kin san dai Bobbi ya zama naki an gama tunda harya amince tunda baiko ma goben na za ai maku shi, duk wani abu ki bari sai an ɗaura auren sannan ki mallake zuciyar Mijinki ke kamar ba mace ba" ajiyar zuciya Maheer tai, Mammi tana ƙara kwantar masa da hankali
*BOBBI*
Zaune yake a katafaren office ɗinsa ya kwantar da kansa kan kujera ya tafi duniyar tunanin daya saba, ajiyar zuciya ya sauke yana ɗauka Cup ɗin Tea yana kurɓawa a hankali, P.A ɗinsa ne ya shigo hannunsa ɗauke da takardun
a ladabce Hafiz ya gaida shi gyaɗa masa kai kawai yai yana nuna masa wajen zama, zama yai sannan ya dubi Bobbi yace "Sir sun kawo mana share na Company S.M sunce ka faɗi kaso nawa kake so su zuba"
gyaran zamansa yai ya ɗauko Paper da biro yayi ƴan rubuce_rubuce ya basa amsa yai yana miƙa masa takardu ya cike ya miƙo masa, karɓa Hafis yai yana risinawa ya fice da kallo ya bisa harya fita yana motsa bakinsa "kunyi naku S.M yanzu lokacina ne" ya faɗa yana shafa dogon gashin kansa wanda bai ɗauresa yau ba ya zubo sa a kafaɗa ne
Sallar azabar yayi ya nufi wani meeting daya haɗa na manyan ƴan kasuwa masu neman Share na Company sa wanda harda turawa, tunda ya shiga idonsa ya shiga kan na Alhaji Madu wanda ya hakimce waje guda, murmushi ya saki ganin wasan na tafiya yadda ya kamata zama yai suka fara tattaunawa tareda faɗin duk wanda ke son Share na A.A.B Company dole sai ya zuba kaso 50 na rabin dukiyarsa, ba tareda ɓata lokaci ba suka zuba dukkansu, da kallo Alhaji Madu ke bin Bobbi,Wanda Bobbi na lura da hakan ɗage gira guda yai yana ɗan murmushi ya miƙa masa hannu cikin wayancewa sukai musabaha, tare da ɗan taɓa firar kasuwanci wanda duk dan Alhaji Madu ya fidda tantama a kansa ne
Bayan kwana biyu anyi baikon Maheer da Bobbi iya one month aka saka, wanda tunda tazo koda so guda ne basu haɗu ba, danshi gogan mantawa ma yake da wani baiko nasa, su Mom ne kaɗai ke rawar gaban hantsi, haka kwanakin keta tafiya harya rage saura sati biyu
*MUNEEBBA*
Zaune take ana mata dilka wanda tayi wani haske na ban mamaki kyau bana kaɗan ta ƙara ba saboda gyaran da take sha wajen wata maƙociyarsu wacce take gyarata saboda gabatowar auren wanda bai wuci 3 days ba, Kasancewar Muneebba bata da wasu ƙawaye ya sata bata wani shirya event ba.............
[5/21, 8:11 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*
book 1
*By Mariam sani Riamcool*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*P.19&20*
________Kasancewar Muneebba ba tada wasu ƙawaye ya sata bata wani shirya event ba, tun bayan Sati aka kawo lefe wanda akwati goma sha biyu haka yai mata kuma dukkan kayan masu tsada ne wanda Hajiya da kanta ita ta haɗa don tasan abinda take shiryawa shi yasa ta nuna ta saduda,
Kallonta Hafsat tayi tana faɗin "wai kinga kuwa wani kyau na ban mamaki da kikai Muneebba, wannan idan Nazeer ɗin ya ganki anya zai ganeki?"
dariya Muneebba tai tana miƙewa, sallama sukai wa Matar sannan suka nufi gida, da sallama ɗauke a bakinta ta shiga sai dai fara'arta ce ta ɗauke sakamakon ganin Mamma Ladiyo wacece ta wani caɓa ado Alamun kuɗi da hutu sun zauna mata, harga Allah Matar batai mata ba, sai dai ta danganta hakan da azabar data bawa Mahaifiyarta shi yasa bata sonta
kallon Mamma Ladiyo Muneebba tai tana gaisar da ita da ƙyar, fuska a sake ta amsa tana binta da kallo ƙasa_ƙasa wanda take ayyana abubuwa da dama a ranta, shafa haɓar wuyanta tai tana maida kallonta ga Mamma, wani Munafukin murmushi ta saki ko iya haka tabar A'ishatu tayi farinciki sai dai dukkan wani abu da zai kawowa Shatu kwanciyar hankali da jin daɗi ba sonsa take ba, ya zama dole kuwa ta ƙara tashi tsaye
Washe gari Mutane ne cike da gidan anata hada_hadar buki wanda yawancinsu duk ƴan unguwar ne sai kuma ƙawayen Mamma Ladiyo
Sanye take da wani material fari tas ɗinkin Fitted gown na bride an zuba mata Make up fuskar nan sai sheƙi take da haske ga jan lallen da aka zana mata wanda ya ida fiddota sosai, kallonta Nazeer yake ta Vedio call yana ƙara tazbihi ga Ubangiji da zai mallaka masa wannan Kyakkyawar halitta "Masha Allah Hayatee nagodewa Ubangiji sarki gagara misali da zai mallaka man wanna haɗaɗɗiyar kyauta, Muneebba ba zan kwatanta miki yanda nake ji a raina ba kwatankwacin yadda nake sonki ba zai faɗu ba bana fatan wani abinda zai gifta a tsakanina dake bana fatan kalmar rabuwa ta gifta a tsakanimmu, zan riƙe ki na tarairayeki kamar tsoka ɗaya a miya zan kula dake mu haifi ƴaƴa mu tarbiyantar dasu"
Wani murmushi ta saki mai kashe zuciya tana lumshe ido ta waresu a fuskarsa "Thanks dear insha