tace "Ohh rayuwa kenan shi kanshi Nazeer ɗinfa tunda aka ɗaura auren ya faɗi wanda yanzu haka yana asibiti bai farfaɗo ba,ance saima an fitar dashi ƙasar waje yau zasu tafi don ko motsi bashi yi" ta faɗa da sigar gulma wacce ke cinta
wani kalar dum gaban Muneebba yai ba zata iya jurewa ba ita ƙara ace ciwon ya hau kanta da gudu ta tashi ta nufi Toilet tana kullewa sakin shawa tai tana sulalewa ta fashe da wani matsanancin kuka mai cin rai sai da ta daɗe sannan ta wanke fuskarta ta fito wanda kallo guda zakai mata kasan cewa kuka tasha sai dai ganin babban Mutum kamili hakimce a gadon yana sakar mata murmushi ya sata sadda kanta ƙasa tana gaisar dashi a ladabce,
Amsa mata yai yana sakin Murmushi gefe kuma ga Iftihar wacce take mata kallon raini da wulaƙanci tana tauna chewing gum
yafitota da hannu yai yana mata nuni data zauna, ƙasa ta nemi waje tana zama kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, haƙuri ya fara bata da kuma tabbatar mata zata gudanar da rayuwar farinciki daga bisani ya haɗa mata da nasiha mai sanyaya jiki wanda jikinta ya ƙara sanyi laƙwas,sosai ya kwantar mata da hankali wanda hankalinta ya ɗan kwanta ganin yadda Dad bai ɗauki girman kai ya ɗorawa kansa ba dukda matsayi da kuɗaɗen dake garesa wanda ita sai a Jarida ta sanshi batai tsammanin haka yake da son mutane ba, sai dai tana fatan ace kamar yadda yake haka kingin Ahalin nasa suke
ya ɗan daɗe sannan yai masu sallama suka tafi wanda Iftihar kamar ta fasa ihu haka take ji, suna fita Mamma Ladiyo ta bisu da kallo tana jijjiga kai idanunta sun sauya kala ya zuwa ja, ganin komai zai iya faruwa ya sata ficewa daga ɗakin ta dinga tafiya harta nufi ƴar wata hanya cikin asibitin inda ba kowa tsayawa tai tana huci "me na aikata kenan? Wallahi da nasan haka abin zai kasance da ban hana auren ba wace mafita garan yanzu nasan dama guda gareni kuma nayi amfani da ita babu batun sake dawo man da ita yan ya zanyi? Muneebba ta tsallake tarkona, wallahi bazan taɓa bari A'ishatu kiyi rayuwar jin daɗi ba keda ƴarki" ta faɗa tana huci tare da zama tana tunanin mafita, ta daɗe kafin yanayinta ya dawo, da murmushi ta shiga ɗakin tana faɗin "wai ɗan zazzagaya marassa lafiyar nai kinsan ana son dubiyar marar láfiya, kai jama'a wasu mutanen na cikin hali wallahi A'ishatu ba kiga wata mata dana gani ba sai da na zubar mata da ƙwalla" ta faɗa tana matso ƙwallon ƙarya
Murmushi Mamma tai tana faɗin "Allah sarki ai kin kyauta Mamma Ladiyo"
koda Doctor yazo yaga jikinta yadda yai sauki sosai ya basu sallama, tattarawa sukai suka koma gida, nan mutane suka dinga shigowa dubiya akasarinsu gulma ce ke kawosu
Wata ashariya Mom ta danna jin zancen Iftihar "ƴar talaka kika ce? Dad ɗinku ya rasa wacce zai aurawa sai ƴar talaka kuma ƴar matsiyata wallahi ba zata saɓuba"
"saɓuwa kau taka tas da soso da sabili Naja'atu wallahi aure anyishi an gama babu wanda ya isa ya warwaresa muddin ina numfashi da rayuwata wurin zama kuwa tuni na tanadar mata ki shirya tarbarta a goben nan" Dad ya faɗa da ɓacin rai
kallon baka isa ba Mom tai masa tana tashi fuuu ta bar wajen, Aunty Meera ce tabi bayanta kallonta Aunty Meera tai tace "Mom calm down mana kinsan dai kina da iko akan Bobbi ranar da aka kawota ma zaki iya sakasa ya saketa to name tada hankali"
kallon ashe ba kida hankali Mom ta wurgawa Aunty Meera tana faɗin "Ameera wane iko garan akan Bobbi? banida wani iko akansa tunda har yaga kirana bai maido ba kuma yake ƙaurace man ki faɗa man wane iko nake dashi akan Bobbi" ta faɗa tana tauna leɓenta na ƙasa
"koma dai miye Mom ki kwantar da hankalinki kisa yarinyar can kamar ta bar gidan nan" banza Mom tai da ita dan ita kaɗai tasan abinda ke damunta, shigowar Maheer da akwati a hannunta ya sata kallonta tana faɗin "Maheer ina zaki? "gida Mom" ta bata amsa a taƙaice tana murmushi
"Maheer duk lallashinki da nai baki haƙura ba?" "Lah ko kaɗan Mom haka Allah ya tsara man can dama ba ni kaɗai bace Matar Yah Bobbi"
girgiza kai kawai Mom tai tana tashi ta rakota har garden wajen Parking space shiga Maheer tai tana jan Motar wanda zuciyarta kamar ta rabe gida biyu haka take ji
*YOLA*
**************
*FATTU*
duƙe take tana rizgar kuka kamar ranta zai fita "Baffalo ka yiwa girman Allah kada ka aura man Ja'e wallahi ban sanshi kisa fa yake a gabanmu fa ya kahe Haruna, nima ya ce zai kasheni"
sandar dake hannun Baffalo ya rafka mata yana hankaɗata yace "Fattu ki shiga hankalinki baƙin cikin Shanayen da mai gari zai bani kike? da zaki ce ba kya auren Ja'e to aradun Allah ko mutuwa kika sai na aurawa Ja'e gawarki..........
[5/21, 8:12 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*
Book 1
*By Riamcool*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*P.23&24*
__________"Wallahi Fattu ba zakiyi man buƙulun arziƙi ba, arziƙi na biyoni kina masa dundu, ki sani aurenki da Ja'e kamar anyi an gama ne ko mutuwa zaki bazan fasa aurar dake ba"
kallonsa take da rinannu idanunta tana girgiza kai bakinta na karkarwa alamun magana take so amma ta kasa koda furta A saboda baƙinci, da gudu ta tashi ta nufi bukkarta kuka tasha sannan ta miƙe tana fita, ta bayan gari tabi don bata son wani yabi sawunta ballantana har aga JODDi
kai tsaye dajin ta nufa, dutsen da take hawa tai busa nan ta hau tana shesheƙar kuka har tayi mai isarta saukowa tayi tana bin dajin tana zagayawa tana tsigo da ƴaƴan itatuwa
Kai tsaye inda tasan zata sameshi ta nufo zaune yake ya haɗa kansa da gwiwa wanda wannan ya zame masa Al'ada, murmushi tayi tana tunkaro inda yake da dariya, ɗago da fuskarsa yai yana kallonta wanda itama shi ɗin take kallo
Zama tai tana ɗibar ƴaƴan itatuwan data tsigo tana bashi, sannan ta ɗauki madarar shanu tana basa, sai da ya ƙoshi sannan ya miƙe yana haɗe rai yana shiga bukkar da kallo ta bisa tana murmushi ta bi sa a baya,kwance yake rigar jikinsa a cire daga shi sai dogon wandon jikinsa ko ina ka kalla yana glowing dukkan wata sura ta jikinsa ta fito duk mace mai lafiya ta kallesa tabbatas sai taji wani abu a kansa lumshe manyan idanunta tayi tana jin wani abu na daban na ziyartarta tun daga ƙafafuwanta har ya zuwa brain ɗinta
kallonta yai yana nuna ta da yatsa alamun magana yake so yayi amma ya kasa,dafe kansa yai yana ƙara sama da hannunsa,
Fattu ganin halin da JODDi yake ciki ya saka hankalinta ya ɗan tashi ta nufosa,hannunsa ta kama tana saukewa sannan ta ɗago da fuskarsa tana ƙare masa kallo tare da lumshe masa ido,kallonta ya keyi kamar mai son tuno da wani abu ya haɗe rai yana fincike hannunsa tare da tu reta yana miƙewa ya fito daga bukkar,ƴar ƙara ta saki tana miƙewa tare da turo baki ta miƙe itama tana fita sai dai turus tayi tana ɗora hannu a ka da zaro ido waje ganin waɗanda suka kewaye JODDi da kuma makamai a hannunsu
*MUNEEBBA*
rungume take a jikin Mamma tana faman rizgar kuka fuskarta lulluɓe da mayafin Lifaya wacce ta amshi jikinta fari mai ratsin zanen Flower gold jinta take duniyar tai mata ƙunci ji take da mutuwa zata zo mata tabbas babu abinda zai hana tai taimaraba da ita,ranar data daɗe tana mafarki da son kasancewa a ɗakin mijinta yau ita ce tazo mata a yadda batai zato da tsammani ba, wanda taci burin tarewa a gidansa ba shine wanda Ubangiji ya rubuta a Alƙalamin ƙaddararta ba
Kuka ta sake fashewa dashi tare da sake shigewa jikin Mamma,shafa kanta Mamma tai itama hawayen na son zubo mata amma tai ƙoƙarin hanasu tana ƙara rarrashin Muneebba tare da mata nasiha mai kwantar da hankali wacce ta ratsa jikin Muneebba ta kuma shirya zaman aure tsam a ɗakin mijinta tare da amsar ƙaddararta
Ƙwallon da akai a tsakar gida shi ne ya janyo hankalin su Muneebba da kuma Mutanen tsakar gidan
kallon jiga_jigan matan suke yadda ko waccensu ke taunar Chewingum fuskarsu sanye da Glass ko wace fuska ba fara'a ko annuri wata uwar Ashariya Aunty Meera ta ƙunduma tana faɗin "ban zaci baƙin talaucin ya kai har haka ba,ko a mafarki ban zaci zan shigo area irin wannan ballantana haɗa zuriya da irinku"ta faɗa wani tuƙuƙin baƙin ciki na cinta
wani wawan tsaki Seemah ta buga tana faɗin "Amma Dad yaci mutuncinmu da kuma arziƙimmu ko a ƙaddararren mafarki ban taɓa tsammanin zan haɗa hanya da wannan cin mutuncin ba,ke dalla fito muje" ta faɗa tana faɗawa ɗakin da Mamma da Muneebba suke harda yunƙurin take ƙafar Mamma
cikin takaici da tuƙuƙin baƙinciki Muneebba ta ɗago tana dubanta baccin rashin kunya ba halayyarta bace da babu abinda zai hanata ciwa matar nan Mutunci ,kauda kanta tai tana taune leɓe tare da saukar wasu siraran hawaye waɗanda ta rasa gane na miye
Miƙewa Mamma tai tana dafa kafaɗar Hafsat wacce itama baƙinciki ya hanata magana, kama Mamma tai suna fitowa tsakar gidan wanda lokacin su Aunty Meera har sun wuce suna jiran fitowar su Muneebba
Mamma Ladiyo ce ta shiga ciki tana kamo Muneebba tana ƙara gyara mata mayafin lifayar tare da sakin wani Munafukin murmushi wanda ba kowa ne zai gane ba,hannunta ta kamo tana fitowa da ita tsakar gida, ɗakin Mamma Muneebba ta shiga wacce ta tsirawa waje guda ido Alamun tayi nisa a tunani
da fata Muneebba tai wanda ya saka ta dawowa duniyar tunanin data lula, murmushin dole ta ƙaƙalo tana mata wanda ya kashe jikin Muneebba, dubanta Mamma tai ta ƙara mata nasiha wanda ta dinga kuka,har sai da aka fito da ita, koda zata fita taga Yaya Khabir ta rumgumesa tana sake fashewa da wani irin kuka, kallonta Khabir yai yana rarrashinta wanda shima dauriya kawai yake
kamar kada ta bar gidan haka take ji har suka fito daga gidansu da ƴan rakiyarta sai Hafsat, kasancewar lungun nasu ba wajen ajiye motoci ya saka su ƴar tafiya har suka fita bakin Titi wanda security ne tako ina, ga manya manyan Motoci na Alfarma ƴan ubansu baƙaƙe wuluk, guda biyar, cikin ta tsakiyar Muneebba ta shiga kingin kuma ƴan rakiya ta gaban kuma su Aunty Meera da Seemah ne a ciki,
A hankali Motocin ke tsula gudu cikinsu sai ƙamshi da kuma wani ni'imtaccen sanyi mai ratsa gaɓukka, a hankali ta runtse idonta ƙirjinta na mata wani nauyi wanda kamar an saka nannauyan dutse an danne mata shi haka take ji,ji take a yanzu ne shafin littafin kundin ƙaddararta ya buɗe, ta gaza fitar da Nazeer a cikin ranta,wanda tuno halin da yake cikin shine ke sakata kokowa da ɗaukewar Numfashinta,rufe idonta tai wasu hawaye masu ɗumj na sauka a kuncinta
Wata haɗadɗiyar Anguwa ta jiga_jigan manyan masu kuɗi suka nufa tun daga get ɗin farkon shiga Unguwar kansa abun kallo ne, ƙerarrun gidaje ne haɗadɗi kai kace a ƙasar London aka ƙera su, ko a London sai ka amsa sunanka zaka iya kera gidaje irin wannan,ba zaka taɓa cewa a Nigeria akwai Anguwa irin wannan ba,zamanta sai shahararren mai kuɗi da jiga_jigan ƴan siyasa masu amsa sunansu da kuma manyan shahararrun ƴan kasuwa
gidan da yafi tsari da haduwa nan suka nufa inda driver ya Danna Remote nan take Makeken Get ɗin farko ya wangale,ga samudawan sojojin dake ta muzurai suna tsaye sun kame a wajen
Wani kalar dum gaban Mamma Ladiyo yai lokacin da taci karo da kalar gidan yadda get ɗin farkon kansa kamar ka shiga a wata duniya ta daban sbd haɗuwarsa da tsaruwarsa get na biyu suka tunkara inda zuciya ta kawowa Mamma Ladiyo iya wuya, gani kanshi get na biyu yanda yake wani sheƙi da walwali kamar da zallar Zinare aka kerasa,ga wasu kalar samudawan Security da suka kame a wajen, ɗaya daga cikinsu ne ya tunkaro Motocin yana dubawa, kafin ya koma ya danna Wasu Numbers nan take ya wangale suna kara danna hancin motarsu a ciki
Wayyo zuciyar Mamma Ladiyo kasa ne kawai ke bata fado ba Sbd takaici,mazgewa tai tana ƙakalo fara'ar dole ta sakawa kanta, a get na Ukku suka ƙara shiga nan Aljannar duniya ta bayyana,(ku hasaso irin tsaruwarsa da haɗuwarsa, don sai na kare Page 3 ban gama zayyano maku shi ba) fitowa mutanen suka fara yi, sannan Muneebba ta fara zuro da farar ƙafarta wacce ke cikin flat shues haɗaɗɗu ƙafarta tasha jan lalle wanda ya ƙara ƙayata kyakkyawar ƙafarta a hankali ta ida zurowa da gudar tana fitowa Rabi da Hafsat ne suka kamata suna bin su Seemah wanda suka nufi wani Coridor wanda ya sada su da wani haɗadden Part mai kyau................
Only call me 08109554986
Chat me 09074759493
[5/21, 8:12 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*
Book 1
By: RIAMCOOL
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
Bismillahirrahmanirrahim
*P.25&26*
____________Wani Coridor suka bi wanda ya sa da su da haɗaɗɗen Part, Ƙofar Seemah ta tsaya tana danna wasu Numbers nan take kofar Falon ta buɗe
haɗaɗɗen Falo ne wanda yaji Funiture da kayan more rayuwa, ga wani uban sanyi da ƙamshi dake tashi, A hankali kowa ya shiga suna zama kan lallausan Cafet ɗin dake Malaye a tsakiyar Falon,
ɗago da kanta Muneebba tayi ta cikin mayafin lifayar tana duban Falon wani iska mai zafi ta fuzar hawaye na bin kuncinta, duk daular da ta shigo ji take kamar ta shigo a matsatsin kurku ne, hatta sanyin Ac dake fita ji take kamar ana buso mata da hucin zafi, lallausan Cafet ɗin da take zaune ji take kamar tana zaune a bisa ƙaya ne, ta ina zata fara karɓar ƙaddarar data tunkarota?ta riga da tasan yanzu ne zata fara buɗe babin kundin ƙaddararta
ƙwas ƙwas ƙwas sautin ƙarar takalminta ke badawa tana bin step ɗin a hankali tare da tauna Chewingum jikinta sanye da dakakkiyar Shadda blue color wacce taji aiki da Stone sai walwali take,wuyanta sanye da sarƙar Gold, hannunta ɗaure da Watch ɗin Diamond yatsunta ma ɗauke da zabban Diamond sai walwali suke,wani kallon ƙasƙanci da ƙyama Momm ta bisu dashi tana zama ɗaya daga cikin kujerun Falon ta ɗora ƙafa ɗaya bisa ɗaya tana ƙare masu kallo, "Meera!!! Meera!!!" ta faɗa da ƙarfi
fitowa Aunty Meera tayi,"Meera me yasa zaki kawo man jinin talauci a Falo? kamar ba ki san inda zaki saka ƴan aiki su kaisu ba" ta faɗa da ɓacin rai
kamar ba Mahaifiyarta ba haka Aunty Meera ta taɓe baki tana faɗin "To Ni miye laifina zaki iya sakawa a kaita a Falon" ta faɗawa tana shigewa wani Coridor
Indo ta ƙwalawa kira tana sakawa ta nunawa su Muneebba Part ɗinta,tare da ƙaresu da zagi da cin mutunci, Indo na gaba suna biye har suka iso Part ɗin mai kyau da tsari shima,Falon suka shiga wanda komai na ƙawa da kayan more rayuwa yaji, kamar wacce ƙwai ya fashewa haka Muneebba taja ƙafafunta tana faɗawa bisa ɗaya daga cikin kujerun Falon ta fashe da kuka mai tsuma zuciya,
kama hannunta Mamma Ladiyo tayi tana faɗin "Muneebba kiyi haƙuri da kalar rayuwar da kika tsinci kanki komai na rayuwa muƙaddarine da Ubangiji ya riga ya rubutasa tun kafin dirowarki a doron duniya, ki sani shi bawa baya wuce ƙaddararsa,duk yadda kika tsinci kanki a rayuwa ki godewa Mahaliccinki,sannan kiyi haƙuri da juriwa wajen zaman aurenki mu muna miki fatan Alkhairi zamu tafi dan ba zamu tsaya a ƙara ci man mutunci ba"
wani kukan ta sake saki tana kama hannun Hafsah tare da furta "Hafsat kema tafiya zaki yi ki barni a cikin wannan baƙin gida mai cike da tarin Azababbiyar jarabta,na san ke masoyiyata ce ta gsky Hafsat kada ki barni a gidan nan mu tafi a tare wallahi ba nison auren nan mai cike da tarin ma'anoni da ƙangin bauta tun a saka ƙafata gidan nan nasan da cewar na riga da na shigo baƙin kurku, akwai abinda zai sameni Hafsat idan kuka barni ku tafi dani"
Kuka Hafsat ta fashe dashi tana girgiza mata kai "don't say that Muneebba kiyi haƙuri in sha Allah komai mai wucewa ne,kiyi haƙuri kiyi zaman aurenki da zuciya ɗaya, mu zamu tafi saduwar Alkhairi" ta faɗa tana ɓanɓare hannunta da fita da sauri wani kukan na tafo mata don ba zata iya jurar ganin halin da ƙawar tata take ba
tana ji tana gani haka suka fice kowa jikinsa mace laƙwas, sulalewa tayi tana gunsheƙar kuka mai ban tausayi wanda har muryarta ta sauya, sbd tsabar kuka
shigowar da aka yi ce ta sakata ɗago da fuskarta tana duban Indo wacce itama ita ɗin take kallo "ga Abinci Hajiya kici" ta faɗa tana ajiye mata warmer ɗin a gabanta
Ɗaga kai kaɗai ta iya mata, da tausayawa Indo ta bar Falon tana ja mata ƙofar, miƙewa tayi kamar wacce aka yiwa shegen duka, Bedroom ɗin da ke Falon na gefe ta faɗa tana ƙarewa ɗakin kallo, zuciyarta taji ta ƙara cunkushewa da wani Azababben baƙin ciki da ɗaci, Toilet t faɗa tayi wanka da Arwalla ta mayar da sallar Magriba da Ishsha'i, Abinci kuwa kaɗan ta ɗan tsakureshi tana jiran shigowar Mijin da aka ce an ɗaura mata aure
ganin har 10pm ta wuce ya saka ta kulle ƙofar ɗakin tana kwanciya don jin kanta na ciwo kamar ya tsage gida biyu
*MAHEER*
kwance take bisa cinyar Mammi idanunwanta na tsiyayar da hawaye "Mammi wata ta fara shiga rayuwar Yaya Bobbi ba ni ba, wata ce ta fara zama uwar gidan sa kafin ni, amma na san haka Allah y ƙaddara man, Mammi na tashi da soyayyar mutun biyu na kaunacesu a lokaci guda sannan nake tsantsar kishinsu su biyu kafin Mutuwar Yah DEEN na soshi na ƙaunacesa da tsatsagwaron kishinsa,shi da Yah Bobbi, cikin ɗayan biyu na rasa wane nafi so"
shafa kanta Mammi tayi cikin tausayin ƴar tata, "Daughter zanyi komai domin ganin farincikinki tabbas zan raba Auren Bobbi dashi da yarinyar ke ɗaya ce ƙwal a wurinsa "
"Mammi ba zan barki ki aikata wannan zunubin ba a kaina zan zauna da