x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 10 - BAYAN WUYA free pages complete

  • 27001 words
  • 30000 words
  • Out of 37650 words

Category: Tale Stories

Views 167

27 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
tururaku masu masifar ƙamshi


"Wow Mrs Asad BObbi wanna kyawu haka kamar zaki tafi gasar kyau" Zulaihat dake shigowa ta furta da ita da sauran ƙawayensu, dariya Maheer tayi tana juya idanu,zuzuta irin kyawun da Maheer tayi suka ci gaba da yi kanta na ƙara fasuwa


Sai bayan la'asar sannan dukkansu suka nufi gidan Mommi, cike gidan yake sosai anata hada_hadar biki,Kai tsaye Part ɗin Mommi suka nufa



*Muneebba*

Sauri _sauri take tafiya har tana neman yin tuntuɓe, bakinta ɗauke da bismillah ta tura ƙofar ɗakin tana shiga hannunta riƙe da tsintsiya alamun shara za tayi, tun daga Falon take ƙare masa kallo tana jijjiga kai, dubanta takai kan wani tangameman Photon Bobbi dake liƙe jikin bangon ɗakin, ƙare masa kallo take tana taɓe baki tare da ƙara godewa Allah da zata zauna ma ba tare daya santa ba duk da kasancewarsa Mijinta amma bata fatan haɗuwarta dashi, tun da shima kansa bata ita yake ba, cikin sauri ta gyara ɗakin kasancewar ba datti dan kullum sai ta gyara kuma da alamu ba'a amfani dashi yadda ta gyara sa haka zata zo ta iskesa shi yasa wani lokacin take kwanciyarta a ciki ganin babu mai amfani dashi, yau tana gamawa ta fice kanta ƙasa take tafiya dan hankalinta sam baya a jikinta, karo ɗin da taci da Mutum ne ya sakata ɗagowa da azama tana dubansa sai dai gabanta ne ya faɗi tana zaro manyan idanunta tare da ja baya ganin wanda ta bangaje, ba tare daya kulata ba ko ya kalleta ya ida haurawa sama yana kakkaɓe jikinsa tare da kakkaɓe inda ta shafesa "Yeah shine Bobbi dai Mijina" ta furta a hankali tana bin sa da ido


Daga kafaɗa tayi tana ida safkowa kai tsaye side ɗin da aka bata ta nufa dan tayi wanka, tura ƙofar Falon tayi taji ta a buɗe da mamaki ta shiga sai dai mamakinta ne ya koma ganin Mom zaune ta hakimce tana dubanta a ladabce ta durƙusa tana gaisar da ita, a yatsine ta amsa tana dubanta "ke ga kaya nan kiyi wanka ki saka zan turo miki da mai kwalliya yanzu, anjima za'ai Mother's day ɗin Mijinki da abiyar zamanki shine zan haɗeku koda wasa idan kika rufe fuskarki karki buɗe"


Da to ta amsa jiki a mace,tun da Mom ta fita ta samu damar fashewa da kuka ko zuciyarta zata samu salama, sai da tayi mai isarta sannan ta tashi ta shiga wanka


fitowa tayi jikinta ɗaure da Towel jikinta ta goge sannan ta shafa Lotion tana zama, bata daɗe ba mai kwalliyar tazo ta tsantsara mata,make up haɗaɗɗen Bride Material red color ta saka, wanda ya fiddo ta tai masifar kyawu haɗaɗɗen ɗauri mai kwalliyar ta kashe mata wanda ya fiddota sosai, sarƙar Gold ɗin ta saka a Awarwron kafin ta yana mayafi a kanta, zaune tai bakin Bed hannunta riƙe da Hand bag tana jiran Aiken Mom



Iftihar ce ta shigo babu ko Sallama "ke taso muje" ta faɗa tana yatsina ba tare da tabi ta kanta ba ta miƙe suna fita, tunda ta fito ta rufe fuskarta da mayafi har suka fito farfajiyar gidan inda Mutane ke nan mata da maza ƴam Mata da samari tun da ta doso wajen gabanta yai mummunar faɗuwa ganin wanda ke tsaye a wajen Mutane na ɗaukarsa pictures da murmushi Mom ta tunkarosu tana kama hannu Muneebba ta nufi inda Bobbi ke tsaye shida Maheer ana daukarsu picture, hannu Bobbi ta kama da murmushi ta haɗa dana Muneebba,ba tare daya kalleta ba aka ci gaba da pictures har Ishsha'i ta wuce sannan aka kawo manyan Motocin da zasu nufi wajen Mother's day ɗin motar da tafi ko wace haɗuwa ita Amaren suka shiga, hadda Bobbi Wanda babu wacce ya kula ko ya kalla, kamar Muneebba ta fasa ihu haka take ji



haɗaɗɗen Hall Wanda ya amsa sunansa yaji Naira nan suka nufa, maƙil da jama'a wajen yake tun daga tsayuwar Motocin aka fara vedio wanda Bobbi ya fara fitowa sai kuma Muneebba wanda ya sagalo hannunsa da nata haka ma Maheer tafi da sowa wajen ya ɗauka har suka nufo cikin Hall ɗin, kai tsaye wajen da aka tanaza dan su suka nufa suna zama, Anci an sha Anyi bajinta an gwada wa Naira zallar rashin imani, sannan anyi rawa ta bajinta da tsari basu suka tashi ba sai wajen karfe 1 na dare, sannan suka dawo gida,


Muneebba da sauri take tafiya dan ta nufi part ɗin ta ganin dare yayi gata da tsoron dare, abu taji ta buge a gabanta har mayafin kanta na zamewa da sauri ta ɗago tana duban Zaidu dake tsaye wanda shima Binta da ido yai gabanshi nan take yai mummunar faɗuwa yana ƙare mata kallo From top to bottom , baki na rawa ta furta "yi haƙuri wallahi ban ganka ba"


bai iya magana ba illa lumshe idanuwansa da yai yana ɗaga mata kai, sannan ta wuce da kallo ya bita yana cije leɓensa na ƙasa cikin zafi da raɗaɗi "Me yasa Bobbi yai man zarra a komai ne, yanzu wannan ce matar tasa?kai ina wallahi ba zan bari ya mori yarinyar can ba dole ne nayi mai yiyuwa wallahi








*********************************


*Yola*
*Fattu*



Sosai akai nisa dasu JODDi a garin sannan aka ajiyesu, ko wanensu yashe suke a dokar dajin wanda baka jin motsin komai idan ban da kaɗawar itatuwa da kuma kukan tsuntsaye,



Tunda sanyin Asuba ya doso numfashin Fattu ya fara dawowa tana buɗe kumburarrun Idanunta "JODDi!!!! karku kashe man Joddina ku ƙyalesa ku ƙyalesa karku kashe man shi dan Allah na roƙeku" ta furta da ƙarfi jin shiru ba'a amsa ba da kuma jinta kamar a ƙasa kwance ya sakata ƙara ware idanunwanta dishi_dishi ta fara gani kafin ta murza idanunwanta ta ɗan fara gani, ganinta kamar a dokar daji ya sakata miƙewa da ƙyar tana bin ko ina da kallo idanunwanta ne suka sauka kan JODDi wanda yake kwance babu alamar numfashi a tare dashi ƙara ta fasa tana miƙewa ta nufesa don ta manta ma ciwon dake jikinta da kalar Azabar dake ratsata, hannu biyu ta saka tana tallafo fuskarsa fashewa da wani matsanancin kuka mai ban tausayi tayi tana furta "Innnalilahi wa'inna ilaihirraji'un sun kashe man JODDi , dan Allah ka miƙe karka mutu kar ka tafi ka barni bani da kowa, wajenka nake raɓa naji sanyi JODDi bana da wanda ya Fika ka taimakeni ka tashi" ta faɗa wani kuka mai ciwo na ƙara kufce mata









ganin shiru ba Alamar zai tashi ya sakata miƙewa tana ratsa wata hanya da gudu tana binta sosai take gudu har Numfashinta na shiɗewa taci uwar tafiya sosai amma babu motsin koda Mutum ɗaya ne a cikin jejin, kasancewar ta san magunguna ya sakata ƙara dosar cikin Jejin tana ƙara duba itatuwan dan ta tabbatar JODDi ba mutuwa yai ba, ganyayaykin data sani ta ɓallo tana biyo hanyar ta dawo kamar ranta zai fice haka take tafiyar kota ciwo jikinta bata bi da jirin dake ɗibarta






*Pls Habibties ayi manage da wannan dan Allah love U All my lovely Habibties ina matuƙar ƙaunarku har cikin zuciyata*


*Riamcool ce*
[5/21, 8:18 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*

*Book 1*

*By Riamcool*


*MIKIYA WRITTER'S ASSOCIATION*


*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*



*P.35&36*





A haka harta ƙaraso inda ta barshi kwance, har iyanzu koda ɗan yatsa ne baya motsawa, hawayen da take riƙewa ne suka ƙara samun damar zubowa, a hankali ta saka ɗan yatsanta tana ɗaukesu tare da duƙawa ƙasa ta ɗauko ganyen maganin tana matsa ruwansa, a hankali take buɗa masa bakin tana matsa masa ruwan a haka harta ɗan bashi ya shiga, kingin kuma ta shafe masa jiki dasu babu kamar inda yaji raunuka


sun ɗauki tsawon kwanaki cikin jejin kafin ta samu jikin Joddi ya fara dawowa dai_dai


Kwance take ta ɗaga kanta sama tana tunanukan dake ƙara karyar mata da zuciya, hawayen da taji ya biyo kuncinta ne ya sakata sanya hannu tana sharewa tsawon kwanakin da suka ɗauka basu ga koda gibcin wani mutum a cikin jejin ba hakan ya sakata yanke shawarar dan tafiya ko sunga mutane, miƙewa tayi tana zuwa wajen JODDi masa magana "JODDi miƙe muje" miƙewar yayi dan a ɗan zamansu yanzu yana fahimtar magana sai dai mayarwa ne baya iya yi,


tafiya suke iya ƙarfinsu dan sunyi tafiya mai ɗan nisa kafin su shiga wani ɗan ƙaramin ƙyauye, hamdala Fattu tayi tana sauke wahalallen numfashi kafin ta samu wuri ta ɗan tsaya shima tsayawa yai ƙyam yana ƙarewa wurin kallo hannuwansa mai dai a baya, kallonsa tayi taga kamar wani mai cikakken hankali dan babu wanda zai kallesa yai masa kallon mahaukaci "Zauna" ta furta masa da Yaren fulatanci zama yayi bakinsa na motsi amma ya gaza furta wani abun, murmushi kawai ta saki tana kawar da kanta gefe sun juma anan zaune rasa inda zasu nufa, "Bayin Allah tun ɗazun na ganku anan zaune amma ku baƙi ne?"



ɗan Dattijon ya tambaya da murmushi sosai a fuskarsa, itama Fattun Murmushin ta saki da hausarta marar fita tace "Ye mu baƙi ne bamu shan kowa anan ba dan Allah ko zaka iya taimaka mana wallahi bamu da kowa a duniyar nan bawan Allah ka taimakemu idan har kana da hali" ta faɗa wasu hawayen na sake biyo kuncinta


da tausayawa mutumin yace "Ayya ku taso muje gidana" babu musu suka bisa har gidansa, iso yai masu suka shiga har cikin gidan ruwa ya fara sakawa a kai musu na wanka dan yaga suna da buƙatar hakan,bayan sun gama aka basu Abinci da ruwa suka sukai nak,kallonsu mutumin yai yace "ko zaku iya bani ɗan takaitaccen labarinku?"



"Eh Baba" Fattu ta furta nan take ta faɗa masa labarinsu tun daga farko har ƙarshe batai masa ƙarya ba, da tausaya yake binsu da ido shi kanshi yai matuƙar tausaya musu, "Sannu kunji ko, lallai Ubangiji ya kareku daga ma sharrin shaiɗan da har baku aikata wani abun ba dukda ba isasshen hankali ne dashi ba amma bai kamata kuna yawo babu aure a tsakaninku ba, abinda nake gani a karo na biyu zan sake taimakonku, zan ɗaura muku aure a goben nan in sha Allah"



wani dummm gaban Fattu ya faɗi jin kalmomin mutumin taya zata iya rayuwar aure da JODDi? ita fa a matsayin Yaya ɗan uwanta ta ɗauki Joddinta da kuma soyayya ta Addini musulunci ita haka take gani, amma komai Ubangiji ya ƙaddara mata mai kyau bata da ikon jayayya akan lamarin da Ubangiji ya tsara mata, zata amshi ƙaddararta a yadda tazo mata, ita a yanzu dukkan wata rayuwa da zata zo mata hannu biyu zata saka ta karɓeta ta godewa Ubangiji, "Ƴata naji kinyi shiru" ɗago da fuskarta tayi tana faɗin "Baba duk hukuncin daka yanke mai kyau ne yadda ka taimakemu Ubangiji ya baka mafiyinshi mun gode shoshai"


"babu damuwa Ƴar Nan Addinina na hidimta mawa taimako shi wani abu ne mai tsananin lada a duk lokacin da kaga ɗan uwanka na buƙatar temako kayi ƙoƙarin tai maka masa da iyakar ƙarfinka kaima Ubangiji zai taimake ka a dukkan wani hali da ka tsinci kanka, rayuwa kake amma gaba kaima baka san inda zata kaika ba"


ɗaga kanta tayi tana matsa yatsun hannunta, dukkan maganganun da suke tsab JODDi ya riƙesu yana binsu da ido wani abu na daban na masa yawo a brain ɗinsa tsab kalmomin da Mutumin yai suka buɗe masa wani abu daya rufe masa ƙwalwarsa "waye Ni?" ya furta yana dubansu



a mugun razane Fattu ta ɗago idanunta tana kallonsa "Joddi kana magana dama, ka tuno waye kai??" Tai masa tambayoyin a jere


da ido ya bita yana faɗin "Ni dai ban san waye ni ba nima haka kawai na ganni" jijjiga kai tayi sannan tai hamdala ga Ubangiji daya buɗewa JODDi bakin yin magana



"Masha Allah tun da Ubangiji ya buɗe masa baki yanzu dare yayi kije wajen mai ɗakina ki kwanta zuwa gobe da safe zan isa wajen mai gari na sanar masa da buƙatarmu" Dattijon ya furta



da to ta amsa zuciyarta na bugawa dan bata san kalar matar da zata taras a gidan ba wataƙil ma ƙara Innaro da ita, bakinta ɗauke da sallama ta shiga amsa mata ƴar Dattijuwar dake zaune tayi tana furta "shigo ƴar nan kin jiko Malam ya sanar Mani da zuwanki" ta faɗa da Murmushi tana miƙewa



Ajiyar zuciya Fattu ta sauke ganin Matar ba irin Innaro bace, a ladabce ta gaisar da ita tana zama, amsa mata matar tayi da fara'ar sosai, kamar ta goyata haka ta dinga nan da nan da ita harta kwanta tana tunanin halayen Mutanen nan biyu dama akwai mutane irin haka? ta tambayi kanta, a ranar dai wani bacci mai masifar daɗi ya ɗauke ta wanda zata iya rantsaewa tun da take bata taɓa yin Bacci mai daɗi irin wannan ba


*Washegari* koda suka tashi daga Fattu har JODDi Mutumin ya kaisu wajen mai gari, tsab cikin hikima Dattijon ya ɗan faɗa masa wani abu daya saka su baro gida sannan ya kawo musu buƙatarsa, babu musu mai gari ya Amince sannan ya tara mutanen garin ya faɗa musu buƙatarsu, mai gari ya bayar da sadaki, kallon JODDi Dattijon yayi yana furta "Ya sunanka?" kamar wani mai Imagine haka JODDi ya tafi can kuma sai ya cije baki da ƙyar yana furta "Muhammad"


"Sunan Mahaifinsa fa?" Mai gari ya tambaya "Ahmad" JODDi ya furta, babu ɓata lokaci aka ɗaura auren JODDi da Fattu





***********************

zaune take bisa Ƴa kujera ta guragu tana kallon fuskar mijin nata da tausayawa wanda take matsa mata ƙafafuwan ta, Allah kaɗai ya san irin ƙunci da baƙin cikin Abinda take ji idan harta ga Mijin nata cikin wannan hali kullum hankalinsa ba a kwance ba ga matsanancin ciwon da yake fama dashi, itama kenan da take kallonsa ina ga A'ishatu wacce yai mata nisa a iya tsawon shekaru to ita wane baƙin ciki ma ne bata ƙunsa ba?


hawaye ta share tana jana Majina, ɗago da idonsa Abbie yai yana kallonta "Mansura kukan ne baki daina ba, ita fa ƙaddara babu yadda bata zuwar wa mutum ko wane bawa kika gani da tashi jarbtar sai dai wata tafi wata kiyi haƙuri da rayuwar da kika gammu a ciki, kiyi tunani da Ƴar Uwarki Aysher mana ki hasaso dake ke cikin halin da take ciki ya zakiyi? amma tai haƙuri ta jure taci gaba da rayuwarta ba wai dan bata jin ɗaci da zafi bane a a sai ɗan wadatar zuciya da Ubangiji yai mata,nayi Imani da mahaliccina babu ranar da zata fito ta koma Aysher ba tayi tunanimmu ba ko kuma kewarmu, tabbas akwai ciwo ke kin rasa ƙafa da baƙi ita ta rasa idanuwa, kin san ma kuwa irin tsangwamar da take fuskanta a Al'umma da ita da yaranta ƙazafi babu wanda Aysher bata gani ba, kuma duk ina kallo amma babu halin taimaka mata abin na man zafi da ciwo yadda baki tunani, babu ranar da zata fito ban zubar da hawaye ba,amma a haka Mansura kullum ƙara godewa Ubangiji nake"Abbie ya ƙarashe da murmushi mai ciwo



tunda yake zancen hawaye masu raɗaɗi da zafi ke biyo kuncinta tabbas ita tafi tausayin A'ishatu a kanta A'ishatu Ƴar uwa ta ɗauke ta ba a matsayin kishiya ba, tabbas tasan duk ɗaci da raɗaɗin da take ciki A'ishatu ta fita shiga cikinsa shin ita ya take ji? share hawayen tayi tana mai kawar da kanta



haka shima Abbie bai ƙara magana ba kasancewar Abinda Ya tsaya masa a maƙoshi ga zuciyarsa dake wani harba masa da sauri_sauri daman ya san za'a rina domin duk lkcn da yai maganar A'ishatu haka ce take faruwa dashi, Anya zai iya wannan rayuwar tabbas zai karya Alqawarin daya ɗauka ya fito da gaskiya fili sannan ya fashe rufaffen ƙwan daya daɗe ba a ƙyanƙyasa sa ba sai dai komi zai faru ya faru koda kuwa hakan yana nufin zai rasa nasa numfashin ne






*********************************

Alhamdulillahi anyi biki lafiya an ƙarashe lafiya inda Maheer ta zama matar Bobbi, ba ƙaramin farinciki Maheer ta tsinci kanta ba a lokacin da ta zama mallakin Bobbi sai dai zullumin ta ɗaya ne yadda zata sace zuciyar BOBBI ta tabbatar abu ne mai wahala sace zuciyar mutum kamar Bobbi


ba ƙaramin kuka da dana sanin son maso wani Maheer tai ba a lokacin data kwana ɗaya bata ga Bobbi yazo gunta ba da niyyar raya wannan dare, ko wace Amarya na farinciki A daren farkon data kwana ɗakin mijinta amma ita sai tarin baƙin ciki da takaici ta ƙunsa tabbas ta shiryawa wannan rana domin fayyacewa Bobbi soyayyar da tayi mata mugun kamu tayi niyyar fayyace masa dukkan wani sirri na zuciyarta a daren farkon ta amma sai dai kash bata samu wanna ikon da damar ba



kwance dake jikinta lulluɓe da blancked idanunwanta sunyi luhu_luhu saboda kukan data sha Nocking ɗin da taji anyi ne ya sakata miƙewa da ƙyar tana gyara gashinta "come in" ta furta a hankali,

kanta a sunkuye ta ɗago tana duban Maheer tace "Am Hajiya tace ki sabko kici Abinci" fuskarta da ɗan murmushi tace "ok you can go"



harta tafi kuma sai taji Yarinyar ta birgeta cikin ɗan ɗaga murya tace "Nace ba" ɗan juyowa tayi tana haɗiye abinda ya tsaya mata a maƙoshi tace "na'am" tana kallon Maheer wacce ke murmushi "Ya sunanki?" Maheer ta tambaya tana kallonta



"Muneebba" ta furta ba tare data kalleta ba "wow nice Name you can to be my friend?"



"Yes Mah" ta furta tana ƴar dariya, itama dariyar tayi "ok you can go pretty" ok ta furta tana fita tana mamakin halayen Maheer a farko ta saka zata yi girman kai da wulaƙanci amma sai taga saɓanin hakan, a yau da ta samu wacce ta ɗan sake mata fuska sai taji ta wata ta daban,duk damuwar da take ciki sai taji ta ɗan rage, amma sai dai idan tasan da cewar ita ɗin ko wacece ta tabbatar sai ta sauya mata ta musguna mata may be tama fi su Mom ƙuntata mata Dan ganin Mijinta take aure da wannan tunanin harta safka ƙasa ba tare dama tasan ta safka ba "ke!!!" taji daka tsawar Mom



A hanzarce ta ɗago tana dubanta "na'am Mah" ta furta bakinta na kyarma, a wulaƙance Mom ta bita da kallo "gidan
End Ads