x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - BAYAN WUYA free pages complete

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 37650 words

Category: Tale Stories

Views 168

27 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
da farincikina Nazeer," ta faɗa tana mai ƙara sakin wani murmushin





kallonta Hafsat tayi tana mai girgiza kai saboda tana tausayin ƙawarta akan mugun son da take yiwa Nazeer ɗin, saboda tasan halin mahaifiyar Nazeer ɗin yadda ta tsani talaka, "Allah dai ya barki da Nazeer ɗin nan Muneebba,amma fa wannan son da kike masa yayi yawa Allah."





ɓata fuska Muneebba tayi tana faɗin "kinga Hafsat idan ba zaki ƙara ƙarfafa man gwiwa akan naso Nazeer to ƙara kawai kiyi shiru."






"Allah ya baki haƙuri keda kan Nazeer sai ki ƙulla gaba da mutum." banza Muneebba tayi mata har aka tashi babu wanda ya kula wani,saida kowa zata shiga lungun gidansu sannan Hafsat tayiwa Muneebba Sallama shima Muneebba nata fushi ta amsa, sannan shiga wani ɗan ƙuƙut ɗin lungu wanda duka gidajensu na marassa ƙarfi ne,wani ɗan ƙaramin gida da yafi na lungun nasu lalacewa naga ta duƙa ta ɗage zanen da suka lulluɓe ƙofar ta shiga da sallama ɗauke a bakinta ta shiga cikin gidan,







Sallama tayi taji tsit hakan ya tabbatar mata da Mamma ta shiga lazimi,wucewa tayi ta cire uniform ɗin, wayarta ta ɗauko INFINIX HOT 10 wacce Nazeer ɗin ya siya mata, Number Nazeer ta dannawa kira,saida tayi 3 miss call sanna ya ƙara kira,sosai tai mashi ƙorafi ya lallasheta sannan suka ci gaba da hira da junansu cikin so da ƙaunar junansu, a ranar ne kuma Nazeer ɗin zai ako gidan su Muneebba, sosai ranar Muneebba ta yini cikin farinciki da murna





*Bayan kwana biyu*

sosai Muneebba ke murnar saka musu baiko da akayi da Nazeer, saidai matsalarta guda ita ce Mahaifiyarsa,don tayi mata warning yafi a ƙilga akan ta rabu da Nazeer amma taƙi, don saida Baban Nazeer ɗin yai mata jan ido sannan ta bari akayi baiko amma ta ci alwashin bazata taɓa bari Nazeer ya auri Muneebba ba,



Kwance take bisa cinyar Mamma, Mamma na mata fira tana dariya, shigowar Mutum suka ji babu ko Sallama,



ɗaga kanta Muneebba tayi taga Maman Nazeer ce,miƙewa tayi tana ce "Hajiya ina yini"





"dalla rufe man baki da ban yini ba kin ganni, Warning nazo buge miki, akan ki ni sanci kanki da yarona,don bani son haɗa jini da marar asali da galihu,ku ɗin nan da ba'a san asalinku ba anfi danganta ku da ƴaƴan shegu, to wallahi na faɗa akan ki auri Nazeer ƙara na saka a nakasa ki,na faɗa miki karma ki ce ban faɗa miki ba" sosai maman Nazeer ta ciwa Muneebba da Mamma mutunci tana gamawa ta kaɗa bujenta ta ƙara gaba






faɗawa jikin Mamma Muneebba tayi tana fashewa da wani Matsanancin kuka ta ce "Mamma shin laifi ne danna auri Nazeer saboda ina Talaka, me yasa ake ƙyamar Talaka? talaka yafi kowa ƙasƙanci a gurin wasu masu kuɗi ne???, ni ɗinnan Mamma saboda na kasance talaka kuma marar Mahaifi shiyasa nake shiga cikin tozarcin Al'umma" ta faɗa tana sake fashewa da matsanancin kuka




a faƙaice Mamma ta share hawaye tana murmushin takaici ta ce " ko kaɗan Muneebba ke ɗinnan baki rasa uba ba kina da cikakken uba nagartaccen Mahaifi,da Mutane sunsan wanda ya haifeku da ba zasu kuskura ko kallon banza suyi maku ba, sai dai ko wane bawan da tashi ƙaddara mu tamu jarabtar kenan,kiyi haƙuri komai lokaci ne"






"Mamma kullum ce mana kike inada uba kuma yana raye, me yasa ya zaɓa mana wannan tozarcin me yasa bai nemu ba duk tsawon shekaru, shin anya uba ne??? bana tunanin cikakken Mahaifi zai iya ƙyale yaransa suyi rayuwan tozarci a cikin Al'umma,Mama naji na tsani Mahai......."





wata uwar tsawa Mamma ta daka wa Muneebba daya saka ta yin shiru, cikin matsanancin ɓacin rai Mamma ta ce "kina da hankali ? zaki ce kin tsani Mahaifinki wanda ya kawoki duniya,to karna sake ji idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci" Mamma ta faɗa cikin ɓacin rai





Kallonta Muneebba tayi ta ce "Mamma hakan bazai ƙara fitowa daga bakina ba kiyi haƙuri,amma har yanzun kina son wanda ya banzatar dake a rayuwa yaja miki tozarci a cikin Al'umma ya ci amanarki........"

"Muneebba!!!! bana son wannan zancen ya ƙara fitowa daga bakinki ki" sosai Mamma take yiwa Muneebba faɗa




hawaye kawai ta share tana tashi ta shige ɗaki,ji tayi duniyar yai mata zafi da ɗaci ta ƙara jin tsanar Mahaifinta fiye da kowa na duniyar dukda bata sanshi ba sai dai a labari, sosai take kuka,kukan da ya zame mata jiki a duk lokacin da irin wannan abun ya faru, sosai take baƙin ciki yadda Mamma ke son Mahaifinta


har yanzun sosai take ganin tsantsar ƙaunar mahaifinta a idon mahaifiyarta, ita dai har abada ba zata taɓa son mahaifinta ba.........✍️







*Wai minene asalin su Muneebba,me yasa ta tsani mahaifinta insha Allah a next Page zamu ji mafarin lamarin*





Wannan kenan Comment Share fisabilillah



*Waɗannan sune karsashin Dukkan Marubuci*











*By Riamcool, Star of the Squad*







Only Call

*08109554986*
[5/21, 8:07 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*


Book 1


By Riamcool



*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*







*بسم الله الر حمن الر حيم*






*Page* 7&8






*WAIWAYE*

*Wacece Mamma*

Mamma dai ƴa ce ga Malam Shitu wanda ƴan asalin garin Agadaz ne su biyu iyayensu suka haifa shi sai yayarsa Ladiyo wanda sai da Ladiyo tai aure sannan Allah ya amshi ran iyayensu, hakan yasa Ladiyo ɗaukar Shitu a hannunta dan akwai tserayya sosai a tsakaninsu haka ya taso a gurinta harya isa munzalin aure



Ladiyo wata irin muguwar mace ce tun tasowarsu ba wani ƙaunar Shitu take ba, hakan yasa ta dinga gallaza masa, har kawowar Samartakarsa, koda Shitu ya gwada mata aure yake so hakan yasa tace zata samo masa Mata shi kuma ya gwada mata a'a, hakan yasa ta barshi yai aurensa inda ya auri Mariya wacce Kyakkyawar buzuwa ce, koda aka auro Mariya sai da Ladiyo ta dinga gallaza mata tana bata azaba harya kai ta samu ciki ta haifi ƴarta wacce taci sunan A'isha, kowa cikinsu ba daɗin zama da Ladiyo yake ji ba, don dama tuni Mijinta ya rasu ta dawo da zama gidan Shitu


hakan yasa ta ƙara gallaza masu, don tuni ta mallake Shitu da Mariya duk abinda tace ayi shi za'ayi, gadon Shitu na raƙumma dukta cinye, har Shatu ta fara girma bata canza zani ba, don Ai'shatu tafi kowa cin wuyar Ladiyo, ganin a ɗan kwai sauran dukiyar Shitu yasa Ladiyo ƙwaceta suna bin ƙasa_ƙasa suna kasuwancin siyar da dabino,




A hankali take tafiya cikin Sahara ranga_ranga kamar zata faɗi, saboda zafi da ranar da ake ƙwalawa,ga ƙishin da take ji wanda shine ya ida tagayyarar da ita, so take ta tsaya ta huta amma babu halin hakan saboda wata matsananciyar rana da ake ƙwalawa,ga yashin sahara kanshi ya ɗauki zafi, bare ta zauna ta huta,ga fitinannanen ƙishin daya addabeta wanda shine ya ida galabaitar da ita da yunwar dake ƙwaƙwular hanjin cikinta, a haka harta iso inda mahaifanta suka yada zango,sun kafa runfa a wajen



A galabaice ta iso wajen tana kamfatan ruwa domin ta kai a bakinta, kofin dake hannunta taji an kwaɓe ruwan ya zube a ƙasa, kallon ruwan take yadda ƙasan wajen ya shanye,kuma tayi imani waɗannan ruwan da suka zube ba lallai ta sake iban waƴansu tasha ba,




hawaye taji ya cika mata ido ɗago da fuskarta tayi tana duban iyayenta waɗanda suka kauda kansu a gefe guda suka nuna kamar ma basu ga abinda Yaya Ladiyo ta aikata ba, durƙusawa wajen tayi tana share hawayen da suka samu damar gangarowa a kuncinta, a hankali ta samu waje ta sulale tana mai ƙara jin yadda maƙoshinta ya ƙara ƙafewa yana buƙatar ruwan da zai shiga a ciki



gashin kanta taji Mamma Ladiyo ta kamo tana jansa da ƙarfi,wanda ya sakata ƙwalla uwar ƙarar azaba, mari taji ta kira mata tas, wanda yasa fatar wajen tai jajir shatin hannuwa ya fito ruɗu_ruɗu


cikin ɓacin rai Mama Ladiyo ta dubeta tana faɗin "Shatuwa tun yaushe kika fita saido hatsi a cikin gari? tunfa jiya kamar yanzun tunda kika fita baki dawo ba sai yanzun, ki faɗa man wajen uban wa kika je ya ƙwaƙuleki, jibi yadda Nonuwanki suka sakaka duk an latse su" ta faɗa tana sake faska mata wani marin wanda yasa bakinta fashewa


mahaifanta kuwa sun sadda kansu ƙasa, duk wani mari da Ladiyo tayi mata sosai yake sake sake tsarga musu zuciyoyi, basu da wani halin yin magana don mugun shakkun Mamma Ladiyo da suke ji,



ita kam A'ishatu wani marayan kuka ta saki tana mai dafa ƙafar Mamma Ladiyo tace "Mamma Ladiyo dan Allah kamar yadda Allah ya temakeki nima ki taimakeni ki bani ruwa da Abinci idan ba haka ba mutuwa zanyi,kuma na rantse miki da Allah ni babu Namijin daya taɓa taɓa man koda ɗan yatsa" ta faɗa da ƙara fashewa da wani irin marayan kuka wanda da kajishi kasan mai yinsa yana fitar da ɗaci da kuma raɗaɗin zuciya ne


Ƙafa Mamma Ladiyo tasa tana shure A'ishatu sannan ta ɗaga hannunta mai kama da diga ta ɗaka mata duka a baya wanda yasa cikinta wani irin juyawa bayanta ya riƙe daga duƙen da take ta dinga sheƙa Amai wanda har ta hanci saida ya dinga biyowa dukda ba komai a cikin sai wa ƴansu korayen ruwa da take amayowa kai kace zata zubda ƴan cikinta



wani shurin Mamma Ladiyo ta ƙara kai mata wanda yasa numfashinta tsayawa cak idanunta sun wani ƙaƙƙafe, da gudu Mahaifanta suka yo kanta suna kuka wanda kallo guda Mamma Ladiyo tai masu suka janye idonsu daga gareta hawaye na bin kuncin Maman A'ishatu Mariya



jawota tayi yadda ta sume ta sakata cikin yashin saharan wanda cikin iyayenta ba wanda ya iya magana ko wane abin na ci masa rai




A hankali zafin rana ya fara dukanta wanda kamar ya gasata buɗe lumsassun Idanunta tayi ta ganta cikin rana yashe jikinta na mata tsami ta miƙe tana duƙawa a inda take, don tasan babu damar shiga tantin da suka kafa, don Mamma Ladiyo ba zata barta ta shiga ciki ba koda kuwa Mutuwa zatai hakan yasa ta zama cikin ranar wani masifaffen zazzaɓi na rufeta har dare yayi tana makyarkyatar sanyi wanda yasata yin baccin dole sai safe ta farka



A hankali ta buɗe idonta ta miƙe jiki ba ƙwari abinda ta gani ne da kuma Ihun Mamma Ladiyo da take ji ya sakata ware ido tana ƙara duban jinin data gani malale da gudu ta miƙe ta shigaTantin sai dai tana shiga turus tayi tana ƙara ware idonta ganin Iyayenta kwance anyi musu yankan Rago ga Mamma Ladiyo zaune tana sharce hawayen ƙarya wata kalar ƙara A'ishatu ta saki tana sumewa, ganin haka Mamma Ladiyo zuwa ta ɗauko ruwa ta malaya mata don karta zargi wani abun, don kuwa Mamma Ladiyo ce tabi dare taiwa su Malam Shitu yanakan Rago, koda Shatu ta tashi haka ta dinga jan ajiyar zuciya tana saukewa dan ko kukan ya kasa fita sai dai bin ko ina da kallo da take yi, ganin haka Mamma Ladiyo ta rarrasheta tace mata ɓarayi ne suka zo suka yanka su saboda kuɗaɗen dake garesu da suka ƙi badawa, ita kuwa ta bada nata harda na fansar A'ishatu shi yasa basu kashesa ba



ko kallonta Ai'shatu ba tayi ba hakan yasa Mamma Ladiyo fita cikin gari ta samo waɗanda zasu sallaci Shitu da Mafiya, A'ishatu naji na gani aka binne iyayenta




haka rayuwa taci gaba da tafiya ba wani sauyi, illa sauyin Azaba daya ƙara nunkuwa wa Shatu,



haka rayuwa ta tafiyarwa Shatu wanda Mamma Ladiyo tun sadda ta kashe su Shitu ta tattara suka koma Kaduna da zama, can take sana'ar siyar da Abinci tana ɗorawa Shatu talla sannan da dare ta ɗora mata tallar goro, wanda ƴan iska sukai wa Shatu caaaa ko wane da baƙin ƙudirinsa a kanta, wanda sai dai A'ishatu tai kuka ta share hawaye tana ƙara kaiwa Allah kukanta




ganin yadda ɓata gari ke kawowa Shatu farmaki yasa Mamma Ladiyo jin daɗi hakan yasa ta ƙara kaimi wajen ɗora mata tallar dare kuma idan bata saido shi ba haka zatai mata shegen duka kuma ranar sai tayi mata tsarki na kwaɓaɓɓen barkono





Wannan kenan




A dage da comments











*By Riamcool Star of the Squad*
[5/21, 8:08 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*

*Book 1*

*By RIAMCOOL STAR Of the Squad*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*


Bismillahirrahmanirrahim



*P.9&10*


_________✍️Haka taita gallazawa Shatu azaba kala da kala, da daddare idan ta fita talla goro haka zata daɗe bata saido ba wanda kowa zai siya saiya nemeta da iskanci ita kuma taƙi,hakan yasa take cinɓun goro kuma idan ta koma ba zata canza zani ba daga azabar Mama Ladiyo



Tunda ta taho take sharan hawaye don tasan muddin ta koma da goron da bata saido ba sai Mama Ladiyo ta ninka mata azaba fiye data kullum dama da zata fito saida tai mata jan Warning saboda rashin saido goron dare ko abinci tabar bata, sai dai tabi dare ta kankari ƙanzon tukunya tasha ruwa ta kwanta


tayi nisa cikin tunani ga dare daya fara ritsawa taji an rufe mata fuska an ɗauke ta ihu take son yi amma babu halin haka saboda rufe mata fuska da akayi, wani kango suka kaita suna ajiyeta wuf tayi ta mike tana cire abinda suka rufe mata fuska dashi kwaɗa mata Mari ɗaya yayi wanda ya sata kwala ihu da ƙarfi, fusata ɗayan yayi ya ƙara faska mata wani marin yace "don ubanki yi mana shiru uban wani yasa iyayen naki su doro miki tallan dare? to wallahi ba zamu iya maida kwaɗayimmu ba dole sai mun tasta ki" ya faɗa yana zuge mazagin wandonsa


Ihu ta ƙara fasawa cikin gunjin kuka mai cin rai tace "dan Allah bawan Allah ka dubi girman Allah ku ƙyaleni wallahi ni marainiya ce kada ku yaga man mutuncina da darajata" ta faɗa tana sake fashewa da wani irin masifaffen kuka


tunda ya doso wajen yake jin kukan mace cikin kango na tashi sharewa yayi zai wuce sai kuma yaji ba zai iya ba hakan yasa shi kutsa kai cikin kangon, turus yayi yana kallonsu da ɗai_ɗai ganin ɗaya daga cikinsu yana kokarin yaga mata kayan jikinta tana roƙonsa wata zuciya ce ta ciyosa ganin yadda Mutumen ke ƙoƙarin keta mata haddi, nufar wajen yayi yana kaiwa wancan bahaggon naushi wanda yasa shi ƙwalla ƙara har haƙoransa biyu na zubowa, ganin haka wancan ɗayan da gudu ya taketa ya fice, cikin ɓacin rai Mahamud ya shaƙo wuyan rigar wancan yana naushi sai da ya haɗa masa jini da majina sannan da ƙyar ya ƙwaci kansa ya gudu, ita kau Shatu ta rakuɓe waje guda tana gunsheƙar kuka, a hankali ya tako gareta cikin takonsa mai cike da izza ya nufota yana faɗin "miƙe" babu musu ta miƙe suna fitowa daga kangon, tana fitowa taga yadda tiren goron duk ya watse wani kukan ta sake saki tana faɗin "na shiga ukku nasan na koma wallahi sai ta kusa kasheni ƙara karna koma na kwana anan" ta faɗa da wani sabon tashin hankali wanda ya bayyana ɓaro_baro a. fuskarta, da mamaki yake kallonta ya tambayeta akan me take magana, nan ta kwashe komai ta faɗa masa da kalar azabar da zata fuskanta idan ta koma



girgiza kansa yayi yana cije lips ɗinsa na ƙasa yana mamakin mugun halin wasu mutane cikin tausayinta ya tambayeta goron na nawa ne, ta faɗa masa na 1k ne, hannu yasa Aljihu ya zaro 3k yana miƙa mata



zaro ido tayi tace masa ba zata karɓa ba, wanda da ƙyar ya samu ta amshi 1k da kanshi ya talata gida wanda har Mamma Ladiyo ta kulle gidan tana baccinta hankali kwance, cikin bacci ta taso ta buɗe mata tana shiga ta maida gida ta rufe tana jawo hannu A'ishatu tare da ɗakko wani makeken faskare ta miƙo mata hannu tace "bani kuɗin goron kada ma kice man wani abu ya bata a ciki dan tsab zan iya bazar dake anan ki mutu ubankowa ya huta" jikin Shatu na kyarma ta fito da Naira dubun ta bata wanda ya sata washare haƙora tana amshewa ta miƙe, babu tuhumar inda ta tsaya har dare yayi, tashi tayi ta tafi ta kwanta, ita kam A'ishatu sai da Mama Ladiyo tai bacci sannan tabi dare tana kankare ƙanzon tukunya taci tasha ruwa ta kwanta




tunda sadda A'ishatu suka haɗu da Muhammad yake jin bala'in tausayinta hakan yasa da yaga ta fito tallan goro zai mata juye ya bata kuɗin ta koma gida wanda yaiwa Mama Ladiyo mugun daɗi don a tunaninta iskanci Shatu keyi tana siyar da goron, yau da gobe shaƙuwa ce mai karfin gaske ta shiga tsakanin Muhammad da Shatu wanda harya kaisu ga faɗawa soyayya mai ƙarfi wanda hankalin Shatu ya fara kwanciya, nan take ya ɓullo mata da son aurenta zaiyi ta biyu da ita don yana da Mata harda yaro guda, ba tare da wata nuna damuwa ba ta amince masa sai dai matsalarta guda a lokacin ita ce Mama Ladiyo, wanda tunda ta tunkareta da maganar aure Mama Ladiyo tai mata jan Warning akan ta rabu da Muhammad ba shine mijin daya dace da ita ba don ta riga tai mata Miji ɗan Aminiyarta Jimmai wani ɗan shaye_shaye ne, kuka sosai Shatu tayi tana roƙon Mama Ladiyo akan ta barta ta auri Muhammad amma fir taƙi saima horon kulleta a ɗaki da tayi ta ɗaureta da sarƙa wai damma kada ta gudu



shi kam Muhammad tun sadda Shatu ta faɗa masa abinda Mama Ladiyo tace hankalinsa yai mugun tashi, babu yadda baiyi ba har da kanshi yaje gun Mama Ladiyo don ta barshi ya auri Shatu amma fir taƙi saima ƙarin cin mutunci da tayi masa





*wanene Muhammad*


Muhammad ɗa ne ga Alhaji Alhassan mai gwalagwalai Mahaifinsa mashahurin mai arziƙi ne inda ya auri Mahaifiyar Muhammad Hajiya Zinatu wacce babu ruwanta suna zamansu lafiya da mijinta harta haifi Khadijah ita ce ƴarta ta farko sannan ta haifi Sagir sannan Abdulkarim sannan autanta Muhammad wanda shima yai karatunsa har yai digiri ɗinsa, sannan ya auri Mansura wacce ita ce ta liƙe masa harya aureta suna da ɗansu ɗaya, haɗuwarsa da Shatu ita ce ta fara sauya masa rayuwa ta maida shi mai son jama'a da son taimakon Al'umma ta maida shi mai wasa da dariya ga dukkan wanda ya gani cikin ƙunci, ya faɗa cikin tarkon sonta da ƙaunarta haka zalika da son kasancewa
End Ads