x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 1 - BAYAN WUYA free pages complete

  • 1 words
  • 3000 words
  • Out of 37650 words

Category: Tale Stories

Views 145

27 Aug 2025
Start ads
After Image Ads

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[5/21, 8:02 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*

*Book 1*


By
*Mariam sani Riamcool*



*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*


*Bismillahirrahmanirrahim dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangiji maɗaukakin sarki gagara musali da zai bani damar rubuta wannan littafi,Yadda na farashi lafiya ya Ubangiji ka bani ikon kammala shi lafiya, kuma ya Ubangiji ka bani damar Rubuta Abinda Al'umma zasu amfan




بسم الله الر حمن الر حيم



*Page 1 &2*


Duƙe take a cikin ɗan kurkun kichen ɗinsu tana ta faman, fura wuta hayaƙi duk ya cika kichen ɗin,sai uban hawaye take, da ƙyar ta Samu ɗanyun itacen Suka kama da wuta, fitowa tayi daga kichen ɗin don ida kaye_kayen kayan da ke cikin ɗan ƙaramin gidan nasu,ga wani Hadari da ya harhaɗu garin yai baƙiƙƙirin, Sai uban zafi,


Sauri_sauri ta dunga yi harta kammala kaye_kayen,tana kammalawa taje ta kaɗa miya sannan ta shiga wanka,tana fitowa ƙasa_ƙasa ta dinga jin ana kiran *MUNEEBBA*

Da sauri ta ɗaura Alwalla kasancewar Magriba tayi,ɗaki ta shiga,tana shiga ta iske Mahaifiyarta ta taso tana daddafa bango,Alamar tana son fitowa tayi Alwalla,Da sauri taje ta kamata tana faɗin "Mamma ki daina tashi ke kaɗai kinga, ga ciwon ƙafa sannan ba gani kike ba,kuma kije wajen tashi ki zame ki ƙara jawo wani ciwon,na ce maki idan zaki tashi ki dinga
kirana," ta faɗa a shagwaɓe tana turo ɗan ƙaramin bakinta,

Murmushi mai Sauti Mamma ta saki,tana faɗin "MUNEEBBA baki gajiya da Rigima,yanzun dai taimaka man nayo Alwalla nan,naji hadari ya taso,"



Kamata MUNEEBBA tayi ta taimaka mata tayo Alwalla,Suna fitowa suka shiga ɗaki suka kabbara Sallah,Sun daɗe Suna kaiwa Allah kukansu,


Bayan Sun kammala Sallar ne MUNEEBBA ta tashi ta shiga kichen ɗin ta ebo masu Abincin da zasu ci, da Kuma na Khabir, zuwa tayi ta ajiye a gaban Mahaifiyarta Sannan ta dinga ebo Abincin tana bata,Saida ta ƙoshi, Sannan ta fara eba tana ci itama,saida ta ƙoshi, Sannan ta tashi ta wanke hannunta tana kauda kwanonin da suka ci Abinci,tana gamawa sai ga Nepa an maido,ta haska ko ina,ƙura ma,kyakkyawar Matashiyar da ke tsaye Ido nayi,don ganin Madarar kyau a gurinta,
Doguwar Mace ce wacce ta haɗa tsayi da ƙwari,ƴar duma_duma da ita, ga dara_daran idanu,da zara_zaran gira, hancinta mai tsayi dai_dai misali sai ɗan Cute ɗin bakinta pink lips,fara ce,amma ba irin can ba,ga gashi da ya kwanta yai Luf_Luf a gaban goshinta,da Saje,
Kyawu kuwa Allah ya bata saidai muce Alhamdulillahi da Masha Allah,


Kallona na maida ga wata dattijuwar Mata,dake Zaune, ta tanƙwashe ƙafafunta,itama kyakkyawar mace ce, Fara ƙal da ita don da ka ganta kaga cikakkiyar buzuwa,ga idanunta dara_dara don idan ka kalli idanunta baza ka, taɓa cewa bata bata gani da su ba, Saboda buɗe suke tarau dasu, itama,da ka kallesu Mamma da Muneebba suna kama Sosai saidai Haske da Mamma ta ɗarata,ga diri ba'a cewa komai kanshi,






Tana Tsaye ne taji an tafka mata Dundu a baya, juyowa tayi a hanzarce tana faɗin "Kai fa Yaya Khabir wallahi ƙetarka tayi yawa kana shigowa kawai sai ka wani sakar man Dundu a baya," ta faɗa kamar ta fashe masa da kuka,


Fashewa da dariya yayi yana faɗin "Nifa kawai gaisuwa ce na miƙo amma har zaki gwada mana halin auta,"



Kallonshi tayi tana turo baki tana faɗin "nidai yanzun ina Alƙawarina? wanda ka ce zaka tafo man da shi,"


Kallonta yayi yana faɗin "Au ke nayi mawa ma kenan? Ni Mamma nayiwa bake ba," ya faɗa yana tunkaro inda Mamma ke zaune,yana Zuwa ya zauna kusa da ita yana Mammatsa mata ƙafafu,Murmushi tayi tana dafa kanshi tana faɗin "Allah yai maku Albarka Khabir haƙiƙa kunyi man Abinda dukkan ƴaƴa ya kamata ace sunyi wa Mahaifansu yadda kuka yi man Ubangiji ya baku mai yi maku kuma,"


Da Ameen Suka Amsa Khabir na faɗin "Mamma koda yaushe cikin sa mana Albarka kike, tabbas munyi dace da Mahaifiya ta gari wacce ta zauna ta bamu tarbiyya ta ilmantar damu, Sannan dukda Zagin da ake mana a gari na cewar mu dukkammu bamu da Uba,hakan baisa kin bi takan zantukan Mutane ba kikan haƙuri ki danne wa Zuciyarki,kota wannan ɓangaren kin koyar damu iya Zama da Mutane Sannan Uwa Uba haƙuri da juriya,



Ƙara Shafa kanshi da na Muneebba tayi tana faɗin "Saka Albarka wa Yaranka a koda yaushe shine zai sa Allah ya kareshi daga dukkan wata taɓarɓarewar Rayuwa, Tabbas wasu iyayen suke Rusa Rayuwar ƴaƴansu da kansu ta hanyar zagi da la'anta, zaka ga Abinda baikai ya kawo ba, Uwa zata jefi yaronta da Mugun kalami, kuma wannan babban kuskurene mu iyaye muke aikatawa,zaka ga yaro Tun yana ƙarami, Idan yai wani abun zata kirashi Sakarai, ko ɗan banza da sauransu dai,haka zalika tarbiyya ita ce jigon Rayuwa, tabbas duk macen da bata ma yaranta tarbiyya ba bata ceto Rayuwarshi daga hanyar lalacewar zamani ba,kuma ki sani duk wani Abu da kika ɗora yaronki da shi to tabbas da kalar halayyar zai tashi, idan hallayar kirki gareki to da ita zai tashi ko kuma akasin hakan,haka haƙuri shine jigon rayuwar zaman duniya,indai kana da,haƙuri tabbas zaka ci ribar rayuwar zaman duniya, duk mai haƙuri zai dace,sannan juriya da jajircewa kan abinda yake dai_dai,shine zai sa kakai dukkan wani mataki na Nasara wanda yake dai_dai,sannan ina sake gargaɗarku da karku sake ku biye Zancen ta Mutane,Don idan ka biye ta mutane wannan shi Ake kira ba shiga ba fita wai an saka mahaukaci a gadin ƙofa,"
Mamma ta ƙarashe zancen da sakin Murmushi,


Dukkansu Ajiyar Zuciya Suka sauke Suna mai tsananin jin ƙaunar Mahaifiyarsu, gefe guda ga kuma tausayin halin da Suka tsinci kansu a ciki, dogon numfashi Khabir ya sauke yana faɗin "shiyasa a kullum muke ƙara gode wa Allah muke kuma ƙara gode maki, bi ga hanyar Turbar da kike ɗoramu,"


Murmushi Mamma tayi tana faɗin "ga kiran Sallar Ishsha'i can Maza tashi ka tafi Masallaci, Sannan ka dawo kaci Abinci,"



Da To ya Amsa yana miƙewa,Sannan yace "Auta tashi ga Alƙawarinki na kawo maki, Sannan kije ki dafa man Ruwa ina son dana dawo nayi wanka," ya faɗa yana miƙo mata ledar hannunshi,



Amsa tayi tana zabga mashi godiya har sai da ya ɗallar mata baki sannan tayi shiru,

Yana fita ta ajiye ledar ta Taimaka ma Mamma ta tashi suka kabbara Sallah, saida Sukayi Shafa'i da Wutiri Sannan Muneebba ta tashi ta haɗa ma Khabir Ruwan wanka,tana gamawa yana shigowa,kai Tsaye bayi ya shige, ita kuma ta dawo ɗakin ta Zauna tana jawo ledar da Khabir ya bata, Tana buɗewa ta haɗiye wani miyau don ganin balango mai zafi ga sai ƙamshi yake,ɗaukar Naman tayi takai bakin Mamma, kaucewa Mamma tayi tana faɗin "Auta ki ci Ni na ƙoshi,"

Ɓata rai Muneebba tayi kamar Mamma na ganinta,ta ce "Mamma idan dai baki ci ba Allah nima bazan.ci ba,"

Jin hakan yasa Mamma amsa don tasan muddin bata ci ba itama Muneebba baza ci ba, saida suka cinye tare da Mamma Sannan Muneebba ta ƙyale Mamma,Ruwa masu sanyi a randa ta ebo mata tasha sannan itama tasha,







Koda Khabeer ya fito ya zauna ya gama cin Abinci Sannan ya zauna wajen Mamma tanata basu labarirrika masu daɗi,wanda cikin labaranne take ƙara Nusar dasu Abu mai kyau da kuma Marar kyau,
Sai wajen 9:30 sannan Khabir yai masu Sallama
ya shige ɗakinshi don yin Bacci.

Itama Muneebba Zuwa tayi ta ɗaura musu Net Sannan ta zo ta kama hannun Mamma tana taimakamata ta shige ta kwanta,Suna kwanciya ana ɗauke Nepa, Saboda iskan da ake tayi, maƙalƙale Mamma Muneebba tayi tana jin tsoro, a ɗaɗɗare bacci ya ɗauketa, ita kam Mama bacci ya kasa ɗaukarta,Tunaninka ta dunga yi, wanda ya dinga Tuna mata Rayuwar baya,tunawa tayi da yadda kullum yaranta ke cikin hantara da kuma zagi na cin Mutumci,ga kullum a cikin yi masu gorin Uba ake duk ta sanadiyyarta,hawaye ta dinga jin na bin kuncinta










**********************

Saukowa take daga Step ɗin benen, cikin ƙarar takalminta mai tsini a haka harta ƙarasa saukowa daga kan benen Zuwa Falon nata,


Kallon Riɗa_Riɗan matan dake Zaune a Falon take, ko waccensu da manyan Wayoyi Suna sarrafasu cikin gwanancewa,yadda suka maida hankalinsu a kan waya kai kace karatun ƙur'ani ne Suke,



Itama Dattijuwar zuwa tayi ɗaya daga cikin Manyan kujerun Falon tayi ta zauna, Tana ɗaukar Wayarta, ta fara Operating ɗinta cikin gwanancewa,a Haka dukkansu suka ɗauki tsawon 30 minutes babu wacce ta ɗago daga Abinda take yi,daga Su har Mahaifiyarsu hankalinsu ya karkata kan Wayar da ke hannunsu.






Tunda Kyakkyawan Dattijon ya shigo ya Zuba musu idanu dukkansu,yana kallonsu,koda yaushe yaga iyalinshi,cikin wannan ɗabi'a da Mahaifiyarsu ta ɗorasu bisa kanta ya kanji ya shiga damuwa sosai,



Sallama yayi har sau biyu Sannan Mom ta ɗago tana amsa mashi, daga bisani kuma ta maida hankalinta kan Wayarta............✍️






Wannan kenan




*Comment Shine karsashin Dukkan Marubuci,So Comment, Share fisabilillah*



Waɗannan sune ƙwarin gwiwata






*Daga Alƙalamin Riamcool*










*08109554986*
[5/21, 8:05 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*
*
Book 1



*By Riamcool STAR OF THE SQUAD*



*MIKIYA WRITER'S ASS*






*Bismillahirrahmanirrahim*



Page 3&4


_________✍️girgiza kansa kawai yayi ya haura sama Zuciyarshi na mashi zafi bisa ga halayyar Matarsa,ya san da cewa Uba shi ke zaɓar ma ƴaƴanshi Uwa ta gari amma shi sam baiyi da cen Mata ba dukkan yaranta babu wanda ta Koyar da shi tarbiyya,kowa dukkan abinda yaga dama shi ya keyi,shiya sa ga Matannan duk wacce aka aura sai ta dawo.





Tunda Dad ya shiga Mom tana nan tana danna Wayarta bata tashi ko sannu batayi mashi ba ballantana ta tashi tabi bayanshi.





Kwance yake bisa tamfatsetsan gadonshi, ya lumshe idanuwanshi, Kyakkyawan Saurayi ne ajin farko,wanda kallo ɗaya zakayi mashi kasan cewar ya kai duk inda ake son ɗa Namiji ya kai,yana da kyakkyawar ƙira irin ta ƙarfafan Maza, dogo ne, fari tas da shi, yana da kwarjini duba da yadda ya haɗe rai kamar bai san miye dariya ba, ƙarar wayarshi ne ya saka shi buɗe lumsassun idanunsa masu kama da na Mage,a hankali yasa hannu ya ɗauki wayar yana yatsina Fuska,ko duba sunan waye ke kira bai tsaya yi ba, yana ɗagawa yaji anyi shiru,shima shiru ɗin yayi na tsawon wasu mintuna,har zai kashe Wayan yaji Muryan Dad yana faɗin "Son duk inda kake kazo ina nemanka,"

"Ok Dad," shi kaɗai ne abinda ya furta kamar wanda akayiwa dole,ajiye wayan yayi yana ƙara ɓata fuska yana motsa ɗan ƙaramin bakinshi me ɗauke da pink lips,tashi yayi ya shiga Toilet yayi wanka sannan ya fito ɗauki Lotion ɗinsa masu daddaɗan ƙamshi ya shafa,kai tsaye wajen Wardrope ya wuce, kaya ne jere kala_kala, ko wanne da ɓangarensa,ƙananun kaya ya zaɓo wanda zasu amshi jikinsa, a gurguje ya shirya ya fito Securities ɗinsa na take masa baya,da sauri wani security ya buɗe masa Mota ya shiga Driver na jar Motar, cikin shakku Driver ya ce "Sir ina muka nufa?," Da hannu yai mashi alamar inda zasu nufa, kaɗa kanshi Driver yayi ya maida hankalinsa kan aikinsa


Haka har suka isa Tamfatsetsan gidan nasu, danna Horn Driver yayi,da gudu masu gadi suka wangale masu makeken get ɗin,suna shiga Driver yai parking da gudu Security yazo ya buɗe masa Motar, a hankali ya zuro ƙafarshi guda, sannan ya ziro ɗayar ya fito cikin Izza da ƙasaita,da kuma taƙama,tafiya yake irin ta ƙarfafan Maza masu ji da kansu, a haka har ya iso Side ɗin Mom, Yana shiga ya harɗe hannuwanshi a ƙirji yana kallonsu da ɗai_ɗai,gyaran murya yayi wacce ta maido da hankalinsu daga kan Abinda suke yi,har Mom da sauri Mom ta taso tana isowa wajenshi tana faɗin "Son miye haka kayi? Kai daga yi maka Maganar aure shine zaka ɗauki fushi dani har kai ƙaura daga gidannan,kasan kuwa irin tashin hankalin da na shiga?," Ta faɗa tana kafeshi da idanunta,


A hankali ya buɗe Bakinsa yana faɗin "afuwan Mom," yana gama faɗa ya haura Sama,da Sallama ɗauke a bakinsa ya shiga,ɗagowa Dad yayi Fuskarshi ɗauke da yalwataccen Murmushi ya amsa,zama ƙasa yayi yana tanƙwashe kyawawan ƙafafunsa, Sannan ya gaishe da Dad,amsa masa yayi cikin kulawa yana maido da hankalinshi kanshi," bayan wasu ƴan Second Dad yai gyaran murya yana faɗin "Son miye hakan da kayi? Tsawon 2 weeks baka ɗaukar Wayar Mom ɗinka sannan kabar gidan, dama kaga za'a isheka shine ka kashe Wayoyinka gaba ɗaya ba'a samu,saida na dawo jiya Mom ɗinka ke faɗa man daga tayi maka Maganar aure shine kayi fushi da ita, kana tunanin abinda ka aikata kayi dai_dai kuwa? Ka sani ita Mahaifiya sam ba'a musu da maganarta ballantana har kayi fushi da ita,kasan kuwa iya baƙincikin da ka ƙunsa mata? To maza _maza ka nemi yafiyarta idan ba haka ba kana cikin fushin Ubangiji,"


ɗago kanshi yayi a hankali ya ce "ayi man Afuwa Dad insha Allah zan nemi yafiyarta,kuma insha Allah hakan bazai sake faruwa ba,"


"Yawwa ko kaifa Son Allah yai maka Albarka," Dad ya faɗa yana sakin Murmushi


Tashi yayi ya fito ya samu Mom zaune ta zuba uban tagumi,a hankali ya tako yazo ya sauke mata hannun daga tagumin da tayi, kallonta yayi yana sakar mata Murmushi sannan ya samu waje kusa da ita ya zauna, sadda kanshi ƙasa yayi yana faɗin "Mom ina mai neman gafararki da ki yafe man akan abinda na aikata maki,"


Murmushi ta saki tana faɗin " na yafe maka *ASAD* dama ni ban riƙeka da komai ba,Matsalata guda shine rashin amincewarka ga wannan auren," ta faɗa fuskarta ɗauke damuwa Sosai

"Indai aure ne damuwarki Mom na amince zan auri Maheer," ya faɗa yana mai tashi daga Falon ya haura zuwa ɗakinsa



Kowa na Falon da Mamaki ya bishi,ganin yadda ya amince cikin sauƙi haka don ko ita Mom batayi tunanin zai amince ba,ɗaya daga cikin Matan dake zaune su Ukku, wato Suhaima ta ce "anya Mom bada wata a ƙasa ba? ace Yaya Asad shine ya amince da wuri haka," ta faɗa fuskarta na nuna Alamar tantama.












*MUNEEBBA*
Tunda sanyi safiya da ta tashi ta kammala ayyukanta da wuri komai ta riga da ta kammalashi, a gurguje ta shirya ta nufi islamiyya,tafiya takeyi sam hankalinta baya tare da ita ta lula wata duniyar ta tunanin Rayuwa,batai aune ba taji ta ci karo da Mutum,ƙamshin Turarensa ya tabbatar mata da ko wanene, a hanzarce ta ɗago dara_daran idanunta tana kallonshi......✍️.





Wannan kenan


*Comment







*Comment Shine karsashin Dukkan Marubuci, So Comment, Share fisabilillah*




Waɗannan sune ƙwarin guiwata







*Daga Alƙalamin Mariam sani✍️*










*08109554986*
[5/21, 8:07 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*





*BY RIAMCOOL*

*MIKIYA WRITER'S Ass*







*بسم الله الر حمن الر حيم*






*Page* 5&6




___________✍️A hanzarce ta ɗago dara_daran idanunta ta saukesu akan Nazeer wanda ya kafeta da idanu yana sakar mata lallausan Murmushi,itama murmushin ta sakar masa tana gaida shi, sannan ta turo ɗan ƙaramin bakinta tana faɗin "jiya fa da naita kiran wayarka ban samu ba,gashi kamin alƙawarin zaka zo," ta faɗa tana sake turo ɗan mitsilin bakinta wanda turosa ya zame mata al'ada,






Murmushi yayi yana faɗin "kinga yanzun jeki islamiyya idan kin dawo mayi magana."




Sallama sukayi cikin shauƙi da ƙaunar junansu,tunda taje islamiyya taketa walwala,don yau batama wani nuna damuwar kyaran da ƴan ajin nasu ke mata ba, Hafsat dake zaune kusada ita ce ta kalleta tana faɗin "waini yau Muneebba wane albishir aka miki ne? kike ta faman farinciki haka."




juya fararen idanunta tayi tana faɗin "wannan ai yama fi albishir ɗin Hafsat saboda na haɗu
End Ads