naki kudin da zaki yi duk abin da kike so inhar be fi karfina ba ..,
tashi tsaye tayi ta ninke dadumar ta , tace '' ah barshi wallahi kayi wani abin da bakai ba , bani da bukatar komai ba abin da na tsara, ba abin da zanyi..,
saboda me ranar fa farin ciki ce..?
limshe idanuwan'ta tayi ta saki sani murmushi wanda ake kira da yafi kuka ciwo tace '' Mamman kenan ni nace kayi abin da ya dace..,
tashi tsaye yayi yana karkadai rigarsa yace '' karfa ya zamo abin Magana yumna ace ba kiyi komai ba..,
au kenan dan riya zaka bani kudin, da ba dan haka ba ko karfanfana dattin aljihu ba zan gani ba
ta faɗa tana tsare shi da manyan idanuwanta.
ajiyar zuciya ya sauke yace '' wallahi Allah ko ɗaya kawai dai kinsan halin mutane musamman ma kawayen ki da suke yan duniya kar su dinga ganin kamar bakiyi sa'ar miji ba , bana so a dinga yi miki kallon kaskanci yumna idan ina da hali duniyar nan gaba ki ɗaya ace mallakina ce zan iya mallaka miki..,
kallon sa take baki sake tace '' gwara da ka fito fili ka faɗa min abin da ke cikin ranka ka dena boyewa a zuciyar ka, kaga kawaye na ne ni da su kallon da kake mana kenan to ba komai bakomai Mamman akwai can za ayi hisabi wato shi ya saka yan gidan ku suke min wani irin kallo dana kasa fassara shi...,
Haba yumna wai me ya saka duk hanyar da na kauce kar na biye miki sai ki ƙara fasa wata ni da baki na , na faɗa miki haka yumna ki dena abin da kike yi kar hakkina ya kama ki..
banza tayi mai ta shiga cikin gida tana kun kuni.
Baba lami tace '' yumna lafiya kika shigo kamar an jewoki...?,
saita kan'ta tayi domin kar su gane me yake faruwa tace '' tofa na shiga uku gani kika yi an cillo ni..?,
kallon kallo suka shiga tsakanin inna Hadiza da baba lami ganin haka yumna ta shiga daki tana dariya tunawa da tayi ta bar wayar ta a tsakar gida da sauri ta fito ɗaukan ta tayi ta shiga dakin su zama tayi ta zuba ta gumi shamsiyya ce ta shigo zama tayi tace '' yauwa yumna me kika shirya lokaci fa yana kurewa ga katin can ma da Mamman ya bani jiya baki taɓa , ba ni nawa har na gama rabarwa kamar wacce bakya son auren nan yumna me yake faruwa..?,
afusa ce tace '' uwar ki ce daman tun ɗazu naga bakin ki yana motsi ashe abin da zaki tambaye ni to ban sani ba idan ma wani ya turo ki kije ki faɗa mai duk abin kikai niya yau nake jin bakar jaraba ina cewa ni nakawo Mamman gidan nan ina son sa ....? sai kuma na dawo nace bana son sa saboda bani da hankali ban san me yake damuna ba to wallahi duk wanda ya ƙara tarata da wannan maganar nan sai na gurje mai baki, haba daman tun da na dawo kallon da ake min kenan to yasin zan wasa wuƙa ta wani ya kara tarata da wannan zancen zai ga me zai faru tun da ku baku san zuru ba..,
sum sum shamsiyya ta tashi ta fita baba lami ta fito tace '' wai ke yumna me ya saka kin iya neman magana da tujara yanzu da ace tayi abin nan bata neme ki fa Allah ne yasan kadai me zaki yi mata wallahi ki gyara halayen ki gidan wani zaki duk wani datti ki zubar dashi a kofar gidan nan idan kika tafi dashi wallahi ba lallai su raga miki ba , kamar yadda mu muke raga miki ba...,
baba lami muna ganin mutuncin ki tun kafin ranki ya ɓaci ki ɓace mana daga gani ko yanzu mu tarwatsa miki ƙwaƙwalwa..
da gudu baba lami ta fita har tana tun tuɓe yumna tana ganin ta fira, ta kwanta tana dariya har da riƙe ciki ta sani sarai idan ba haka tayi mata ba , ba zata rabu da ita ba zatai ta Magana ne ita bata san zuru ba , har sai malam ya shigo ya iske ta , daman ta lura haka take so ɗaga ƙafafuwan'ta sama tayi tace ''maganin biri ɗan katan uwa wace miki barno gabas ce wallahi kafin na bar gidan nan sai na saita muku zaman ku yan durin uwa haka kurum ku takura min da wani banzan zance aita magana ɗaya aure ne , na yarda zanyi to me kuma kuke bukata bayan wannan..,
Bayan fitar baba lami dakin inna Hadiza ta tafi ta zauna tana zare ido sai leke take yawa wacce tayiwa sarki karya ganin haka inna Hadiza tace '' lami lafiya naga kina ta gumi..?,
hmmm yaya yau ni naga tashin hankali daman ni nasan yarinyar nan wallahi ba ita kaɗai bace shi yasaka take iya shegen da ta ga dama malam be sani ba tsoro na ɗaya na fadawa malam abu ga ɓaci..
Kama haɓa inna Hadiza tayi tace '' me tace miki an shiga uku..?,
hmmm ce min tayi zata fasa min ƙwaƙwalwa idan ban fita daga sabgar su ba ta faɗa ƙasa ƙasa domin tana gudu ta jiyo su lamari ya ɓaci..
wani yawu ya haɗiye me ɗaci tace '' mun shiga uku ni wallahi dama yau zata bar gidan nan , taje zan ta ƙarata sai barazana take mana da rayuwar mu daga wancan sai wannan kalli fa abin da tayi mana ƙwanaki Allah ne yayi da sauran kwanan mu a gaba..,
Dari biyar ne ba yawa ki biyani hakkin rubutuna karki bari a sato ki karanta...
8141785374
amina Alhasan Muhammad opay
Yan niger
My nita
1000fcfah
Ku turo sheda ta wannan number
08141785374
Dan Allah idan baki shirya ba kar kiyi min magana.
Copy is not allowed
Domin jin audio din Yan zaman Makkah Ku danna wannan link din sannan kuyi subscribe Dan Allah.
https://youtu.be/cDE5bjYY2HY
___________________
https://www.arewabooks.com/chapter?id=6817816be532b4a92550458c
Episode 12
Baba lami tace '' wallahi kuwa gwara tatattara ta bar gidan nan ko masa mu sukuni haba wannan masifa haka dame tayi kama..,
har karfe tara suna tattaunawa akan wannan matsala ta yumna washegari shamsiyya ta fita tana rabon katim yumna tun da ta fita yumna take Allah Allah ya dawo ta, taci uban'ta tun da ta faɗa mata bata ji ba to za tayi maganin ta.
tamkar wacce tayiwa sarki karya haka ta ɗinga za gaye tana kaiwa tana komowa su inna Hadiza ido ne kawai nasu.
domin lamarin yumna sai addu'a har wajen azahar tana wannan kaiwa tana komowa domin yau dole ta hukunta shamsiyya dan uwar baban ta.
Assalamu alaikum da sauri ta fito jin sallamar shamsiyya sai dai wani abu da be mata dadi ba tare suke da malam dole tayi saranda ja da baya tayi malam yace '' yumna ashe baki da lafiya yanzu yar uwarki ke faɗa min me , me ya saka tun da wuri baki faɗamin ba.?,
ƙasa tayi da kan'ta tace '' naji sauki ma bakamar lokacin da na tashi ba..,
zama yayu cikin kulawa yace '' meke damin ki..?,
yumna tace '' zazzaɓi da ciwon kai ne amma alhamdulilah yanzu naji sauki.,
to Allah ya ƙara sauki,
amin ya Allah tace.
tashi yayi yace '' shamsiyya jeki ki dauko min allo nayi mata rubutu..,
shamsiyya da , daman tana tsaye tun da ta shigo ta kalli yumna tasan yan bala'in sun motsa.
shiga dakin sa tayi ta dauko mai allo yumna ta shinfiɗa mai tabarma zama tayi a kusa da shi rubutu ya zauna yana yi jefi jefi yana tambayar ta ko tana da , damuwa.
yana tausayin rayuwar ta sosai saboda bata da uwa shiɗin ba mazauni bane balle ya san me yake faruwa duk da yasan halin yar tasa ba kanwar lasa bace.
yumna bata nuna mai akwai wata matsala ba da ya gama ya wanke ya bata , tasha amsa tayi tasha suka ɗan yaɓa hira ana kiran sallar magariba ya fita ita kuma, ta tashi tayi sallah,
bayan ta idar ta kwanta a tsakar gida tana jij Radio da wayar ta zama kusa da ita shamsiyya tayi sarai ta ganta sai tai kamar bata ganta ba ta ci gaba da jin radio ta idon ta a rufe yaran gidan suka ta wasan jakai kwarai yumna tayi lafiya da , dane tun da ta fito tsakar gidan nan , ba wanda zai ƙara wani kwakkwaran motsi idan kuma mutum yayi taurin kai tofa jikin'sa zai faɗa mai.
tana cikin jin radio shazali dan gidan baba lami ya faɗi mata aikuwa yaci ubansa domin duka tayi mai tas tare da han kaɗa shi, taja tsaki ta koma saki ta kwanta.
baba lami tana jin ta amma batayi ƙoƙarin magana ba domin ba mutunci za tayi mata ba.
washegari shamsiyya ta dinka musu kayan su da yake ta iya ɗinki yumna ce dai bata iya ba saboda ita bata ga me za tayi da sana'ar basir ba.
bayan ta gama ta kai mata wajen kayanta ta ajiye.
haka rayuwa taci gaba da wakana yau ana sauran kwana ɗaya daurin auren su kowa ya zo na arlit amma ban da ahlam da juraij hakan be wani bawa yumna mamaki ba tun da tasan shi dai ba mutunci ya cika ba ,
shi da matar sa biyu ce ta haɗu shi ba mutunci haka ma ita, juhud ma bata zo ba sai yusrah sai mommy da kakarta tawajen uwa sosai suka nuna mata gata domin ko dinki ɗaya bata saka ba akayan da Mamman ya kawo mata.
zazzabi ne ya rufe ta fa'iza da nana suna tare da ita fa'iza ce tace '' wallahi yumna banga bin damuwa ba duk kinbi kin takura kanki ke wallahi ki godewa Allah ma zakije kici yancin kanki..,
murmushin tayi, ta gyara kwanciyar ta zuciyar ta ba dad'i in banda tsabar rashin hankali wanne cin yan cin kai ce mata aka yi anan gidan, ba tacin yan cin kan'ta.
ita wannan ciwon bawai na damuwa bane tana ganin bakwan watan ta dab yake da zuwa cikin ta ma ciwo yake , tashu tayi ta dafe kan'ta tace '' dan Allah cewa mommy bani da lafiya kaina ciwo yake da ciki na..,
tashi fa'iza tayi ta fita ba jimawa gabaki ɗayan su , suka zo har da yusrah.
mommy tace "subbanallahi tun yaushe ne baki ɗa lafiya amma kikai shiru da bakin ki...?,"
amai ne ya taso mata da sauri ta fito tsakar gida ta dinga kwara shi kowa sannu ya dinga yi mata bayan ta gama mommy ta wanke mata jiki kamata tayi suka shiga daki ta kwantar da kan'ta a cinyar kakarta tana sauke a jiyar zuciya daman haka period ke mata , bata mata , ta dad'i baka ramar wahala take sha ba.
magani mommy ta bata , tasha bacci ya dauke ta kamu ba , ba ai yi da ita ba saboda ba lafiya sosai take jin jiki,
washegari
RANA bata karya sai dai uwar ɗiya taji kunya.
sosai mutane suka taru daga gari daban daban domin malam na mutane ne ga kuma mahaifin Mamman alhaji Dauda me wuƙa sarkin fawa, masallaci ma kasa daukan mutanan yayi wasu suna waje daurin auren shamsiyya aka fara sannan na yumna lokacin da me shela ya sheɗa an daura auren ta ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba , tuni ta fara kwara a mai jikin ta ya zugage tas mommy ce ta gyara ta tare da bata magani bayan an gama MAMMAN da saurayin shamsiyya suka shigo domin gaisuwar surukai sai a lokacin ma ya ga bata da lafiya sosai ya tausaya mata .
bayan ya fita ya koma gida mahaifiyar sa sai cika take tana batsaiwa.
ko gaisuwar'sa bata amsa ba.
wannan kenan
da misalin karfe biyun suka tafi sukai mata jere dole sai da aka dawo da kaya da yawa saboda daki daya ne da ban daki sai kitchen shima ba wani babba ba yusrah tace '' kinga ko abin da nake faɗa miki yanzu ya za kiyi da wannan kaya..?,
Mommy tace "'siyarwa zanyi na bata kudin sa mata wani amfanin taja jari..,"
shiru yusrah tayi bata ce komai ba Hajiya anni kakar mahaifiyar ta , tace '' aikuwa kin kyauta Allah yayi albarka...,
amin tace da misalin karfe Biyar Na Yamma mommy ta shirya yumna cikin wani lece pink colour ba ƙaramin kyau yayi mata ba duk da saboda da cutar da tayi ta zabge ta rame lokaci ɗaya.
nasiha tayi mata kuka kawai take yi share hawaye bayan ta gama yi mata faɗa ta haɗa su, su da shamsiyya ta kara yi musu sannan malam da su inna bayan sun gama daman masu daukan amarya suna jiran su yumna da ta fito sai da ta juyo ta kara kallon gidan su hawaye ne suka ƙara zubo mata , da kafar dama mommy tace ta shiga cikin motar.
shiga tayi ta kifa kanta ta ci gaba da kuka.
har suka isa nan ma da kafar dama mommy tace ta shiga batai musu ba ta shiga da ita kai tsaye gurin mahaifyat sa , suka nufa sallama su kayi kanwar sa hindatu ce ta amsa amma innar su Mamman ko nunawa ba tayi ba tasan da tsayuwar su.
shigowa su kayi wasu suka tsaya a waje mommy tace '' barka da yamma ya taro..?,
dakyar tace '' barka dai alhamdulilah..,
sosai mommy take mamaki to ya akai bata san da wannan matsalar ba , da baza ta bari ayi auren nan ba , kar ta takurawa yumna danne abin tayi tace '' masha Allah to ga amana nan mun kawo miki duk..
ai bata karasa ba tace '' da kata ban amshi wannan amanar ba dan haka ku tattara ƙafafuwan'ku ku fitar min daga daki kafin ba gurza muku tashin mutunci.
tashi su mayi yumna tamkar zata fadi saboda tashin hankali daman fa'iza ta dade tana faɗa mata innar su hindatu bata da kirki sai yau ita tashe da , da maganar fa'iza a gaban jama'a ta tozarta ta lallai jiya ba yau ba , ban da tayi sanyi yasin sai dai ta saka danta ya sake ta daman haka take bukata.
dakin ta suka kaita sosai mommy take cikin ɓacin rai faɗa ta kara yi mata tai mata sallama su fa'iza ma ba jimawa suka tafi.
zazzabi ne ya kara rufe ta da gudu ta fito tana kwara amai tamkar zata amayar da ya'yan hanjin ta innar su hindatu fitowa tayi ta kama kugu tace '' wallahi ba zata sabo ba daman da ciki kika shigo min cikin gidan ɗana..,
ba karamin daga mata hankali wannan maganar tayi ba da sauri ta ɗago lokacin Mamman ya shugo yana baza babbar riga jin abin da mahaifiyar sa tace da sauri ya ƙara so cikin ɗaga murya da faɗa tace '' gata nan ta shigo maka da ciki cikin gidan ka dan haka wallahi sai ka saketa ba zan yarda ba ta zauna min da cikin shege a cikin gidan nan ji yadda ta ɗashe tayi fari anzo za'a cuci ɗana ayi laulayi a gidan sa dan kirufawa kanki asiri kawayen ki ba ƙananan karuwai bane dan haka kaji na rantsai maka idan baka saketa ba sai na tsine maka kuma saki uku nake so kayi mata domin wa'yannan mayu ne tsaf ubanta zai ƙara rubuce ka akan sai ka sake ta ga yarinyar nan yar mutunci na kawo maka amma kaki ka aura ka ɓuge da aurar ragowar titi..,
ji yayi kan'sa ya sara mai shi ba mace bane balle ya iya tantance abin da innar sa take faɗi amma tabbas duk abin da ta faɗi gaskiya ne shima kan'sa kyan da yumna tayi ba ƙaramin mamaki yake bashi ba sai kawai ya barshi a gyaran jikin da aka yiwa amare ne shi ya mai data haka baya zargin yumna ya yarda da tarbiyar ta amma ya ya iya mahaifiya ba wasa ba.
hawaye ne yake zubowa a idanuwan'ta tace '' be kamata ba dan bakya sona kiyi min wannan ƙazafin ba , ko da ace Mamman zai sake ni karka sakeni da wannan baƙin tabon da har abada ba zai taɓa gogewa ba a idanuwana da zuciyar'ta kina da ya'ya mata kin haifa be kamata ki jefeni da wannan kalmar ba.
wata uwar buda ta saki tace '' au Allah maza saketa ina gani kuma ta taso na kaita har gidan su na shedawa kowa abin da , ta aikata..,
Mamman dakyar ya iya haɗiyar yawu ganin yayi shiru innar sa ta saka kuka tare da kakorin tsine mai da sauri yumna ta girgiza kan'ta tace '' Mamman bakomai karka bari saboda dani ka ɓata lahirar ka , komai me wucewa ne wallahi..,
a hankali ya furta na sake ki saki biyu..
share hawayen ta tayi ta tashi ta shiga daki mayafin'ta ta dauko ranar daurin auren ta an sake ta saki da ashe daman haka yake da ciwo ashe daman jin sa kawai take abaki amma wata zuciyar'ta ta murna take wata na bakin ciki saboda da bakin tabon da aka sake ta dashi.
a daidai nan mahaifinsa ya zo hindatu ta kira shi saboda abin da yake faruwa.
yana zuwa inna ta kora mai bayani tabbas ga amai nan amma yace '' ke kin tabbatar da wannan zargi tabawa kiji tsoran Allah Ubangijin fa baya yafe hakkin wani akan wani idan kinyi haka ne domin ki tozarta su wallahi Ubangiji zai jarabbe ki ta inda ba kiyi zato ba..,
a dai-dai nan yumna ta fito tana saka mayafi mahaifinsa yace '' ya'ta koma ki kwanta gobe sai mu yi magana...,
na rantse da Allah sai ta tafi ta zauna tayi me a cikin gidan nan..?,
tashi yumna tayi ko gaban ta bata iya gani ta fita Mamman kuwa ya zama tamkar wani mutum mutumi,
dakyar take iya tafiya ikon Allah ne ya kawo ta gida amma ba dan haka ba , da tuni wani zancen ake yi malam yana zaune asoro shida mommy suma magana ta shigo da yake akwai hasken fitila da sauri mommy ya zaro idon'ta tare da dafe kirjin ta da yake dukan uku uku malam kuwa daskarewa yayi dakyar ya iya cewa yumna me ya dawo dake..?,
ɗurƙusawa tayi tana kuka tare da shashsheka ta kasa magana ganin haka mommy tace '' malam mu shiga daga cikin dakin