x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 5 - YAN ZAMAN MAKKAH BOOK 1

  • 12001 words
  • 15000 words
  • Out of 37750 words

Category: Romance Story +18

Views 119

02 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
shiga kitchen juraij ne ya shigo yace '' yusra me kuka girka ne ki zubo min...?,
share kwalla tayi ta nuna yumna da yatsa tace '' ga mommy nan zata je ta ƙaro mata abinci yawa jaka dan baka ga abincin da dazu na zuba mata ba kaga yadda ta zubar yawa me bulallan baki..,
Zama yayi akan ɗaya da kujerun parlour kallon mamaki yake mata yace '' wannan plate din ta cinye dukka kuma take neman ƙari to wallahi ba zata ci ba yau sai taci uban'ta a cikin gidan nan...,
tashi yumna tayi ta murguɗa baki tare da daukan jakar kayan ta tace '' dan kunga bani da gata shine kuke zagin mahaifina, to wallahi bazan zuba ido ba nan da kuka ganni na iya rashin mutunci buhu buhu yasin zan maganin ku..,
sakar baki yusrah da juraij sukai kwafa juraij yayi ya maida hankalin sa kan wayar sa yana dannawa ganin fitowar mommy.
mommy kallon yumna tayi tace '' yumna lafiya na ganki da jaka..,
kuka ta fashe dashi ta saka mayafinta tana kare fuskar'ta tace '' mommy gwara na koma garin mu tunkafin abin ya gangaro kan mahaifiyata da take ƙasa yanzu wannan mutumin zagar malam ya gama yi.,
salati mommy ta saki tace ''juraij da hankalin ka..?,
ɗagowa yayi kamar be san me yake faruwa ba yace '' mommy me ya faru yanzu na shigo aka ce kina parlour ban dade da zama ba..,
kuka yumna ta ƙara fashewa dashi tace '' kallo yadda yayi maganar kamar be san abin da sukai ba wallahi mommy ya zagi malam..,
Kiyi hakuri dauki abincin ki zau dauki babban mataki akan su ɗauka tayi ta nemi guri ta zauna a hankali take cin abincin dan ta tura wa juraij haushi tashi yayi ya fita, be jima ba ya dawo huce wa yayi ta gaban ta da sauri ta ɗauke abincin ta sakamakon kyankyaso da ya saka mata kuka ta fashe dashi ganin irin abin da yayi mata gashi ko rabi bata ci ba.
mommy ce ta fito take tambayar ta lafiya shiru tayi tace '' bakomai na koshi..,
Kallon yusra tayi da har yanzu take zaune tace '' ya kafar taki ta samu sauki..?,
ajiye wayar ta tayi tace '' eh na samu sauki..,
zama tayi tace '' yauwa kikai yumna dakin ki, tayi wanka ta kwanta bacci ta samu hutu..,
da sauri juraij yace '' mommy kawai ta zauna a part dina kinga ahlam ta Dan samu me debe mata kewa idan bana nan..,
ba ƙaramin dadi mommy taji ba domin ko ba komai ya nuna cewa yumna yar uwar sa ce kuma ahlam zata ɗauke ta da mahimmanci batare da ta kawo komai a ranta ba tace '' okay ba damuwa yumna bi yayan ku part din sa ...,
da sauri yumna ta kalli mommy ita dai wallahi ko rantsaiwa za tayi ba za tayi kaffara ba akwai abin da ya shirya amma koma mene ita dai-dai da su take daga shi har matar sa me katon kai tace '' to mommy yaya taso nagaji wallahi..,
sakar baki yusrah tayi to me yaya yake nufi da yin haka daga shi har matar sa basa son hayaniya barin yanzu da take da ciki a jikin ta sai taɓara take mai yana dada shagwaɓa ta yawa yar kwai baya san damuwar ta ko yana gun aiki ta kira shi sai yaje ba kuma ta buƙatar wani ya zo mata dan kishin masifa ne da ita tab lallai za ayi ta ta fadi cikin ranta tare da tashi tabar gurin.
bin bayan sa yumna tayi yana gaba tana binsa a baya har suka isa part dinsa ahlam da take kallo da sauri ta tashi zaune tana yi mai kallon tuhuma ga hannun sa na dukan cinya ba abinci cire earphone tayi tace '' sweet wannan fa me tazo tayi min Avant que ma colère ne s’aggrave, j’ai dit quelque chose que je n’avais pas l’intention de dire, alors elle a quitté l’endroit..,
zama yayi kusa da ita ya kamo hannun ta ƙasa ƙasa yace'' na kawo tane ki rama abin da duk tayi miki ita zata dinga komai yanzu ma ki faɗa mata me zata girka..,
ahlam uwar son jiki tuni ta washe baki ta yi mai kiss a kumatu dauke kai yumna tayi tana jan ƙara min tsaki abin nan yana baya haushi wallahi ashe daman yan iska ne ga abin da suke yi yawa za su cinye junan su ta faɗa ƙasa ƙasa da sauri juraij ya juyo domin tas yaji me tace ,
dan haka tashi yayi yace '' su waye yan iska..?,
yadda yayi maganar cikin i don't care manner ba ƙaramin shakkar sa taji ba sai taga ya koma mata wani iri ja da baya tayi tace '' ni ban ce komai ba baiwar Allah dan Allah kin ji nayi magana..,
tashi ahlam tayi tana gyara zaman rigar'ta tace '' karya take tayi magana, naɗa mata na jaki ba ɗazu mu zaki rainawa hankali da aljanun karya to ina me sanar dake kin zo inda za'a gyara miki zama da hallacan jeki kitchen ki dafa min tuwan shinkafa miyar ɗayar kuɓewa..,
kallon sa tayi tace '' ba cewa tayi ba nayi wanka na kwanta na wuta..,
ta fadi haka tare da gyara zaman ledar kayan ta ..,
ƙara shan toka yayi yace '' kafin na kirga uku ki tafi kiyi abin da ta saka ki ko jikin ki ya faɗa miki..,
fakar idanuwansa tayi ta fita a kuje sai dai gate a rufe yake ba ta yadda za a yi ta fita.
juyowa tayi tana yana haɗe hannun riga daman gashi ingarmar namiji sako sakon da yake mata shine har ta samu damar ya faɗa ta bashi amsa amma yanzu zai saita mata kan'ta.
ɗurkusawa tayi da ledar kayan ta tace '' dan girman Allah kayi hakuri..,
ke kin san shi ne..?
ɗago kan'ta tayi ta kalle sa idanuwanta tab da hawaye tace '' dan Allah ba danni ba karka dake ni kaga ni marainiya ce...,
tsawa ya daka mata yace '' shige ki tafi kiyi abin da ta saka ki...,
to tace ta tashi tana daɗa rungume kayan ta wayar tace tayi ringing da sauri ta buɗa ledar ta ta ciro ta sunan Mamman ta gani dogon tsaki taja tare da mayar da ita cikin ledar ta.
dan ubanki wa kike wa tsaki...?
da sauri ta juyo tace '' gidan layi ne suka kira ni shine nayi musu tsaki. ..,
bake bakin ta yayi yace '' mara kunya su din sa'an wasan ki ne..,
girgiza kai tayi tace '' kai hakuri nadena..,
yaro besan wuta ba sai ya taka tabbas za tayi maganin su ta fadi haka a cikin zuciyar ta , tana shiga ta ajiye kayan ta , tace '' ina ne kitchen din..?,
wani banza kallo tayi mata tace '' gashi nan sauran naga ba dai-dai ba..,
leƙawa tayi tace '' ban iya amfani da wannan abin ba sai kin koya min..,
tsaki taja tana tashi ta shiga kitchen din bin bayan'ta tayi ta tsaya juyowa tayi tace '' kalli bana son dakiƙanta sau ɗaya nake magana na biyu sai dai kiji duka..,
zumburo baki tayi ranta yayi ba dad'i baya kaunar hulakanci ta ɗauke kanta ji tayi kamar ta dauki fry pan ta buga mata akai sai wani juya mazaunan ta take .
ke ina magana kina tunani to wallahi mijina da gidan nan yafi karfin ki.
murmushi yumna tayi tace '' da ace ina son shi da be aure ki ba tunda ko ba komai wata kusan tafi wata da arziki a garin wasu gwara a garin ku acikin dakin ku dan uwa dan uwa ne mijin ki baya gaba na da ace ina son sa ina me tabbatar miki da wallahi ko za kiyi hauka sai na aure shi ki godewa Allah yanzu ba kune agaba na ba , akwai abin da yafi ku mahimmanci...,
Kut lallai yarinyar nan ta fadi haka tana dauke ta da mari sai dai yumna ta kauce ta ja da baya tace '' ke waya faɗa miki yanzu ana yayin yar doke doke wannan sai karurnuka da karya ki godewa Allah da ba a zamanin da wannan abin ya faru ba da nayi tsalle na duro akan ki na bawa hammata iska naci kutumar ubanki hankali kwance..,
kasa magana ahlam tayi sai nuna yumna take yi da yatsa lankwasa yatsan tayi tace '' la la lah ba'a nuna ni da dan yatsa ban tauna shegeba kinyi sa'a ɗaya ke matar yaya ce da yau hmmm sai dai wani labarin hajiya ta...,
Sweet sweet sweet kana ina kana ina zo kafitar min da yarinyar nan tun kafin naci uban'ta...,
da sauri ya shigo daga shi sai towel shaf ya manta da yumna a cikin gidan da sauri ta dauke kan'ta tana cewa a'uzubillahi..
kaga ko daga shugowar ka tana maka ta'awizi ga babban sheɗan ya shigo kaga irin maganar da ta faɗa min kasa komai nayi dan haka kai kazo ka naɗa mata duka ka nuna mata matsayi na a gurin ka..,
Ahlam ta faɗi tana ɗauke kan'ta daka kallon yumna.
ran juraij ne ya ɓaci domin baya son yaga ƙaramin yaro yana raina babba haka kurum ya ƙara jin tsanar ta ta sami guri a cikin zuciyar sa yowa kan'ta yayi ya zabga mata mari ai wasu taurari ta gani ta faɗi a ƙasa bakin ya fashi yace '' ki tashi kuma ki girka mata abin da tace miki idan ka yi mata ba nan ma jikin kine zai gaya miki...,
jikin ta rawa ya fara ta miƙe tace '' banga kayan aikin ba , ban iya kunna wannan abin ba..,
ta faɗa tana nuna gas..
kunna mata ahlam tayi ta kama hannun mijin ta suka bar gurin kuka yumna ta fashe dashi ko a gidan su ta manta yau sharabon da tayi girki da kan'ta ta nemo komai tayi wa ahlam girki bayan ta gama ta zuba a plate takai mata.
tana kwance akan cinyar sa a hannun sa wani story book ne yana karanta mata daga shi sai boxer ita kuma wasu English wears ne rigar iya gwuiwa ba wando kenan wanka tayi haka ta raya a zuciyar ta ajiye wa tayi a inda taga yusra dazu ta ajiye mata abinci..,
zama tayi a gajiye tace '' gashi na gama..,
ɗagowa ahlam tayi tace '' oh tashi to ga can dakin nan ki dauke wa'yannan kayan naki tun da kika ajiye dakina yake wari..,
ɗauka tayi bata ce komai ba ta shiga dakin da ta nuna mata zama tayi akan dan madaidaicin gadon dakin komai akwai har da wardrobe.
fito da wayar tayi ta yiwa Mamman Flashing.
ba jimawa ya bugo yace '' masoyiya ashe kin yi tafiya shine ba sallama..,
juya idanuwan'ta tayi ta maida su dai-dai ta taɓe baki tace '' oh na manta ne yanzu dai turo min kati zanyi waya da kawata..,
shiru tayi ta saurara domin taji me zai ce kwanciya tayi tace '' kadai ce min ba zaka turo ba amma wannan kwana kwanar da kake yi ban gane mata ba gwara ka fito fili ka faɗa min yumna bazan turo ba..,
kwantar da murya yayi yace '' yumna bani dashi ne wallahi amma zan ranta na turo miki..,
kashe wayar tayi tana jan ƙaramin tsaki kwanciya tayi sosai saboda ɗazu kawai ta kishingiɗa ne tane cewa katin fcfah 1000 ya gagare shi haba Allah ina neman tsari da talauci dukka abin da Allah da manzon sa suka ce ka nemi tsari da shi ba karamar masifa bace haba talauci ai dan ta'adda ne lokaci ɗaya yake maka kaca kaca ya sauya maka kamannin ka ni yumna da auren Mamman aha ai kwai wannan auren shi ake kira da auren manufa ko wata bazan ba , zan fito daga nan kuma sai makka ina da yancin yin komai ina da yancin aurar wanda naga dama.
YAN ZAMAN MAKKAH
domin fara paid na wannan littafin zaku biya ₦500
0423988701 amina Alhasan Muhammad wema bank
Ko
8141785374
Amina alhasan Muhammad opay
ku turo da sheda tanan 08141785374
Yan niger kuma
Zaku turo da kudi ta my nita 1000fcfah
da shedar biya ta wannan number 08141785374

copy is not allowed
https://youtu.be/WoCX8WbJOuU
Episode 7
ɗaga wayar ta tayi tana kallon ta ko zata ga sakon kuɗin can sai ga alert ya shigo wani dad'i ya kamata ta , tashi zaune tace '' ihuu huuu bara na kirawo na'ima..,
tana wannan maganar sai ga kiran sa ya shigo tsaki ta ƙara ja ta ɗauka tace '' naga ni Nagode sosai Allah ya ƙara budi..,
jin dadin addu'ar ta yayi yace '' wallahi yumna idan ina da shi ba abin da bazan miki ba kedai Allah ya saka noman mu yayi kyau kar fari ya mamaye mana gona akuya zan siya miki na dira miki kiyo lokacin da bani dashi kinga zaki siyar kiyi abin da kike so..,
da sauri ta miƙe ta dafe kirjin ta lallai sai yau ta kara tabbatarwa wanda yayi nisa baya jin kira ita da kiwo amma dai ba'a ƙin ta mutun ko wani abin tayi da kudin mugun fatan sa kuma ya koma masa kansa ɗan uwar ubansa tace '' uhmm amma dai ni zaka bawa na siya ko sai na zabi kalar da nake so.?,
ai masoyiya tare za mu je ki zaɓa ki darje har da dan bunsuru zan siya kinga mun haɗa aure ɗaya..,
zaro ido tayi sai kuma ta danne zuciyar ta , ta yayyafa mata ruwan sanyi tace '' eh haka yayi sai anjima zan kirawo ta karta ga na hulakanta ta..,
to ki wuta lafiya abar kauna'ta wani takaici ne ya tokare mata zuciya hmmm zatai maganin sa very soon.
zare wayar tayi ta kashe ba tare da tace komai ba number na'ima ta kirawo sai dai har ta gama ringing bata ɗauka ba dogon tsaki taja ta ƙare kira amma nan ma ba'a dauka ba sai dai da ta kirawo ta har sau biyar kamar wata mayya ta kasa haƙura.
sai da taga ba sauki ciwon arne ta hakura ta ajiye wayar zuciyar ta na tsalle babban burin ta , ta kirawo na'ima su gama wannan maganar a saka mata date din tafiya insha'Allahu ba zata basu kunya ba.
ji tayi anyi knocking dib kofar dakin da take da sauri ta tashi ta bude domin taɓa kyautata zaton wa'yannan yan wahalar ne aikuwa ilai ahlam ce kallon ta , tayi tana yatsuna fuska tace '' ki fito ki kwashe kayan da nayi amfani dasu sannan nayi baki zaki kawo musu Boissons (drink's) da friandise (snack) sauran kuma ki musu rashin hankalin da kika saba kar kuma ki nuna kina da alaka da me gidan saboda abin kunya ne a gare shi..,
da sauri ta ɗago jin karshen zancen ta zaro nata kananun idanuwanta tayi masu kama dana yan chaina tace '' karya nayi ke ba abin kunya ce a gare shi ba fitsararriya mara kunya..,
bata nuna mata taji haushin maganar ta tace '' oh amma dai baza a iya canza wa tuwo suna dole ace da mijin iya baba..,
wani mijin sunan sa muna miji saboda baza a iya nuna shi a ko wanne waje ba , ba zai iya zame maka wata babbar ƙaddarar ba.
wani yawu me ɗaci ta hadiya jin zancen ahlam amma ta cita wasa binta tayi da kallo har ta juya sai kuma ta dawo tace "ki canza kayan nan na jikin ki, ki kuma saka hijabi..,"
ɗagowa tayi tace '' bani dashi ko kin siya min ne..?,
dariya tayi cikin salon tura haushi tace '' a'a amma dai a matsayina na wacce take amsa sunan matar gidan nan dole kibi doka ta ki zauna lafiya..,
gani tayi mene amfanin ta tanka mata banga je ta tayi ta fita sakar baki ahlam tayi ganin baki sai kuma ta saita kan'ta kallon bakin tayi ba hausawa bane turawan France ne.
gaishe da su tayi suka amsa cikin sakin fuska.
kwashe kayan da ahlam tayi amfani dashi tayi takai kitchen buɗe fridge tayi ta dauko lemuka da kayan motsa baki ta saka akan tray ta kawo musu sai yanzu ta lura ashe har da bakar fata tana tunanin duk yadda akai ba dan nan bane saboda hausar da yayi amfani da ita gurin cewa mun gode sannu da aiki da ga gani dan Nigeria ne murmushi tayi har beautiful point dinta ya loɓa tace '' bakomai wallahi bisimallah..,
dariya yayi yace '' amma dai nawa kason yafi na kowa ko..?,
da sauri ta kalle sa tace '' eh naka ne duka..,
daukan lemo ɗaya yayi yana kallon ta tace '' really..?,
kai ta ɗaga mai wani takaici ne ya kama juraij da ahlam su kuwa sauran sai dariya suke dan haidar ya iya barkwanci sosai gwanine gurin wannan baya barin waje tsit..
har tayi nisa yace '' baki gama aikin ki ba..,
yumna bata da duhun kai dan haka ya juyo batare da wani kauyenci ba tace '' to ina sauraron ka me kake so..,
DO YOU LOVE ME...?,
da sauri ta kalle sa kaɗan kaɗan tana Ingilishi akwai wani malami da yake dan koya musu dan haka ta fahimci me yake nufi zaro idanuwanta tayi tace '' ka taɓa ganin jin inda musulmi yaƙi dan uwan sa musulmi..?,
Haidar yace '' right amma ni ba irin wannan nake nufi ba..,
Juraij ne yace '' ke tafi daki..,
shiga tayi daki kirjinta yana lugudan uku uku duk abin da take karfin hali ne zama tayi tai tagumi murna za tayi ko kuka garin dad'i yana nesa ta tabbatar daga ganin wannan mutumi be san talauci ba duk da ba lallai ne ba ya kai ya juraij. anya kuwa ma zai bari saboda tasan halin su sarai shi da matar sa me kan tasa tsaf zata iya wargatsa abin.
to amma fa ya za tayi Mamman to hakan yana nufin mafarkin ta da burin ta ba zai cika ba wannan mutumin fa bata iya tai mai abin da zatai wa Mamman ya sake ta ba tun da wayewar ba ɗaya ba wayar tace tayi ringing da sauri ta ɗauka ganin kiran na'ima tace '' na'ima ke kuwa kina ina ..? nake ta kiran wayar ki amma baki dauka ba kira har biyar ki bacci kike ya kamata ace kin ɗauki wayar nan..,
cikin raɗa da rawar murya na'ima tace '' cikin tsakiyar dare zan kira ki yanzu ina aiki ne dan Allah yumna karki kirani zan kira ki..
kit ta kashe wayar bata jira me zata ce sauke wayar tayi akunne tana kallon screen din wayar to me yake faruwa jin muryar ta tayi
End Ads