x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - YAN ZAMAN MAKKAH BOOK 1

  • 9001 words
  • 12000 words
  • Out of 37750 words

Category: Romance Story +18

Views 118

02 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
, dan Allah malam karka ce min a'a ina son zuwa.

Please subscribe.
https://youtube.com/@nasreenminallah?si=fWc7Wzd4nPx_TifU
EPISODE 5
Shiru malam yayi yana tunanin maganar ta ajiyar zuciya ya sauke yace '' yumna kunfa kusan komawa makaranta..,
marairaice murya tayi tace '' dan Allah malam.,
to Allah ya tsare hanya ya faɗa yana dauke kai da ga kallon ta yafi kowa sanin wace yumna shi ya saka baya barin ta taje ko ina , shi da ta zamewa dole ya riƙe abar'sa ɗayan kan yumna yawa ne dashi riƙon mahaukaci sai sarki.
ganin yayi shiru ta tashi tana washe baki ta fara tafiya a kofar zaure taci karo da mommy cikin jin dadi tace '' mommy ya barni..,
momy tace '' kai Masha Allahu haka ake so jeki ki debo kayan ki.,
da gudu ta kara sa shiga cikin gidan ba wanda tayiwa magana baba lami da take raba abinci tace '' yumna zo ki dauki naki..,
uhmm na koshi
ta faɗa tana shiga daki tare da bude kwabar kayan ta tana sauko da su ƙasa.
da sauri ta ɗago ta kalle ta tace '' kin koshi fa kika ce me kika ci..?,
ɗagowa tayi tace '' ɗazu aka kawo min farfesun kaji..,
zaro ido baba lami tayi ta kalli yaya Hadiza ta jin jina kai lallai lamarin aljanun yumna abin kullum gaba yake yi.
ganin sun lula kogin tunani tace '' ko na saka a kawo muku, kuna so ne..?,
da sauri inna hadiza tace '' a'a yumna mun gode..,
bata ce ƙala ba ta ci gaba da shirinta zuciyar'ta fes bayan ta gama hada itana ina ta , ta fito tsakar gida tace '' to saduwar alkairi ni na tafi arlit..,
cikin jin dadin tafiyar ta ya'yan su zasu sake su wahala baba lami tace '' Allah ya kiyaye hanya,
amin yumna tace tana ci gaba da tafiya tana fita waje tararwa tayi har sun shiga mota ita suke jira da sauri ta kwankwasa musu bude kofar mommy tayi ta shigo tare da jakar kayan ta
ɗora su tayi a kan cinya mommy ta rufe kofar suka fara tafiya kwantar da kanta tayi a kan kayan ta , tai shiru tana sake sake kala kala a zuciyar ta ,
sun fara daukan hanyar arlit mommy tace '' dan Allah yumna ki nutsu aure da kike gani ibada ne kinga wannan aikin da kike so ki tafi babban hatsari ne idan har baka hadu da na gari ba.,
shiri tayi tana sauraron zancen tamkar tana busa mata sarewa babban burin ta , sudai isa za nemo agent din na'ima tunda ai a arlit yake itama yayi mata visa bayan ta fito daga gidan Mamman ta , tafi makka dole ayi gwagwarmayar rayuwa da ita dan cimma burin ta ba abin da ake samu ta cikin sauki dan haka ta daura damarar yin komai tun da dai ba wata hanya mara kyau zata bi ba amma sun bi sun ɗaga hankalin su yawan wanda zata tafi yawan karuwanci tafiya ce ba fashi kamar tayi ta ta gama ne.
anya kuwa ma sun san me duniya take ciki kai gaskiya basu sani ba da sun sani da sun mara mata baya.
da wannan tunani bacci ya kwashe ta . Cikin ikon Allah suka isa
*ARLIT* ungumar Cité COMINAK
Horn yayi mai gadi ya bude masa tura hancin motar sa yayi ya shiga cikin hamshakin gida kallo ɗaya zakai mai kasan cewa gida ne masu hannu da shinu..
a parking space ya ajiye motar ya kashe tasowa yayi ya budewa mommy fito wa tayi tana cewa dan Allah juraij tasar min ita ka dauko mata kayan ta jikin ta ya saki yanzu ba zata iya daukan komai ba.
takaici ne ya tukare shi bazai iya yi mata musu ba dan haka yace '' mata to..,
zare kayan yayi ya buga mata ledar kayan ta akai da sauri ta zabura tare da danno wani uban ashar tace '' wane dan takazar uban ne ya dake ni akai.. Alkur'an ba zan yarda ba sai naci kaniyar mutum.
bata ƙarasa faɗa ba juraij ya buge mata baki kuka ta saka tana kallon sa cikin tsare gida yace '' zaki dena kallo na ko sai na fasa miki fuska da wani idon ki me kama dana mujiya..,
share hawaye tayi ta fito daga cikin motar tace '' ai a dangin ku ba maƙeri duk wanda ya raina tsayuwar wata ya nemo tsani ya hau ya gyara..,
da sauri ya zare Écouteur (earphone) da yake ƙoƙarin sakawa yace '' me kika ce..,
kai ta shiga girgizawa tana ja da baya jin tayi taci karo da mutum kafin ta gama tantance wa taci karo dashi taji an zabga mata mari da sauri ta dafe kuncinta ta kurawa wacce ta mare ta ido ko kifta wa ba tayi a cikin fusata ahlam tace '' chérie (honey) a ina ka samo wannan bagidajiyar wallahi ina upstairs na hango ku ban san ma na sauko ba , bana iya ganin gaba na.,
ahlam ta fadi haka cikin tsananin zafin kishi tare da tallafo habar juraij.
hannun ta ya sauke ƙasa ya riƙe be yi magana ba ya fara tafiya kin binsa tayi tace '' magana fa nake maka kayi shiru badai da kaje sabon gari ba suka aura maka ita..,
murmushi yayi yace '' aahhlam wallahi ina tsoran randa kishin ki zai illatar min dake, ko dan abin da ke tare da ke ya kamata ki rage damuwa zuwa tayi hutu..,
ajiyar zuciya ta sauke tace '' wallahi juraij zan iya kisa akan ka duk randa wata tayi gigin shigowa rayuwar mu to sunan ta gawa na yarda na ƙarshe rayuwata a prison da ka auri wata..,
bata ƙarasa ba taji saukar sanda a dokin huyan ta durkusa'wa tayi ta saki wani irin wahalallan ihu..
juraij da ya shiga wani hali a riki ce yace '' sweet me ya faru badai cikin bane na shiga uku ya Allah, duk tattalin da na ke yiwa wannan abu kar ace zu bewa zai yi..,
da hannu tayi mai nuni domin bata da bakin magana ɗagowa yayi ido hudu sukai da yumna tana murguda baki tare da cin ɗamara da mayafin'ta tace '' ce miki akai jaka ce tayi yaye ni da zaki dake ni ku da tattabaru sarkin aure ko to wallahi duk wanda yayi min ba zan raga mai ba ai ba jaka aka kawo miki ba , Allah ya saka mazalkwaila ce uwar alawa kuma idan baki sani ba ki sani yau aka ɗaura mana aure sai ki mutu dan kishi..,
sakar baki juraij yayi yarinyar ta soma ba shi tsoro yawa aljana kai anya kuwa kanta ɗaya dole ya koya mata hankali shu'umancin'ta yayi yawa dole ya tauna tsakuwa domin a'ya taji tsoro a fusa ce ya taso yayin da ahlam ta zun duba ihu ta danƙi huyan, yumna.
duk karfin yumna kasa kwace wa tayi da ga rikon da ahlam tayi wa wuyan ta zaro ido ta din ga yi
idon ahlam ya rufe babbar buƙatar taga ta kai yumna kasa , taga ko motsi ba tayi cikin ɗaga murya tace '' wallahi ina gamawa da ita kanka zan dawo daman ni naji a jiki na wannan yarinyar zaka auro ka kawo ta Cikin gida na to wallahi Allah ahlam daka kai har ita yau sai na koya muku *DARASI* wanda ko gaba aka ce ka ƙara gigin kawo min wata cikin gida na ba zaka ƙara ba...,
Mommy da yusra suka fito cikin tashin hankali saboda me bawa shukoki ruwa ya je ya faɗa musu ahlam zatai kisa dakyar mommy ta karbi yumna a hannun ahlam yumna kuwa zubewa tayi a ƙasa tana farfari da idanuwanta zata tada aljanun karya ganin hankalin kowa yayo kanta ta maƙe murya tace '' wallahi ba zamu yarda ba , ni turkwa dan gidan Sarkin aljanu zata shaƙewa wuya to yasin sai na kwashe mata hanjin cikin ta tas...,
ahlam tana jin wannan magana ta ɗora hannu akan ta , ta zunduma ihu gumi duk ya karyo mata ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba da jin wannan zance shikkenan unborn din su zai dena rayuwa itama tasan mutuwa za tayi ƙara shiga wani hali jin surutan da yumna ke yi.
Mommy kuwa rasa me yake mata dadi tayi ta kalli juraij tace '' juraij dan Allah temaka ka dauke ta ka kaita parlour muyi mata addu'a ko a samu ta dawo dai-dai...,
ƙara lankwasar da kai yumna tayi ta mai da hannayen ta baya tace '' yasin kana ɗaga kafar ka sai na cire maka jijiya ɗaya a wuyan ka ka dena motsi na tsawon shekaru goma sha biyar..,
cikin fusata juraij yace '' ke zanci ubanki idan baki dawo dai-dai ba mu za kiyi wa Prétendre (pretending ) zan babɓallaki idan baki tashi ba.,
sandarewa tayi ta mimmiƙe tare da miƙe hannayen ta tace '' yau zaka ga me zai faru dole su aljani tsifur su tafi dakai..,
mommy tace '' juraij bana son wauta karka sake ka ƙara cewa ƙala ka tafi gidan liman ka kirawo shi..,
bece komai ba ya juya yumna najin haka ta dinga sakin atishawa zunbur ta tashi tace '' mommy jikina ciwo yake min..,
mommy kamo yumna tayi ta rungume ta tace "sannu Allah ya baki lafiya.."
ɗagowa tayi ta kalli mommy tace ''me ya faru..?ni lafiya ta qalau...,
tausayin ta ne ya ƙara kama ta , mata tace '' bakomai tawo mu je ki ci abinci kiyi wanka...,
washe baki yumna tayi ta juya ta dauki kayan ta , tace muje mommy..
mommy tace '' yusra kuje parlour ke da ita ina zuwa juraij tsaya..,
to yusra tace ta riƙe hannun yumna suka shiga daga ciki kallon ahlam tayi da har yanzu ba ta dena kuka'ba tana shafa cikin'ta takaicin tane ya kama mommy tace '' ahlam sai kiyi shiru tunda komai ya lafa me ya faru..,
ba kunya ta rungume juraij tana kuka tace '' wancan sandar ta dauko ta buga min a kafaɗata haka kurum kuma ashe juraij cin amanata yake wallahi ba zan yarda ba sai ya sake ta ko kuma na cire mata wuya..,
cikin mamki mommy tace '' kanki ɗaya kuwa kinsan me kike fadi..? wa za ki cirewa kai ..?,
dukan kirjin juraij ta fara tana wani gunjin kuka riƙe mata hannu yayi yace '' ahlam kanki ɗaya kuwa..? karya take fadi..,
a fusace tace '' kai na dubu ba ɗaya ba daman kana da kunyar da zaka iya kallon idanuwana ka faɗa min haka...? to yasan ka jawa kowa na gidan nan sai na kona yarinyar nan..,
mommy danne zuciyar ta tayi domin a ƙaramin takaicin halin ahlam take ba , ta mai da kan'ta yawa ' wata naga akan kishi bata ji bata gani tace '' juraij wai me yake faruwa ne ka tsaya ka zama gunki..,
cikin takaici yace '' wannan yarinyar ce tace mata wai an daura mana aure Ita kuma batare da dogon bincike ba ta soma kuka shine fa ta shaƙe mata wuya..,
wacce yarinyar mommy ta tambaya cikin tsare gida ban da rashin kirkin juraij sunan yumna ne ba sani ba kome.
da sauri ahlam ta kalle ta tare da share hawayen ta tace '' mommy sannu da zuwa..,
kai mommy ta dauke tace '' yauwa..,.
tare da juyawa ta bar gurin.
ahlam kallon sa tayi tace '' baby bazan iya zama ni kaɗai ba dan Allah karka fita kana dai ji abin da aljanunun nan suka ce ko dan girman Allah karka fita.,
kai ya girgiza yace '' ahlam kardai ki ce min kin manta abin da kikai min yanzu..?,
turo baki tayi tace '' kai hakuri..,
kama hannunta yayi be ce mata komai ba suka soma tafiya kai tsaye shashin su , suka nufa,
zama juraij yayi yace '' ahlam yunwa nake ji me kika dafa..,
zama tayi tana kauda kai tace '' ni ba abin da na dafa bana son jin kamshin abincin dan Allah idan kaga yusra tayi abinci nima sai ka samamamin na dan samu naci yunwa nake ji tun safe da kai mana breakfast ban ƙara cin komai ba.,
bece komai ba ya tashi yace '' ki haɗa min ruwan wanka.,
turo baki tayi tace '' beb nagaji wallahi yarinyar nan duk ta wahalar da rayuwa ta Please kai hakuri karka ce kana ta saka ni aiki ban yi ba nasan ba zaka ji dadi ba...,
juyawa yayi ya shiga bedroom yana shiga ta kwanta ta ɗauki wayar ta , taci gaba da kallon ta a YouTube.
Wannan kenan
yumna tana shiga main parlour gidan ta nemi guri ta zauna tare da ɗora kafa ɗaya kan ɗaya a zuciyar ta cewa take ina ma wannan gidan nata ne , Allah dai ka kaita makkan nan ta kwashi arziki ta barshi a mazaunin sa.
ga abincin naki yusra ta fadi tana ajiye mata tray a kan center table.
da sauri ta sauko ta zauna tare da sauke tray din ƙasa tace '' Nagode..,
ya tsuna fuska yusrah tayi ta dauki remote ta zauna ta chanza channel.
taɓe baki yumna tayi tace '' halin ki ɗaya da wanki..,
da sauri yusrah ta juyo tace '' ke magan kike..,
shinkafa yumna ta watsa a bakin ta tace '' ah waka nake..,
ke dan ubanki ni kike faɗawa haka kaga shegiyar kauye..,
yusrah ta faɗa tana yowa kan yumna.
juya idanuwan'ta yumna tayi tace '' ina matsowa sai na hanaki kashi na tsawon kwana takwas tare da ciwon ciki me tsanani..,
Chak yusra ta , tsaya gaban ta ya fidi yace rass dafe kirji tayi ta bar gurin tane cewa juhud juhud juhud.
juhud fitowa tayi tace '' lafiya yusrah kike kirana yawa wacce na ci miki wani abin..?,
wallahi juhud mun shiga uku mommy ta kawo mana annoba cikin gidan nan.
cire glasses din'ta tayi tace '' annoba kuma a ina ..?,
zama tayi akan wasu kujeru da suke jere a gurin farare tas dasu gwanin sha'awa tace '' wallahi annoba yar gidan aunty halima..,.
tunani juhud ta shiga yi domin ta dade ba'a kasar ba sannan koda can bata shiga sabgar mutane balle yanzu da ta taka wani matsayi me girma aiki take yi a babban Company wutar lantarki tace '' wace aunty halima ke ba'a raba ki da kwashe kwashe ke da mommy halin ku ɗaya wallahi..,
sister din mommy fa
dafa goshin ta tayi tace '' wallahi na manta ikon Allah ita tazo ..? da kike cewa annoba aka kawo mana akan ki zata zauna ne yusra ki deba abin da kike yi wallahi haka kurum ki dinga damun kanki da damuwar mutane..,
Ya Allah ya juhud baki fa ki tsaya kin ji me zance ba kin hau faɗa.,
sarke hannuwanta tayi a kirji tayi '' oya faɗa min ina sauraren ki..,
bata labari ta soma yi tun daga farko har karshe.
dariya juhud tayi tace '' wallahi kun ban dariya da ilimin ku da komai ku tsaya ana raina muku hankali dama mom ta bar big bro yaci uban'ta gaba ko ce mata akai tayi wallahi ba za tai ba karya ne ba wani aljanu yanzu ke saboda ta faɗa miki haka shi ne kika tawo nan kafin ta hanaki kashi right..?,.
cikin matsanancin tsoro yusra ta gyaɗa mata kai
murmushi tayi tace '' jeki ki dauke shegiya da mari zata fahimci nan ba can bane..,
cikin kwarin gwiwa yusra ta tashi juhud tace '' yauwa ta gida na idan da hali ki dauki tray din da kika kai mata abinci ki kwaɗawa shegiya ni wallahi bana son irin wannan rainin hankalin.,
to kawai yusra tace mata ta sauka ƙasa samin yumna tayi ta zauna sai zuba uwar loma take yi damarar ma da taci da mayafin'ta ta kunce ta ɗan acewar ta wannan damarar da taci hanata sakewa za tayi gwara ta sakata ta wala ta fararraje gidan mommy ne taci duniyar ta da tsinke.
kaza ta dauka taci ta limshe idanuwan'ta wani dadi na ratsa mata jijiyoyin jikin ta ga sanyin AC kai jama'a dole ta nemo arziki dole ta tashi tayi faɗa da talauci miƙe ƙafafuwan ta tayi tare da harde su guri ɗaya tana sakin gyatsa
karasa gyatsannan ke da wuya ganinta ya dauke na wasu da kiƙa sakamakon marinta da yusra tayi tace '' dan ubanki wa za kiyiwa karyar aljanu Allah ya saka kukar bulukiya ce aka ce ki , ki bini a hankali kar kafin ki tafi ne sauya miki halitta..,
yumna ba tai wata wata ba ta sunkuya kamar be neman wani abu ta kama diga digin yusra ta gartsa mata cizo.
kasa koda motsi yusra tayi banda ihu ba abin da take mommy ce ta fito da sauri tana cewa me kuma ya ƙara faruwa...?
karaf a kunnen yumna sakin jikin'ta tayi tana mimmiƙe'wa kamar yadda tayi a dazun nan mommy tace '' yusra me kuma ya daki da ita yusra wallahi kike yaye ni be kamata ba ki kulata kome tayi miki tun da kunga ba hankalin ku ɗaya ba kin girmeta ga kuma wannan lalurar da take yi dan Allah yusrah ki dinga sara kina duban bakin gatari.,
dakyar ta iya zare kafar ta , ta zauna tana sakin ajiyar zuciya tace '' mommy rashin kunya tayi min fa...,
kwafa mommy tayi ta durkusa ƙasa ta ɗago yumna ta ɗora ta akan cinyar ta tana yi mata addu'a atishawa tayi ta dawo dai-dai da yake uwar hanjinta, ta dauka gyara kwanciyar ta tayi nan da nan bacci ya dauke ta..,
cikin tausayi mommy tace '' dan Allah yusra kome za ta faɗa miki kada ki kalle ta ni wallahi bansan tana da aljanu ba , Allah sarki malam shi kuma irin kaddarar sa kenan.,
turo baki yusrah ta yi tace '' yanzu mommy ko haka zan zuba ido tai ta gasa min magana son ranta..?,
a'a yusrah biye mata ku raba abib fade, shi dai aljani ba kamar mutum bane jeki,
ki kirawo juhud ta zo ta gyara gurin nan saboda idon ki ya rufe ga yadda kuka zubar da abincin nan .
mommy bazan iya tashi ba ina jin kashina ya karye wallahi kafata wani irin zugi take min.
08141785374
09061890481
Only charting

copy is not allowed
https://youtu.be/WoCX8WbJOuU
Episode 6
Yumna tace '' mommy ban koshi ba...,
tashi mommy tayi tace '' to bara na karo miki idan baki koshi ba sai kiyi min magana...,
washe baki yumna tayi zuciyar ta fari kal tace '' to nagode mommy..,
wata uwar harara yusra ta banga mata itama yumna ta mayar mata ita mommy kuwa girgiza kai tayi ta
End Ads