an daura auren ne naga take taken ta ɗan haka tun kafin dare yayi mata tabar min gida na.
Yumna ce ta fito jin abin da take faɗi ta yi murmushi iya labɓanta domin ta kara tun zura ahlam ai kuwa tayi faɗa ta shiga yi ta inda take shiga ba tanan take fita ba.
ɗurƙusawa tayi tace '' aunty ina kwana..,
tayi pretending bama ta gane me take nufi ba da faɗan da take yi.
haushin ta ne ya kama ahlam ganin ta mai da ita yar iska cikin zafin rai tace '' ke kwaso kayan ki , kibar gidan nan.,
da sauri yumna ta kalli juraij ganin ba abin da yace tashi tayi ta shiga daki daman itama ta gani haka kurum su dinga saka ta bauta sai kace wata jaka da sassafen nan shi gashi me mata yar gwal ta tashi ta yi musu breakfast itafa wannan abu gaba ya kai ta gobarar titi ajos.
kwaso kayan ta, tayi ta fito bata ko kalli inda suke ba ta fita taci sa'a gate din a buɗe yake fita tayi kai tsaye part din mommy ta nufa shima nan sun tashi suna breakfast ga mahaifin su juraij yana zaune shima sallama tayi ta sunkuyar da kai da sauri mommy ta ɗago tace '' yumna ya kika dawo na ganki kuma da kayan ki Allah i saka lafiya me ya faru...?,
Alhaji Mahmud ya goge bakin sa da tissue ya tashi yace '' yusrah idan kin gama ki zo sai salisu ya ajiye a makarantar taku ya wuce dani motar da ake kai ki ta lalace..,
tsugunawa tayi tace '' ina kwana..,
bata re da ya kalle ta ba yace lafiya qalau alhamdulilah kin zo lafiya ya su malam..
suna lafiya tace mai tare da tashi gaishe da mommy tayi batare da ta bata amsar tambayar da tayi mata ba Alhaji sallama yayi musu ya fita yusrah ta bi bayan sa zama tayi tace '' mommy ta koro ni wai karna aure mata miji..,
dariya mommy tayi juhud kuwa daman tasan za'a rina an saci zanin mahauciya ci gaba da cin chips din'ta mommy tace '' to shikkenan za mu haɗu dashi da yazama saunan namiji matar ka ta kori yar uwar ka kuma ka zauna kana yaƙe mata baki sosai mommy take faɗa juhud ko tari ba tai ba da ta gama sai ta rataya jakar ta tace '' mommy sai na dawo...,
harara ta zabga mata tace '' Allah ya tsare hanya..,
murmushi tayi tace '' amin ya Allah ta fita.
gyara zama tayi tace '' mommy ni bazan ƙara zuwa gidan sa ba tun da korata suke yi..,
bata dai ce mata komai ba sai daukar wayar ta da tayi ta lalubo number juraij bugu ɗaya ya dauka cikin bada umrani tace '' kazo ina son ganin ka..,
bata tsaya amsa gaisuwar sa ba ta kashe wayar ta.
ɗaukan plate tayi tace '' yumna kin ci abinci..?,
girgiza kai tayi tace '' a'a banci ba.
zuba mata tayi ta tura mata gaban ta farfesun kaji ne ga buredi ci ta fara yi tana ci da biredi sosai duniyar yumna tai mata dad'i.
tashi mommy tayi ta hau sama
juraij ne yayi sallama yumna da take tsaka da cin kazar ta , bata amsa ba tsawa ya daka mata yace '' ke bakya amsa sallama ne..?,
lashe hannun ta tayi ta saki wata uwar gyatsa ta kora da kunun tsamiya takaici ne ya ture zuciyar juraij ransa a matukar ɓace yace '' ba magana nake miki ba ..,
da sauri ta juyo tace '' uhmm ban jika ba ..,
kwafa yayi yace '' ina mommy take ..,
nima ban san inda take ba da zata tashi bata sanar min ba.
da sauri ya ɗago jin amsar da ta bashi lallai yau idan be karya yarinyar nan ba to be ciki jinin Mahmud ba.
fisgota yayi ta faɗi ƙasa tare da sakin razananniyar ƙara saboda ball da yayi da ita ya mare ta sai da taga wasu taurari sun gilma mata a idanuwanta.
ba shiru mommy ta dinga hada matattakala biyu uku tana saukowa tace '' juraij lafiyar ka kuwa me tayi maka banda ci mata mutunci da kuka yi kai da yar gwal shi ne yanzu ka biyota zaka karya ta ko to wallahi idan ka jamata wata nakasar wanda zai aure ta yace ya fasa kai zaka aure ta ko kana so ko baka so..,
da sauri ya ɗago jin furucinta na ƙarshe me zai yi da yarinyar nan , to ma ya sakata a wanne gurbin cikin kwantar da murya yace '' mommy yarinyar nan bata da kunya wallahi dan baki ga maganar da ta faɗan ba tambayar ta nayi kina ina tace bata san inda kike ba lokacin da zaki tashi baki sanar da ita ba , ke sa'ar ki ce ko kuma ni sa'an tane take faɗan wannan maganar wallahi taci sa'a da banyi rugurugu da ƙashin ta ba dalilin kenan da ya saka ahlam tace baza ta iya zama da ita ba jiya cikin girma da arziki ta dauke ta , takai ta daki tace ga dakin ta to wallahi yarinyar nan ta daddaƙara mata bakar magana ahlam ta faɗa min ban goyi bayan ta ba ,
to nayi abokai sun zo suma tace ta zo ta dauko musu abinci ta kai musu nan ma sai da ta faɗa mata magana yau ma da safe sai da su kayi..,
jikin mommy yayi sanyi ta ɗaga yumna tace '' kiyi hakuri jeki daki...,
tashi tayi tana ɗin gisa kafar'ta ,ta shiga dakin mommy zama mommy tayi tace '' wallahi abin da ahlam tayi raina ya ɓaci wanne irin shashanci ne wannan yarinyar da an ma kusan bakinta kaima bita zai zai har ka bari yumna ta , tawo yawa wani shanyayye..,
shiru yayi ya zauna a ƙasa yace '' kiyi hakuri mommy insha'Allah zan gyara kuskurena Alhaji ya fita ne..,
Eh wallahi be jima da fita ba tun da kuka dawo daga masallaci sai aka kira shi a waya bayan fitar ka za ayi meeting gaggawa shine fa ya fita da wuri shi zai sauke yusrah ma saboda motar da za'a kai ta , ta lalace...
Juraij yace '' to Allah ya kiyaye hanya nima yanzu zan fita office..,
yauwa kama tuna min maganar auren yarinyar nan biki sai matsowa yake ya kamata kai a matsayin ka na babban wanta kuma ga ba ran mahaifiyar ta mu za mu zama komai nata mahaifinta ba karfi ne da shi ba bikin ya'ya har biyu kuma mata ba wasa ba ni ba zan iya tambayar mahaifinku ba idan ya ga dama yayi to falillahil hamdu amma dai kai , ka kawo abin da zaka kawo ai mata siyayyar kayan daki nima daga gurina zan mata na daki dana kitchen da kuma sutura...
Mommy ta fadi haka tana kallon juraij domin jin me zai ce .
Shiru yayi yana nazari Sannan yace '' to zan turo miki kudin abinda ya dace sai kiyi mata Allah ya bada zaman lafiya bama lallai ayi bikin da mu ba zan tafi Ingila wannan project ɗin tare da ahlam...,
To Allah ya temaka amma da son samu ne ka zauna a yi komai da kai.
tashi yayi yana cewa ni zan tafi Allah ya tsaɓa mana abin da yafi zama alkairi.
Mommy tace '' Allah ya kiyaye hanya.
to haka ranaku sukai ta zuwa suna wucewa kullum da abin da yumna za tai wa ahlam duk da bata barin ta shigar mata guri amma sai ta san yadda akai ta takaleta sukai faɗa tun mommy bata lura har ta gane yumna matsokaniya ce hatta juhud da bata fiye zama a cikin gidan ba bata kyale ta ba mommy ta dage sai gyara mata jiki take yi tayi kyau gwanin sha'awa ga hutu da jin dad'i da take ciki.
Yau tun da safe take buga number na'ima amma shiru ba'a dauka karshe ma dai a ka kashe layin babban tashin hankalinta gobe zata tafi gashi batai abin da ta dace ba idan ta bar arlit bata san yaushe za ta dawo ba , bata kuma da kuɗin dawowa tun da suna komawa jarabawa za su zane ta gama secondary sai kuma auren su.
zaman dirshen tayi a ƙasa ta rasa me yake damun ta ko wayo za tai wa mommy ta , tafita ta nemo inda ake daukan mutane zuwa Saudiyya tana cikin wannan zance a zuciyar'ta taji sallamar juraij da abokinsa ahlam na take musu baya wannan abu na bawa yumna haushi dul inda juraij ya taka sai ta taka tamkar bata yadda dashi ba ta dinga leƙe mai dogon tsaki taja ta mai da hankalin'ta kan wayar ta tana amsa sallamar'su.
zama Muhsin yayi yace '' my friend...,
da sauri ta juyo gashe dashi tayi ta matsa daga gurin tayi nesa da su juraij yace '' ina mommy take..?,
tun safe ta fita unguwa ta bashi amsa still hankalinta na kan wayar ta.
ji yayi tamkar yayi ball da ita Muhsin yace '' yumna ba magana daga gaisuwa shikkenan nifa zuwa nayi muyu hira..,
ɗago da idanuwanta tayi ta kalli juraij da yayi kicin kicin da haɗe rai banda iskancin muhsin ya da faɗa mai an kusa bikin ta amma shine be jiba da yake kan albasa gare shi.
tashi tayi ta shiga kitchen tray ta dauki ta zuba mai snack da lemo ta kawo mai ta ajiye a kan center table.
godiya yayi mata ta mai da kan'ta ƙasa tace bakomai.
ahlam kuwa ji tayi tamkar ta har bata juhud ce ta sako farim ciki ne ya cika ta , ganin muhsin gaishe dashi tayi tana zama amsawa yayi cikin kulawa yace '' ya aiki..?,
Alhamdulilah wallahi sai godiyar Ubangiji.
ta fada na kallon sa
Muhsin yace '' ashe jamcy tayi aure..,
eh wallahi tayi aure ina ga wata biyu kenan da yin auren ta.
Kai ya gyaɗa yace '' ta zubar da makaman boko kenan hakan na da kyau aure sittira ce ga diya mace ..,
dauke kai juhud tayi a zuciyar'ta tace kaga shege ko ina ruwan sa owo.
a fili kuma sai tace '' haka ne wallahi shawarar da ya kamata ni da kai mu bawa kan mu kenan..,
dariya yayi yace '' aini na samu juraij yana neman hana ni..
da sauri ta kalle sa cikin rashin fahimta tace '' ya juraij ne ya hanaka yin auren..,
Muhsin yace '' kusan haka ne wacce nake so yace an riga da an bada ita..,
kallon juraij tayi tace '' yaya wace ita ...?,
juraij yace '' shi da yake baki labarin ba sai ki bari ya karasa miki ba..,
kallon ahlam tayi da tai kicin kicin ta ɓata fuska tamkar ambata bishira da cewa ita yar wuta ce.
mai da kallon ta tayi gare sa tace '' ya Muhsin fahimtar dani me yake faruwa..? wace ita yar gidan wace haka..?,
yumna da take zaune tana jin su sai tai kamar bata wajen juhud ƙara mai maita maganar tayi Muhsin yace '' yumna..,
Da sauri juhud tace '' Qu'est-ce que tu dis...?,
Murmushi Muhsin yayi yace '' juhud laifi na aikata ne..?,
kai ta girgiza juhud tayi tace '' a'a amma ka kusan aikatawa saboda ba kyau nema cikin nema..,
Yumna tashi tayi daga gurin ta shiga daki da harara ahlam ta raka ta da ita.
Muhsin shiru yayi juraij yace '' Muhsin yanzu mene amfanin abin da ka aikata...,
Muhsin yace '' idan rabona ce Allah zai bani ita wallahi ina son yarinyar nutsuwar ta , ita ta ƙara jan hankalina gurin ta...,
da sauri juhud ta zaro ido sai kuma ta sheƙe da dariya har da riƙe ciki lallai ya Muhsin be san wace yumna ba wata ran sai ta saka shi hawan jini juhud tace '' aunty ahlam bakya jin abin da yaya Muhsin yake faɗi.. ,
https://youtu.be/_IOc2pOwgKk
Copy is not allowed
Episode 10
Juhud naji mana bani da amsar bayar wa amma lokaci shi zai bashi amsa da kan'sa zai bambance tsakanin aya da tsakuwa.
kallon ahlam juraij yayi da sauri ta dauke kan'ta ganin irin kallon da ya jefe ta dashi Muhsin kallon juraij yayi yace '' tun da ban same ta ba zan tafi idan ta dawo kuce ina gaishe ta.
tashi juraij yayi ya saka hannuwansa a aljihunsa yace '' okay insha'Allah zata ji muje na raka ka ko..,
dafa kafadar sa yayi yace '' no basai ka raka ni ba Nagode sosai...,
kai kurum juraij ya ɗaga ba tare da yace komai ba ,godiya su ahlam sukai mai ya tafi.tashi ahlam tayi tace '' juhud sai da safe..,
ɗagowa judud tayi ta kalle ta tace '' oh Allah ya tashe mu lafiya..,
a takaice tace amin ta fita a hanya suka ci karo da mommy suka gaisa mommy ta shigo zama tayi direba ya shigi da kayayyaki yusrah da ta sauko daga sama tace '' mommy wanna siyayyar batai yawa ba ..? ke ba ganin inda za a kai ta kikai ba kike lodar wannan kayan..?,
judud tace '' yauwa yusrah faɗa mata gaskiya mutumin da yake almajiri ina yaga inda zai zuba wannan kayan nan ni dan dai kar na fadi ne ace ni ban yi ba na hana ayi..,
murmushi mommy tayi tace '' juhud kenan amma dai ko ba mu ga wajen ba hakkin mu ne mu siya mata ko..?,
hakane tace ta tashi tare da , daukan wayar ta , tabar gurin mommy kallon yusrah tayi tace '' gobe fa dake zamu tafi...,
gyara zama mommy tayi ta miƙe kafar ta , tace '' zama tayi akan kujera tace '' dani kuma gaskiya ina da zuwa makaranta ki tafi da ya juraij..,
yana da uzuri nasan da zai kai ni, bana son tafiya ni kaɗai ne wallahi.,,
Ni da ace bani da zuwa makaranta dana raka ki wallahi amma gobe ina da test har biyu
Tashi mommy tayi tace '' Allah ya temaka..,
Amin ya Allah tace da sauri yumna ta fito tace '' mommy sannu da dawowa..?,
cikin sakin fuska mommy tace '' yauwa ya kaɗaici..?,
murmushi tayi tace '' alhamdulilah an daman mommy ina so naje gidan su kawata da suna Agadez suka dawo nan yanzu mukai waya da ita tai min kwatance wallahi tun da nazu nake neman number sai yau na samu ita ce wacce nake baki labari ban san ko ba zan ƙara dawowa ba nan kusa gwara naje mu gaisa..,
dan jim mommy tayi sannan tace '' to ba damuwa bara na saka akai ki amma karki dade kinga dare na kawo kai abin da ya saka ma zan barki gobe zaki tafi..,
ran yumna be so ba da mommy tace kai ta za ayi to ta tafi ta zaga gari ko Allah zai saka ta ga masu daukan mutane tafiya makka amma bakomai za ta san yadda za tayi tace '' to mommy ba damuwa bara na shirya..,
okay kiyi maza ki shirya bara na kirawo Salisu ya kai ki.
da gudu ta fita tana murna zama tayi a bakin gado rasa ina za tayi addu'a ta shiga yi a ranta tare da kiran layin na'ima cikin ikon Allah ta shiga ta ɗauka cikin zumuɗi tace '' na'ima wannan wanne irin hulakanci ne ina ta kiran ki karshe ma sai kika kashe wayar wato wasa tare ci banban ko abin da kika samu shine bakya so na samu ko to wallahi bakomai kinyi da yar halak..,
hmmm wallahi aikine ya sha kai na amma ba damuwa bara na turo miki yanzu dan Allah idan na turo miki karki ƙara damuna da kira wallahi kina katsai min aiki na ..
saboda bakin ciki yumna kasa Magana tayi ta saki baki ta ma rasa abin da za tace .
jin alamar kudinta yana dab da ƙarewa sai ta kashe wayar ta ɗan jima a zaune sanan ra ji shiguwar messages da sauri ta dubu wani tsallam murna tayi kamar gurin ba nesa da inda suke da sauri ta fito tace '' mommy ta turo min address din gidan ba nisa da nan gurin ashe ni kwatance da tai min ban gane ba Allah ya saka na kara kiranta na tabbatar basai ma ya kai ni ba dan gaba da kune kaɗan..,
Oh to Allah ya temake sai kin dawo komawa daki tayi cikin sauri take shiryawa har ta gama ta saka hijabinta sallama tayiwa mommy ta fito gate me gadi ya buɗe mata ta fita kallon ko ina take tun da ta zo yau ne ta fita unguwar shiru baka jin motsin komai sai na tsuntsaye da yake kusan rabin su ma'aikata ne a zaune a unguwar kuma manyan ma'aikatan gwamnati da na Company tafiya ta dinga yi tana dubu sakon da yake cikin wayar ta da yake har da sunan Company da yake daukar Mutane aikatau ta saka mata cikin sa'ta ta gano gurin anyi rubutu da manyan baki cikin harshen French an saka Fais semblant d'être humble (do garo da kai) da sauri ta tsaya tana tunanin to ta ina ce kofar shiga tana wannan tunani wani ya zo wucewa da sauri tace '' bawan Allah ina wuni..?,
Tsayawa dattijon yayi yace'' barka dai ya'ta..,
am Dan Allah tambaya nake..
dattijon nan yace '' Allah ya saka na sani..,
yumna kallon gurin tayi ta nuna mai yace '' dan Allah ta ina ake shiga gurin nan naga kamar katanga ce sai karamar kofa itama a kulle..?,
dan jim yayi yana karantar yanayin ta Sannan yace '' eh ba nan ce kofar da ake shiga ba kofar tana can baya ina ɗaya daga cikin ma'aikatan gurin office wa kike nema...?,
ajiyar zuciya ta sauke ganin kayan ta ya tsinke a gindin kaba tace '' daman ina so na tafi makka aikatau ne to ban san yadda ake abin ba wata kawata ce ta kwatanta min nan gurin...,
Oh masha Allahu ki godewa Allah ni ke da alhakin daukan duk wasu ma'aikata na turasu ƙasashe akwai agent din da zai raba su inda za su yi aiki acan amma muna da sharadi zaki saka hannu muje nayi miki bayani..
to ba damuwa muje zagayawa baya su kayi ta wata kofa suka shiga sai kalle kalle take ganin ma'aikata suna ta sabgar gaban su wani office suka shiga ya zauna ya fito da wasu takardu yace '' kin shirya nayi miki bayani..?,
yumna tace '' eh na shirya..,
yauwa a ka idar tafiya aikin nan bana ɗaukan ƙasa da shekara Shata kwas sannan mun fi son bazzawara wacce tai aure tana da yara biyu haka amma yan matan ma muna ɗauka amma da saka hannu iyayen su sannan za mu kai ki muyi